Sashe 82
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
banda koyawa ta addininsa da babu abinda zai sa shi amsawa, dan sarai ya shaida muryarta, kuma ko ba komai taji daÉ—in amsawar saboda muryarsa nan me daÉ—i, daÉ—in da take jin yafi na sarewa tsuma zuciya.
daga kan gadon da ta ke tasa tissue ta ƙara goge idonta, with littile courage tace masa,"barka da asuba. ya amarci?".
tsabagen mamaki ma bai san me zai ce mata ba, last kira da tayi masa Bello ne ya karɓi wayar ya keta mata rashin mutuncin da ko kare ba zai shinshina ba, kuma in ace Bello gaban fadawa yay hakan abu ne me kamar wuya idan ba'a fille masa kai ba, dan tsananin shock na irin maganganun da ya dinƙa yaɓa mata matsayinta na ƴar Sarki tsayawa tayi kamar statue, and a zaton Turaki ko ace shi ɗaya ya rage namiji a duniya Gimbiya Aisha ba zata ɗauke shi ba saboda abinda Bello yayi mata, amma shine yau take daɗa kiransa?.
dama bata tsammaci zai amsa mata ba, saboda haka maganarta kawai taci gaba da yi.
"ƙawata Ilham bata faɗa min zancen aurenku ba kwata-kwata, amma na gani a duniya, naga the best couples in the year of 2022, na jima banga perfect match couples irinku ba.
duk da kai babu farin ciki a tare da fuskanka but hakan ba shi ya hana fiddo da ainihin kyawun surar da ubangiji yay maka ba, and wannan rashin bayyanar annuri da fara'a na fuskanka ya shaida min cewa auren dole ne akayi maka, kai baka so but ita tana so dan tata fuskar ta bayyana hakan 100%, but duk da haka fa duniya zata judging rashin walwalanka da a haka kake, amma to me da na riga na san fuskan da bai rabo da murmushi na san sam auren ba so yake ba. Anyway i congratulate you dear, Allah ya baku zaman lafiya. sai dai you have to know one thing, ni Aisha Sanusi M2 ni ce zan zama uwar Æ´aÆ´anka, keep this in your mind".
Turaki dai tun sanda ta fara maganar ya kunna TV yana sauraron karatun alƙur'anin da aka saka a channel ɗin saudi tv, abubuwan da ta faɗa ma ba komai yaji ba banda na ƙarshen.
bai bari ta ƙara cewa komai ba ya datse kiran da ya haddasa masa ciwon kai. ya wurgar da wayar a gefensa yana daɗa jin ransa duk babu daɗi.
yana gama bin azkar É—in da yake sauraro ya jinginar da kansa da kujera, lokacin tuni gari ya waye har 6:30 ta kusa.
idonsa a lumshe hoton Fillo nata haska masa, lokacin ne Gimbiya Ilham ta fito daga bedroom tana takowa da ƙyar har ta ƙaraso wajensa, abaya ne yello colour jikinta me bala'in kyau, ta ɗora hular chantly akan kwantacciyar sumar kanta, tayi kyau sose da light makeup ɗin da tayi sai zuba ƙamshi take yi, ta ɗauke hannunsa akan kujerar sannan ta zauna a kusa da shi ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, hannun nasa kuma ta ɗora akan cinyarta.
muryarta a sanyaye kuma a shagwaɓe tace,"Hammah fever na son kamani, kaina yana ciwo sosai, jikina ma duk ciwo yake yi".
ta ƙarasa maganar yana jin saukar hawayen nata a kafaɗarsa, yana jin yanda ɗumin hawayen ya tsarga fatar jikinsa, yana kwatanto shi da zafin hawayen Fillo, wacce ya san a duk inda ta ke yanzu kuka take yi.
bai ce da Gimbiya Ilham komai ba har wucewar daƙiƙa ɗaya, lokacin wayar dake kusa da shi tayi ringing, yana kallon new number ne ajiki yaƙi ɗauka.
