← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 176

Sashe 10

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amir dai dubanta yake da mamaki, ita ba aljanu ba amma kusan sati biyu kenan da ta ke ciwon nan ta kafe akan ita dai a kira Malami yay mata karatu, ba maganin asibiti bane maganin ciwon da ke damunta.
kuma anyi anyi ta faɗa me ta ke ji tace ita babu komai zazzaɓi ne kawai. Asibiti kuma a duka test ɗin da suka mata sun ce ma babu maleria.

Cikin kwantar da murya yace,"insha'Allahu kin daina shan maganin, amma ki bar kukan gaba É—aya hakan kawai zai sa na kira Malam yay miki adu'a".

Ta É—an kafe shi da ido tana tunani cikin ranta, maganarsa da ta kutso cikin kanta ta katse abunda ta ke tunani.

"amma tun da nima kusan Malamin ne nayi maki adu'an ko Halimatu nah?".

Kai kawai ta gyaɗa masa, ta sani ɗin in har ba'a kira Amir Babban Malami ba to ba za'a kira shi ƙarami ba, Babansa Malami kai kafatanin gidansu ma, kwatancen gidansu ma idan za'ai gidan malamai ake cewa, kuma kusan shi ya gado mahaifinsa 100% cikin yara 28 da Allah ya ba shi.

Ya taso ya matso kusa da ita, ya bar tazaran inches tsakaninsu. "me da me kike ji?".

Ya tambayeta yana kai hannunsa ya taɓa goshinta. Sai ta rufe ido tana jan numfashi, so ta ke ta tambaye shi abin da Kaka taƙi amsa ma ta, ta tambaye shi makomar wanda ya ƙona asirin da ba nasa ba, kuma so ta ke ta yi musu bayanin ta ƙona asiri, ko ta samu ta waraka daga wannan masifar da ta jawa kanta.

to amma ta ya?, ta ina zata fara?, da wanne irin bayani zata faɗa musu?, wacce fahimta zasu yi ma ta?, shin zama su yarda da ita ne?. Bama zata soma wannan katoɓarar ba, saboda idan Kaka ta fahimceta ba lallai Amir ya fahimta ba, kuma wataƙila idan wani yaji ta ɗaure kanta akan cewar ita ke da niyyar masa asirin.

Ita dai ta sa ni ko meke damunta a halin da take ciki yanzu yana da nasaba da ƙona asirin da tayi, ba zata iya tantance irin mummunar halittar da ta ke gani cikin mafarkinta ba, ita tayi hakan bisa tausayi da kuma son taimakawa wanda ake son cutarwa, to amma kuma shikenan daga taimako?.

Sai kawai ta rumtse idonta sosai, tabbas ba Muhammad Turaki kaÉ—ai ba da akayi asirin saboda shi, tun daga kan wanda tunanin yin asirin yazo kansa, da mai zuwa ya amso asirin, da masu zuwa suyi aikin asirin, duka sun shiga uku, rubuce yake a tafin hannunta sai taci uwar uban duk wanda yay sanadin shigarta wannan mawuyacin halin.

"ya kike jin ciwon kan?".
Amir ya tambaya with a look of concern and sympathy.

Ta haÉ—iye abun da ba zata kira shi da yawu ba, sannan ta buÉ—e ido ta kalle shi.

"ina jin kan kamar ba nawa ba, kamar ma ba na mutane ba".

Ya sauke numfashi kamin yace,"sannu".
ita kuma ta gyaÉ—a masa kai kawai.

Nan Amir ya kama kan nata ya shiga karanto adu'oi yana tofa mata, tsawon mintuna yana yin hakan kamin ya tsaya. Sannan ya miƙe ya ɗauko ruwan faro da yake siyo mata yanzu ya buɗe sabo ya tofa adu'ao aciki ya bata tasha, kana ya rufe ya aje mata sauran a kusa da ita.

Fillo ta rufe idonta ta jinginar da kanta ajikin bango, her breathing slows down, abu kamar almara sai taji ciwon kan da ya addabeta tsawon sati biyu ya fara tafiya, har ma tana neman ta rasa shi gaba ɗaya. Hatta wannan nauyin da jikinta yay shima ya fara saki, to 10minutes sai taji komai yayi sauƙi kamar ba ita ba.

