← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 176

Sashe 159

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Antyn Kano ta gyara zama tana duban Fillo, ta kama haɓa ta riƙe cikin izgili ta ce,"shegiya kuma?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ashe abun har haka yayi muni, yanzu tsakani da Allah ina gamin haɗi tsakanin tsarkakke da gurɓatacce, shege ai sai ɗan uwansa shege, gaskiya wallahi an zalunci yaron nan, ko da yake aikin asiri babu abin da ba yayi.
to ni su Mai Martaba ma mene na haÉ—a Ilham kishi da Æ´ar gaba da fatiha?. kai talaka dai akwai zubarwa da kai mutunci, da zarar an ce an rasa cin na yau da na gobe shikenan sai kiga an faÉ—a harkar karuwanci kuma. Allah dai ya kyauta yasa kar a haifi iri".

tun a zancen farko zuciyar Fillo ta buga da ƙarfin gaske, ranta ya ɓaci sosai.
a yanzu da Antyn Kano tayi magana ta ɗago da kanta tana kallon su, lokaci ɗaya idanuwanta suka cika taf da ƙwalla.

Mama Asabe ta sake cewa,"um to mu yi dai abin da ya kawo mu".
ta kai dubanta ga Fillo ta ce,"ga shi ba sanin sunanki muka yi ba, to ma dai in aka kira ki da shegiya ai ba'ai lefi ba sunan yanka ne irin naku na haihuwar kan titi. allura muka zo ki bamu idan kina da ita za'a cire sartse".

a lokacin zazzafar ƙwallar da ke cikin kurmin idanun Fillo su ka gangaro saman kumatunta, wani irin baƙin ciki ya turnuƙeta, jin zuciyarta take yi kamar zata yi bindiga.
she can't stay any more ana cin mutuncinta da na iyayenta. in ba haka ba za'a iya kaiwa gaɓar da wataƙila zaman aurenta ya ƙare yau a gidan nan.

taji yo maganarsu su na ƙara faɗin,"ai Ilham ma tafi ƙarfin kishi da wannan wallahi, ta maishe da shegiya ƴar aiki kawai".

cikin raɗaɗin zuciya Fillo ta miƙe zata bar wajen.
Hajiya Zaliha ta dakatar da ita da faÉ—in,"ke figaggiyar kaza dama ba ki da tarbiyya, ina allurar da muka ce ki ba mu?, saboda kin mayar mu Æ´an iska za ka kaÉ—a kai ki wuce ba ki ko tanka mana ba".

Fillo ta runtse idanuwanta, ji take yi kamar ta tanka musu, kamar ta faɗa musu maganar da har mutuwa ba za su manta da ita ba, ta ci musu mutunci irin wanda ba za su ƙara sha'awar zuwa gidan nan ba har a tashi duniya, duk kuwa da cewar sun ajiye ƴa acikinsa.
but ɗayan ɓarin zuciyarta sai ya haneta hakan, ba halinta ba ne, ba tarbiyar da aka bata ba kenan, tayi banza da su da maganar da suke yi ta haye sama tana goge hawaye.

ba ta shiga É—akinta ba sai da ta daidaita nutsuwarta tukunna, gudun kar Maijidda ta fahimci abin da ya faru.
ko da ta shiga ba ta kalli in da Maijidda ke zaune ba tayi saurin shiga toilet ta wanko fuskarta, tana fitowa sai ga Hannatu ta shigo ɗakin, ta durƙusa tana faɗin,"Anty baƙi a ƙasa sun ce ki ba su allura".

ta dafa kafaɗar Hannatu suka fita, su na tsaye ta wuce kitchen ta fito, ta tsaya tare da musu kallon banza kafin ta buɗi ba ki ta ce,"ban da zubar da mutunci ina ku ina aron abu?, anyway matar so bata da kayan faci a ɓangarenta balle tayi ajiyar wata allura".

tana faÉ—ar hakan ta haye sama abin ta, fiye da haka ta so ta faÉ—a musu, to gudun tashin hankali yasa ta rabu da su kawai.
ko da ta koma É—aki bata bari Maijidda ta fahimci komai ba, ta zauna suka cigaba da hira.

"kin san Allah da tafiyata zan yi. ni kin san ba son ƴan aikin nan nake ba balle in zauna muyi hira da su. yanzu dai ina zamu je ƙunshin?".

"to ai ma Maama tace wadda ta yiwa su Adda Zaytuna ita ce zata yi min, yanzu wurin saloon kawai zan je, mu bari sai da yamma ma je ko?".

Maijidda tace,"a'a kin san halin lalle da cin lokaci, mu fara zuwa saloon É—in tukunna".

"to shikenan. bari naje na faÉ—a masa. kin san nace miki ina son zuwa gidan Yaya Yusuf, shi ne fa yau na buga musu sammako".
ta yaye mayafin jikinta ta ajiye sannan ta fito ta nufi ɗakin Turaki, yana zaune kan kujera yana operating laptop, hannunsa riƙe da ƙaramin glass cup yana kurɓan coffee.

yaji shigowartata amma bai ko É—ago ya kalli wurin da take ba, sai dai yayi mamakin ganinta É—in, dan rabonta da É—akinsa tun ranar da ya faÉ—a mata cewar zai dawo da Ilham, yau kusan kwana tara kenan.
ko abinci idan ta gama a parlo take barinsa, ta ci nata ta bar masa nasa, ruwansa ne yaci ruwansa ne kar ya ci, yacca ya lura ma kamar girkin ma ba yi take ba sai dai Æ´an aiki su yi, shiyasa shi ma baya shigowa sai yaci abinci a gidan su ko gidan su Bello.

