← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 176

Sashe 131

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

can suka ji buɗewar ƙofa an shigo, Zaytuna ta shigo tana ajiye jakarta, ta cire labcourt ɗin jikinta tana zazzare idanu wajen kallon kowa kafin ta buɗi baki tace,"Mum, Maama lafiya?".
babu wanda ya kalleta balle ya amsa ma ta, sai tayi tsuru-tsuru ta kalli Nihal suka yi magana da ido ta nuna ma ta Fillo dake durƙushe a ƙasa.
sai taja bakinta tayi shiru ta fasa sanar da saƙon Turaki da ya faɗa ma ta cewa tace da Mum yaje kano ne after magrib zai dawo, wayar da take kira ba ta ɗaguwa.

shirun da yay yawa yasa Mum miƙewa ta fita, aka bar Maama da Fillo har sai da akayi sallar la'asar tukunna tace da ita ta tashi tayi sallah.
gida dai sai yay ɗiff kamar gidan mutuwa, ran iyaye babu daɗi yara kuma duk sun shiga damuwa saboda yanayin da iyayensu suke ciki, bayan sallar magriba Hajiya Madina tana lazimi Turaki ya tura ƙofar ɗakinta, haka kawai yaji gabansa ya faɗi duk da bai san abun da ke faruwa ba, Hajiya Madina ta waigo dan ganin mai shigowa, tana ganinsa ta miƙe ba tare da ta shirya ba ta fuskance shi.

murya a sama ta nuna masa hanyar fita ta ce,"fita, fitar min da ga ɗaki kafin na sa ƙafa na takeka in take banza". muryarta ta fita da tsananin ɓacin rai.

yay tsuru tsuru ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga hannu ta wanka masa wari, ta shiga nuna shi da yatsa tana faman huci tace masa,"daga ranar yau zuwa ranar da za'a busa ƙaho babu ni babu kai, in har ka ƙara shiga sabgata tabbas hukuma ce zata rabani da kai, ma za juya ka bar min ɗaki".

ganin ba zai fita ba ta rarumo ƙaramar kujerar da take zama zata buga masa, babu shiri ya juya cikin sauri ya fi ce.

yana zuwa part ɗin Mum ya tarar da ita zaune a parlo ta zabga uban tagumi, zuciyarsa ta shiga lugude, ya tafi kamar munafiki ya tsuguna a gefen ƙafarta, bai san dai laifin da yay ba amma saƙon da Khalil ya ba shi ya san akwai laifin da ya aikata.
muryarsa a hankali ya ce,"Mum lafiya?".

ya tambayeta yana ƙoƙarin cire hannun da tayi tagumin da shi, sai dai tun kan ya kai ga taɓata ta make shi da mugun zafi.
"matsa da ga kusa da ni".

ta faɗa tana sauke masa rikitattun idanuwanta da ke nuna zallar ɓacin rai, nan da nan hankalinsa ya tashi ya shiga tambayar laifin da yayi.
"wallahi tallahi idan har baka matsa daga kusa da ni ba ko me na ɗauka sai na buga maka in yaso ka mutu in huta da baƙin ciki da takaicin rashin dacen haihuwarka da nayi".

ya buɗe baki ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yana kallonta zai ƙara yin magana a mugun tsawace ta dakatar da shi,"na rantse da Allah ka ƙara min magana a wurin nan sai na fiddo maka da nonona ka biya ni wanda ka sha, banza mara mutunci shashasha butulu kawai wada bai saka halacci da halacci sai dai ya saka halacci da sharri, daga ranar yau ina me tabbatar maka da babu ni babu kai har abada kuwa".

ta sauke yatsanta da ga kansa, ta É—au wayar da ke kusa da ita ta kira Khalil, cikin mintina kaÉ—an sai ga shi ya shigo, tai masa nuni da kujera ya zauna a É—arÉ—arce, ta É—auki takarda da biron da ke kusa da ita ta wurgawa Turaki wanda ke dafe da kansa yana ta amabaton kalmar innalillahi a zuciya da fili, magana yake so yayi amma babu dama saboda rantsuwar da Mum tayi.

"mu ba matsiyata ba ne, kai tsiya ta yiwa ƙatutu, Allah ya hore mana yay mana arziƙin da zamu iya siye duk abin da ka mallaka har kake taƙama da shi, ka rubuta kuɗin matsiyaciyar wayar da kashe hannun ƴar mutane saboda ita, ko nawa ne za'a biyaka dan kai ne faqararre".

ta ƙyasta yatsunta biyu ta ce,"kuma ka sa ni, duk illar da hannun ƴar mutane yayi wallahi sai mun shiga kotu da kai".

ganin zai yi magana ta kuma doka masa tsawa,"kuÉ—inka nace ka rubuta".

yay taking deep breeth yana kulle idanuwansa yay rubutu ajikin takardar, da ido Mum taiwa Khalil nuni da ya karɓa, ya karɓa yana kallon abun da ya rubuta, Galaxy fold Z2 1.3ML tare da kuɗin gyara 700k. ya kalli Mum zai ma ta magana ta ce,"tura masa kayansa".

Khalil ya ɗau wayarsa in few minutes ya turawa Turaki kuɗin, seconds kaɗan sai ga ƙarar shigowar alert a wayar Turaki.

"Mum sun shiga". Khaleel É—in ya faÉ—a yana dubanta. ba tare da ta kalle shi ba tace,"ka kira min Madam".

ya tashi ya fita, babu jimawa sai ga Hajiya Madina ta shigo fuskarta sam babu annuri babu walwala, ta tsaya cak da ga baya tana cewa da Mum,"ya za'ai ki kirani alhalin wannan É—an banzan yaron yana zaune anan, ko kaÉ—an yanzu bana son ganinsa, zan dawo in sameki after ya fita".

ta faÉ—a tana juyawa Mum ta dakatar da ita da cewa,"so nake ki zame min shaida dalilin da yasa na kiraki kenan".

hakan yasa Maama dawowa tazo ta nemi kujera ta zauna, ta juyar da fuska yacca ko kaÉ—an ba zata fuskanci Turaki ba.