Maijidda tayi sallama cikin ɗakin daidai da buɗe idon Fillo, ta ajiye ƙwaryar furar tana zama kusa da Fillon.

"sannu". Tace da ita kamin ta juya gun Amir tace mishi,"sannu da zaman jinya Amir".

Yay murmushi kaÉ—an sannan yace,"yauwa Kuluwa".

Ya faɗa da zola dan bata son sunan, tace,"ni dai daga yau idan ka ƙara kirana da wannan sunan sai na rushe gwamnatin da ka kafa a zuciyar ƙawata".

"yaushe kika yi wannan isar?".

Yay tambayar yana kallon inda Fillo ta ke, wadda ta samu relief a yanzu, dan har idanuwanta sun yi tangarau, tana kallonsu ne kawai bata cewa komai.

Maijidda tace,"ka dai bi a hankali kawai, ita masoyiyar taka ai tasan girman isar da nake da ita".

"ah lallai ne mai girma Kuluwa". Suka yi gajeriyar dariya su duka.

Amir yace da Fillo,"ya kike ji yanzu?".

Idonta akan ledar magungunan da ke can bayansa tace,"idan ka tashi tafiya ka tafi da waccan ledar ka jefar a bola".

ya waro ido waje yace,"haka likitan ya karanta mana dama?".

ta ɓata rai tace,"koma me ya karanta ni dai a zubar da su kawai, ai naji sauƙin".

Maijidda tace,"ai sai ki bari idan Kaka tazo kyayi mata wannan bayanin".

Sai kawai Fillo tayi narai-narai da idanuwa, fuskar nan a marairaice tana duban Amir kaɗan tace,"dan Allah Amir...wallah idan Kaka tazo ba zata bari a zubar ba, ni kuma naji sauƙi".

Tana yin shiru ya É—auki ledar ya saka a aljihunsa yana faÉ—in,"yanda kika ce ranki ya daÉ—e".

Wayarsa tayi ƙara ya ɗauka, ƙaramar waya ce ba wata babba ba, yayi shiru yana sauraron maganar cikin wayar kamin yace,"tom shikenan Bandirawo ina kan hanya insha'Allah".

ya ƙara yin shiru for seconds kan yace,"ahh mai jiki da sauƙi, yanzu haka ma ina wurinta".

"tom zata ji insha'Allah, mun gode".

Ya katse wayar ba tare daya dubi Fillo ba yace,"Bandirawo ne, yana yi miki sannu da jiki".

Tace,"ina amsawa".

Sannan ya miƙe yana roƙonta akan ta daure taci abinci, gyaɗa kawai tayi, ta yunƙura itama zata miƙe dan yi masa rakiya yace a'a ta koma ta zauna.

Zuciyarta na harbawa da soyayyarsa ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, cikin sanyayyan muryarta da ciwo yaywa lahani tace,"na gode".

Ƙwayar idonsa akanta da tsananin shauƙinta yace,"da me?".

Still idonta kan yatsunta tace,"ni dai kawai na gode, Allah ya bada lada".

Ya sauke numfashi yace,"amin". Sannan ya nufi ƙofa, ita kuma tana ce masa ya gaida su Inna.

Bayan fitarsa Maijidda tace,"ke kam Fillo kin more da mijin aure, Amir mutumin kirki ne, ki ga fa tun da kika kwanta yake sunturi akanki".

Fillo dai bata ce mata komai ba, don ita tunaninta ma na wani waje can na daban.

Dogon tsakin da Fillo taja na takaici shi yasa Maijidda saurin kallonta da mamaki. "shi kuma tsakin fa?".

Fillo tayi shiru tana jin wani ɗaci a cikin ranta, tunda tazo gidan nan bata taɓa shiga ɓangaren masu gida ba, kai hasali ba matar gidan ma bata taɓa ganinta ba balle ƴaƴanta, idan aka cire wadda tazo ranar nan ta kawo musu kwancen kaya, abunda kawai ta san bakin kowa na faɗa shine Uwar ɗakinmu Hajiya Madina.