a ciki ya amsa sallamar da yaji tayi, ta ƙasan idonsa yake kallonta, tana tsaye daga jikin madubi ta maƙale, fuska sam babu annuri.
yacca take fushi da shi haka shi ma yake fushi da ita, ranar da ya faɗa mata zai mayar da aure ta ƙona masa rai, yanda ta nuna ko kishinsa ba ta yi, irin ma ba sonsa take ba, kawai da ya faɗa mata ta kalle shi da fara'arta tace Allah ya sanya alkhairi, daga nan taci gaba da harkokin gabanta tamkar ba wadda kishiyarta zata dawo ba, shi kuma wannan nuna rashin kishin nasa ya ba shi haushi har ya ɗauki fushi da ita, kuma ganin bata bi ta kan fushin nasa ba ya ƙara hawa sama.

ita kam tun da tayi masa kallo É—aya ta É—auke kanta, ba komai take tunawa ba sai ranar da ya sameta a É—aki tana kuka.
ba kamar yacca ya tsammaci kukan nata ba, kuka take yi akan ciwon mara da ya matsa mata kwana biyu, amma buɗar bakinsa a lokacin ce mata yay,"ya fi miki ki koyawa zuciyarki haƙuri da son zama da kishiya akan wannan kukan da kike yi mara amfani, domin kuwa dawo da matata babu fashi, Allah ya halasta min na zauna da irinki har guda huɗu, balle kuma matar da na fara zama da ita kafin ke, ki san da wannan".

idonsa kawai ta kalla a lokacin ta san ya faɗa mata hakanne saboda kawai ya ƙuntata mata.
ita sai a yanzu ta yarda da batun sauyawar da maza suke yi idan zasu ƙara aure, duk da bata ga yana wani rawar ƙafa ba amma ya sauya fiye da tunaninta, magana wannan bata haɗa su acikin gidan, kuma ba nata laifin bane, nasa ne, don ita ko kaɗan bata ma bari kishinta ya fito ƙarara ba yacca zai gane, tun tana ɗora hakan akan tilasta masa ɗin da akayi har ta daina, ta fahimci zallar bura'uba ce kawai irin ta ɗa namiji, don sosai ya tsiri wa su halaye da bata sansa da su ba, ko zata narke tana masa magana baya tanka mata, ban da jiya da yaci zarafinta.

"Jannaty..."
ta kira sunansa a hankali, taji ta gaza ƙarashe abin da zata faɗa saboda kukan baƙin ciki da ya taso mata.
Turaki yay banza da ita kamar bai ji kiran da tayi masa ba, sai dai still bai bar kallonta ta ƙasan ido ba, yana duban kumbararrun idanuwanta, ga wanda bai sani ba zai ce ciwon ido take yi, but to him da yasan kayarsa ya san uban kuka taci ta ƙoshi har ta godewa Allah.

sai ya É—auke kansa ya sauke ajiyar zuciya, kamar ba zai bi ta kanta ba, sai kuma ya É—an ji tausayinta a ransa, ya maido da dubansa gareta sannan yace,"ke ba kya gajiya da kuka ne, kin shigo min É—aki kin min tsaye sai wani faman cin magani kike kina faman É—aga hanci".
Ya ida maganar yana yi mata kallon sama da ƙasa.

Cikin sanyin murya ta ce masa,"don Allah kayi haƙuri ka bar ni in yi lallen".

ya tamke murya ya ce,"na ce ba za'ai ba".

"to ya zan yi da Maama fa?, ita fa ta ban umarni akan in je ayi min".

yay ɗan jim kafin ya ce,"fita ne daga gidan nan zuwa gidan mu ba za kiyi shi ba, idan me lallan zata zo nan tayi miki ta zo, idan ba zata zo ba ki haƙura".

ta haɗiye ƙullun abu a maƙogoronta na takaici, ta sunkuyar da kanta ta ƙara cewa,"don Allah ka bar ni in koma gidan ku in zauna har a gama biki, don Allah don Annabi".

É—ago kansa yay ya bita da kallo, duk tayi sanyi sosai kamar mara lafiya. nazartar yanayinta ya shiga yi, so yake ya gano dalilinta na dagewa akan sai ta koma gidan su har an gama biki sannan ta dawo.
yaga ta ƙara kawar da kai gefe tana goge hawaye.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce,"matsayina na mijinki wanda aljannar ki ke ƙarƙashin ƙafata, ina me ba ki umarnin ko nan da parlo kar ki bari ayau, har sai an kawo abokiyar zamanki tukunna".
yay maganar cikin muryar ba da umarni.

ta dube shi a sanyaye,"yan zu ba zan iya cin alfarmar Maama ba?".
tayi maganar cikin wani irin rauni.

yan da bai tanka mata ba haka itama bata ƙata cewa komai ba ta fita.
tana fita ya ɗauki waya ya kira Maama yace mata wai sun fita ita da shi sai zuwa yamma za su dawo, a faɗawa me ƙunshin sai gobe ayi.

ƙarfe bakwai na dare aka kawo Ilham, sai da aka fara kaita gidan su Turaki sannan aka yo da ita gidanta.
lokacin da Fillo ta jiyo guɗa sai da zuciyarta tayi wani mugun matsewa, yunwa take ji a lokacin ta ɗauko abinci zata ci, amma lokaci ɗaya taji ta ƙoshi, bata buƙatar komai a wannan lokacin sama da tayi kuka.
Chapter 159 · 0% Book details