har sau biyu kiran na katsewa tunaninsa duk Gimbiya Aisha ce, sai kira na uku ya shigo da lambar Inna Falmata, kamar ba zai É—aga ba sai kuma ya É—aga yana yin sallama.
daga can ɓangaren Boɗejo ta amsa sallamar tasa tana ɗorawa da faɗin,"ban kiraka da lambata ba saboda nasan ba ɗagawa zaka yi ba, ashe sabuwar lambar ma baka ɗagawa, sai ka ɗaga ta Falmata da yake kasan ta ƙanwar ubanka ce, ko ba komai halin girmama manyanka na burgeni, duk uban miskilancinka ka san manyanka".
yaji kamar ya kashe wayar dan mugun haushinta yake ji, amma sai bai yi hakan ba.
a daƙile yace,"ina kwana". tace,"lafiya lau, kun wayi gari lafiya?". yace,"lafiya lau". tace,"yauwa dama zan tambayeka ne ya ka sami Ilham ɗin?".
ta faɗa tana yin ƙasa da murya. yace,"lafiya lau, ba ki da lambarta ne?". tace,"ya salam, baka gane nufina ba ne?, ita yarinyar a ya ka sameta nake nufi?". ya ƙara cewa,"lafiya lau, ba ki da lambarta ne?".
Boɗejo taji kamar ta kai masa duka ta cikin wayar, dan in kusa gareta yake ma ba abinda zai hana faruwar hakan. cike da takaici ta ƙara yin ƙasa da murya tana faɗar,"ya zanyi tunda kai farin shiga ne, sai nayi opalli-opalli tukunna zaka gane. dama haka zancen ya zancen budurcinta?, ya ka same shi?, fatan dai ta kawo shi lafiya?".
da ƙosawa yace,"gata ki tambayeta". ya faɗa yana direwa Ilham wayar akan cinyarta.
ta buÉ—e idonta da ke rufe bacci na so ya É—auketa, ta kalla wayar da call ke tafiya, da sauri ta É—au wayar ta saka a kunne tana cewa,"Inna ina yini". BoÉ—ejo tace,"Ilham ni ce, lafiya naji muryarka haka, kuka kika yi?, ko ba kya jin daÉ—i?, mene matsalar faÉ—a min, Turaki ne ya gaya miki magana babu daÉ—i?".
Ilham tace,"a'a". ta faɗa tana sakin sabon kukan shagwaɓa. hankalin Boɗejo a tashe tace,"ni bana son kuka, ki buɗe baki ki min bayani, ko sai na zo?". cikin muryar kuka Ilham tace,"Boɗejo jikina duk ciwo yake min, zazzaɓi ne ajikina. kaina kamar zai cire, kizo dan Allah".
BoÉ—ejo tace,"bawa mara mutuncin wayar". Ilham ta kai hannu ta É—ora masa wayar a kunne, da masifa BoÉ—ejo tace,"daga mugu sai kai Turaki, yanzu yarinyar babu lafiya shine dan tsabar zalunci baka wuce ka kaita asibiti ba?, haka kaga ubanka na yiwa Madina?. gaskiya ban yafe ba sai Allah yay mana sakayya tsakanina da kai. kuma dan uwarka Madina ka amsa min tambayar da nayi maka tun É—azu, in kuma sai nazo har gidan kaga tsayina inji".
Turaki yay guntun tsaki yace,"ni dai karki ƙara zagar min uwa. amsar tambayarki kuma ta kawo shikenan, karki ƙara kirana ki kira wayarta idan kina son magana da ita, ni ban haɗa komai da damuwa ba so ki barni inji da abinda ya damen".
bai jira cewarta ba ya kashe wayar yana miƙewa ya bar wajen, Ilham tabi bayansa da kallo tana jin hawaye na sakko mata.
