← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 176

Sashe 68

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace,"i know you are tired, kayi kwanciyanka sai da safe tukunna. have you eaten your dinner?". yay shiru bai ce komai ba, tace,"na dafa maka tea, yana perlonku ka duba. ka tabbata kaci ka ƙoshi before you sleep".
yace,"to Maama, thank you, Allah ya ƙara miki lafiya". tace,"yauwa bye bye, sleep tight. karka manta da adu'a".

ya ajiye wayar yana kwantar da kansa jikin kujera. Fillo dai nata kallonsa tana jin wani tausayinsa na ratsata. gani tayi ya tashi ya fita yanayinsa na juyawa zuwa na marasa lafiya, kuma kamin ta yunƙura tabi bayansa sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da basket, ya wuce ya ajiye kan table ya shiga toilet ya fito.

kaɗan ya zuba tea ɗin, soyayyan bread da ƙwai ne, slice biyu ya ɗauka yaci.
zuwa lokacin bacci har ya fara ɗaukar Fullo, ta kifa kai a jikin gadon. a cikin baccin nata taji yana waya yana cewa,"haka fa, ai dalilin da yasa ma ba'a fiya son a tsaya ƙofar gidan ba kenan, both the two side, an ma fi samun wannan matsalar daga ta gate ɗin ma'aikatan gida. yes, ai kwanaki ma akwai baƙuwa da muka yi tana taɗi anan main gate so basu ankare ba sai jin abu tayi ya nannaɗe mata jiki, ana dubawa akaga ashe maciji ne. the same abin da ya faru da wata ƴar aiki ma, tana compound nasu ne ko tana bakin gate tana zance, na dai manta but itama ce akai abu kawai taji yana shiga cikin kayanta, ashe wani tsohon maciji ne yayi girmana, da ƙyar aka cire macijin nan a jikinta, ƙarshe ma mutuwa yarinyar tayi, shiyasa ai duk wanda ya san hakan yana kiyaye tsayuwa a compound ko bakin gate, don akwai ɓoyayyun macizai da yawa, shiga jikin mutum kawai suke kamar an aiko su, most especially masu tsayawa suyi zancen nan, suna tsaye sai dai suji maciji ya shige jikin...".

ai bai ƙarasa ba Fillo ta kurma wani uban ihu tana haɗewa da salati, cikin second ɗaya ta tashi a ƙasa ta dire akan gado. ta cure a wuri ɗaya tana faɗin,"na shiga uku na lallace, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, maciji wayyo Allah na". faɗa take tana ƙara maimaitawa ataimaka mata maciji ne, maciji ya shige mata jiki, shi dai kawai yana zaune yana kallonta kamar tv, yay hanging wayar ƙaryar da yake yi, sai da ya tabbatar tsoron ya shigeta sosai ta yanda gobe ko uban Amir ne yazo ba zata sa ƙafa ta fita wajen ba, tukunna ya buɗe baki yace,"keee".
ya faɗa da ɗan ƙarfi, wannan kiran sai ya ƙara tunzurata ta saki ƙara me uban ƙarfi tana dunƙulewa ta kai ƙarshen gadon ta cure wuri guda.

"ka kore shi dan zatin Allah, wayyo gashi nan ya hau ƙafata, innalillahi Kaka kizo ki taimka min, Maciji ne ajikina gashi nan yana bina". tunda Fullo take bata taɓa tsorata irin yau ba, hawaye a fuskarta kam tamkar an kunna famfo, acikin blanket ɗin da ta rufe kanta da shi ta ɗan buɗe ido kaɗan sai taga duhu, nan ta ƙara sakin wani uban ƙaran da yafi wancan, ɗiff kuma sai tai shiru kamar ruwa ya cinyeta.

