Sashe 133
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta wuce tana ƙunƙuni ta ɗauke table ɗin ta mayar da shi ainihin in da yake, sai maganganunta take yi ita ɗaya har Bello ya shiga ma bata sa ni ba, sai da ta baro wajen zata koma kitchen sannan ta lura da shi. tai murmushi tana gaida shi, ya amsa ma ta yana tambayarta ya lafiyarta, ta ce,"Alhamdulillah".
yana kallon bandage na hannunta ya ce,"subhanallah ciwo kika ji haka?".
ta ce,"ehh jiya ne na yanke, amma da sauƙi".
ya ce,"ya salam to Allah ya sauƙe".
"amin na gode". sai kuma ta ce,"ka zauna mana".
ya ce,"nop ina sauri ne, MT fa yana nan ko yana É—aya part É—in?".
ta ce,"na ga ya hau sama".
Bello ya fito da flash da ga aljihunsa ya ce,"please ki ba shi wannan".
tana tsaye da ga in da take tace,"ka hau ka same shi mana".
ya ce,"no anata min waya daga office ne, ki ba shi yanzu please kice masa yay calling É—i na".
ta wuce taje ta amsa, shi kuma yay ma ta sallama ya tafi.
kamar ta hau saman taje ta kai masa sai ta fasa tai wucewarta kitchen suka ci gaba da aikinsu, haka kawai yau ta tashi da kwaɗayin dambun gero, sanda ta shiga kitchen taga hannu ɗaya gareta har ƙwalla sai da tayi, kuma sai Allah ya taimaketa yaran suka zo a lokacin, nan da nan kuwa suka shiga kitchen ɗin tare.
kuma sai da suka kamma dambun kawai taji gaba ɗaya bata son cinsa, tun safe da ta tashi take jin mararta na murɗa mata kaɗan kaɗan, yanzu kuma ciwon ya ƙaru sosai, ta san ba komai ba ne illa period ɗinta, haka yake yi mata da ma, da zarar yazo kuma duk sai ya cika mata ciki taji bata son cin komai, fatanta ɗaya ne kar tayi wahalallan ciwon da ta saba.
ta kalli É—aya cikin yara me suna Sakina ta ce ma ta,"kinga É—auko wancan flask É—in ki cika shi sai ki kaiwa Baba me gadi, idan kuma ba zaku iya cinyewa ba ki bawa Baban kice dan Allah ko da wanda zai bawa".
É—ayar me suna Hannatu ta ce,"Anty ke ba za ki ci ba?".
Fillo tai mata wani kallo ta ce,"na ce miki sunana Halima, bana son wani Anty. na ƙoshi naji ya fita a raina".
ta juya ta fita, Sakina da Hannatu suka shiga gulman wai ciki ne da ita, su na cikin ƙusƙus ɗin su sai gata ta dawo, ta ce da su,"yauwa yanda ma za'ayi, dan Allah ku kaiwa Kakata, ai kun san ɓangaren masu aiki ko?".
Hannatu ta ce,"anan gidan?".
ta ce,"no can gidan su me gidan nan".
Sakina tace,"ehh mun sani, kwananmu biyu ma a can".
haka kawai taji wani daÉ—i tace,"kun san Yami?".
suka haÉ—a baki wajen cewa,"ai a wajenta ma muka kwana".
"yauwa to ita zaku kaiwa, kuce ina gaisheta kuma don Allah ta sa Maijidda ta zo".
ta faÉ—i hakan ta fita a gaggauce saboda ciwon marar da ya fara tsananta ma ta.
tana hawa upstairs taji karatun qur'ani na tashi a room É—in da ke kusa da nata, ta yi wucewarta É—akinta sai faman yamutsa fuska take tana danne mararta.
har ta kwanta akan gado sai ta tuna da saƙon Bello, hakan yasa ta miƙe ta fito cikin ƙarfin hali ta wuce ɗakinsa, ta tura ƙofar tana sallama aciki-ciki, shi kuwa kamar bai ji sallamar ba dan bata ji ya amsa ba.
ganinsa babu riga yasa tai saurin rufe idonta, ta shiga ciki tana lalube kamar makauniya har ta isa inda taji kamar mudubi ta taɓa, ta ɗora flash ɗin da Bello ya bata akai sannan tai saurin ficewa ta bar ɗakin.
around 5 kiran wayar Maama ya shigo wayar Turaki, lokacin ya rufe laptop kenan, ya ɗaga da ga can ɓangaren Maaman ta ce masa,"ka na office ko gida?".
