Sashe 92
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Turaki yaji saukar muryar a cikin kunnensa, yaji shigar sunan acikin kansa da cikin zuciyarsa, daga jin muryar kasan muryar babbar macece, amma hakan ba shi zai hana shi gane mamallakiyar muryar ba, ba shi zai hana shi gane muryar kowa ce ba a duk inda ya jita, tsawon shekaru da yawa ba tare da suna tare ba, hakan ba zai hana shi gane muryar wadda ta kawo shi duniya ba, da wayonsa ta tafi dan haka a ko'ina kuma a kowanne hali yaji voice enta zai shaida.
sai dai kafin komai dake cikin kansa ya gama wanzuwa sai ganin Hajiya Ramla yay a gabansa, ganin nata kuma ya firgita shi sau ɗaya yaja da baya, sai kuma ya dakata yana binta da kallo ƙwayar idonsa duk a waje.
an ɗauki tsayin shekaru da yawa, sai dai duk tsayin shekaru da dogon zamanin da zata ɗauka ba tare da ƴaƴanta ba, hakan ba zai hana tana kallonsu ta shaidacewar su ɗin jininta ba ne, kamar yanda shima ba zai taɓa manta mahaifiyarsa ba, babu tantama wannan ɗanta ne, haka shima yake jin babu tantama wannan wadda ta kawosa duniya ce, ɗanta ne wanda ta tafi ta barsa a lokacin da yake shakaru shida a duniya, kamar yanda shima yake ganin uwassa wacce ta tafi ta barsa lokacin da yake da shekaru shida a duniya.
sai kawai ta fashe da kuka, Turaki ma da yay mutuwar tsaye ya fashe da kukan farin ciki, ya taho da sauri ya rungumeta yana faÉ—in,"Mum, Mum are you really the one?, da gaske idona ba gizo suke yi min ba?, Mum ina kika tafi?, ina kika je Mum?, me yasa kika tafi kika barmu?, laifin me muka yi miki Mum?".
maganarsa ta katse, kukan tsananin murna da farin cikinsa ya ƙaru. ya janye daga jikinta yana daɗa kallonta, daga shi har ita babu wanda zai iya kwatanta irin abinda yake ji a tare da shi. kallonta yake sosai da irin wannan tsananin so da tausayin da Allah ya halicce shi na daban a tsakanin uwa da ɗanta.
Hajiya Ramla na hawaye ta kai hannunta ta kama fuskarsa, É—ayan kuma ta dungure masa kai fuskarta É—auke da tarin murmushi, tace,"babu Alhamdulillah sai wannan tarin tambayoyin Babana".
bai iya cewa komai ba, haƙoransa duka suka bayyana a waje kamar yanda nata ma suka bayyana, ya kuma rumgumeta sannan yace,"to Mum na faɗa Alhamdulillah...then you too should answer my questions".
Hajiya Ramla ta ture shi daga jikinta tana cewa,"to ba zan amsa ba É—in, in kuma ka zama Me girma Turakin Taraba sai in ji". ta faÉ—a da irin salo na wasa dake tsakanin uwa da É—anta. ta kamo hannunsa tace,"where is Zaytun?".
ya kasa ce mata komai, kawai sai ya ƙara rungumota yace,"to Mum aina kika ɓuya?, there are alot of questions but ki fara amsa min wannan".
tace,"Babana muna gaban mutanene fa". ya zare jikinsa anata ya kama hannunta yaja ta zuwa wajen kujeru dake wajen ya zaunar da ita. shi kuma ya zube gwiwoyinsa a ƙasa tare da kwantar da kansa saman cinyarta yana kamo hannunta duk biyun ya riƙe su da kyau kamar wanda za'a ƙwaceta.
