← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 176

Sashe 151

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yinin ranar gaba É—aya tana tare da Maama, da ta motsa Hajiya Madina zata ce Daughter me kike so?, menene?, ko jikin ne mu tafi asibiti?.
haka ita ma ana ta ɓangaren, motsi kaɗan Hajiya Madina zata yi ta fara tmbayarta Maama me za'ayi miki?, akwai abin da kike so?, a ranar gaba ɗaya sai take jin Hajiya Madina acan cikin zuciyarta, taji tamkar tana tare da Umminta ne.

bayan isha'i su na zaune duk ɗin su a dining za su ci abinci, Hajiya Madina ta ce ita bata jin daɗin bakinta ta ƙoshi, babu yanda Hajiya Ramla ba ta yi da ita ba but ta kasaci kwata-kwata, ciwon kan da taji ma yana damunta sosai sai ta miƙe ta koma ɗakinta, Fillo ta ɗauki flask ta bi ta.

"Daughter ya ba ki zauna cin abincin ba?".

Fillo ta ƙaraso ciki ta ajiye abincin, sannan ta kamo hannun Hajiya Madina ta ce,"don Allah Maama ki sauko kici ko kaɗan ne".

haka ta dinƙa roƙonta har sai da Maama ta sauko, da kanta ta riƙa ba ta abincin tana ci, ba ƙaramin daɗin hakan taji ba, kuma Fillo ta ƙara samun wani gurbi acikin zuciyarta, ta ƙara yin farin ciki da jin alfahari a game da dacen mata da Me Babban suna yayi.

and sosai taji daɗin hirar da Fillo take yi ma ta, sai wajen ƙarfe 9 sai ga Turaki ya shigo ɗakin, kallo ɗaya Fillo tayi masa ta ɗauke kanta, ya shigo ya zauna a gefen Maama yana kama hannunta ya riƙe.

"my happiness ya sauƙin jikin?".
Hajiya Madina ta kalle shi cike da so da ƙauna ta ce,"na ji sauƙi me babban suna, ya office?".

"masha'Allah, Allah ya ƙara miki lafiya, Zaytun ta ce min Bp ɗin ya koma normal".

"ai na faɗa maka na ji sauƙi, ɗa zu ma da kayi ta kira bacci na sa mu".
ya sauke numfashi ya ce,"insha'Allahu za ki rabu da ciwon nan Maama, ciwon nan yana takura ni da yawa".
"to Allah yasa, amma ka san girma ya riga ya kama mu, lafiyar sai a hankali, sai dai ai tayi mana adu'a ciwo ya dinƙa zuwa da sauƙi".

sai kuma ta lura da yanda Turaki ya ƙurawa Fillo ido, ita kuma kanta yana ƙasa tana matsa mata ƙafarta ta ɗaure fuska.
sai tayi murmushi tace,"Daugher ina fatan dai baku da wata matsala ko?".
Fillo tace,"ehh Maama babu".

"to Allah yayi maku albarka, ubangiji ya wanzar da zaman lafiya na har abada a tsakaninku, Allah ya kauda mugun ido akanku".
a tare suka amsa da amin.

sai ta kamo hannayensu duk ta haɗe a waje ɗaya tana cewa da Turaki,"me babban suna ina roƙonka da kar Fillo ta rasa farin ciki ko da na sakan ɗaya daga wurinka, amana na baka ita, ka kula min da ita don Allah kaji, tayi min taimakon da ba zan taɓa iya biyanta ba, thats why nake so ka raineta da zallar soyayyarka, ka mayar da ita tamkar jaririya".

ya shafo wuyansa bai iya cewa komai ba. sai ta dubi Fillo ma tace mata,"Daughter É—ago ki kalle ni karki ji kunyata".
Fillo ta kasa har sai da Hajiya Madina tasa hannu a haɓarta ta ɗago fuskarta ta ce,"yaushe za'a haifa min jika?, a yanzu banda burin da ya wuce naga jikana Daughter, so nake na ga ina wasa da jikokina, ina fatan za ki samar min su da wuri".