yanzu shikenan irin wannan zaman zasu dinƙa yi da shi?, ana aure dan farin ciki amma tun ba'aje ko ina ba ta fara fuskantar ƙalubale, tana ji ana faɗar tun daga daren farko mace ke fara samun kula da tarairaya daga wajen mijinta amma ita nothing like that, ya sameta a virgin ɗinta amma kamar wadda ta zo masa a fafe, sai faman haɗe rai da kumbura yake ba, duk uban kukan da ta sha daren jiya sannu wannan bata samu ba, balle taimako daga garesa.
and cikin ƙarfin hali ta gyara kanta duk da zafi da raɗaɗin da take ji amma hakan bai sa yaji tausayinta ba a sanda ta tabbatar da yaji uban zafin dake jikinta sanda take kwantar da kanta jikinsa, yanzu shikenan ita wannan soyayyar da take ta kwaɗayi a gidan aure ba zata samu ba kenan?, dama haka illar auren wanda baya sonka yake?.
sai kawai ta kifa kanta a hannun kujerar ta fashe da kuka mai ban tausayi.
daga can masarauta kuwa tuni ko'ina ya ɗauka da batun Gimbiya Ilham ta kai budurcinta gidan miji, kowa kuma sai ya shiga saka kyautukansa acikin wata ƙatuwar kwalla da ke dire a ƙofar turakar Fulani Azima, guɗa kawai kake ji na tashi da tafi ana son barka ana yabon Fulani Azima da tarbiyar da ta bayar.
ƙarfe goma sai ga manyan motoci ƴan ubansu na jiniya a ƙofar gidan Turaki, mota guda biyu ɗauke da hadimai mata, suka fito suka isa inda wata baƙar mota ta ke cike da sassarfa. acikin motar ne aka shiga fito da manya manya coolers na abinci, wasu coolers ɗin abinci ne cikinsu irin na gidan saurata, sai wasu coolers ɗin kuma uban kayan gara ne kamar hauka. dan Gimbiya Ilham tsab zata shekara da su indai ba cin abinci aka dinƙa musu ba.
haka suka dinƙa shiga da coolers ɗin suna fitowa suna kuma ɗibar wasu, sai da suka gama shigar da su tas sannan kuma sai ga ma'aikatan kamfanin Arewa culture Decoration suna shigowa ɗauke da kayan aiki a hannunsu suna nufar can baya inda ƙaton haraba yake wajen filoti guda, a wajen harda swimming pool irin tafkeken nan. suka baje kayan aikinsu kuma cikin ƙanƙanen lokaci suka shiga gyara wajen da decoration irin na gidan sarauta bango zuwa bango, haka ƙasan wajen ma duk an malale shi da uban carpet me taushi an baza uban tumtum sai ka rantse ko fadar mai martaba ake haɗawa.
wata ƙawar Fulani Azima na zuwa taga irin yacca decoration ɗin ya haɗu sai tayi tsaye ta kasa motsi ta saki laɓɓa tana bin wajen da kallo cike da burgewa.
"wow, la'ila ha'illahu, dan Allah aina aka samo waɗan nan masu iya aikin. kan uba ke kiga wuri kamar dama can a haka aka ƙera shi, na rantse da Allah wanda bai sani ba yazo wajen nan sai yace gidan sarauta ya shiga".
sai tayi saurin zaro waya a jaka tana miƙawa ɗaya daga cikin ma'aikatan tana cewa,"ungo maza lafta min lambarku a wayata, ina zanyi saken wannan azababben decoration ɗin da bikin ƴata, habawaa ai dole jama'a suzo suyi kallo na kece raini ma, ta yanda gobe ba zasu ƙara ɗaukan gajigarin masu decoration na musu aikin wofi suna asarar kuɗi ba".
ma'aikacin na murmushi yace,"Hajajju bari na karanto miki kawai". Hajja Balkisu tace,"yi da sauri, ai ni duk a tsume nake. yanda kasan in É—auke wajen nan in tafi da shi".
Ma'aikacin still da murmushi fuskarsa ya shiga karanto mata lambar yana rubutawa,"08067261323". tace,"me zan saka a sunan?". yace,"kawai rubuta Arewa Culture Decoration".