Sashe 9
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaka ce ke maganar tana daga cikin É—aki tana gyara, dan yau tun before 7 ta tafi kai Fillo asibiti, dalilin ma da ya sa suka dawo da wuri saboda Amir ne ya kaisu, a can asibiti suka tarar da shi da wuri yaje ya kama musu layi, tun daren jiya ya kasa zaune ya kasa kwance saboda yanayin yanda ya tafi ya barta da jikinta.
tun wancan ranar da Fillo ta ƙona asirin nan shikenan ta kwanta ciwo, har sati guda tana kwance jiki sai dai yay ta tsamari ba sauƙi. Sai ma yau ɗin da ta ɗanji daɗi.
A yau ɗin ne Kaka ta ƙara ƙudurtar cewar Fillo bata da wani miji a wannan duniyar sai Amir, saboda samun namiji a wannan zamanin kamarsa babu shi, yau ta daɗa yabawa da hankalinsa, yana da duk wasu good qualities da ake buƙata a wurin ɗa namiji, ga uwa uba ilimin addini.
ko sisinta bata kashe ba shi ya biya komai da akai bill, duk da ba kuɗi ne da shi ba, amma akwai zuciyar nema da kuma kyauta, babu yanda ba tayi ba akan ya karɓa ya ƙara amma yaƙi. dai-dai da ruwan sha wannan sai da ya siya mata na Faro da suka dawo, da kayan marmarinsa iya koƙarinsa. tana lure da shi banda tayi masa da gaske a ɗazun bai so tafiya ba.
Fillo dai kukanta ta ke rerawa da ƙarfin sauti ba kaɗan ba, da Kaka ta gaji da halinta tayi mata banza. Har ta gama duk abinda take Fillo dai bata daina kuka ba, kukan da bana komai ba ne sai na allurar da akayi mata. allurar da taja akaita fushi da masoyin da ake ji da shi, dan har Amir ya ƙaraci zamansa a parlon nan ya tafi bata ko saurari duk kalar lallashin da yake yi mata ba.
"kinga yau burabusko akayi...Allah sarki su Yami sun sha aiki".
Maganar Kaka keyi tana É—iban burabuskon a cikin kwano ta saka a baki.
ta kalli Fillo tace,"tunda kina sonsa daure ki tashi kici".
Fillo taja majinar hancinta tana ƙoƙarin tsaida kukan da takeyi tace,"miyar mene?".
Kaka tace,"miyar ganye ce, kuma yayi daÉ—i sosai".
Fillo ta koma ta kwanta,"ki aje min zanci anjima". ta faɗa sannan taci gaba da kukan kamar ƙanƙanuwar yarinya.
"Allah ya shirya min ke...ni banga wani hankali a tare da ke ba da Amir ya gani ya nace miki".
"ni daga yau ai babu ni babu shi, can yaje ya nemi wata ba dai ni Haliman Ammi ba, dan ba zanje gidan da za'a kassara rayuwata ba".
Kaka ta taɓe baki,"to dama Fillo wa ya ɗauko shi ya kawo miki. Ke kika yayibo abinki".
Kaka na sauraron radio akai sallama daga bakin ƙofa, ta amsa tana cewa a shigo. Zaytuna ta ɗaga labulen ɗakin da ya sha jiki ta shiga ta ƙara yin sallama.
"jaɓɓama lale". Kaka ta faɗa a sanda ta ke bin Zaytuna da ido da rashin gane wacece. Ita kuma ta nemi wuri zata zauna a ƙasa Kakan tace,"ah haba dai ga darduma yi haƙuri ki shimfiɗa hannuna da maiƙo".
Zaytuna ta karɓi darduman ta shimfiɗa ta zauna akai. Kaka tace,"sai dai ban gane wacece ba wallahi". Tai maganar fuskarta ɗauke da fara'a, tana so kuma ta gano a inda ta san kamannin da ke fuskar.
"ehh ba lallai ki shaidani ba gaskiya. Daga cikin gida dai nake".
