Sashe 143
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da rana suna zaune su na kallon pixx na ranar dinner kiran Mum ya shigo wayarsa, yana É—agawa bayan sun gaisa tace masa,"gobe idan Allah ya kaimu zamu je taraba, Yaya Naja tayi accident zamu je dubata, so sai ku shirya har da ku zamu tafi, but ita Halima zata zauna tare da mu ne, zamu yi 7days acan".
kaman wanda yaji mugun abu ya zabura wajen tambayarta,"Mum har ita za'a yi 7days É—in?".
Mum ta ce,"bayanin da nayi ne baka gane ba ko me?, nace maka har kai zamu tafi but zaka dawo ita zaka barmu tare da ita, nima ina so na shiga wurin families so duk zamu je da ita taga Æ´an'uwa".
yanayin Fuskar Turaki ya sauya, sam bai ji daÉ—in hakan ba, yay shiru kamar ba zai amsa ba sai kuma yace,"to Mum, by what time zaku tafi É—in?".
ta ce,"da sassafe mana, za'a fita da ita india ne aikin ƙashi za'ai ma ta, so ina so na samesu kafin tafiyan na su".
"to Mum, mu zamu bi flight ne".
ta ce,"duk yanda kayi. and ku shirya anjima kuje ku duba BoÉ—ejo, bata ji daÉ—i ba ashe har kwana biyu".
ya ce,"gobe kafin mu tafi ba sai muje".
"anjima nace Babana, ko so kake ka jawo mana magana, da ma kowa yaje tana faÉ—a masa mun san bata da lafiya amma bamu je dubata ba, alhalin ba'a sanar mana ba, ka san Baffanku ba ya nan. to bana son fitina ka shirya kuje anjima mu ma yanzu can zamu wuce, ina nan ina fama da Madam, itama wai sai dai a bari sai gobe".
ya amsa ma ta da to sannan suka yi sallama.
ya kalli Fillo wacca ta fara lumshe ido akan cinyarsa yace,"Fulani nah ba kya gajiya da bacci ne?".
ta ce,"naji kana waya ne".
"to tashi muyi hira, bana son wannan yawan baccin idan ina nan, if na fita sai kiyi ta baccinki".
ta miƙe zaune ya sarƙe yatsunsu yana cewa,"after la'asar zamu je duba Boɗejo, wai bata da lafiya".
ta ce,"Allah sarki, me yake damunta?".
"ban sani ba nima, kin san jikin tsufa".
ta ce,"to Allah ya bata lafiya".
kwanto ta yayi jikinsa yana janye wani silin gashi da ya hau saman leɓenta yana ƙoƙarin shiga bakinta. ta buɗe lumsassun idanuwanta da bacci ya fara cika su ta kalle shi, ƙwayar idonsa ya maƙale akan plumpy lips ɗinta, ya ɗora yatsansa a saman lips ɗin ya shafa, numfashin bakinsa da ya fito ya haɗe da tambayar da ya jefa ma ta.
"wanne irin alawa kike sha?".
"da ina shan kowanne".
"yanzu fa?".
"guda É—aya nake so, ibon".
"É—an naira goman?".
"yes É—an goman, flavour É—inta yana min daÉ—i sosai".
"kaman flavours É—in ta yana da yawa ko?".
ta ɗaga kanta,"diffrent flavours, but na fi son pink one ɗin me ƙamshin strawberry".
"tana sa ƙamshin baki ne?".
ta buɗe hannayenta alamun itama bata sa ni ba, sai yay murmushi me faɗi bai ce komai ba, sai ta gyara zaman kanta a cinyarsa ta fuskance shi, ta kalli yanda yatsansa ɗaya ke nannaɗo jelar gashinta wanda ta fahimci yana son taɓa gashinta.
tace,"kayi shiru?, ko alawan bai da daÉ—i?, ko in daina sha?".
sai tayi shiru tana jin babu daÉ—i, zuciyarta na faÉ—a ma ta ko teste É—in bakinta yaji babu daÉ—i shiyasa yay ma ta wannan tambayar, lura da sauyawan mood É—in nata yasa shi tambayarta,"what?".
tasa hannu ta rufe idonta sannan tace,"ya sa bakina babu daÉ—i ne?".