"ina gida Maama".
ta ce,"jiya Daughter ta manta magungunanta sai yanzu nake ganinsu, ka zo yanzun nan ka amsar ma ta dont waste time, ya hannun na ta?".
ya ce,"da sauƙi".
ba tare da tace masa komai ba ta kashe wayar, ba'a son ransa ba haka ya shirya, ba ya son wani faɗan dan haka bai tsaya ɓata lokaci ba, kuma ko da ya karɓo direct gidan su Bello ya wuce, Umma ya gani zaune a falo tana yiwa ƴan jikokinta karatun ƙur'ani, ya durƙusa ya gaishe da ita, tayi ta saka masa albarka kuwa tana jadadda masa akan ya gaida iyali.
ya ce,"Umma Bello ya dawo ne?, na kira wayarsa ban samu ba".
ta ce masa,"yana ciki bai jima da shigowa ba ma".
ya wuce É—akin Bello, kuma yana zuwa ya tarar da shi kwance rungume da pillow yana waya, Turaki yaja dogon tsaki na takaici, ya jefa masa flash ya juya ya fice ba tare da yace masa komai ba.
bai koma gida ba sai bayan sallar magrib, yana shigowa parlo Sakina da Hannatu suka yi saurin durƙusawa su ka gaida shi, bai amsa musu ba illa bin parlon da yayi da kallo, ganin babu Fillo sai ya haye upstairs ɗin, yana buɗe ɗakinta ya ganta shame-shame a ƙasa sai murƙususu take yi, ya wuce ya dire ledar drugs ɗin akan stool, har ya juya zai fita sai kuma shashsheƙar kukan da ke fita a hankali ya dakatar da shi.
dawowa yayi ya durƙusa a gabanta, ya tsayar da ƙwayar idonsa akan fuskarta da hawaye ke ta zuba, ga uban gumi ta haɗa kamar an watsa ma ta ruwa, ga wani irin nishi kamar me naƙuda, sai ka kasa kunnenka sosai tukunna zaka ji kiran sunan Kaka da Ummi da take yi a wahalce.
ya ɗan taɓa hannunta yana cewa,"ke".
ta damƙo hannunsa ba tare da ta sani ba ta murgina tare fashewa da kuka sosai.
"wayyo Allah nah, wayyo Ummi nah, wayyo zan mutu".
yasa hannu ya taɓa jikinta yaji zafi rau, sai kawai yaji ta ɗan ba shi tausayi, ya kamota zai ɗagota daga kannanaɗewar da takeyi kamar miciji tace,"a'a".
muryarsa a hankali ya ce,"me yake damunki?".
sai a sannan ta iya buÉ—e idonta a wahale tana kallonsa a disashe saboda ruwan hawayen da ya cika ma ta ido.
shi kuma ganin tana kallonsa ya tamke fuska yana haɗe gira sama da ƙasa ya ce,"me?".
ta mayar da idon ta rufe tare da kamo hannunsa ta ɗora akan cikinta, ya kalli cikin ya ƙara cewa,"me ya sami cikin?".
cikin kuka ta ce,"don Allah ka kira min Kaka mutuwa zanyi, ko kuma ka kaini asibiti su cire min cikina don Allah".
yay shiru for some minutes sannan ya ce,"me kika ci?".
tai shiru ta kasa ce masa komai sai burgima take yi tana kuka sosai.
