Sashe 110
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai a yanzu da tasa tazo ƙarshe yaji sonsu da ƙaunarsu matuƙa na bin jinin jikinsa, sai yanzu yake jin ina ma ace ba ya zata dawo da ya kyautatawa iyalinsa, babu abinda yake buƙata a yanzu irin ubangiji ya basa aron lokaci, sannan ya ara masa lafiya ko ta ɗan kaɗan ɗin lokaci ne dan ya faranta ran iyalinsa, ya gyara halinsa, ya gyara lahirarsa, to amma ya san ƙarshensa yazo, ba zai ƙara samun wata dama ba a wannan duniyar balle kuma lokaci.
yana ta kallon Fillo yana kuka sosai yace,"na karɓi sadakin aurenki tuntuni, na san da cewa hakkinki ne, dole na baki hakkinki, amma saboda son zuciya nawa ban nemeki ba balle na baki, sai na gina kaina da kuɗin motar da na siyar, ban ko fara morarsu ba Allah ya jarabceni da shiga wannan mawuyacin halin, dan Allah ki yafe min kar in mutu da hakkinki akaina".
ya faɗa yana kuka sosai. "na san ƙwarai na zalunceku, ba'a taɓa mugun mutum irina ba da ya ƙuntata rayuwar iyalinsa, ban baku ilimi ba balle na baku tarbiya, hasalima duk naƙi karɓarku a matsayin ƴaƴan da na haifa, alhakinku kaɗai ba zai barni in ƙare da duniya lafiya ba, dan Allah ku yafe min ko na sami sassuaci a ƙabarina, kuce kun yafe min ko naga da kyau a ranar gobe".
ya kamo hannun Hamid yace,"haƙiƙa banda tamkarka ɗana, Allah ubangiji yay maka albarka, Allah ya saka maka da mafificin alkhairin, ya baka masu kayatata maka fiye da yanda ka kyatata min, fiye da yanda ka dinga kare martabata da mutuncina, na san ba zan ƙara wani lokaci me tsayi ba, idan na mutu ka ɗauk Atm ɗin da na baka ajiya kaje ka ciro miliyan hamsin ka bawa ƴata, hakkinta ne".
ya faɗa yana shafa fuskar Fillo, sannan yace,"ka nemi adalin alƙalin da zai raba maku gadonku babu zalunci, duk wata kadara da na mallaka taka ce Hamid na bar maka, na rubuta hakan a takarda ta nan cikin kayana, abinda kayi min ba zan taɓa iya biyanka ba Hamid, na gode, na gode, na gode Hamid, baka taɓa fushi da ni ba, baka taɓa guduna ba saboda mugun halina, matana da ƴaƴana sun guje ni amma kai ɗaya namiji da Allah ya bani kana liƙe da ni, kana faɗa min gaskiya a lokacin da nake da dama amma naƙi saurarenka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya, dan Allah yayin da babu ni ka zama uba a wurin ƴan'uwanka, kar ka bari zumuncinku ya yanke, kayi musu gatan da ni banyi musu ba, ka zama na gari Hamid, ka zama na gari, mutum ba ya danasanin zama mutumin ƙwarai har mutuwarsa, amma idan ka zama mutumin da wasu suke kuka da shi zaka yi danasani a sanda kazo mutuwa har bayan mutuwarka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya".
Hamid ya kasa cewa komai yana dai riƙe da hannunsa yana hawaye, Hayyo na shaƙuwa ya kalla Fillo yace,"zan ƙara ruwan me sunan Umminta".
