← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 176

Sashe 30

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalil na yin parking Hajiya Madina ta fito daga cikin motar, ƙafarta ma ko takalman babu ta barsu a mota, a guje ta tsallaka side ɗin da motar Turaki take har tana bigewa da dutse, ko gabanta bata gani da kyau, burinta ɗaya ne a lokacin taga lafiyarsa, hawayen nata ma nema suke su tsaya da zuba saboda kamar sun ƙare.
tunda ta fito daga motar ƙwayar idon Turaki ta tsaya cak akanta, kamar wanda aka sassaƙa haka ya kasa ko da motsawa, kallonta kawai yake, kallonta yake tana tahowa gare shi da irin tashin hankalin da bai taɓa ganinta aciki ba, da wannan tausayin na uwa shimfiɗe a fuskarta, da wannan tsoron na mahaifiyar da bata son rasa ɗanta acikin ƙwayar idonta, yana gani tayi tuntuɓen amma ya kasa motsin da zai fita ya tareta daga faɗuwar, alhalin kuma so yake ya fita ya rungumeta, amma ya kasa, ƙafafunsa sunyi nauyin da ba zai iya ɗagasu ba, sai kawai ya rufe ido wani hoto na can lokacin baya yana haska masa.

Hajiya Madina na ƙarasowa ta buɗe motar hannunta sai karkarwa yake. "me babban suna". sunan da ta kirasa kenan a sanda ta buɗe motar ta gansa kamar gunki. kuma ganinsa a hakan sai idanuwanta suka haska mata hoton wani abu da ba zata iya jurar gani ba, haka ma zuciyarta ta ɗarsa mata faruwar wani lamari da ba zata iya ɗaukarsa ba. a hankali ta shiga sauke ƙafafuwanta har gwiwarta ta kai ƙasa, sai kawai ta kifa kanta akan ƙafafunsa ta fashe da wani gunjin kuka me taɓa zuciyar duk wani me sauraro, irin kukan da duk wani me rauni yaji shima sai yayi.

sai a wannan lokacin ne Turaki ya iya motsa hannunsa ya kamata ya É—agata, sannan ya fito daga cikin motar, ya kasa magana haka itama ta kasa, kuka takeyi shima hawayen yake, ya jata zuwa jikinsa yayi mata wata runguma, itama wata runguma tayi masa wadda take daban da tasa, har tsakiyar babban yatsansa yaji rungumartata, irin rungumar da rabon da tai masa ita tun yana yaro.

likitocin dake cikin ambulance É—in suka fito cikin hanzari, da gadonsu suka iso wajen motar Turaki, Khalil ne ya buÉ—e bayan motar, yayin da nurses suka janyo yarinyar suka É—orata akan gadon suka yi ambulance da ita.
cikin sanin makamar aikinsu wasu nurses ɗin suka shiga goge jinin da yake kan fuskarta, yayinda wasu daga cikinsu kuma suka shiga ƙoƙarin ganin sun saita numfashinta ganin cewar da ranta.

duk aikin da suke gudanarwa akan idon Khalil dake tsaye hannayensa acikin aljihunsa, kuma tsananin mamaki ya wanzu a fuskarsa lokacin da suka gama goge fuskarta tayi tas, wa zai gani?, yana gani dai-dai kuwa?, ba yarinyar daya kai asibiti bace ɗazu, Fillo ce fa me aikinsu. sai kawai ya fuskanci wurin da Hajiya Madina da Turaki ke tsaye har yanzu, tana ta aikin tattaɓa shi da kallon ko'ina a jikinsa kamar wadda ta ɗauki tsawon lokaci bata gansa ba.

Turaki yake kallo ba Maama ba, kallonsa yake yana recalling back wani moment da Fillo tace masa,"tsoronsa nake ji". haka ta faɗa masa jikinta na kyarma, sanda ya shigo kitchen zai ɗauki abu. tambayarta yayi kawai menene ya faru yaga kamar a tsorace ta ke, shine ta faɗa masa hakan, kuma ko da ya tambayeta me ta ke tsoro sai ta kalli ƙofar kitchen ɗin sannan tasa hannu ta goge hawayenta tukunna tace masa,"Hammah".

