← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 176

Sashe 66

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya ƙara hasko lokacin da yasa hannu a aljihunsa dan ɗauko kuɗi, amma sai yaji babu komai. sai ya ƙara kallon Hayyo wanda ya gano tsananin kama ta Fullo a tare da shi, ya sauke numfashi yana me jin wani iri a ransa, zuciyarsa na ƙara ƙarfafa masa miƙa sadakin Fillo, ko da bai aureta saboda taimakon da tayi masa ba, tabbas ta cancanci a aureta saboda rashin dace na uban ƙwarai, dan ko kaffara ba zai yi ba Hayyo shi ne mahaifinta.

to amma da me zai bayar da sadakin nata?, yay shiru yana tunani cikin ransa, ko kaɗan ba ya so ya miƙe daga kan tabarmar nan ba tare da ya mallaki yarinyar da ta dinƙa cusa kanta a haɗari ba saboda kawai ta cece shi, ba don so ko kuma wani abu daban ba, sai son kyakykyawar zuciyarta.
yana iya tuna yacca ya dinga jin kallon da Hayyo keyi masa, yana tuna furucin da Hayyo yayi masa kan cewar,"ranka ya daɗe in har babu sadakin yarinyar nan kazo ayau, to ina mai tabbatar maka da cewar ba rabonka ba ce, domin kuwa tun tana ƙarama akwai wani tsoho da ya roƙi a bashi ita, to banda ma dai tasa ƙafa ta gudu da maganar da nake shaida maka yanzu tayi ƴaƴa kusan uku. dan haka kana tafiya zan yi masa magana ya bada sadakinta, in yaso tunda Allah yasa kai kasan inda take, sai kayi mana jagora muje mu taho da ita".

"zan bayar da sadaki, amma sai naga shedu".

haka yasan ya faɗa masa, kuma minti goma ba'a ƙara ba sai ga Hayyo ya dawo tare da mutum huɗu, ya shaida mutum ɗaya wanda Hayyo ya nuna masa yace shi ne limamin babban masallacin anguwarsu, saboda lokacin da ya shigo unguwar ya tsaya yayi sallah a masallaci, dalilin da yasa ya gane shi kenan, sai mutum ukun da bai sansu ba, amma daga tsufansu ya san ba mutanen banza bane.

yana tuna sanda Liman ya buɗe baki ya tambayesa ina waliyansa, kuma a lokacin magana ɗaya ya faɗa wadda daga ita ba wanda ya ƙara cewa komai Liman yace ya miƙo sadakin. "ni maraya ne, bani da kowa sai Allah".

hakan ya faɗa musu, kuma daga faɗar hakan babu wanda ya ƙara masa wata tambaya aka ce ya ajiye sadaki. still idonsa na kan Hayyo yace,"banda kuɗi yanzu".
kuma tun bai rufe bakinsa ba Hayyo yace,"kana iya tashi ka tafi, yarinya dai ba rabonka ba ce".

zuciyarsa ta faɗa masa cewar in har Fullo zata iya sadaukar da ranta da kuma lafiyarta akan ta kuɓutar da shi daga wani ƙulli, alhalin ba dangi iya bare na Baba, to ba ya jin shi zai kasa iya sadaukar da komai nasa don ganin ya mallaketa, mallakarta kaɗai shi ne sakayya mafi kyautatawa da zai yi mata. saboda haka take a wurin a ajiye key ɗin motarsa a gaban Liman yace,"na bayar da motata a matsayin sadakinta".

ba zai taɓa mance yanda Hayyo ya dinƙa kallon maƙullin motar ba with so much expression, har ƙwayar idonsa irin ta Fullo na yin kamar zata faɗo waje. amma duk da haka sai da yasa aka shiga cikin gida aka kira masa wani saurayi, saurayin shima me kama da Fullo sak, idan bai manta ba sunan da Hayyo ya kira saurayin da shi ne,"Hamid". saurayin ya amsa masa da,"na'am Abba". sannan Hayyo ya ɗago kai ya kallesa yace ya zagaya baya, ya gano masa motar da ke wajen kuɗinta zai kai nawa.

