← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 176

Sashe 58

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bata san ta yanda bakinta ya buɗe ba ma har take iya magana haka duk da uban tsoronsa dake tare da ita, dan wani irin faɗuwan gaba da take ji. ta ɗan kallesa kaɗan ganin yana kallonta tayi saurin ɗauke idonta, taja yatsanta ɗaya tace,"ba zaka iya kula da kanka ba ai, amma shi naga yana sonka, kuma yana da mutunci, Maama zata basa amanarka...Allah ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya, Allah yayi maka katanga kan katanga daga dukkan sharrin me sharri, Allah ya ɗoraka akan maƙiyanka, Allah ya tsareka da tsarewarsa ya kiyayeka da kiyayewarsa, ka kula sosai da kanka Maama zata ji daɗin hakan, kar ka yi wasa da shan magani".

tunda ta fara maganar yake kallonta babu ko ƙifce, da wani kalar tunani da yake akanta. kamar ya buɗe komai a yanzu, but zuciyarsa na faɗa masa not now, this is not the right time da ya kamata ya buɗe komai.
yana ji ta zame jikinta a hankali tana miƙewa tsaye, so take yi ta bar ɗakin amma kamar an riƙe mata ƙafa, kuma kamar tana jiran umarninsa ne. tayi dai tsaye ta kasa motsawa balle ta tafi.
tsaye shima ya miƙe yana kulle idanuwansa, jikinsa duk babu ƙwari haka yake jinsa, bai taɓa jin zai yi tafiya yana fargabar tafiyar ba ko kuma yana tsoro, amma this time around da zai tafi yayi just 4days ji yake kamar wani mugun abu zai faru kafin dawowarsa, ko kuma wani mugun abu zai faru da shi.

bayan ya zuba hannayensa cikin aljihu taji yace,"bana son yawan kuka. when am back you will help me find Mum".

kallon da take yi masa bana mamaki bane tunda a yanzu ta riga tasan komai, kallo kawai take yi masa me cike da tausayawa, bata ankara ba sai ganinsa tayi tsaye a gabanta dab da ita, tayi wani ƴar guntuwa a gabansa dan da kaɗan ta wuce cikinsa, magana take so tayi masa amma bata san ta ina zata fara ba, hannunta nata karkarwa taji ya sunkuyo da kansa ya ɗora goshinsa akanta yana kama hannayen nata ya riƙe.
muryarsa can ƙasa taji yace,"yauahe hannayenn zasu daina kakkarwa?".

sai taji kamar numfashinta zai yi seezing, jin an turo ƙofar ɗakin ta firgita taja da baya, ganin Zaytuna duk sai ta rikice, so take ta fice daga ɗakin da gudu before Zaytuna ta ɗago daga sunkuyawar da tayi tana ajiye abu, amma ya riƙe hannunta ta yanda duk abinta ba zata iya ƙwacewa ba, Zaytuna ta ajiye aiken Boɗejo da ta shigo da shi ta fita. tana fita Fillo ta fashe da kuka tana ture hannunsa daga riƙon da yay mata.
ƙarar shigowar text a wayarsa yasa ya saketa ya nufi wayar, ita kuma ta buɗe ƙofan ta falle da gudu. Turaki ya buɗe messge ɗin Zaytuna da ya shigo yana karantawa. _Boɗejo and Maama are coming._ yana gama karantawa ya juyo da kallonsa inda ya bar Fillo, sai gani yay babu ko ɓurɓushinta, yasa hannu ya shafo wuyansa yana smiling.

