← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 176

Sashe 176

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

a hankali ya furta,"I have missed you, I am always missing you Fulani Nah, i am missing you like crazy".

Muryarsa ta fito kamar zai fashe da kuka, duk da cewar hawaye tuni sun sauka saman kuncinsa masu zafi.

muryar yaransa da ya jiyo su na nufowa É—akinsa yasa yay saurin saka handky ya goge hawayen.
suka shigo ɗakin su na zama kan kujera, ya juyo yana kallon su, yaji wani sanyi ya ratsa ƙasan zuciyarsa, a yanzu kaf duniya baya tunanin akwai wani abu da yake ƙauna sama da yaransa, sama da su biyun nan, babu shi.

ya taka ya ƙarasa ya zauna a tsakiyar su, yaran suka sarƙafo da hannayensu ta wuyansa. "good morning Abie".

sai Maama ta miƙe ta tsaya a gaban su.
"this way! good morning Mr Sir".

ta kwatanta gaisuwar a irin yanda suka taɓa ganin wani vedion Fillo da Turaki ya nuna musu, lokacin suna honeymoon a Ausburg, hakan yasa suka ƙyalƙyale da dariya dukansu, har sai da Turaki yaji damuwar dake ƙasan ransa na bin iska.

lokaci ɗaya dariyarsu ta mutu a san da suka jiyo sautin muryar Fillo ya karaɗe cikin ɗakin, ta cikin audio record ɗin da ta taɓa yi tana karatun alƙur'ani.

Maama tasa hannu a laptop É—in ta kashe, ta juyo tana kallon mahaifinta da ya tusa hannunsa cikin sumar kansa, Ayan kuma na hawaye, sai kawai ita ma hawayen ya sakko mata, ta kifa kanta akan laptop É—in da hoton Fullo ya bayyana akan screen É—in.

muryarta ta fito gwanin ban tausayi da cewa,"Allah ya jiƙanki Ummina".

Ayan ma yace,"Allah ya gafarta miki Ummi".

Turaki yace,"Allah yasa kina aljannah Halima".

ya faɗi sunan nata da zai ce karo na biyu kenan da ya taɓa kiranta da shi.

"Abie when zamu je taraba mu gaisar da Granny?".

Ayan ya tambaya yana kallon mahaifin nasa.

"yaushe hutun ku zai ƙare?".

Maama tayi karaf ta ce,"2weeks reamaning".

ya sauke numfashi kafin yace,"ku haÉ—a kayan ku sai mu wuce in Allah ya kaimu gobe".

"photocopy of me".
Turaki ya jiyo sautin muryar Maama na faÉ—in hakan, ya É—aga kansa yana kallonta, ta kafa hoton Fullo a gaba tana kallo.

"Abie ka taso muyi break fast". cewar Ayan da ke tsaye bakin ƙofa.

"takeaway zamu yo ko mu tafi wurin Mum? tunda Anty bata nan".

Maama tayi saurin tashi tana cewa,"Abie mun dafa ni da Ayan, tun saven o'clock muka gama, mun dafa maka favorite naka kunun shinkafa da ƙosan bread".

da sauri Turaki ya miƙe cikin tsananin farin ciki, yana ta sakawa yaran nasa albarka, daga bisani suka fita cikin farin ciki zuwa downstairs domin yin breakfast.

_Sauran rayuwar Turaki da Yaransa, Da rayuwar Amir, da Rayuwar Fulani Azima duka na barwa tunanin ku._

*THE END*

*Alhamdulillah!Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!*
_*A yau fri 07/10/2022 muka kawo ƙarshen labarin LULLUƁIN BIRI, Alkhairan da na rubuta Allah ya haɗa mu a ladan, kurakuran da suke ciki Allah ya yafe min tare da ku da ku ka karanta.*_

_*Godiya mai tarin yawa da masoyan rubutuna a duk inda suke, waɗanda na sani da waɗanda ban sa ni ba, Musamman waɗanda Allah yake bawa ikon bibiyata a ko da yaushe, it really means a lot to me, Allah ya bar ƙauna tsakanina da ku, Allah ya faranta muku duniya da lahira.*_

_sannan ina me ƙara baku haƙuri da ta'aziyya akan rashin Maama da Fulani da muka yi. Babu yanda muka iya, adadin yanda ubangiji ya ɗibawa rayuwar bawa dole idan lokaci ya cika sai an tafi, duk soyayyar da muke yiwa mutum bamu kai yacca ubangiji ke son bawansa ba, illa iyaka mu bi mu mutum da kyakykyawar adu'a._

_hakana waÉ—anda ba su ji daÉ—in yacca asirin Fulani Azuma bai tonu ba, ina so ku tuna ko a rayuwarmu ba ko da yaushe asirin macuci ke tonuwa ba, wata shari'ar sai dai a lahira!_

_Sai mun sake haÉ—uwa da ku a sabon littafina in Allah ya kai mu da rai da lafiya._
_masu tambayar sunan sabon book ku dakace ni a status ɗina don har yanzu ban gama yanke sunan labarin ba, sai dai abu ɗaya da na sani zai zo ne ana kuɗi kan naira ₦500, kuma wataƙila a Arewabooks kawai zan ɗora shi amma dai ban gama deciding ba, kawai dai waɗanda basu da account a ArewaBooks kuyi ƙoƙarin mallaka sai kuyi following ena acan._

_Nagoode! Nagoode!! Nagoode!!_

Taku har kullum.
*Halimahz*
_(Anyway)_

_kuyi min dropping ra'ayinku game da labarin nan ta wannan number 07018098175 , insha'Allahu idan na sami lokaci zanke dubawa a hankali ina baku amsa._

_Allah ya sadamu da alkhairinsa, a yafe ni don Allah, sai an ajiman ku._

*Tarin godiya tare da jinjina ga:-*

1-Muhammad Kareem
2-Abbas Haruna
3-Mu'az
4-Nazifi Yareema
5-Abubakar Saleh
6-Abubakar Saraki
7-Anty Nice
8-Maryam Jam'are
9-Mum Sayyeed & Noor
10-Ummu Abdallah
11-Anty Bilqees
12-Ummu Adnan
13-Gamji Book Store
14-Halimahz Palace
15-Ummu Nabil
16-Nana Halima
17-Fatima S Haruna T/fulani
18-Ramat Novels facebook
19-Masarautar Billyn Abdul
20-Taskar Littafan Hausa
21-Nuraddeen Light
22-Surayyahms
23-SisNah
24-Matan Buri Fans
25-Ummu Nabil Novel groups
26-Basheer S Basheer
27-Surajo Salman

_Kuna da adadin yawan da idan na tsaya lissafo ku sai mun É—auki sabon chapter, amma ku sani kowannenku na raina, kuma kowanneku bani da bakin godiya gare shi sai dai adu'ar samun Aljannah._

*For gyara ko shawara am available ta number na da ke sama.*
Chapter 176 · 0% Book details