Sashe 6
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna Wuro dai da ke kallo hankalinta ya rabu gida biyu, tun shigowarsa ta ke jera ƙwafa. Ji ta ke kamar ta tashi ta fizge wayar ta rotsa ta a ƙasa, sai taga ta tsiyan shigo mata waje babu sallama. Ta lura ma gaba ɗaya yaran gidan sun maida ita ƴar iska, kowa ya tashi shigo mata waje sai ta kaɗo masa yake shigowa da sallama, sun fi gane su shigo kullum su na ɓaɓatu a waya kamar dan su bature ya ƙera wayar.
Yusuf da ya gama wayar sai da yay typing message a wayarsa kana ya sakata a aljihu, sannan ya kai idonsa kan Kakarsu yace,"Ina Kwana".
Ba tare da ta dube shi ba a fusa ce tace,"yana kwano".
Yay ɗan murmushi ya ƙara cewa,"kin tashi lafiya?".
"da baka ganni anan ba ai".
Yace,"to Allah ya ƙara lafiya".
Bata dai amsa mishi ba taci gaba da kallonta, kallon da gaba ɗaya ba fahimtarsa ta ke ba. Bakinsu kawai taƙe kallo tana yin dariya a inda ya kamata, ta kuma ja uban tsaki a inda akai mata ba daidai ba.
Ta gefen ido ta ke ta kallon Yusuf, wanda ya sauko ƙasa ya takwashe ƙafafunsa, ba tace da shi ƙala ba sai da ya janyo flask gabansa sannan cikin hanzari ta dakatar shi.
"me haka?, kwanon abincinka ko nawa da zaka wani janyo shi gabanka?, ko kuma Uwarka ta dafa ta kawo min ne da zaka nuna min iko da shi?, salon dai neman magana irin ta bawa...ina ce da ka shigo ko sallama baka min ba balle na sami arziƙin gaisuwa, saboda ka maida ni abar banza shine sai da ka gama waya da wanda ya fini tukunna zaka durfafi abincina...to baka isa ba, kuma ba'ai wannan halittar da zata taɓa min kwano ba, ka tashi ka koma ka zauna ko kuma ka bar min parlo tun bamu samu saɓani da kai ba. Ni bana son tashin hankali haka kawai".
Yusuf ya miƙe ya koma kan kujerar ya zauna ba tare da yace mata komai ba, ta kalle shi kaɗan ta kwaɓe fuska kamin tace,"yafi maka dai".
"amma dai ina ce bayan na gama wayar na gaishe ki". Yace da ita yana kallonta.
"bata yi min bane".
"wa?".
"ita gaisuwar taka".
"ohh to Allah huci zuciyarki". Ta amsa da amin.
Yaci gaba da danna wayarsa, tsawon mintina kusan uku yaji maganar Inna Wuro na cewa.
"aiko ka akayi ne?".
Bai zaton da shi ta ke ba, dan farko É—agowa yay yana dube duben ta inda zai ga mutum, sai da yaga ba kowa sannan yace. "ba wanda ya aiko ni".
"to kuma zaman ma mene?, zuwa da sassafe haka, babu fa jimawa aka gama min gyaran wurin nan. bana son a ɓata min waje dan ni ba fiya son ƙazanta nagi ba...da ba za'a bar mutum ya huta ba dole sai anzo ɗaukar magana".
Rufe bakinta kenan Aliyu ya shigo parlon, ta bishi da ido har sanda ya nemi three seater ya kwanta yana ɗora ƙafafunsa akan hannun kujeran.
Haushi ya tuƙeta tace,"idan ka tashi Amadu ya gyaran wajen".
Shi dai bai kulata ba ya ɗauko earpice a aljihu ya saka a kunne, Yusuf na kallonsa yana mamakinsa, shi dai a wannan zamanin bai ga namiji mara lissafi ba irin Aliyu, yana namiji tunda akai hutun ASUU shikenan ya zama kamar mace, kullum yana gida sai shegen aikin jin waƙoƙin banza, yaƙi sana'ar fari balle ta baƙi, idan anyi magana yace ai Babansa ya tara musu...kuma in ana faɗa masa gaskiya Ammi tace ba haka ba.