"me yasa to?, yayi miki wani abunne?". tambayar da yayi mata kenan. amma amsar da ta ba shi ita ta ɗaure masa kai,"babu abinda yayi min amma yace zan cutu idan har ban bar inda yake da rayuwa ba, wai haka yaji zuciyarsa tana faɗa masa...kuma ni bana so mu daina wannan aikin saboda da kuɗin muke rufawa kanmu asiri, kuma ni wallahi Hammah Khalil banda mugun nufi, bana cutar da kowa sai ƙoƙarin ganin na kare wanda za'a cutar".

abunda ta faÉ—a masa kenan tana hawaye, bai ce mata komai ba a lokacin, kawai ya É—auki abinda zai É—auka ya fice daga kitchen É—in.

kuma yana zuwa É—akin Turaki ya maimaita masa abunda ta faÉ—a, Turaki bai mu sa masa ba, hasalima ce yayi masa. "Khalil haka jikina yake bani, haka zuciyata take faÉ—a min...kamar yanda nake jin Granny zata iya cutuwa idan muna rayuwa a wuri É—aya, haka nake ji akan wannan yarinyar itama".

Khalil ya sauke ajiyar zuciya sanda tunanin nasa ya katse, sukai magana da wani police sannan yayi tattaki ya ƙarasa wurin su Hajiya Madina. yana zuwa ya sanar mata cewar,"Maama DPO yace zamu wuce".

ta haÉ—iye wani yawu sannan tace,"pack anything that is very important daga cikin motar nan ka kaisu cikin taka...sai a bar wannan anan, ko ta zama rabon wani ko kuma in Allah yayi azo a É—auketa daga baya, tunda babu me drving É—inta yanzu".

Khalil na kallonta da tsananin tausayi yace,"wani police ɗin yay driving ɗinta, ko kuma ni na tuƙa, ku sai ku tafi tare da wani acikinsu".

tana kama hannun Turaki ta riƙe tace,"a'a mu tafi dai taren, wani cikin nasu yaja wannan ɗin, sai ka faɗa musu key ɗin na jiki". da faɗin hakan taja hannun Turaki suka yi gaba, shi kuma Khalil ya shiga motar ya ɗauko wayarsa sannan yabi bayansu.
hakan akayi, cikin police mutum É—aya yay driving motar Turaki.

sai da suka yi nisa a tafiya sannan Khalil yace,"Hammah kasan wa ka kaɗe?". Turaki bai ce komai ba, kuma sai a wannan furucin nasa Hajiya Madina tama tuna da wata halitta da aka buge, ta manta da wannan batun ta ɗanta kawai take, kuma tana ganinsa lafiya shikenan ta ƙara mancewa da batun gaya mata da yayi ya buge wani.

tace da Khalil,"koma wacece fatanmu ta rayu, idan ta dawo hayyacinta sai ta faÉ—i inda take ko kuma akai sanarwa gidan radio".

Khalil yace,"Maama ai wadda muke tare ce, Fillo ce". da maÉ—aukakin al'ajabi Turaki da Hajiya Madina suka waro ido a tare. tace,"wace kuma Fillo?". Khalil yace,"me aikinmu dai". Turaki dai bai ce komai ba, bai san ya zai kimanta yanda yaji maganar acikin kansa ba.

Hajiya Madina tace,"me yasa kace itace Khalil?". ya sauke numfashi yace,"idan munje asibiti za ki gani Maama".

*Taraba.*
ɗan ƙaramin tsakar gidan share yake tass, sai simintin yay haske kamar sabo. daga ɓangaren yamma wata ƙaramar ƙofa ce ta langa-langa, inda yake nan ne kitchen.
wata dattijuwar mata ta fito daga ɗaki wanda yake daga ɓarin yamma ta buɗe ƙofar kitchen ɗin ta shiga.

ta sunkuya ta sauke tunkuyar daga kan gawayin da take girki da shi. tana saukewa sai ga ƙaramin yaro da bai wuce shekara bakwai ba yazo wajenta yana faɗin,"Yaya ki zuba min abincin kar mu makara". sunan da suke kiran mahaifiyar tasu da shi kenan Yaya.

