Sashe 121
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tazo wucewa Dada ta rarumi sandarta ta buga ma ta.
"can ina?, dan ubanki ko sheɗan ya san can ne da zan tambayeki kice min wani can... sai yanzu ma na gane mugun halin da Fullo ta kwaso wajenki ta koya, ai Hausawa basu yi ƙarya ba da suka ce abokin ɓarawo ɓarawo ne, haka ma zama da maɗaukin kanwa...sam sam ba kiyi halin ƙwarai irin na kakarki ba, dole na raba ƙawancenku dan ba za'a kaita gidan miji ba kije ki lalata mata aure".
Maijidda ta sosa wurin da ta duketa saboda zafi ta ce,"tana sashin Kawu Musbahu É—akin Adda Amina". zata fita Dada ta dawo da ita,"ke zo nan".
ta dawo tana rakuɓewa wuri ɗaya kamar mara gaskiya, Dada ta kalleta tsab sannan ta ce,"me aka yi miki da ma?".
Maijidda ta fara hawaye tana cewa,"tun jiya take ta kuka kuma duk na tambayeta abin da aka yi ma ta taƙi faɗa min, ina ta rarrashinta ma taƙi yin shiru, zazzaɓi ya rufeta na bata magani ma taƙi tasha".
"wacece da ma?".
tace,"Hussainata mana".
Dada ta miƙe tana dogara sandarta ta fita a fusace, ta shiga parlon Amina mutane na ta gaida ita babu wanda ta amsawa ta wuce kai tsaye cikin ɗakinta.
tana shiga ta sami Fullo kwance akan gado tayi ruff da ciki, ta taƙarƙare ta buga ma ta sandarta a baya, babu shiri Fullo ta miƙe a tsure tana dafe wajen, idonta na fara zubar da hawayen da suka tsagaita ma ta, sosai zafin dukan ya shigeta dan ƙashin bayanta har sai da ya amsa.
Dada ta dinƙa kallon idanuwanta da suka yi jawur, sun kumbura tsabagen uban kukan da take sha a ƴan kwanakin nan, fuskarta kanta tayi jaa ko tausayin kanta bata ji.
ran Dada a matuƙar ɓace ta ce,"ke wai dan uwar ubanki tare da kuka aka haife ku ko kuma an haifeki ne dan ki yi ta kuka a duniya?".
ta nemi wuri ta zauna tana ta faÉ—a.
"ƴar banzar yarinya mara tawakkali, idan ba za ki iya jurar rashin uban naki ba ki sha fiya-fiya ki bi shi mana, idan kuma auren ne ba kya so ki buɗe baki ki faɗa mana, ko an gaya miki mu muna kai zuri'armu gidan wanda basa so ne. nan na tayar da jijiyoyin wuya akan sai an sake ki saboda ina so na ƙwatar miki ƴancinki, iyayen yaron nan suka zo su kai ta bani haƙuri naƙi na haƙura har sai dai aka kai ƙarata gaban mahaifina tukunna, shi ma ɗin saboda ban iya ƙetarewa maganarsa ne amma da sai na dage akan bakana saboda ko kaɗan ni bana jurar naga za'a wulaƙanta min jinina, da kika san ba za ki iya zama da shi ba tun ranar da suka kawo lefe ba sai ki faɗa ba ace su juya da abinsu, to wallahi tallahi ki shiga hankalinki da ni tun banyi mugun saɓa miki ba, dan tsab sai in baɗawa idona toka nasa Jagarɗo ya kai ki barikinsu ya ƙulleki, ni bana son halin ƴan iska saboda haka ki kiyaye ni".
Fullo ta É—aga idanuwanta da take jin sun ma ta nauyi ta kalla Dada ta ce,"banda lafiya ne".
Dada ta zabga ma ta uwar harara ta ce,"da ba ki da lafiya kuma sai aka ce kuka ne zai yi miki magani ko?, mtswww".
ta miƙe ta fita ta bar ɗakin tana ta faɗa, a parlon ta sami Ammi cikin mutane tana raba musu Dakkere(abinci ne na fulani), ta kirata tazo tace ma ta.
"É—anki ya wuce ko yana nan?".
Ammi ta ce,"wanne a ciki?".
ta harare ta ce,"mutanen ƙwarai ake nema ba ƴan wiwi ba, likitan nake tambayarki ba wannan mara kunyar ba".
ta ce,"yana nan, amma ina jin kamar shi ya wuce kai Maudo airpot É—azu".
"to ina waccan yarinyar ƙanwarsa, me aikin asibitin?".
"sun je gidan Fatima anjima kaÉ—an zasu dawo".
Dada ta ɗanyi tsaki tace,"ma za kirawota ta dawo ta zo ta duba jikin yarinyar nan, tayi mata allura yanda zazzaɓin zai fi saurin sauka kinga ajima akwai taro, ba'a tara jama'a babu amarya ba, ko kuma an gayyota jama'a kuma su zo ace musu ba taro".
Ammi tace,"bata da lafiya ne?".
"yo gata can dai tana neman kashe kanta ai, ciwo yana cin ta babu wanda ta faɗawa saboda shegen nurƙufanci da miskilanci da baƙin hali irin na Hayyo".
Ammi ta ɗauki waya ta shiga kiran lambar Yusrah, tana ɗagawa ta ce da ita ta dawo yanzu sai ta koma. Dada ta sa aka kira ma ta Ummi, tana zuwa Dada ta ɗaga sandarta ta rafka ma ta a ƙafa. Ummi ta ɗan ja da baya tana bata haƙuri tun bata ji laifinta ba.