wannan shirun nata sai Turaki yay zaton ko tsoronne yasa ta ɗauke wuta, saboda haka kawai ya ɗauke kansa akanta yaci gaba da aikinsa, computer yake kallo amma babu abin da ke haska masa acikin ido sai lokacin da Amir ya riƙe hannunta ya kuma ja hancinta.
haka ɗaya kuma yaji ya kasa natsuwa, yaji kamar tsoro na so ya kamasa, yana typing a wayar hannunsa yana kallon kan gadon inda ta dunƙule, a ransa yaji kamar shirun nata ba lafiya ba, in bacci ne takeyi minutes ɗin da tai taking a haka tuni ta mirgina, in kuma tsoronne zuwa yanzu ai ya barta, sai yaji hankalinsa bai kwanta da hakan ba, ya ajiye wayarsa ya miƙe ya isa kan gadon yana dukan ƙafarta dake cikin blanket, shiru shiru bata motsa ba.

sai yaji kamar zuciyarsa ta harba a lokaci ɗaya, ta-ke ya haye kan gadon ya yaye blanket ɗin, yana taɓata yaji jikinta ya saki ta tafi luu ta faɗa gefensa, tuni idonsa yayo waje yana furta innalillahi, kamin ya diro akan gadon ya shiga toilet ya ɗebo ruwa.
tun bai haye kan gadon ba ya watsa mata ruwan a fuska sai gata ta farka a matuƙar firgice tana ƙwala kiran,"Umminaaaa". ta faɗa tare da fashewa da raunataccen kuka, irin kukan da duk wanda yaji sai ya taɓa zuciyarsa.

tsakiyar gadon ya haye ya janyota jikinsa ya kewayeta da hannayensa duka biyun yana me rufe idonsa. wani abu da bai san menene ba yaji ya tsarga tun daga tsakiyar kansa har tsakiyar tafin ƙafarsa, sunan Ummina da ta ambata shi ya daki zuciyarsa, bai taɓa jin tausayinta ba sai ayau.
"Ummina". ya ƙara jin sunan ya haska cikin kansa, kenan ta tsorata ainun, tsoron da ya kai gejin da har take ganin babu mai iya taimakonta sai Umminta, ta tsorata ta kira sunan Ummin da bata raye akan tazo ta taimaka mata.

idonsa ya buɗe ya sauke a tsakiyar kanta, tunawa yake da san da Kaka ke shaida masa cewar,"marainiya ce Mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta ma haka". to amma har yau neman dalilin da yasa Kaka ta ɓoye masa cewar mahaifinta na raye yake, sai dai tunaninsa na bashi ko don saboda Hayyo baida kyan hali ne.

sai yaji ruwa ya cika idonsa kamar zai yi kuka, bata da Ummi bata da Abba amma tana da shi, tana da shi har abadan abadina, kuma alƙawarinsa ne zai tsaya mata kamar Umminta, zai tsaya mata ba kamar Hayyo da ya sani ba, zai tsaya mata ne kamar nagartaccen uba.
sai ya ƙara rungumeta a jikinsa yana jin yanda zuciyarta ke bugawa kamar zata faso ƙirjinta saboda firgicin da ta ke aciki, numfashinta kuma na fita a wani fiffizga, tana ta kiran sunan Ummi a hankali.

ya buÉ—e ba ki zai yi magana yafi sau uku duk sai yaji yama rasa me zai ce. can kuma a hankali ya kira sunanta dai-dai satin kunnenta,"Fulaniii". ya ambaci sunan kamar me koyon magana, haka kuma amon muryar kamar ba nasa ba.
Fullo ta ƙara ƙanƙame shi tana daɗa tattarewa a jikinsa kamar zata shige jikinsa duka.

he took a deep breath hugging her more, yasa hannu yana shafa sumar kanta a hankali ya kasa cewa komai.
kusan 3minutes yana jin yanda heart ɗinta ke beating fast, a hankali yace"menene?, me ya tsorata ki?, kiyi shiru babu komai, am with you". ya furta cikin sigar rarrashi yana riƙe da hannunta guda.

acikin fizgar numfashi tace,"Maciji ne".
yace,"aina?".
ta daɗa shigewa jikinsa sosai tace,"a ƙafata, ka kore shi please, gashi nan zai shige jikina".
tai maganar duk a ruɗe tana daɗa ƙanƙamesa.

ya sauke numfashin yana murza tafin hannunta murya can ƙasa yace,"babu wani maciji fa, buɗe idonki ki gani".