and abinda Hamid ya dawo ya sanarwa da Hayyo shi ne,"kuɗinta zai kai miliyan hamsin ko sama da haka". kuma ba tare da ƙara yin wani bincike ba Hayyo ya kalli ƙwayar idon Turaki yace masa,"kaje yarinya ta zama mallakinka, aure ya ɗauru".
haka ya baro garin Taraba a train zuciyarsa cike da tarikan mamaki iri-iri a game da lamarin Fullo da mahafinta, duk da cewar yaso ya keɓe da Hamid to amma bai samu dama ba.

Fillo ta buÉ—e idonta dake yi mata zafi tana kallonsa, idonsa a rufe yake, har sannan kuma bai saki kan nata ba.
in cool voice nata tace da shi,"please ka daina taɓani any how babu kyau. kuma dan Allah ko kuɗin napep ne ka bani na koma gida, Maama da Boɗejo zasu neme ni, turarenka kuma zan biyaka insha'Allah".
a sannan Turaki ya buɗe idonsa yana ɗauke hannayensa akanta. yana kallon gefe daban kamar zai yi magana sai ya fasa ya miƙe.
ya nufi ƙofar fita yana cewa da ita,"biyo ni". ta tashi cikin sauri tabi bayansa.

tunda suka hau titi take ta kallon hanya har suka iso asibitin Miyetti, fita yay a motar ya barta ita É—aya ya shiga pharmacy ya sayo magunguna ya dawo, sannan suka É—au hanyar gida.
ko da suka ƙarasa gida Turaki yay parking sai Fillo ta kasa fitowa a motar, ta tsinci ƙafafunta da kasa yin motsi su fita daga motar. tana kallo ya fice ya barta a ciki, sai ta bisa da ido tana kallo ya wuce side ɗin Boɗejo, gaba ɗaya ta rasa me take ji a tare da ita, tasa hannu zata buɗe motar ta fita sai ga motar Samha tayi parking kusa da ta Turaki.

da dukkan alama tun fitar safe da tayi sai yanzu ta dawo, Fullo tayi saurin maida ƙofar tana rufewa a hankali gudun karta ji ƙara, kasancewar tend glass ne amotar hakan yasa babu me hangota a ciki sai dai ita ta ga na waje. tayi ɗuff ta ɗauke wuta dan ji take kamar zasu iya jiyo numfashinta.
Sameer taga ya fito daga driver seat sannan Samha ta fito ta ɗayan seat ɗin, ta zagayo ta side ɗin Sameer ta karɓi roban Maltina a hannun Sameer, sun ɗauka atleast 2minutes su.na magana kamin su saki murmushi, tukunna suka bar wajen su na wucewa cikin gida.

Fullo taji ta wani girgiza, bata san wannan shirin nasu kuma na menene ba, bata ji su ba, bata san me suka ce ba. taja nunfashi ta ɗauka ledar maganin da Turaki ya saya ta fita daga motar, cikin saurin tafiyarta tayi side na Boɗejo cikin zuciyarta tana ta fatan kar Allah ya bawa Samha ikon ganin Turaki, haka kawai zuciyarta ke faɗa mata wannan roban malt ɗin ba malt bane kawai a ciki, haka kuma ba don kowa aka shigo da shi ba sai don Turaki, tafiya take tana harɗewa tana ƙara jin tsoron mutum acikin ranta, idan ba a film ba bata taɓa tunanin za'a iya samun siblings ɗin da zasu iya kashe ɗan uwansu a gaske ba, sai ga shi yanzu ta gani a zahiri, abin na faruwa a inda take rayuwa.