*please vote, share and comment.*
[8/27, 20:40] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

_not edited._

*26*
Ilham ta shigo parlon Yarima Abbas bakinta ɗauke da sallama da wani irin emotions a tare da ita. tun shigowarta kanta ke sunkuye a ƙasa kamar ta shiga fadar Me Martaba.
ta ƙarasa gaban table ɗin dake tsakiyar su Yarima Abbas ta ajiye ƙaramin tray dake hannunta, bayan ta ajiye ta ɗago ido ta kalli ɓangaren da tasan anan ne zata yi tozali da Turaki, tunda from there hancinta ke jiyo mata ƙamshinsa, wannan ƙamshin turaren da ita ta basa kyautarsa har ya zama choice ɗinsa.

idonsa da nata suka haɗu wuri ɗaya, kuma ba tare da ƙwayar idonsu ta fita ata junansu ba suka saki wani sanyayyan murmushi wa juna. wanda hakan ya wanzar da jin kunya a tare da ita, Turaki kuma da har sannan murmushin bai ɗauke masa ba yace,"zo nan".

Yarima Abbas dake cike da jin girma na izza yace,"kafi kowa sanin bana son yara suke zuwar min sashina ko, amma duk sanda kazo sai ka dinƙa wani kiransu suna shigo min da dattin ƙafafu".

ba tare da Turaki ya dube shi ba yace,"da wa kake?". rai ɓace Yarima Abbas yace,"yaushe wannan rainin hankalin zai bar jininka Turaki?".
Turaki ya É—auke idonsa akansa yay masa banza bai tanka masa ba.

Ilham ta zauna akan hannun kujerar da Turaki yake, ya kamo hannunta ya riƙe yana cewa,"wai ni wannan Kunyar tawa da kike yi tun sanda kika dawo ta mene?". kanta na ƙasa tace,"kunya kuma Hammah?". yace,"ehh mana, kuma ni ban haihu ba, balle nace ɗana kike kamu".
ta ke fuskanta yay turning zuwa na shagwaɓaɓɓu tana ɗan dukan ƙafa a ƙasa tace,"yanzu Hammah ka rasa da wa zaka haɗani sai ɗanka".

murmushi kawai yayi yana shafa beard ɗinsa. idonsa akan tray ɗin da ta aje yace,"mene wannan?". tace,"your favorite, since morning na dafa idan zan tafi na kai maka...". sai ya katseta da cewan,"have you forgotten?". sai ta ɗan ɓata fuska tace,"ban manta ba, but ai naga ada ne". ya gyara zamansa yana faɗin,"ba da bane har yanzu Ilham. girkin Maama da Zaytun kawai".

wani irin rashin jin daɗin ya ziyarci Ilham, fuskarta ta nuna hakan, Turaki ya kalleta yace,"fushi?". ta girgiza kanta da sauri,"a'a". yace,"to saki fuskan". ba tare da tayi hakan ba tace,"to har girkin matarka ma ba zaka ke ci ba Hammah?". yace,"dalilin da yasa zanyi aure na zauna a kusa da Maama kenan". tace,"amma Hammah akwai...". ya tari numfashinta da faɗin,"akwai mutuwa ko?, na san da hakan. ki tayani adu'ar na riga Maama mutuwa ba naga tata ba". Ilham tace,"to Allah ya ƙara mata lafiya ya kuma bata tsawancin kwana me albarka". ya amsa da,"amin lelen Boɗejo". ya sauke numfashi sannan yace,"ina gyalenki?".

tace,"na barosa kan bed É—in Mami saboda kace na hanzarta".
hannunsa akan fuskarta yace,"je ki É—auko ki dawo, ki faÉ—awa Mami zaki min rakiya".

fuskarta ta washe da murmushi tana tambayarsa,"ina zamu je?". ya shafo wuyansa sannan ya bata amsa,"perfume zamu sayo".
idonta ya ƙanƙance a sa'ilin da take kallonsa. "ƙarewa yayi?, in ɗauko maka nawa?".
yace,"a'a wani zan sauya". idonta na ƙara ƙanƙancewa tace,"canjawa kuma?, perfume naka ɗin? your best choice ɗin?".
ya ɗaga gira ɗaya,"yes, bana son ƙamshinsa yanzu". tayi knodding kanta sannan ta miƙe ta fita.