Fullo ta ɗago kansa ta kuma basa ruwan yasha, a lokacin sai da ya shanye jarkan guda, yana kallon Fillo yana murmushin ƙarfin hali yace,"ki tayani roƙon yafiyar mahaifiyarki, ki faɗa mata ina sonta, ina sonta fiye da yadda baki zai furta, dan Allah ta yafe min ko na na samu naga haske a ƙabarina".
yana faɗar hakan kansa ya langwaɓne gefe yana shaƙuwa sosai, ya dafe ƙirjinsa yana jin tsananin azaba na ratsa shi, magana yake so yayi amma shaƙuwa sam ta hana shi, can kuma sai ga jini yana fita daga bakinsa kamar zubar yawu, ya damƙo hannun Fullo da Hamid yace,"tawa tazo ƙarshe, ba zan ƙara ko da minti uku ba, mutuwa zanyi ƴaƴana, bana so na tafi na barku amma ban isa na hana mutuwa ta ɗaukeni ba, ba'a son raina zan rabu da ku ba sai don mutuwa ta zama dole a gareni ko ba yanzu ba, idan na mutu ku nema min gafarar Allah, karku gushe face kuna me nemar min gafararsa a ko da yaushe, haƙiƙa ni ɗin me laifi ne a gare shi, mutuwa zanyi babu makawa, iyayena sun rasu tun ina saurayi, baƙin cikina ya zama ajalinsu, ku nemi dangina a ƙauyen Ngurore-Jabu under local government ɗin Karim-Lamiɗo, Wurkum district gidan Hakimin Wurkum, nanne gidanmu, anan ahlina suke, Allah yayi muku albarka, dan Allah kuce da mahaifiyarku ta yafe min, la'ila ha'illahu muhammadurrasulillahi sallahu alaihi wassalam".
ɗif kamar ɗaukewar wuta haka numfashin Hayyo ya ɗauke, hannunsa ya saki ya faɗi daga riƙon da yaywa yaransa, Kaka ta fashe da kuka tace,"shikenan, Hayyo Allah ya jiƙanka yay maka rahama yasa can tafi nan".
Fullo ta ƙwala wata ƙara tana jijjiga shi,"Abba nah, Abba don Allah ka tashi, Abba kar ka mutu, Abba kar ka tafi ka barmu muna buƙatarka, wallahi mun yafe maka duk abinda kayi mana, dan Allah ka tashi Abba nah, muna sonka a yanda kake Abba ka tashi please".
Hamid dai kukansa a hankali yake yi, shi ɗaya yasan me yake ji a zuciyarsa, Kaka ta tashi ta fita dan kiran Ummi idan bata yi nisa ba, tana fitowa ƙofar parlo ta tarar da ita a tsaye tana goge hawaye da mayafinta, ta kalleta tace,"ya mutu ai".
wasu sabbin hawaye suka ƙara zubowa a fuskar Ummi, Kaka ma ta goge nata tace,"ki shigo ciki asan abin yi kafin dare yayi, anan za'ai jana'izarsa ko sai mun koma can?, in sai mun koma can dole sai gobe za'a kai shi tunda kinga daren yayi, in kuma nan ɗin ne to na shiga masallacin can na faɗa in yaso ko bayan magriba sai a kaishi".
kukan da Ummi ke ta riƙewa ya kubce mata, ta fashe da kuka sosai ta shiga parlon da gudu ta tafi kan gawar Hayyo, wanda take kallonsa kamar zata yi masa magana ya amsa mata, ta kifa kanta a ƙirjinsa tana riƙe hannunsa, kukan da bata taɓa yi ba a duniyarta yazo mata, da ƙyar muryarta ta samu ta fito acikin kukan tana cewa,"na yafe maka, Allah ya yafe maka, Allah yasa ka huta, ubangiji ya lulluɓeka da rahamarsa".
lokaci ɗaya parlo ya karaɗe da kukan uwa da ƴaƴanta, zuciyoyin da su kaɗai suka san me suke ji, duk rashin kyan halin mutum yayin da akace babu shi mutuwa ta ɗauke shi sai mutuwarsa ta taɓa zuciya musamman makusantansa, ji suke yi inama zasu iya dawo da shi suci gaba da rayuwa tare da shi a yanda yake.
kukan da Fullo da Hamid ke yi ya ƙara tsinkar da zuciyar Ummi, kuka sosai babu me iya lallashin wani, lokacin kuma Dr Yusuf ya shigo parlon, da Yami ya fara cin karo, yana kallonta jiki a sanyaye yace,"lafiya Yami?, waye babu lafiya?, ba dai jikin Ummi bane ya tashi?".
tana goge hawaye tace da shi,"a'a ba ita bace, wanda ma aka kira ɗin kazo ka duba shi Allah ya karɓi abinsa".
ya kalla wurin da su Ummi suka kewaye gawar sannan ya kalla Yami yace,"ban gane ba Yami?, waye mutu?".
tace,"Baban Fullo ne yazo, kuma ashe ajali ne ya kawo shi".