maganar Hajiya Madina ta haska cikin kanta, lokacin da tace mata,_"ba halina ba ne, ba haka zuciyata take ba, tunda Allah ya halicceni banda mugun nufi akan kowa, zuciyata bata da tsatsa ko kaɗan, kullum roƙon Allah nake kar yasa na cuci wani a rayuwata, amma ban san a ina Samha da Sameer suka ɗauko wannan mugun halin ba, ban sa ni ba, dan ba halin mahaifinsu ba ne..."._ kasa ƙarasa maganar tayi a lokacin saboda kukan da ya ƙwace mata.

kamar wadda tayi gudun famfalaki haka Fullo ta shiga parlon Boɗejo, gaba ɗaya ma sallamar ta mance da ita. babu kowa a parlo dan haka kai tsaye bedroom na Boɗejon ta wuce, ta san ba zai wuce can Turaki yayi ba, ta buɗe ƙofar tana shiga da sallama.

Ilham da ke gefen Turaki a zaune ta amsa sallamar tana faÉ—in,"bismillah".
gaba ɗaya Fillo sai taji ƙafafuwanta sunyi matuƙar sanyi, bata san dalili ba amma haka kawai taji gabanta ya faɗi da ganin Ilham da tayi da kuma yacca ta ganta zaune manne ajikin Turaki.

zuciyarta taji na faÉ—a mata cewar kawai tayi reverse, amma sai taji ta kasa gaba ta kasa baya.
Ilham na kallonta sosai tace,"ki shigo mana, ba aiki za ki yi ba?".

kan Fullo a ƙasa tace,"ehh". Ilham tace,"to bismillah".
Ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, ta shigo ciki idonta a rufe tana jin kamar jiri ne ke neman ɗibarta ya zubar.
Ilham na riƙe da hannun Turaki tace,"to Hammah ba sai mu tafi tare ba, tun fa da na dawo ban ƙara zuwa ko'ina ba, Mami sai tace wai a'a, kuma ni ko dubai ina so naje na sha iska, please Hammah zan bika".
ya kama hancinta yaja ba tare da ya ce komai ba, wucewar 3seconds ya miƙe ya fita Ilham tabi bayansa, Fullo kuma da ke tsaye gefe guda ta bisu da kallo.

su na fita ta jefar da ledar hannunta akan kujera, taji kamar tana so tayi kuka, amma ba zata yin ba saboda har yanzu kanta ciwo yake yi mata. ta rumtse idonta sosai, da ƙyar ta iya gyara abin da zata gyara a ɗakin cikin few minutes ta fice.

tana fitowa parlon ta tadda Turaki zaune a kan kujera shi É—aya, da remote hannunsa yana sauya channel. ta tsaya tana kalle-kalle ko zata ga Ilham, sai dai da dukkan alama bata nan.
table É—in gabansa tabi da kallo, fruites ne acikin plate sai roban malt a gefen plate É—in.
tayi tsaye daga inda take sai kallon roban take yi, kamar me son ganin wani abu aciki.

tayiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai, bata san me yasa ba haka kawai taji tana mugun jin haushinsa for the first time. inda yake ta ƙarasa ta aje ledan maganin kusa da shi tana cewa,"ka manta a mota". sannan ta kai hannu kan table ɗin ta ɗauke roban malt ɗin zata bar wajen.
yay saurin riƙo hannunta ya dawo da ita,"ɗauka ki tafi da su".

ta waiga ta kalla ledan sannan ta kallesa, tace,"maganin da ka saya ne fa".
shima É—in yana kallonta yace,"nayi miki kama da mara lafiya?".
Sai ya galla mata harara yace,"É—auka ki wuce da shi".
kamar zata yi kuka tace,"shi maganin dama haka kawai ake shansa?, kawai daka sami magani sai kace dole sai na sha. ka barni na wuce please Kaka na can na jirana".
Ya janyota ta zaune kan kujerar kusa da shi. zai ƙwace roban malt ɗin ta damƙe da kyau.
Chapter 66 · 0% Book details