Sashe 29
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya ƙara kallonta a karo na babu adadi yana jin zuciyarsa na tsinkewa, ya cine fuska ya wani daki stearing da mugun ƙarfi, kamar ya fasa ihu haka yake ji. shi amsar ma da yake so ya sani wai me ma ya fitar Hammansu a wannan salasainin daren?, shin ba ya shiga bedroom ɗinsa yayi masa gud night ba, ya tarar kuma lokacin har ya fara bacci.
ya sauke numfashi yana barin kallonsa ga tuƙin da yake, a hankali yace da ita. "Maama dan zatin Allah kiyi shiru ki daina wannan kukan, wallahi yana ɗaga min hankali, stearing nan nema yake fa ya ƙwace a hannuna".
tasa gefen hinabinta ta goge hawayent tana so ta tsayar da kukan. ta É—ago ta kalle shi idanuwanta duk sunyi jawur sun yi girma. cikin sanyin murya kuma a raunane tace da shi,"to ka kira min Baffan naku".
ya rufe idonsa ya buÉ—e ya sauke agabansa, da zafin nama ya kaucewa bishiryar daya kusa duka. ya furta subhanalla sannan yace,"Maama na faÉ—a miki insha'Allahu babu wani abu da zai sami Hammah, shima nasan bige mutum É—in da yay ne yasa ya rikice har yake faÉ—a miki bai san a inda yake ba...".
ta katse shi da cewar,"ni dai idan ba zaka kira min Baffan ba to ka faÉ—a min, sai na sauka na nemi masu waya su ara min".
yace,"to me za kice masa?".
ta ɗan kalle shi yana mata abu kamar ba ɗanta ba, sai tayi shiru bata ce masa komai ba. shima shirun yayi, can ta ƙara cewar,"yanzu dai ba zanci arziƙin wayar taka ba Khalill?".
buɗar bakinsa yace mata,"kina so ki rasa mijinki ne?". ta girgiza kai da sauri. "to ki haƙura da wannan kiran dan baida amfani, kin san dai Baffa ya fiki shiga tashin hankalin akan lamarin daya shafi ƴaƴansa, yanzu idan kika faɗa masa ya yanke jiki ya faɗi a inda yake fa?, kin san dai yanda ba kya kusa da shi ɗin nan anything can happen. so kiyi haƙuri har mu ƙarasa ai mun kusa zuwa, na kira mijin Inna Falmata yace ga police nan da ambulance zasu biyo mu a baya, dan Allah Maama kiyi haƙuri kita adu'a kawai kinji uwa ta gari".
ta gyaɗa masa kai kawai tukunna tace,"to amma baka sauri ka ƙara speed". yace,"to Hajiya Maama yanzu kam za kiga mun isa...ai wurin ba wata tafiya me nisa bane".
tana kallonsa tace,"Yabayo fa Khalil". yace,"can É—in fa, yanzu za kiga munje Maamancy, situation É—in da kike ciki ne fa yasa ki ganin nisa".
ta kuma gyaÉ—a kai bata ce komai ba, taci gaba da tasbihin da take yi.
a wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke ya kwantar da kansa jikin kujerar, abinda zai iya faruwa da shi dalilin accident É—in nan ba shine damuwarsa ba, ran yarinyar kawai yake ji, baya so ta mutu, idan ta mutu bai san wanne hali iyayenta zasu shiga ba.
ya buÉ—e idanuwansa a hankali ya sauke su akan titin da duhun dare yasa ba'a iya hangen komai. yaji wani abu da bai san menene shi ba ya tsarga masa. ya juya baya yana kallon yarinyar, har yanzu zuciyarsa faÉ—a masa take da gawa yake tare, ta riga ta mutu, irin jinin da ta zubar ba zai barta ta rayu ba.
ya miƙa hannu ya ruƙo nata wanda yayi sanyi kamar ƙanƙanra, hakan ya wanzar da wani abu wai shi tsoro a zuciyar Turaki da bai taɓa ji ba tunda ya girma, babu wata shakka ta riga ta mutu yasan da wannan, shikenan haƙƙin rai ya hau kansa.
idanunsa ya kulle ya bawa kujerar duka yana jin kamar ya saka kuka. me ya yiwa rayuwa ne da take neman tayi masa ɗaurin goro, yana ƙoƙarin buɗe nauyayyun idanuwansa yaji an buɗe ƙofar motar, mamakinsa ɗaya ne ta ya aka buɗe ƙofar bayan yasa lock?, wa ya buɗe?, yasan dai 10minutes bata isa ta kawo su Maama wurin nan ba, duk da he dont have comfirmation of where he is, amma yasan ko ina ne nan da nisa yake.
kuma kafin yay wani yunƙurin juyo da kansa ga ƙofar sai yaji an daki wuyansa, duka bana wasa ba, irin dukan nan da zai yiwa jijiyar wuya lahani, ya rumtse ido saboda tsananin azabar daya ratsa dukka ilahirin jikinsa.
tabbas no any doubt wani ne zai yi attacking nasa, but wanene wannan?, and how comes aka san da wanzuwarsa a wannan dajin?.