kunya ta kama Fillo sosai.
"Allah dai ya kawo mana na gari masu albarka". cewar Hajiya Madina.

cike da zolaya kuma ta ƙara cewa,"kyawawa nake so ki haifa min masu kama da ke fa, kar ki yarda su yi kama da Me Babban suna, shi wani lokacin kamar bai da kyau".

duk suka yi dariya ba tare da sun ce komai ba.
ta ƙara cewa,"Allah Daughter duk ranar da Me Babban suna yayi miki laifi ki zo ki faɗa min wallahi sai na rama miki, kinga haka...". Fillo ta ɗaga ido taga yacca ta kama kunnen Turaki.
"to haka zan murÉ—e shi wallahi har sai yaji a jikinsa". Fillo tayi Æ´ar dariya shi kuma ya wurga mata harara fuska a cukule.

kafin nan tace da su,"to ku tashi ku tafi ko, dare yana ƙara yi".
Fillo tayi saurin cewa,"Maama don Allah zan kwana anan".
ta faÉ—a a marairaice.

Maama tace a'a ta tashi tabi mijinta su tafi, har ƙwalla sai da tayi da suka baro wajenta, sai da suka biya ta wajen Mum suka yi ma ta sallama kafin su tafi.

a compound juyin duniya Fillo taƙi yarda Turaki ya kama hannunta, bata yarda ma sun jera ba ganin babu idon kowa, tayi gefe yay gefe, suka shiga mota ma taƙi kallonsa, sai faman ɓata rai take yi tana cin magana.

da tsokana ya ce,"kika ce ba za ki dawo gidan ba".
ta kalle shi sosai kafin ta ce,"da kayi ignoring message É—in nawa hakan ai bai sa na damu ba".

tun yana tsokanarta har ya rabu da ita saboda ganin ta ɗauka zafi, a lallai fushi take da shi kan ƙin responding messages na ta.
ya koma sai dai ya kalleta yay murmushi ya shafo wuyansa, shi ba abin da ma yake so irin ta kula shi suyi rigima, tayi kuka ko tayi masa tsiwarta.

motar tayi shiru ba abin da kake ji yana tashi sai busawar ac da kuma sautin waƙar i miss you ta Beverley craven.

_here in a silence i wait, there is nothing else i can do, it feels like my heart gonna break, and all i can think of is you, and how my aching arms long to hold you, and show you how much i care, but i'm couting the hours without you, and i don't know how much i can bear, becox i miss you morethan word can say, all i need you here in my life always, yeah i miss you, till you are back with me._

waƙar ta dinga bin gaɓoɓin jikin Fillo tana ratsata, ta kalle shi ta wutsiyar ido taga ya wani sha murr kaman ba shi ke tsokanarta ɗa zu ba fuskarsa a washe da annuri, wanda ta tabbatar na jin daɗin ganinta ne.
sai ta ɗan murguɗa baki kamar yana kallonta kafin ta kai hannu ta kashe waƙar, tana ɗauke hannu yana ƙara kunnawa, zata ƙara kashewa taji muryarsa a tamke yace,"ranki zai ɓaci".

"to bana son jin waƙar ni".
yay mata wani kallo yace,"motarki ko tawa?".
ta haÉ—e gira tace,"ba yanzu aka gama baka amanta ba, aka ce kayi min duk abin da nake so".

murmushi ya suɓuce a leɓensa, ya tuna alƙawarin da yaywa Maama na kula da Fillo tun ba'a ranar yau ba, ya tuna girman alƙawari, sai ya kai hannu ya kashe waƙar.

sai ya koma yi da kansa, Fillo taji waƙar tafi daɗi sosai a bakinsa, sai ka rantse shi ya raira, ta lumshe ido tana ta sauraronsa, har su ka zo gida bata sa ni ba sai da ya danna horn da ƙarfi sannan ta buɗe ido.