Kaka ta washe baki tace,"ƙwarai kuwa ga kamannin Alhaji nan...sannu da zuwa, baƙuwar tamu ashe babbace...bari na kawo miki ruwa".
Ta miƙe Zaytuna tace,"a'a wallah Inna ki barshi ai yanzu zan wuce".
Kaka tace,"ai ko ba za ki sha ba saina kawo". Ta faÉ—a tana nufar inda kwandon wanke-wankensu yake ta É—auko farantin roba, Allah ya taimaka akwai purewater wanda Amir ya siyo musu É—azu mai sanyi kuwa, ta sako guda biyu ta ajiye agaban Zaytuna su na daÉ—a gaisawa.
Zaytuna bata da niyyar shan ruwan saboda a ƙoshe ta ke, amma gudun kar Kaka taji babu daɗi dole ta ɗauka tasha, tasan tsohuwar zata iya ganin kamar ko ƙyanƙyami ne ya hanata sha. balle ita bata ma ga rashin tsabta a wajen ba, komai fes-fes wajen ɗal-ɗal an share, shi kansa ɗakin sai ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke yake, duk idon da ya ga wajen dai ba zai ce wurin ƙazamai bane.
Æangaren masu aikin a haÉ—e yake, amma kuma kowa da gefen da yake.
kan Kaka a ƙasa tace,"ranki ya daɗe Allah sa dai ba wata matsala bace".
Zaytun tace,"a'a Inna lafiya lau, kawai dai na shigo ɓangaren naku ne ina gaidaku".
"Allah sarki aikuwa mun gode".
Zaytun ta miƙawa Kaka farar leda mai kauri irin ta store tace,"ga wannan, atamfofin marasa ɗinkin naki ne...akwai doguwar riga guda biyu sai a bawa yarinyar, banma san da ita ba ne sai da Maijidda ke gaya min...da yake Maijiddan kawai na sa ni sauran duk sai yanzu nake ganin fuskokinsu".
Kaka tace,"Allah sarki, ai Maijidda ita ta jima a gidan nan, su kam ai duk sai daga baya suka zo...itama ta wurin nawa bayan rasuwar mahaifiyarta na É—aukota".
Lokaci ɗaya idon Zaytuna ya kawo ruwa, kewar tata mahaifiyar ya kamata, tayi saurin danne hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata, wannan ciwon da ke manne a zuciyarta ya taɓu.
Muryarta so cool tace,"Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu". Kaka ta amsa da amin, ita kuma ta yunƙura ta miƙe, dubu biyu ta ciro a purse ɗin ta ajiyewa Kaka. "gashi ai adu'a wa iyayenmu".
Kaka ta zabga godiya ta koma jero adu'oi kala-kala, ita kuma tana ta amsawa da amin cike da jin daɗi. Yayin da taji ƙaunar Kaka ta shiga ranta, dan ita a rayuwa babban abinda zaka yi mata a duk duniya ka burgeta shine kaiwa iyayenta adu'a, tabbas kai mata hakan zata girmamaka kuma zata mutuntaka. Kuma har gaban abadan ba zata taɓa mantawa da kai ba, kuma haka ta dinƙa maka alkhairi kenan.
Har ta fita bata lura da Fillo da ke gefe ɗaya a rakuɓe ba, ta nannaɗe jiki da wani mayafin Kaka me kauri saboda sanyin da ta ke ji, fuskar nan tayi jajur tsabar ansha kuka an ƙoshi. ta haɗe rai babu annuri ko kaɗan. ƙememe tana ganin Zaytuna amma taƙi gaisheta kuma har haɗa ido sunyi, tana lura da yanda Kaka ke aikin jefa mata harara amma tayi fuska, shi yasa itama Kaka ɗin taita adu'a a ranta Allah yasa kar Zaytuna lura da ita balle ta bata kunya.
Kaka da ta dawo daga rakiya tace da Fillo. "ke dai ki sauya hali dan gidan wani za ki je, kuma wannan halin naki dai ba halin zama uwa ta gari ba ne".