Ya jijjiga kansa kawai yana jan ƙaramin tsaki na takaici. Aliyu yace da Inna Wuro,"naga mutanen ƙauye sun zo".
Tace,"to su tsaya a iya ɓangaren ku bana son gayya".
Yay gajeriyar dariya sannan yace,"ya za'ai su zauna a ɓangarenmu?".
Tace,"nima ya za'ai su sauka a ɓangarena?, Ni dai magana ta Allah idan kaje ka faɗawa Uwarka kar a soma turo min kowa, dan wancan karan banji daɗin zuwansu ba. Banda Amadu ya gina masai babba da ban san yanda zanyi ba, abunda ban taɓa gani ba sai a lokacin kashi har bakin masaina. Ɗoyi kuwa iri-iri babu kalar da ban guntsa ba, inda ace Uwarku ce kaɗai a gidan nan ai da warin kashin yaran ƙauyen nan shi zai zama ajalina. To sai Allah yasa akwai Falmata, tazo da kanta wallahi ta wanke min banɗaki nan ta sanya masa turaren wuta".
Aliyu yace,"itama Ammin ai zata yi miki, dan dai bata sa ni ba ne, kuma ai da sai ki faÉ—a mata".
Ta kama baki tace,"to ina ma ta ke zuwa waje na balle na sanar mata. ni fa idan kaga mun haɗu da ita Amadu ne zai yi tafiya mu haɗu a wajen masa rakiya kamar kishiyoyi, amma ni ina nake da wani arziƙi a wajen Zainabu...kana dai kallo ko gaisuwar safe".
Bai sake cewa da ita komai ba, don sam ba ya son abin da take yiwa mahaifiyarsu. Ta miƙe ta ɗauki flask ɗin abincin da aka kawo mata tun ɗazu bata ci ba ta wuce da shi kitchen, dan idan ta barshi Aliyu ma saka masa hannu zai yi, shi kuma ba jin magana yake ba.
Fridge ta buɗe ta saka yanda ma ko da wani ya shigo kitchen ɗin ba zai gani ba, har ta nufi ƙofa zata fita sai ta tuna ta dawo ta sakawa fridge ɗin key dan lemon da yake ciki sauran guda uku, Amadu bai san ya ƙare ba kuma cikin Ƴaƴansa babu mai ɗaukowa a ɓangarensu ya kawo mata, basu iya kawo mata komai ba amma sun iya suzo su cinye mata duk abinda aka ajiye mata.
Bata dawo parlo ba sai da tayi sallar walha, tana zuwa ta tarar da Yusrah ta shigo, ta bita da kallon sama da ƙasa ta ƙarasa bakin ƙofar ta jawo ta rufe tana faɗin,"kamin na huɗu ya shigo, ba dan ba dan ba sai nace Amadu gidan taron jama'a ya buɗe min".
Ta murza key tana mitar,"kai da ɓangarenka amma ba za'a barka ka huta ba".
Sannan ta saƙala key jikin abin maƙale labule tana cewa da su. "idan zaku fita ga key ɗin anan, idan zaku fita nace ba wai idan kunji knocking ba".
Cikinsu babu wanda ya tankawa maganar da ta ke, dan haushi kamar ta rufe su da duka. ta kallesu su duka tace,"Amadu kuka share bani ba". Sannan ta juya ta koma É—akinta.
Yusrah ta zauna kan kujerar da Inna Wuro ta tashi, ta buÉ—e jakarta ta É—auko office pins tare da madubi, ta shiga É—aura É—ankwali. Tana É—aurin ta ke cewa Yusuf.
"Yaya ashe ka shigo. Ɗazu Ammi ke cewa ƙila har ka koma ba lallai ta ganka ba...idan ka gama abinda kake naji dai tana batun zuwa abuja yau".