Allah ya sa ni a situation ɗin nan da yake ciki ba shi da courage ɗin da zai iya encountering ko waye da faɗa don ganin ya ƙwaci kansa.
inda ace ba'a irin wannan halin yake ciki ba, da ace baya cikin fargaba da taraddadin mutuwar wadda ya kaɗe, to zai yi fighting da koma waye dan ganin ba'a cutar da shi ba, zai ƙwaci kansa ta ƙarfi even if ace 1% chance yake da shi, and he most win saboda ba zai taɓa bari yayi failing ba wajen kuɓutar da rayuwarsa, not becouse of burin da yake so ya cimma a rayuwa ko kuma saboda baya son mutuwa da wuri, no!, its just becouse of his Mom, Maama na buƙatarsa a raye, idan ya mutu ya barta bai san ina zata saka kanta ba, ya riga ya sani her only hope and wish is su rayu tare da shi.
but still bai karaya ba haka yasa hannuwansa biyu ya riƙe hannun wanda ke son shaƙe masa wuya, sai dai inaaa girman mutumin ya shallake tunaninsa, ko ace da kuzarinsa ba zai iya gwada jiki da shi ba.
haka yana ji ƙaton mutumin ya shaƙesa da iyaka ƙarfin da numfashinsa zai ɗauke gaba ɗaya, kuma take yaji yana neman shaƙar iska ya rasa, saboda haka kawai sai ya sare ya sallama.
yana jin mutumin na magana da wasu ta waje amma bai san me suke cewa ba, sama-sama yake jinsu. so yake yaji muryoyinsu, so yake yaji ko da kalma É—aya ce tak ta abinda suke faÉ—a, ta yanda ko da Allah yasa yayi surviving zai iya samun hanyar da zai kama su.
daƙiƙa 1,2,3 ta wuce mutanen suna magana, kuma har lokacin jibgegen mutumin na shaƙe da wuyan turaki da hannu ɗaya, ɗayan kuma ya toshe masa baki da hanci, a taƙaice dai babu ta inda iska ke samun shiga lungs na Turaki.
yana ji aka buɗe ƙofar baya, ya hangi siririn mutum ta cikin mirrow ya duƙa akan yarinyar, bai san waye ba dan baiga fuskarsa ba. har yanzu mutanen magana suke da junansu, kuma har yanzu ya kasa jin komai da suke cewa, ya rufe idonsa yana kokawa da cikinsa dake so ya fitar da iska. ƙirjinsa yake jin yana yi masa zafi, ji yake kamar zai mutu, fatansa ɗaya ne a lokacin, kar ya mutu a lokacin sai a hannun Maama, so yake ya mutu yana kallon fuskarta.
wasu adadin sakanni suka wuce ta cikin kansa, a lokacin da ya gama saddaƙar da tafiyarsa lahira, a lokacin ne yaji words guda 22 sun shiga cikin kunnensa, kalmomin da suka fito daga bakin siririn mutumin dake riƙe da hannun yarinyar da ya kaɗe.
_"yarinyar nan zata yi mana amfani, da sauran ranta. ni ko da ta mutu ma ina sonta a hakan, dole ne zan moreta saboda na kwaÉ—aitu da ita"._
furucin da mutumin yayi kenan, kuma furucin da ya sami nasarar shiga cikin kunnen Turaki har ya zarce zuwa cikin zuciyarsa ya dunƙule a waje ɗaya.
ƙarfi da kuzarin da Turaki yake jin ya rasa na ƙwatar kansa shine yazo masa acikin giftawar sakan ɗaya, wasu manyan jijiyo suka bayyana a hannayensa da goshinsa, tamkar idonsa akan siririn mutumin yake, kuma kamar yasan abinda yake shirin aikatawa, dan haka kawai zura hannunsa yayi ta baya ya damƙi hannun mutumin wanda yake shirin ɗaukar yarinyar, sannan yasa ɗaya hannun nasa yana ƙoƙarin ya cire hannun ƙaton daga bakinsa.
damƙar da Turaki ya yiwa siririn mutumin ta shiga ratsa jikinsa, mutumin ya ɗaga murya wajen cewa wanda ke riƙe da Turaki"gayen nan fa bai suma ba, ya riƙe min hannu kuma kamar ba zan iya ƙwacewa ba, bugawa shege bindiga akai".
da maganar da yay, da ɗauko bindigar da ƙaton yayi, da samun nasarar da Turaki yay na cire hannun mutumin daga bakinsa, suka haɗe lokaci ɗaya da ƙarar jiniyar motar ƴan sanda dake tashi daga can nesa.
babu shiri ƙaton mutumin ya saki Turaki ya falla da gudu zuwa motarsu, shima siririn ya fizge daga hannun Turaki ya falla zuwa motar, ashe basu biyu bane kawai, suna da yawa, kamin Turaki ya zuro ƙafarsa daga cikin motar ya fito tuni sun bar wajen sai tashin ƙurar motarsu.
tsayawa yayi yana bin bayan motar da kallo, so yake yaga lambar motar ko zai samu wata shaida amma duhun dake cikin idonsa ya hana. can kuma tunaninsa ya dawo kan yarinyar, dan haka da sauri ya buɗe bayan motar, ganinta yasa shi sauke ajiyar zuciya. ya shiga tattaɓata yana jin kamar ko sunyi mata wani abu ne.
ji yake ba zai iya cigaba da jira ba, barin wajen zai yi, idan shi ya cutu ba komai ba ne, amma baya so wani abu makamancin wanda sheɗanin can ke faɗa ya faru da yarinyar, dan haka cikin azama ya koma seat ɗin driver zai tashi motar, dai-dai nan kuma motar Khalil ta ƙaraso wajen, motar police na biye da su a baya, yayin da abulance ke bin bayan ta police ɗin.