"ki shiga ciki kiji damuwar Æ´arki tun da ke dai soluwar uwa ce". ta faÉ—a tana bin Ummi da harara.
Fullo dai na zaune tun da su Dada suka fita, tana riƙe da farar takardar da Turaki ya bata ranar da suka je dubo shi a asibiti bai da lafiya, kallon takardar ta-ke tana juyata gudun hawayenta na ƙaruwa.
ta jinginar da kanta jikin bango idanuwanta a rumtse tana ƙoƙarin danne kukan dake neman cin ƙarfinta, babu abin da ke haskawa cikin ƙwayar idanuwanta sai rubutun da ke cikin takardar, kawai sai ta kasa riƙe kukan ta sake shi ya fito da ƙarfi a sanda Ummi ke shigowa ɗakin.
hankalin Ummi tashe ta yo kan gadon tana tambayarta lafiya, bata ma san ta shigo ba sai a yanzun, da sauri ta cusa takardar a cikin rigarta. Ummi ta kwantota kafaɗarta tana lallashinta da ban haƙuri.
zatonta duk kukan ba na komai ba ne sai irin kukan da wasu amare ke yi idan zasu bar gida.
Fullo ta samu ta rarrashi zuciyarta da ƙyar saboda bata so Ummi ta san abun da yake faruwa, bata san irin damuwar da zata shiga ba in har taga takardar sakin da ke hannunta, ba lallai ta iya ɗaukar wannan ƙaddarar ba, zata ga kamar itama bata yi dacen samun miji ba ne kamar yanda ita ma bata yi sa'ar miji ba a sanda ta auri mahaifinta, dalilin da yasa ta ɓoye kenan kuma ba ta tunanin za ta faɗa, ai tun da har ana zaman idda a gidan miji zata yarda su kai ta, ranar da ta gama iddarta acan sai ta sanarwa da kowa abun da ya faru, amma ba a yanzu ba da ba ta san wanne irin hali Ummi zata shiga ba akan hakan.
Yusrah ta shigo tayi ma ta allura, aka kuma ɗebo uban magunguna a first aid da aka ɗauko a ɗakin Innah aka bata. Ummi ce da kanta ta bata abinci taci, sai da taci da dama sannan ta ƙyaleta.
"ki daina kukan haka nan kinji Auta ta, bari naje ana ta baƙi daga ɓangarenmu, idan kika ji daɗin jikinki sai ki zo ku gaisa da su Yaya Murja".
tana kallon Ummin ta ce,"wace ita?".
"da babarta da Kaka ubansu É—aya, su na can sun zazzo ma fa da yawansu, sai tambayarki suke yi, nayi zaton kuna can gidan Asma'u shiyasa ai".
ta gyaÉ—a kanta kawai, Ummi ta fita daidai da shigowar su Maijidda, waÉ—anda suka shigo suna ta masifa akan É—inkin da tela yayi musu ba daidai ba.
AmaturRahman na faÉ—in,"na rantse da Allah in ace ba yau zamu sa kayan nan ba sai ya biyani zan baro shagonsa, É—an iska me kama da É—an daudu".
Maijidda tayi watsi da nata akan gado ta ce,"ai ni idan kinga na saka waɗannan kayan to sauya ni aka yi, gwara idan na koma gida na dinƙa saka su idan zanyi aiki amma ba'a bikin Hussaina tah ba, ban da rainin hankali ɗinki sai kace ance masa tsofaffi ne zasu saka".
Amatullah ma ta shigo ta jefar da ledar hannunta, Raudha ma haka, duk in ka kalla fuskokinsu ka san ransu babu daÉ—i.
Raudha tayi tsaye jikin wadrobe tana fuskantar Fullo, ta harÉ—e hannaye tana cewa,"kin ga yanda fuskarki ta kumbura kuwa?".
ta rufe idonta kawai ta kwanta tana juya musu baya, Amatullah ta ce,"ai É—a zu Hammah Hamid ce yay idan ya dawo ya tarar ba ta daina ba sai ya zaneta babu ruwansa da matar aure ce".
Raudha ta sauke numfashe ta ce,"i never see such a kind person me shegen kuka ma irinta, da muna saudia zatona ko dan Dada ta ce sai an saketa ne, da muka dawo kuma na kasa fahimtar auren ne bata so ko kuma kukan barin gida ne".
"kin taɓa ganin amaryar da take kuka irin haka dan zata bar gida?, ita dai barta dan ta ga ƴar auta ce shagwaɓa tayi mata yawa shiyasa".
AmaturRahman ta faÉ—a tana wucewa toilet.
Raudha ta zauna kusa da Fullo tana kamo hannunta ta riƙe, ta ɗau wayarta tana kiran lambar me makeup da zata zo ta yiwa amarya anjima da za su yi Fulani Day, bayan sun gama wayar suka ci gaba da maganarsu ta abubuwan da zasu yi anjima.
ƙarfe uku na rana aka fara shirya amarya, wata cousin ɗin su da ta zo daga benue tana ta complain akan rashin zuwan ango da aka ce ba zai zo ba, har sai da aka ce mata ai baida lafiya tukunna ta sarara ta hutar da yawun bakinta daga masifa.
ita dai Fullo duk babu walwala, ƙwayar idonta na manne a cikin mudubi kai kace kanta take kallo, nan kuwa hoton ranar da suka je asibiti ne kawai ke haska mata.
ta tuno sanda suka shiga room ɗin da Turaki ke kwance an saƙala masa oxygen, ga wasu abubuwa da akayi masa connecting, kallo ɗaya dai zaka yi masa idonka ya cika da ƙwalla haka kuma kaji tsoron Allah ya kama ka.