"me É—in?". ya tambaya.
"alawan mana, na sha yanzu da safe ai".
yay murmushi, ya lura jikinta har yay sanyi, sai ya É—ago da fuskarta yana sunkuyo da tasa halfway da lips É—inta, sai yaga ta rufe ido gaba É—aya, cikin sexy voice É—insa yace,"ni ba teste É—in ibon nake so ba, teste É—in ki kawai nake so, ina so duk sanda nayi kissing É—inki to teste only you not ibon".
idanunta a rufe tayi murmushi kawai, nan moment ɗin nasu yaci gaba da yi musu daɗi, musamman a ɓangaren Fillo, hirarsa yake ma ta me cike da tarin tambayoyi kala-kala, da suka haɗa duk detail na rayuwarta, tun daga yarinta har girmanta, abin da yake ɓata mata rai da wanda ke sakata a farin ciki, films ɗin da take so da wanda bata so, her favorite food and drinks, wuraren da ta taɓa zuwa a rayuwarta, da kuma places ɗin da take da mafarkin zuwa, ta yanda akai ta fara taimakonsa and so on.
ita kanta ba zata iya tuna rana na ƙarshe da tayi magana mai yawan ta yau ba, ko murmushi tayi sai ya tambayi dalilin yinsa kuma sai ta ba shi amsa in ba haka ba yay ta ma ta cakulkuli.
ƙarshen tambayoyin suka tsaya akansa, tana tambayarsa yaushe ya fara sonta?. sai yasa hannu ya rufe bakinta da cewa,"turn ɗinki ba yanzu ba, sai watarana, har yanzu ban gama nawa tambayan ba".
tayi murmushi tana kama hannunsa ta ɗora saman chest ɗinta, ta ce da shi,"to a bar sauran tambayan sai zuwa gobe, yanzu ka ban labarin ƙiriniyan da ka yi da kana yaro".
yay guntuwar dariya, ya fara bata labarin sokancin da yay sanda yana ƙarami, but daga lokacin da ya haɗu da best friend ɗinsa Bello shikenan ya zama sai adu'a.
yana faɗa ma ta lokacin yana ɗan ƙarami ba shi da ƙarfi, wani class mate ɗinsa ya kama shi zai zane shi after an tashi a school, ya kasa ƙwatar kansa sai Bello ne ya zo ya tare masa, da ma akwai shi da siyan faɗan da ba nasa ba, har kuɗi yake bayarwa ya siya faɗa, akan siyan faɗa har abincinsa break ɗinsa yana bayarwa.
shikenan daga ranar su ka ƙulla abota da Bello, kuma daga ranar shi ma ya zama me ƙarfi ya ko yi faɗa da ƙiriniya, sai da ta kai ta kawo ya koma kamar wanda ke aiki da battery, kuma duk saboda zama da Bello, Maama tayi ta tofa masa lahaula.
duk friday Bello a gidansu yake yini, kuma shi Bello babu abinda ya iya sai shegiyar fitina da dambe, sai suje can field Bello yay ta koya masa yanda zai ƙwaci kansa in wani yafi ƙarfinsa, har ranar ya gwada masa yanda zai shaƙe wuyan mutum, Bello ya shaƙe masa wuya har sai da numfashinsa ya kusa ɗaukewa, kuma kamar wani Malaminsa ko Babansa Bello yace yaje yay ta practical, tun da yana da ƙanne yay ta gwadawa akansu, ai kuwa da daddare ya shaƙi wuyan Khalil zai yi assignment ɗin da Bello ya ba shi, Baffa kuwa ya tarfa shi yay masa ɗan banzan duka ya kulle shi a store, aciki ma ya kwana dan sai da safe Maama ta sato key ta buɗe shi, kuma a washe garin da suka haɗu a islamiyya ya faɗawa Bello, sai yace zai koya masa yanda ake ɓalle ƙofa in an kulle mutum, ko kuma da an kaishi ɗaki za'a kulle ya fice a sukwance tun kafin a rufe, har haura katanga duk tsayinta sai da Bello ya koya masa, da yacca zai ɗauko key ɗin mota ya fice daga gidan, har yana ba shi labarin wai shi a gidansu sai da ya fasa glass ɗin mota har biyu, Abbansa yazo dukansa ya ɗafe wuyansa yaƙi sakinsa.