Maijidda ta shigo, tayi wajenta tana yi mata dariya tare da tsokanarta akan kukan allura. Bata kulata ba tayi mata shiru, ita kuma ta miƙa mata ƴar ƙaramar waya ƙirar nokia irin ta da can wadda aka fara sakawa sunan rakani kashi, wayar duk ta jeme tasha kyauraye, banda Yami babu ma me iya riƙe wayar.
"Amir ne ya kira yace na kawo miki. Wai ya kira ta Kaka a kashe".
Kaka tace,"ai ita ta tsinka cajar garin shirmen banzanta".
Fillo ta kalli wayar da ke kan cinyarta, sannan ta kalli Maijidda da jajayen idanuwanta da suka sha kuka suka ƙanƙance tace,"kin ɗauke min ita a jikina ko sai na ƙarasa kasheta".
Sanin cewar zata aikata Maijidda tayi saurin É—aukewa tana faÉ—in,"yanda Yami ke ji da wayar nan kika fasa aini za ki jawa faÉ—a".
[8/8, 19:09] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*©ï¸Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
*7*
Acikin ɗan ƙaramin falon nasu, Fillo ce zaune ta takure daga jikin bango, jikinta gaba ɗaya a nannaɗe da babban mayafin da suke rufa da shi saboda sanyin da ta ke ji, kallo ɗaya za kai mata ta baka mugu mugun tausayi saboda yanda ta rame duk da cewar ita ɗin dama asali ba mai ƙiba ba bace, amma kana kallon ramarta a yanzu zaka san ta lalura ce.
Fillo cikin tuƙewar wani kukan ta kifa kanta saman gwiwoyin ƙafarta, kukan da ya kusa yin rugu-rugu da zuciyar Amir da ke zaune yana fuskantarta daga ɗan nesa da ita, yana jin zuciyarsa na matsewa da wani irin zafi.
Ya ɗauke ƙwayar idonsa daga kanta ya mayar kan magungunan da ya ɓallo a hannunsa, sai kawai ya janyo ledar magungunan kusa da shi ya zuba su a ciki ya ɗaure. Ya sauke numfashi very calmly yace da ita.
"ba saboda na takura miki ba, saboda lafiyanki Halima...but kiyi shiru ki bar kukan na zubar kin fasa sha".
zatonsa furucinsa zai yi tasirin da zai tsayar da kukan nata, amma sai yaji taci gaba da abunta kamar ba da ita yay maganar ba.
Sai ya duƙar da kansa a cikin damuwar da shi kaɗai yasan me yake ji, Allah ma ya sani, da ace yana da iko da har abada Halimatunsa ba zata yi ciwo ba, haka kuma da ace da yanda zai yi ciwon nan ya bar kanta ya dawo kansa tabbas da yayi hakan ko da hakan zai zama ajalinsa, shi dai kawai ya ganta cikin ƙoshin lafiya da walwala.
ya ƙara ɗago kansa ya kai kallonsa gareta, ganin har yanzu kamar ba zata daina ba yace da ita,"Halima kin san kuwa irin zafin da nake ji a zuciyata?, ki yiwa girman Allah ki daina wannan kukan wallahi ko kaɗan bana sonsa, yana taɓa zuciyata...indai magani ne nace ba za ki sha ina ce shikenan ko?".
Fillo ta ɗago da kanta, idon nan ya ƙara yin loko yayi jawur, jijiyoyin kanta sun fito raɗau kamar idan kasa hannu zaka kamosu waje. Amir ya tsareta da idanu ita kuma tana saka hannu ta goge hawayen, amma da ike ita ɗin me ruwan hawaye ce tana gogewa wani na kuma sakkowa.
Ita É—aya tasan irin azabar da ta ke ji a gaba É—aya jikinta, ita É—aya tasan me ta ke gani a cikin barcinta tun daga waccan ranar zuwa yau.
cikin muryarta da ta disashe da kuka tace,"ni nace maka waÉ—annan magungunan naku babu abunda za su yi min. ka daina asarar kuÉ—inka Amir, kawai a kira Malami yayi min adu'a".