Amma haka kawai ta ke jin bata son mutanen gidan, dan ta ra'ayinta da tuni sun bar aiki sun koma wani wajen to dan Kaka taƙi ne.

To dan me yasa ma ba zata ji zaman gidan ya fice akanta ba yanzu?, sanadin fa taimakon ɗansu ta shiga halin da ta shiga. sannan again tana kwance cikin wannan halin sun zo sun ɗauke mata Kaka sun mayar da ita aiki ɓangarensu, aikin da idan ta fita tun safe sai dare zata shigo, ta lura sam bata samun hutu da can ɗin.

Akan me ma zuciyarta zata so matar gidan?, tuwo ne a idonta da ta kasa ganin girman tsufan Kaka da har suke loda mata uban aikin da zai gajiyar da ita. Ko da yake in aka ce baka da shi dama shikenan taka ƙararriya ce, talaka dai na ganin rayuwa.

"salamu alaikum". Maijidda ce ta amsa sallamar da aka yi daga ƙofar ɗakin, Fillo kuwa a ciki ta amsa, sai bin ƙofar ɗakin da tayi da ido.

Wata tsohuwar mata ta leƙo kai cikin ɗakin tana kiran sunan Kaka. Maijidda tace,"ki shigo bata nan".

Ta shigo ɗakin tana faɗin,"bata nan?, ina lafiya dai ko?, kwana biyu banga gimlawarta ba acikin ɓangaren nan".

"lafiya lau, ta koma cikin gida da aiki ne shiyasa".
Maijidda ta bata amsa.

Ta ƙara cewa,"Allah sarki shi yasa ashe, ni fa naga kwana biyu bana ganinta a wurin aiki. Kuma da yake ta saba leƙowa a gaisa ko da ba ranar aikinsu ba shi yasa ma nace bari na leƙo naga ko ba lafiya ba".

Maijidda ta ƙara cewa,"lafiya lau, idan ta tafi ne bata shigowa sai dare".

Matar tace,"to kwa sanar mata na nazo idan ta dawo, kuma kuce ina yi mata barka an samu ci gaba".

"to insha'Allahu za'a faÉ—a mata". Yanzu ma dai Maijidda ce ta amsa, dan Fillo ma babu alamar zata yi magana.

Matar har zata fita sai ta dawo tana cewa,"kinga na manta fa ashe Fillo babu lafiya, kusan ni É—aya ce ban shigo dubata da jiki ba".

Ta kalla Fillo da ke kumbure ta haɗe gira duka biyu tace,"ya sauƙin jikin naki Fillo?".

Ba don taso amsawa ba tace,"naji sauƙi".

tace,"to Allah ya ƙara lafiya...sai anjimaku".

Da haka ta fice tana fita Fillo taja uban tsaki tace,"har ga Allah haushin komawar Kaka aiki cikin gida nake, gaba ɗaya an riƙeta da aiki ba'a barinta ta huta. su ko tausayinta ma basa ji, ko ba su da tsohuwa ne oho?, tun fa da ta fara aikin nan idan ta fita da safe bana ƙara ganinta sai wata safen, dan kamin ta shigo nayi bacci, jiya har kusan goma da rabi bata shigo ba...jiya da ta dawo ina ganinta tana miƙa tsabar gajiya, kawai don bana cikin hayyacina ne amma da sai naje gidan nace su sallamemu".

Ta gama ƙorafinta cikin masifa, Maijidda dai bata ce ma ta komai ba, sai ma ƙwaryar furar da ta janyo tana sha.

ruwan hawaye ya kawo idon Fillo, muryar in breaking tace,"ni ban san ba ko basu ga yanda Kaka ta tsufa ba ne...amma me suka É—auki kansu?".

Maijidda tace,"masu kuɗi mana. kuma dai ba za ki ce su na sahun masu kuɗi marasa kirki ba. za ki so kanki ta wannan ɓangaren in kika faɗi haka...ke dai ki yiwa Kaka adu'a kawai, banda ke sanin kanki ne ba zata juri wannan bautar ba tunda ta tsufa da yawa".
Chapter 10 · 0% Book details