Sashe 49
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma cikin nuna ɓacin ran tace,"baka taso a stubborn ba, kuma duk cikin ku shida kai nafi karewa daga duk abinda zai sa ka zama stubborn, amma me yasa sai daka girma?, kana so ka zama Stubborn kamar Khalil ko?. saboda nace duk sanda ka fita ya zama kuna tare da shi ko ina zaka je, ba wai ina nufin ka zama mara ji ba kamarsa, na sani da takurawa ace lallai duk inda zaka je sai da ƙaninka alhalin ka mallaki hankalin kanka, amma ka sani ni uwa ce da ba zan so wani abu ya cutar da ɗana ba, ya kamata ka tuna da akwai masu faraurar rayuwarka a kullum, dalilin da yasa nace duk sanda ka fita ya zam kana tare da Khalil ko Bello duk da nasan dabarata bata isa ta hana faruwar abunda Allah ya shirya ba. amma dai atleast kasancewarka tare da wani zai sa suke tsoron tunkararka. kuma sai da kayi min alƙawarin ba zaka saɓa umarnina ba akan hakan ba, Me Babban suna me yasa yau rana ta farko ka saɓa umarnina?, Khalil yace ko minti 2 baka yi a office ba ka fita, Bello yace kana ɗaukosa a airport kuka rabu. ina ka tafi tun bayan rabuwarku?, me yasa baka dawo gida kaci abincin rana ba?, me yasa kaƙi ɗaga wayata?, me yasa kake son haddasa ciwona ya tashi?, me yasa tun ɗazu ina maka magana kayi min shiru?, rashin maganar na menene?, lafiya?".
tunani da lissafi dake a cikin kan Fillo ya tarwatse, gabanta yay dukan tara-tara, kallon Turaki take yi tana tuna irin tarin tasa soyayyar wa mahaifiyarsa, zuciyarta na faÉ—a mata taje ta same shi ta faÉ—a masa Maama ce, Maama na son yin magana da shi, zai farka idan yaji hakan, tabbas zai farka. ta isa gabansa tana jijjigasa a hankali daidai kunnensa tana faÉ—in,"ka tashi ga Maama". a zatonta ko jin hakan zai sa ya farka daga dogon suman da yayi, amma inaa kamar ma da gawa take magana.
sai kawai wani kuka ya kubce mata. cikin kiɗima Hajiya Madina tace,"innalillaihi wa'inna ilaihi raji'un...". ko salatin bata ƙarasa ba Fillo tace,"Maama ki zo". ta faɗa tana kuka sosai. daga ɓangaren Hajiya Madina ta zabura ta miƙe daga kan kujera, cikin gigita da tsananin tashin hankali na farat ɗaya, me kunnenta yake ji ne?, kamar kukan wani take ji kuma kamar ana so ace mata tazo ga Turaki babu lafiya.
"waye ke magana?, ina Muhammad É—in?, ke wacece?".
kukan Fillo ya ƙaru tace,"Maama ni ce, Hammah ɗin ya faɗi ya suma Maama kizo da sauri". wayar dake hannun Hajiya Madina ta nemi ta faɗi a ƙasa, Samha da idonta ya kai wurin tai saurin taro wayar sanda ta sauka daga saman gadon. ta taro wayar a lokacin da itama Hajiya Madina ke neman faɗuwa, Nihal tai saurin riƙota.
Samha tace,"Lafiya Maama, menene?". Hajiya Madina ta kalleta ido a waje, a hankali ta kalli Nihal, sannan ta kai idonta ga Zaytuna wacce tayi tsaye ƙeƙam. sai kuma ta dawo da idonta ta sauke akan wayar tana kallon call ɗin dake tafiya, Hammah aka ce mata alhalin ga ƙannensa anan tare da ita.
cikin neman fitar hayyaci tace,"to wace me magana a wayar?, wai Hammanku ya suma, to aina?, garin ya?". ta wurga tambayoyin ga Samha.
duk su ukun suka maimaita,"Hammah ya suma?". Hajiya Madina ta É—aga musu kai kawai hawaye na sintiri a saman fuskarta.