daga ita har shi babu wanda ya iya cewa komai, hannunta a sumar kansa tana shafawa, shi murmushi ita murmushi, haƙoranta a waje nasa ma a waje. jinsa yake kamar ya buɗe cikinta ya koma ciki, haka itama ji take kamar ta tsaga ƙirjinta ta sanya shi a ciki, kowanne da maganar da yake son yi amma tsananin farin ciki da murnar da suke ciki ya ha rufe bakinsu.
idon kowa dai tuni ya dawo kansu, aka bar batun Fillo da halin da take ciki, basu san tuni ta farka a lokacin su Dr Yusuf su kai kanta, kuma lokacin da zai shiga É—in ne ya kama hannun Mommi ba tare da sanin kowa ba da hankalisu yay can kan su Turaki ba ya shiga da ita ciki ya tsayar da ita dai-dai saitin da idanuwan Fillo na buÉ—ewa zasu sauka akanta.
Hajiya Ramla tace,"Babana am asking you where is Zaytun?". ya ɗago da kansa ya kalleta kawai sai ya ƙara rungumeta.
a lokacinne kuma wayarsa dake aljihu tayi ƙara, yace,"Mum ɗauko ki min picking ba zan iya sakinki ba".
ta zaro wayar daga aljihunsa tana bin sunan dake yawo a jiki, kamin tace masa,"Beta Half". yace,"pick". tace,"my daughter inlaw right?".
sai ya saketa ya karɓi wayan yana wani murmushin na daban, ya shafo kumatunta yace,"you will soon meet her". ya faɗa yana miƙewa tsaye still holding her hand ya juya yana kallon kowa dake kallonsu, idonsa ya sauka akan Inna Wuro da ta saki baki tana kallon film ɗin da zuciyarta ke raya mata shi take kallo. ya saki hannun Mum ya isa wurin da take, bakinsa gaba ɗaya yaƙi rufuwa, yana zuwa da sigar tsokana yace,"tsohuwa aron ɗan kwalin kanki".
da sauri kuwa Inna Wuro ta kunto Farha da ke bayanta ta jefa masa zanin goyon tace,"komai ma ai sai a baku girmaku ne".
ya karɓa ya juya bayan yace mata,"Thanku, zan baki tukwici after". ya isa wajen ya rufe fuskar Hajiya Ramla da zanin sannan ya zauna kusa da ita yace,"stay quite har inje in dawo kinji". tai masa knodding kanta kawai tana binsa da kallo da jin soyayyar nan ta ɗa na fizgarta.
ya miƙe kenan sai ga Hajiya Madina ta iso wajen hankali a tashe, tana ganinsa ta yo kansa a rikice, za tai magana expression ɗin da take gani a fuskarsa yasa ta tsaya tana ƙare masa kallo. kafin ta ɗauke idonta daga kansa da mamaki tabi mutanen wajen da kallo ɗaya bayan ɗaya, sannan ta ƙara kallonsa tace,"mene haka a fuskarka?, Fillon ta farka lafiya ne?". ya kamo hannunta yace,"insha'Allahu lafiya zata farka, yanzu just close your eyes i want to show you something".
tace,"in rufe idona?, ka nuna min me?".
ya zagaya ta bayanta yace,"suprise". sannan ya ɗora haɓarsa kan kafaɗarta yana fuskantar da ita wurin da Mum ke zaune yace,"gidan da kika gina a Ausburg nake so a matsayin tikwici".
tace,"na ma baka Me Babban suna, amma ni dai barni in buÉ—e idona inga halin da yarinyar mutane ke ciki, ni ce silar condition É—in da take ciki, so this is not time for joke, kaima É—in mamakinka nake".
ya saketa yana faÉ—in,"indai kika buÉ—e ban ce ba isn't a suprise, kuma sai na doka miki yaji".
Hajiya Madina tai shiru ƙirjinta sai duka yake, Turaki ya ƙarasa wurin Hajiya Ramla ya ɗauke zanin daga saman fuskarta, sannan ya ɗora hannunsa a kafaɗarta ya kwantar da gefen fuskarsa a gefentata, Hajiya Ramla tabi Hajiya Madina da kallo tana jin wani irin shauƙi na kewar ahalinta da tayi, tana tuna irin rayuwar zaman lafiya, jin daɗi da kwanciyar hankalin da sukai da Madina.