Yusuf ya isa wajen da sauri, sai dai yana zuwa fuskar da ya gani ita ta matuƙar basa mamaki har ya razana yaja da baya, ya kalla Ummi ya kalla su Hamid yace,"waye wannan ɗin?".
babu wanda ya iya basa amsa acikinsu, ya dinƙa kallon Fullo dake aikin girgiza Hayyo tana faɗin dan Allah Abba ka tashi, ka tashi mun yafe maka kar ka mutu yanzu.
Yusuf ya zube a wajen hoton gawar Hayyo da hoton Kawunsa Muhammad da ya sani na haska masa a ido. a fili ya furta,"Kawu Muhammad".
sai kuma yasa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Ammi, har ta ƙare ringing bata ɗaga ba sai da ya kira lambar Aliyu yace ya kai mata.
murya a daƙile tace da shi,"ya akai?".
yace,"Ammi Kawu Muhammad".
tace,"me ya sami Kawu Muhammad É—in?, ganinsa kayi?".
kamar yana gabanta yace,"Ammi ya mutu".
a matuƙar razane ta miƙe jiki na kyarma tace,"ya mutu?, aina ka gansa da zaka ce ya mutu?, yaushe rabonka da shi ma har da zaka ce ya mutu?, wa ma ya san inda yake?".
yace,"to ban sani ba Ammi ko idona ne yake gane min ba dai-dai ba, amma tabbas gani ga gawar Kawu Muhammad, zan tura address kizo yanzu ki gani ko shi É—inne, amma na tabbata gawar Kawu Muhammad ne a gabana".
Ammi ta jefar da wayar Aliyu tayi cikin É—aki da sauri ta É—auko mayafi tace da shi,"muje muje Aliyu, duba wayarka Yusuf zai turo da address".
cikin mintunan da basu haura ashirin ba sai ga su Ammi sun ƙaraso gidan, ta shigo parlon duk a rikice tayi kan gawar da aka lulluɓeta a yanzu, ta kalla Ummi da su Fullo da babu abin da ke tashi a parlon sai gunjin kukansu, ta kai hannunta na kyarma ta ɗaga zanin da aka rufe shi da shi, tana kallon fuskarsa ta saki zanin ta zabura taja da baya tana ambaton ƙalu innalillahi...
sai kuma ta fashe da kuka sosai tana faɗin,"ashe rabon ba zamu ƙara ganawa ba sai bayan ka mutu zanga gawarka Yaya".
ta kalli Ummi tace,"mijinki ne da gaske?".
Ummi da mamaki take kallonta ta ɗaga mata kai kawai, Ammi tace,"Yayana ne uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya, tunda ya zama ajalin iyayenmu shikenan kuma ya kama gabansa bai ƙara waiwayon kowa ba, rabona da shi tun Yusuf bai fi shekara goma sha ɗaya ba, yazo gidana sau ɗaya lokacin ko sauraronsa banyi ba".
tayi shiru tana bin gawar da kallo tana kuka sosai, "Allah ya jiƙanka Yaya yasa ka huta, Allah ya yafe maka zunubanka, ya haskakaka ƙabarinka, Allah ya sadaka da manzon Allah SAW".
nan da nan kuma sai ta É—auki waya ta shiga kiran Æ´an'uwanta waÉ—anda suke uba É—aya, dama su biyu ne a wurin mahaifiyarsu daga shi sai ita, duk da irin fushin da aka É—auka da Hayyo hasalima wasu sun manta da shi, amma kan kace mene wannan waÉ—anda ke zaune anan Gombe har sun zazzo.