"hello, dan Allah wake magana, ina me wayar yake dan Allah?". Nihal ta faɗa acikin wayar bayan ta amshi wayar daga hannun Samha. babu amsa sai kuka dake tashi kawai, Zaytuna ta silale a wajen, Nihal tayi kanta da sauri. Samha ta ɗau wayar ta kai kunne, dan tuni Hajiya Madina tayi mutuwar zaune, ta koma kamar me paralize idonta a wuri ɗaya kawai yake, jinta take kamar rayuwarta ta ƙare, kamar shikenan ta gama aiki.
daga ɓangaren Fillo tace,"Hammah ne ya suma". Samha ta waiga taga sauran sisters ɗinta suna nan, ɗaya ta suma ɗaya na ƙoƙarin ganin ta sumen ta farfaɗo. to wace ke faɗin Hammah ya suma?. sai ta dakewa faɗuwar gaban da take ji tace,"to waye yake magana, kuma wanne Hammah ɗin?".
Fillo na ƙara jijjiga Turaki tace,"ni ce Fillo, Hammah Turaki ne ya suma Maama, tun ɗazu yaƙi yay motsi kamar ya mutu".
a matuƙar razane Samha ta miƙe tsaye tana faɗin,"what! mutuwa?, dan uwarki ke kina ina?, ta ya kika san abinda ya faru da Hamman'mu?".
jin furucin Samha yasa jikin Fillo yin rawa a lokacin zuciyarta na faɗa mata shikenan tata kuma ta ƙare, ita dama ta sani ita za'a ɗorawa alhakin faruwar komai. "Fillo aina?, aina ya suma?".
Hajiya Madina da ta amsa wayar take tambaya kuka na ƙwace mata. "Maama ɓangaren su Adda Zay...". bata ƙarasa ba taji alamun faɗuwar waya a ƙasa. kuma zata iya cewa rabin second ne ya kawosu, dan ganin su kawai tayi tsaye akanta.
Hajiya Madina ta fizgo Fillo ta miƙe tsaye, ta zabga mata mari a fuska, marin da yasa jinta da ganinta suka ɗauke na wucin gadi. kamin ta dawo dai-dai ta ƙara ɗauketa da wasu marikan har uku. "uban wa ya buɗe room ɗin nan?". babu abinda Fillo ke ji a lokacin balle ta iya bada amsa.
"ba magana nake miki ba, ban yi muku iyaka da wannan room ɗin ba?, bance duk sanda zaku yi aiki babu ruwanku da taɓa wannan ɗakin ba?, wa ya baki key ɗinsa?, me yasa baki hanasa shigowa ba?, kin buɗe baki kin yi min magana ko sai nasa ƴan sanda sun kamaki kin ƙare rayuwarki a bayan kanta?".
Fillo na kuka tace,"wallahi Maama bani na buɗe ba, nazo wucewa ne...". bata barta ta ƙarasa maganar ba tasa bayan hannunta ta kifar da ita a ƙasa, Fillo ta zube a ƙasan tiles kanta na dukan bango, lokaci ɗaya taga giftawar wasu taurari acikin idanuwanta.
abunda kawai zata ce ta ƙara ji shine Hajiya Madina ta mata gargaɗin cewa,"duk abunda ya sami ɗana, duk abunda ya sami lafiyar ɗana sai naga bayanki Fillo, tabbas sai kin ƙwammace ina ma baki zo duniyar nan ba".
daga nan bata ƙara jin komai ba kamar yanda bata ƙara ganin komai ba na tsawon wucewar minti goma sha biyar.
kuma sanda ta dawo hayyacinta daga buguwar kan da tayi, sai taga babu kowa a É—akin sai ita É—aya.
tsawon minti biyar tana kuka, a hankali ta dinƙa kewaye ɗakin da kallo, babu komai acikinsa face shirgin takardu dake cikin locker, sai kuma gadon jarirai irin wanda ta taɓa gani a ɗakin Fulani, sanda Kaka ta zauna yiwa Gimbiya Zahra wankan jego.