watarana sun tashi a school yasa driver ya wuce da shi gidan su Bello, ya koya masa duk kalar yanda zai tseratar da kansa, wata rana kuwa yaywa Granny laifi zata kullesa a ɗakinta yay sufa yabi ta ƙarƙashinta, garin kamo shi ta zame ta faɗi, Anty Sa'adah ta kama shi ta murɗe masa kunne har sai da ya saki fitsari a wando.
yay shiru yace,"kin san Bello har cewa yay inyi kashi a fo sai in dangwala in rubuta sunana ajikin bangon É—akin Baffa, in dai yake ni to baya so na...ai ko in faÉ—a miki ina yin haka washegari Baffa ya kaini Europe wurin Granny".
Fillo ta dinƙa dariya har da riƙe ciki, shi ma ya shiga tayata dariyar kamar yanda take yi.
ta kama hannunsa ta ɗora a saman ƙirjinta tana rufe ido, yayinda dariyarta ke juyewa zuwa sanyayyan murmushi, a yanzu ta ƙara yarda cewa Turaki yana sonta har cikin zuciyarsa, kuma ba ta tunanin akwai abinda zai canja hakan, tana ganin zallar soyayyarta fal a cikin idanunsa a duk sanda ya kalleta, duk da har yanzu da bakinsa zuwa kunnenta dai bai furta ma ta kalmar i love you ba tun bacin wadda ta gani a takarda.
acikin kwanaki ukun nan kacal tana cikin wata duniya ne ta daban me cike tarin kulawarsa da tarairayarsa, ta daina jin tsoronsa dan ya bi ya kulle duk wata hanyar tsoronsa a gareta, ta saba da shi yanzu fiye da tunanin kanta ma, ta saba da hirarsa da yake cikin yi ma ta ko da yana cikin aiki ne, kamar yanda ta saba da jikinsa, dan duk wani motsi nasa cikin taɓata yake yi, ko akan laptop yake to hannunsa ɗaya na cikin nata, ko kuma ya ɗorata ajikinsa yay aikin a haka, haka in bacci ne tana manne a jikinsa.
kuma yanzu duk ta san abubuwan da yake so da wanda baya so, dan a kwanaki ukun nan duk ya lissafa ma ta halinsa, ya faɗa ko mai da yake so ta dinƙa yi masa, kuma sai a yanzu ta fahimci ashe shi mutum ne me sauƙin kai in har ka fahimce shi.
bayan sallar la'asar Fillo na zaune ita ɗaya a ɗaƙin Turaki, wayarsa ce riƙe a hannunta tana game, ta ajiye wayar tana ɓata fuska, Tunda Turaki ya fita masallaci bai dawo ba, wai Baffa yayi baƙi daga ƙauye sun zo ba su sameshi ba, shi ne yace yaje ya kula da su, gaba ɗaya bai fi minti goma sha biyar da fitar ba, amma duk sai take jin babu daɗi, ta san dai akwai ƴan aiki amma gidan duk sai taji yay ma ta girma, ba ta san ta saba da shi ba har haka ba, ji tai tana kewarsa sosai kamar tun safe ya fita ya barta, abu ɗaya kawai ta sani ba zata ji daidai ba har sai ya dawo.