ta girgiza kanta da ke kan cikinsa tace,"a'a akwai, kai ne ka faÉ—a".
yace,"to aini waya nake yi". ta ƙara girgiza kanta, yayinda Turaki ke rufe idonsa yana jin wani iri a jikinsa.

tace,"ai sanda ka faÉ—a shi ne sai na jisa a jikina".
ba tare da ya buÉ—e idonsa ba yace,"to ai ya tafi, buÉ—e idon ki gani babu komai, na kore shi".

tace,"to ka kunna light".
yace,"a kunne yake".
ta buɗe idonta a hankali hasken ɗakin na shigewa cikin idonta, sannan ta zare jikinta daga nasa tana jin yanda gabanta ke faɗuwa har sannan, hannuwanta sai kyarma suke yi. Turaki yay saurin sauka akan gadon ya buɗe ƙofa ya fita, for few minutes sai gashi ya dawo da cup a hannunsa ɗauke da ruwa aciki me sanyi.

har sannan Fillo na takure akan gadon waje ɗaya sai raba idanuwa take yi, motsi kaɗan take jira ta kurma ihu, ya ƙaraso gaban gadon fuska babu yabo babu fallasa, ya miƙa mata cup ɗin, ta kallesa ta kalli transparent glass cup ɗin a hankali tace,"dan Allah...".

bai barta ta ƙarasa ba yace,"amsa Malama ruwa ne".
ta ɗaga hannuwanta da har lokacin kyarma suke yi ta karɓa tasha sannan ta miƙa masa ya ajiye.

"sakko ki tafi to".
da sauri ta É—ago ta kallesa tace,"inje ina?".
yay mata wani mugun kallo kamin yace,"Kaka na can na jiranki".
sai tayi narai-narai da idanu tana marairaice fuska ta leƙo da kanta ƙasa wai ta gani ko macijin yana nan har time ɗin.

"É—aure kanki". ta lalubo É—ankwalinta da yay can gefe ta É—aure tujajjan gashinta.
"oya to yafa mayafinki ki sakko ki wuce".

tuni hawaye ya sakko mata muryarta na rawa tace,"wallahi ba zan iya sakkowa ba".
looking at her yace,"saboda?". tace,"kamar na daina tafiya".

wata dariya ta tahowa Turaki amma ya gimtse, babu me ganinta a wannan condition É—in bai yi dariya ba.
ya isa bakin ƙofa ya buɗe ba tare da ya kalleta ba raising his voice up yace,"zo ki fice".
ta kallesa ta tuna zancen macijin da yay kawai sai ta fashe da kuka sose, ta shiga roƙonsa tana faɗin,"dan Allah don Annabi ka ƙyaleni anan, ba zan iya tafiya ba ƙafana ya daina aiki".

sai kuma ta goge hawayen ta É—ago ta kallesa tace,"to ka É—auko min wayan Yami a perlon BoÉ—ejo sai na kira Kaka tazo ta É—aukeni".

ya haÉ—e rai ganin tana kallonsa yace,"Kakan ce zata zo ta É—auke ki?, rashin imanin naki har ya kai haka?, and you even have the guts to send me right?, yaronki ne ni?".

tace,"Allah baka haƙuri, kuma ni ba zan iya tafiya da ƙafata ba a yanzu, tsoro nake ji dan Allah ka barni sai da safe".

ya zaro ido waje yace,"a É—akin nawa?".
ta gwame fuska tana jin komai babu daɗi a tare da ita tace,"to ni ya zanyi, idan na sakko fa majicin zai kuma bin ƙafata, dan Allah ka ƙyaleni anan sai ka tafi ɗakin Hammah Khalil".

yace,"ke zo ki tafi can ɗin". tayi shiru bata ce komai ba, yanda tayi laƙwas tai mugun basa tausayi, yace,"to idan na barki anan ni aina zan kwanta?, kuma ai kince babu kyau".

tana goge hawayen fuskarta tace,"ai nasan ba zaka yi min komai ba. kuma ai ga kujera can sai ka kwanta akai, amma ka kira Kaka ka faÉ—a mata".
Chapter 68 · 0% Book details