wanne abu ne acikin É—akin da ya haddasa shigar Turaki situation É—in da ta zo ta same shi aciki?, ina abunda yasa ba'a so a buÉ—e É—akin?. ta kalli komai kuma bata ga komai É—in da zai zama dalili ba.
taimakonsa tayi, kuma taimakon take da niyyar yi masa, amma ga da abinda aka saka mata da shi, ya za'ai ta manta?, waye zai taushi zuciyarta akan abinda ta ƙudurce na ramuwa?, Amir ne kawai, kuma yanzu babu Amir a cikin rayuwarta, tsawon watanni huɗu sai taji tana kewar Amir a yau.
sai ta runtse ido tana jin zafi a zuciyarta, ta miƙe tsaye da ƙyar tana dafa bango saboda hajijiyar da take ji, ko'ina na ɗakin take bi da kallo, so take taga illarsa, ba zata taɓa barin ɗakin nan ba sai taga illarsa da kuma dalili, wannan dalilin da ya haifar da komai.
ta miƙe da ƙyar ta tafi tana jan ƙafarta dake yi mata zugi har ta ƙarasa gaban enlargement. kallon matar take yi da kyau cike da nazari da son gano wani abu amma ta kasa, abu ɗaya ta fahimta matar nan na da alaƙa me ƙarfi da Turaki, saboda tsananin kama, kamannin da suka zama kamar an tsaga kara, sai dai irin alaƙar da take tunani zuciyarta na faɗa mata cewa ba ita bace, wannan matar bata yi kama da wacce ta ajiye ɗa kamar Turaki ba, shekarunta kaɗanne, kuma ko da auren ƙauye aka mata baici ace ta haifi ɗa kamarsa ba balle har ta haife shi, ta haifi Zaytuna. ba ma wannan ba, idan ma tayi tunanin ita mahaifiyarsu ce to Hajiya Madina fa?.
ta dafe kanta da take jin kamar zai fashe tana saurin dafa gadon jariran, bata buÉ—e idonta ba har sai da ta daina jin juwar, idonta ya sauka acikin gadon jariran, kan award frame dake kan bargon jariri, tasa hannu ta É—auko tana kallon award frame É—in, tayi concentrating akan hoton jiki da sunan jiki. *her Excellency RAMLA MUHAMMAD TURAKI*, sunan da yake rubuce a jiki kenan.
wai wace wannan matar?, mene alaƙarta kuma da sunan Turaki?, *MATARSA!*, haka zuciyarta ta faɗa mata, kuma tabbas hakan yake, amma ina take?, mutuwa tayi?, rabuwa suka yi?, take anan zuciyarta ta warware mata dalilin da yasa ba'a son buɗe ɗakin, da kuma dalilin da yasa Turaki shiga critical condition. saboda wannan ɗakin na da alaƙa da ita shiyasa ba'a so a buɗesa, sannan ganin hotonta na fama ciwon da ta jiwa Turaki a zuciyarsa, wannan ciwon da tabonsa ya kasa goguwa daga garesa. wanne irin ciwo ne?, me tayi masa wanda ya kasa mantawa?.
ta ƙara ƙulle idonta for 1minutes sannan ta buɗe tana ƙarewa gadon jariran kallon, ta tabbata wannan room ɗin shine silar komai, kamar yanda gadon jariran nan ke da alaƙar komai, kenan idan tunaninta ya bata dai-dai *ƊA* ne silar komai, jaririnsu!, to ina jaririn?, kuma itama uwar tana ina?, ta mutu ne?, ita ɗan da suka mutu?, kenan wannan shine ciwon dake manne a zuciyar Turaki?.
sai kawai Fillo ta sauke numfashi tana hurar da iska a bakinta, ta koma ta isa gaban englargement din ta cirosa, sannan ta dawo ta É—auko award frame É—in ta fice da su daga É—akin.
*6hours pass, Miyyetti Hospital, Room 05.*
cikin vip room É—in, Turaki ne jingine a jikin pillow É—in da aka saka masa a bayansa, goshinsa É—aure da bandage, an naÉ—e wurin da ya ji ciwo da shi sanda yake dukan kansa ajikin glass.