Mum tace,"ko bayan raina ban amince ba wannan É—an banzan yaron yay aure, ina so ki zamar min shaida".

da sauri Turaki ya ɗago ido yana dubanta, me ya yi zafi shi ba wuta ba?, laifin me ya yi har haka?, yaji duniyar gaba ɗaya tayi masa zafi kansa na neman tarwatsewa, da ƙyar ya iya tattaro yawun bakinsa ya ce,"Mum me yayi zafi haka?, wanne irin laifi na aikata muku?, idan abin da naiwa ƴarku ne na roƙeku don Allah kuyi haƙuri ni kaina na san nayi kus....".

maganar tasa ta yanke lokacin da yaji saukar jotter da biro a fuskarsa.
ya kalla Maama da ke kallonsa da tsananin ɓacin rai tace da shi,"ka rubuto min sauran sakinta shi ne zaka tabbatar min da kai isashshe ne, dan ba zan karɓi saki ɗaya ba domin kuwa Fillo ta gama aurenka har a naɗe duniya".

ya kulle ido yana sauke numfashi, sannan ya buÉ—e yace,"Maama ce muku tayi na saketa?".

"ba ka saketa É—in ba ne?".

ya shiga girgiza kansa yana faɗin,"ni ban saketa ba Maama, idan ma haka ta faɗa muku to ƙarya take yi".

Maama ta dinƙa kallonsa babu ko ƙifce, kafin tace,"kai ko dai kayi hauka ne?, ko kuma shaye-shaye ka ke yi a ɓoye?".

ya ce,"Allah ni Maama ban san da wani batun saki ba a tsakaninmu, sai dai idan ita take buƙatar hakan shiyasa ta faɗa".

Mum na ta kallonsa ta kasa cewa komai dan kallon typical mahaukaci take yi masa, Hajiya Madina ta kira Zaytuna a waya ta ce taje part É—inta ta ta zo mata da Fillo.
wucewar minti uku sai gasu tare, Fillo ta rakuɓe waje ɗaya tana rarraba idanu akan carpet, Turaki ya dinƙa kallonta yana ganin yanda fuskarta tayi jawur, da kuma uban bandage ɗin da ke hannunta.

Mum tace da ita,"karki ji tsoronsa ki saɓa shari'ar musulunci, faɗi ya sakeki ko bai sakeki ba?".

cikin dusashewar muryar kuka ta ce,"ya sakeni".

Maama ta ɗauki remote a kusa da ita ta jefawa Turaki sai ga shi a goshinsa, ya dafe wajen da lokaci ɗaya yayi malolo yana,"shhhh, Maama ni wallahi ban saketa ba ƙarya take yi".

Fullo ta É—ago ido ta kalle shi ta ce,"wallahi fa kake cewa?".

yanda tayi maganar dariya ta kusa fito masa amma sai ya dake ya zabga mata uwar harara ta yanda su Maama ba su lura ba, itama ta murguɗa masa baki tare da ɗauke idonta akansa ta kalli Mum tace,"tun a ranar da muka je asibiti duba shi ya sakeni, ni kuma na kasa faɗawa kowa,  shi ne yau yace in dai ban bar masa gida ba sai na ƙwammace da ban taɓa saninsa ba har ma da ku".

ya kalli su Mum da duk idanuwansu ke kansa, da sauri ya ce,"Allah ban saketa ba".

sai kuma ya juya ya kalli Fullon ya ce,"ni da bakina na furta miki hakan?".

ta harare shi tana fito da ɗayan hannunta da ga hijabi ta miƙawa Maama takardar hannunta.
ganin takardar idanuwansa suka fito waje da sauri ya kai hannu zai ƙwace a harzuƙe Mum tasa masa ƙafa ta hamɓarar da shi gefe. ya ɗago daga kifewar da yay yana ɗora hannu aka yana ambaton innalillahi da ƙarfi har sai da kowa ya kalle shi.

sanda Maama ta gama karanta takardar sai ta kalli Mum, ta miƙa ma ta Mum ta kau da kai tana girgiza kanta alamar ba zata karɓa ba.

Maama ta ce ma ta,"dan Allah ki karɓa your excellency, zuciyata zata fashe".

Mum ta juyo da sauri ta karɓa, ta kifar da takardar a cinyarta da ƙyar ta yarda da roƙon Maama ta karanta.
ta kalli Fullo a sanda ta gama karantawar tace,"yaushe ya baki wannan takardar?".

ta tsagaita kukanta ta ce,"ranar da muka je asibiti duba shi".

Mum ta ƙara cewa,"ruwan hawayenki ya wanke wajen adadin sakin, nawa ya rubuta?".

furucin Mum ɗin yasa idanuwan Turaki suka ƙawalalo waje fiye da ɗazu, ƙirjinsa ya ce taratsatsa.
Fullo ta buÉ—e baki wani sabon kukan na tahowa tace,"ai ban karanta ba".

Mum ta miƙa mata takardar tana cewa,"to karɓi".

Fullo ta karɓi takardar zata cusa a hijab Mum tace,"karantawa za ki yi ai, idan ba ki karanta ba sakin ai bai tabbata akanki ba, ki karanta sai ki nuna masa kuskurensa ki ɗau duk kalar matakin da kika ga ya dace da shi".
Chapter 131 · 0% Book details