ta kalli yaron sannan tace,"to Yasir yanzu zan zuba maka, ai kaga sai yanzu na sauke". ta faɗa a sanda ta ke ƙoƙarin ciro farantan roba daga cikin kwandon wanke-wanke.
ta shiga zuba farar shinkafa da mai da yajin a faranti daban-daban, tana ta jin labarin da Yasir ke bata na yacca ake duka a islamiyar tasu.

bayan ta gama rabon abincin tace da shi,"kira su Maimuna su zo su ɗauka, wannan kuma riƙe namu ne ni da kai, ka riƙe da kyau".

ya karɓi filas ɗin abincin ya wuce yana ƙwala kiran Maimuna da Hindu kuzo ku ɗau abinci inji Yaya. yana shiga ɗaki Yaran suma suka fito suka ɗauki nasu, anan tsakargidan suka shimfiɗa tabarma suka zauna suna ci, Yaya na faɗa musu idan suka ɓata wurin sai sun share. hakan yasa Hindu tace da Yayarta Maimuna,"ni dai kinga ban ɓata wurina ba ko".

wani saurayi da bai fi 26 years ba yayi sallama gidan, dogo ne sosai kuma É—an siriri kamar sandar kara, fuskarsa kewaye da saje wanda ya haÉ—e da gemunsa, ga kuma gashin bakinsa shima da yaywa fuskarsa kyau.
yaran suka amsa sallamar tasa suna yi masa sunnu da zuwa, ya amsa musu sannan ya shiga É—akin kishiyar mahaifiyarsa da sallama a bakinsa.

ta gama cin abinci tana siÉ—e yatsu lokacin, ya zauna kan kujerar parlon da duk taji jiki. ta kalle shi da tausayi tace,"an dawo?".

sai dai ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ehh Yaya sannu da gida". tace,"yauwa, ya wurin É—inkin naku?".

yace,"É—inki babu daÉ—i Yaya, yanzu ma gudowa nayi saboda kaina da nake jin kamar zai fashe, jiya kwana nayi ban runtsa ba ina kan É—inkin Æ´an bikin nan".

tayi murmushi tace,"to ya za'ai, neman halal da wuya, wataran kuma za'aji daÉ—i da izinin Allah...amma dai ka kammala musu É—inkin nasu ko?".

Hamid yayi gajeriyar dariya yace,"yanzu ma da su muka gama rigima ai, Suhaila na cewa ba zata ƙara kawo min ɗinki ba balle ranta ya ɓaci, kuma dan nace idan tayi haka ta burgeni shine tayi fushi ta tafi, inaga da kuka ma ta wuce".

Yaya ta miƙe tana cewa,"an dai ji kunya wallahi, budurwar taka ma sai kayi mata halinku na teloli".
gajeriyar dariya kawai yayi baice komai ba, Yaya ta miƙe tace da shi,"ka ɗauko abincinka kaci ka koma ka ƙarasa aikin mutane, bana son saɓa alƙawari Abdulhamid".

ta shiga ɗaki don shirya Yasir, shi kuma ya wuce kitchen ya ɗauko abincinsa. yana cin abincin ne ƙannensa da suka shirya zasu wuce makaranta suka zo suka ce da shi kuɗin makaranta.

yana kallon Maimuna yace,"har lokacin biya ya yi?". ta É—aga kai alamar eh tare da cewar,"shekaranjiya da jiya ma duk sai da aka fito da mu, bamu shiga aji ba".

yace,"kuma dan shirme shine baku faÉ—a ba".
tace,"Kawu ai ban sani ba ko baka da kuÉ—i".
yayi mata wani kallo yace,"ina ruwanki da rashin kuɗina, karki ƙara yin irin haka".
tace,"to Kawu".

Yaya ta fito daga É—aki tana cewa,"ba laifinta ba ne ni nace su bari ba yanzu ba".
yasa hannu a aljihunsa yace,"a'a Yaya to ai zuwan nasu baida amfani kenan tunda ko sunje ba barinsu ake suyi karatun ba, kuma ni ai na sami kuÉ—i kwana biyun nan".

tace,"to Allah ya ƙara horewa dai". ya ɗauki dubu uku ya bawa Maimuna ƴar shekara goma yace,"ungo ki bawa Malam Ado, kice na Yasir da Hindu ne, dan Allah suyi haƙuri su ɗaga ƙafa jibi insha'Allahu za'a bayar da naki".
Chapter 30 · 0% Book details