ya miƙa yaje ya ɗauko ledar drugs ɗin da ya shigo da su, ya fita ya ɗauko ruwa a ɗakinsa ya dawo, ya durƙusa yana ce ma ta,"tashi ki sha magani".
ta girgiza ma sa kai, ya É—aga murya sosai,"na ce ki tashi ko".
ta ce,"Kaka ta hanani shan magani".
haushi ya kama shi ya miƙe zai fita karaf idonsa ya sauka akan tiles inda take kwance, wajen duk ya ɓaci da jini, yay saurin rufe ido yana girgiza kansa, lokaci ɗaya amai ya taso masa babu shiri yay hanzarin ficewa, amai sosai ya yi da ya shiga toilet, bayan ya fito ya tsaya yana tunani, yana jin zuciyarsa duk babu daɗi.
Yay ta so ya tuna sunan abin da ya gani a ƙasa, ya dai san Nihal ma na irin haka wanda har suma take yi ita, sai kawai ya ɗauki wayarsa yay dialling lambar Zaytuna, tana ɗagawa ko sallamar bai amsa ba ya ce,"mene ma sunan wannan abun da kuke yi every month?".
taji yay tambayar kamar a rikice, ba ta fuskance shi ba sai daga ba ya sannan tace,"oh menstruation". yay É—an jim sannan ya ce,"wanne irin magani ake sha?".
ta ce,"zan maka text É—in su yanzu".
yay É—an guntun tsaki ya ce,"babu a gida?".
ta ce,"akwai".
ya ce,"to ki kawo yanzu, idan ana allura ma ki taho da ita".
ya koma bakin gado ya zauna ya kulle idonsa yanata girgiza kansa, yana da ƙyanƙyami sosai fiye da tunani, ko Zaytuna da yake cin abincinta idan tana period ko ruwan hannunta ba ya sha, har yanzu zuciyarsa ba ta bar tashi ba, so kawai yake ya ƙara yin wani aman ko zai ji daɗi, kansa har wani ciwo yake yi.
yana nan zaune yana ta aikin jera tsaki kamar aikin farilla, wayarsa ta yi ringing, yana É—agawa bai ko jira abin da Zaytuna zata ce masa ba ya ce,"ki sameta a É—akinta".
"Hammah ai ban san ɗakin nata ba, ban taɓa shigowa ba".
a daƙile ya ce,"zan kashe fitilar ɗakina".
ta ce,"tom".
Sanda Zaytuna ta shiga É—akin, samu tayi ta kyala amai yafi guda huÉ—u duk wuri daban daban, sai dukan tiles take yi tana ambaton innalillahi, tana faÉ—in azo a taimaka ma ta, ta kira sunan Kaka ta kira na Yami.
Zaytuna ta ƙarasa da sauri, ta ɗauki jarkar ruwan da ke wajen ta buɗe ta tuttula a cup ta bata magani ta sha, sannan tayi ma ta allura, tsabar wahala ma bata san wa ke kanta ba, a hankali a hankali kuma taji ciwon yana ɗan sauƙi.
sai lokacin da iya buÉ—e ido ta kalli Zaytuna ta ce,"Adda".
ta amsa mata tana cewa,"sannu".
Zaytuna ta riƙeta ta kaita toilet ta ce ta daure ko ba tayi wanka ba ta ɗauraye jikinta, haka tayi wanka a daddafe ta fito, zata kuma kwanciya a ƙasan tiles ɗin Zaytuna ta hanata, ta buɗe wadrobe ta ɗauko ma ta riga ne ɗan kauri iyaka gwiwa ta bata, sannan ta kwanta akan gado, tana kwanciya baccin wahala ya ɗauketa.
Zaytuna da kanta ta gyara wajen tas, har kayan da ta cire ta wanke su a machine, ta kunna turaren wuta sannan ta kira Turaki a waya tace masa zata tafi, toh kawai yace ma ta, before ya kashe wayar tayi saurin ce masa,"kar ta sha ruwan sanyi, da abu me zaƙi, da cocumber".