Yarima Abbas ya rakata da harara, yayinda Turaki ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta har sanda ta fice, bai san dalilin da yasa yake tausayin yarinyar ba, ko dan ta kasance ita ɗaya a wurin mahaifiyarta ne?, ba hakan bane, hakan kuma ba zai zama dalili ba. yana son Ilham kamar yanda yake son Nihal, Samha da kuma Zaytun. yana ƙara sonta da burin faranta mata saboda yanda itama take sonsa tun yarintarta, ta ke masa kallon jininta fiye da yanda take kallon su Yarima Abbas.

ya sauke numfashi yana jinginar da kansa jikin kujera tare da rufe idanuwansa, baya manta alkhairi a rayuwarsa ko da ace daga baya zaka saka masa da sharri, wannan alkhairin naka garesa zai mantar da shi girman sharrin da kayi masa. sai dai har yanzu ya kasa mantawa da sharrin da Mami tayi masa, tsawon shekaru da yawa har yau neman dalili yake na ƙala masa sharrin sata da Fulani Azima tayi.

idan ya tuna cewa bayan da mahaifiyarsu ta tafi ta barsu, a cire Hajiya Madina a gefe, babu wata mace da ta nuna musu ƙauna tsurarta gami da tausayi tare da kyautatawa irin Fulani Azima. ta so shi shi da Zaytun kamar zata haɗiye su, tayi sa'insa da Mai Martaba duk akansu. ya faɗa rijiya Fulani ta bisa cikin rijiyar an ɗauko su tare, a matsayinta na matar Mai Martaba ta zubar da gwiwoyinta gaban mahaifinsa tana roƙonsa akan ya bata Turaki zata kula da shi fiye da yanda zata kula da ɗan cikinta har zuwa ranar da Ramla zata dawo.

to amma sai dai me?, a lokacin da ya shaƙu da ita, ya saba da ita, ya shaƙu da ƴarta, yake ganin ta zamar masa uwa, sai Fulani ta rikiɗe ta koma kalar wata mace ta daban, mace me cike da tuggu da makirci, ta shiga muzguna masa tana goranta masa akan zaman da yake yi acikin masarautar alhalin ita ta rabosa da Hajiya Madina, ba wani ya ɗaukosa ya kawosa ba.
ta ƙala masa sharrin satar gwal a lokacin da baiji ba bai gani ba, ta ƙara da faɗin ya satar mata kuɗaɗe, kuma ba tare da wani tunani ko bincike ba Mai Martaba ya yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata, hukuncin da Hajiya Madina tayi tsalle ta dire agaban Mai Martaba tace muddin aka ga an saka ɗanta a prison to wallahi sai dai idan bata numfashi. ta kuma fuskanci Baffa gaba da gaba tace ya sani, idan har matsayinsa na alƙali bai shigar da ƙarar Fulani akan ƙazafin da ta yiwa ɗanta ba, to la shakka babu kaffara sai ya rabu da ita, kuma ya rubuta ya ajiye, rabuwarsu ba yana nufin zata tafi ta bar masa Turaki da Zaytuna bane, a'a zata tafi da gaba ɗayansu ne ta kowanne hali, ko da zai dinƙa yankar naman jikinta yana goranta mata ba ita ta haife su ba.

asalin samo gaba me ƙarfin gaske kenan da ta shiga tsakanin Hajiya Madina da Fulani, har tsawon shekaru masu yawa, har sai lokacin da Turaki ya kammala degree ɗinsa na biyu sannan gabar tasu ta ƙare, bayan Hajiya Madina ta tambayi Turaki ya faɗi kyautar da yake so tayi masa yace mata yana so ta daina gaba da Fulani, domin gaba abar ƙyama ce tunda Allah baya so, kuma ma'aikin Allah yace kar mutum ya rama sharri da sharri dan haka ta bar batun ɗaukar fansa da tace zata yi akan abinda Fulani tayi masa, ta yafe mata kamar yanda shima ya yafe mata.
Chapter 58 · 0% Book details