"a sauka a miƙo kuɗin mota".
ya faɗa a sanda take ƙoƙarin buɗe ƙofa zata fita.
ta juyo ta É—an kalle shi tace,"in doller or in naira?".
"in doller".
ta gyaÉ—a kai kafin tace,"to driver you wait for me".

Turaki ya buÉ—e baki galala, zai kamota tayi saurin ficewa tana dariya, shi ma ya fito ya bi bayanta da sauri don ba ya so ta riga sa hawa upstairs becx akwai suprising É—inta da yake so yayi.

a parlo ya sameta su na gaisawa da su Sakina, waɗanda suke kallo a parlo, su na yi mata sannu da zuwa, ita kuma tana ba su haƙurin tafiyar da tayi bata sanar musu ba.
bai ko amsa gaisuwar da su Hannatu su ke masa ba ya kama hannun Fillo su ka É—auki hanyar upstairs, a steps na uku da su ka taka yasa hannu ya rufe ma ta ido.

ta san duk neman hanyar su shirya ne don haka sai taƙi kula shi har sanda taji ya buɗe ƙofar ɗaki sun shiga.
ƙafafunta suka lume cikin marbles, da sanyin ac'n da ke ratsawa ta ko'ina acikin ɗakin, kafin daddaɗan ƙamshin nan nasa dake motsa zuciyarta ya shiga hancinta, taji san da ya maida ƙofar ya rufe, kafin ya sauke hannunsa a hankali daga idonta ya mayar kan ɗan ƙaramin ƙugunta, tare da ɗora haɓarsa a saman ƙafaɗarta.

"suprise". hakan ya faÉ—a before ta shiga buÉ—e idanunta a hankali.
ba ta san lokacin da ta buɗe idanuwanta duka ba, laɓɓanta suka tale kafin bakinta ya buɗe, fuskarta kuma ta bayyana wani irin farin ciki da jin daɗi.

ƙananun bulbs ɗin dake haskawa zuwa different colours of light su suka fara shiga idonta, kafin baloons ɗin da akai design da heart shape ta ɗauki hankalinta, zuciyarta kuma taji ta motsa da zafin ƙauna a lokacin da ta ɗora ido akan flowers ɗin da aka baza akan gado.

gaba É—aya sai ta kasa magana balle motsi saboda yacca abin ya burgeta, sai ta fara bin kowacce kusurwa ta É—akin da kallo, ta san É—akin, wan nan É—akin ne da suke rayuwa ita da Turaki a cikinsa, kuma wan nan lafiyayyan gadon me É—auke da flowers, gadon su ne me É—auke da katifar nan me bala'in taushi da suke kwanciya akai manne da juna, but ta ya akayi yau ya sauya?, azababben decoration É—in da aka yi masa ya mayar da shi tamkar ba wannan É—akin da suke yini acikinsa ba.

_me hakan yake nufi?._ tambayar da zuciyarta tayi kenan, kuma sai taji hannayen Turaki sun kama fuskarta sun karkartar da ita zuwa gaban body mirrow dake gefe ɗaya, ƙwayar idonta ta tsaya cak akan ballon numbers ɗin da aka jera me ɗauke da 1 and 9 making 19, a hankali kuma idonta ya sauka akan ƙaton cake ɗin dake kewaye da candles.

muryar Turaki tayi whispering acikin kunnenta da faÉ—in,"Happy Birthday to you Fulani Nah".
she was just astonished, ta juyo ta fuskance shi tana faÉ—in,"my birthday?".

ya jijjaga ma ta kai alamar ehh. with great joy tace,"but how do you know Turaki?, i don't think there is anyone who knows my birthday date".

ya ce,"har Ummi?".
tayi ɗan shiru tsananin farin cikinta na kasa ɓoyuwa ta ɗaga masa kai.
Chapter 151 · 0% Book details