Ya É—ago da ido ya kalleta yace,"me zai kaita Abuja?".
Time da ta ke gama ɗaura ɗankwalin tace masa,"biki mana...daughter ɗin ƙawar nan tata da aka haɗaku kaƙi, ita ce zata auri ɗan gwamnan jigawa".
Ya maida idonsa kan wayarsa yace,"When will she come back?".
Tace,"I don't know. but i heard her saying sati guda za'ai ana bikin".
Karo na biyu ya É—ago ya sake kallonta. "kuma Daddy ya barta?".
"kai dai Yaya babu ruwanka. Ka barta taje tai hidimanta ta dawo".
Still yana kallonta yace,"ki shirya ku tafi tare".
Tayi saurin kallonsa da cewa,"niii babu inda zanje. Haka kawai na bita Ammi ta dinga cusa ni cikin yaran nan masu shegen ji da kai su na min kallon raini".
Ya ƙara cewa,"you mean ita ɗaya zata tafi?".
"kamar dai hakan. Amma ƙila Nabla ta bita kasan ita amara ƙirjin biki ce".
Bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihu. Yana cikin saka takalminsa Inna Wuro ta dawo parlon, tayi kasaƙe tana kallon Yusra da ke yafa ɗan yalolon mayafinta a kafaɗa.
"kuma fita za ki yi a hakan?". Inna Wuro ta tambayeta tana kuma ƙarewa shigar jikinta kallo.
Yusra ta jefa cingom bakinta ta amsa mata."yesss mun koma school yau...na manta ma ban faÉ—a miki ba, ko da yake jiyan na shigo ai na tarar kinyi bacci, an kafe mana result na samu pass all".
Inna Wuro tayi mata wani kallo, kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta juya ta dakatar da Yusuf da ke shirin fita tana ce masa.
"wai kuwa kana kallon a yanda yarinyar nan zata fita shine ba zaka tsawatar mata ba, kana babba amma kai sam baka san abin da ya kamata ba, da kai da hoto duka É—aya. Kalla fa gantalallan É—inkin da ke jikinta, wuya duk a buÉ—e kusan rabin nono a waje, amma a haka ta ke ikirarin zata fita har makaranta salon ta jawa Amadu zagi".
Sam Yusuf bai lura ma da kayan da ke jikin Yusra ba balle ɗinkin, sai bayan da ya gama saka takalmin ya kalleta, sai aukin zumɓura baki gaba ta ke yi tana ƙunƙuni, da gaskiyar Inna Wuro dole tace gantalallan ɗinki, shi a wurinsa ma wannan ɗinkin asarar kaya ne.
"ke kar ki kuskura ki fita a haka".
Ta ƙara kumbura kamar za tai kuka ta nuna kayan jikin nata. "fisabilillahi me wannan ɗinkin yay, ni gaskiya babu abunda zan sauya tunda ko Ammi ta ganni da su kuma bata ce komai ba".
Inna Wuro tace,"yo wannan Uwar taki sanin ya kamata tayi da zata hanaki fita tsirara".
Yusuf ya wurga ma ta wani mugun kallo. "yaushe na fara wasa da ke? Ki wuce ki sauya su babu inda za ki fita a haka".
Yana rufe baki Aliyu ya miƙe daga kwancen da yake, shima yana mata wani banzan kallo irin na ba ya son raini yace,"Uban waye sa'anki anan da ana yi miki magana kina ke ba haka ba. Kin wuce kinyi abunda akace ko sai na saka miki ƙafa".
Yusra ta fashe da kuka tana bige-bigen ƙafa a ƙasa, ta wuce Inna Wuro tana faɗin ba zata ƙara zuwa site ɗinta ba sai dai idan sauya mata suna akayi.
Inna Wuro ta bita da cewa,"ai dama bani ke gayyato ki ba, ke kike kawo kanki".
Ta dubi Yusuf tace,"yau zaka koma kano É—in?".
Yace,"may be".