Hajiya Madina na yin kalar tausayi har sannan idonta a rufe tace,"Me babban suna kai ka taɓa saɓa umarnina, amma ni ba zan iya saɓa naka ba, but ai na san kana jin tausayina ko?, to mu jingine wasa gefe kaji ɗan albarka".
muryarsa na fita da wani emotions yace,"gidan da ke Ausburg Maama".
Tace,"naji nace maka, muna komawa gida zan baka takardun".
yay murmushi me kama da dariya ganin duk yanda ta ƙosa yace,"promise?".
Tace,"i do, har ma da key É—in sabbin motocina guda biyu duk na baka".
yace,"zanyi kyauta ne da su nima".
tace,"tunda na riga na mallaka maka ikonka ne kai duk yanda kaso da su, can i open my eyes now?".
yana dariyar jin daɗi ƙasa-ƙasa yace,"not now, untill i say".
kawai sai yaga ta buɗe idon, Hajiya Madina ta buɗe idon da niyyar kai masa duka ganin yau yana neman mayar da ita wata yarinyarsa abinda basu taɓa yi ba, ƙwayar idonta ta sauka akansa sai kuma ta mayar da kallonta kan fuskar da take ganin kamar gizau a kusa da shi.
in ace da abinda yafi mamaki tabbas ta shiga cikinsa, ta ƙara buɗe ido tana kallon Hajiya Ramla dake ta mata murmushi, ta ƙwala wata ƙara tace,"Your Excellency are you really the one?". ta faɗa bakinta na ƙin rufuwa tana ganin hakan kamar a mafarki. sai kawai tai sufa taje ta rungume Hajiya Ramla tana faɗin,"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah". ta faɗa tana ɗagowa daga jikinta ta shiga duddubuta wai ganin dai kamar ba dai-dai take gani ba.
a lokacin ne kuma su Zaytuna suka ƙaraso wajen, abinda kowa ya gani yasa suka tsatstsaya da mamaki suna kallon Maama da tabi ta susuce saboda tsabagen murna. Maama ta waigo ta kalle su tace,"ubangiji yaji kukanmu ya amsa adu'armu ya dawo mana da Mum".
ai kan kace me wannan asibiti ya karaɗe da ihun murna, duk suka tafi da gudu suka faɗa kan Hajiya Ramla suna ta ihu, wanda in ace a tsaye ta-ke sai sun kaita ƙasa.
Zaytuna ce kawai ta tsaya taƙi zuwa wajen tana kaudar da fuskarta da gefe, dan ita bata ganin zata yi farinciki kamar yanda bata tunanin zata yafewa Mum. Ilham kuwa na tsaye daga gefen su tana ta kallon su cike da burgewa, musamman Turaki da ta kasa ɗauke idonta a kansa saboda yacca ta-ke ganin haƙoransa gaba ɗaya a waje, da irin tarin farin ciki da annurin da bata taɓa ganinsa ba aciki. a ɗazu hankalinta duk a tashe yake da bai dawo gida ba, haka da taji wurin kidnappers ya tafi hankalinta ya ƙara kaiwa ƙololuwar tashi, but a yanzu zata iya cewa kamar tana jin kanta ne a saman gajimare tana tafiya, ko ba komai tasan lokaci yayi da zata samu wannan gurbin da Turaki ke cewa ba zata same shi ba a zuciyarta, ta sani wuyarta mahaifiyarsa ta san ita matarsa ce, ita kanta bata san Mum ba dan ba'a haifeta ba lokacin, amma kallo ɗaya ta yiwa Mum ɗin tasan itace mahaifiyarsu da kowa ya taso a family yake jin labarin ɓatanta.