← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 176

Sashe 84

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ƙaton ya jawo jakar kuɗi na biyun da Amir ya kuma kawowa naira miliyan biyu, sai dai basa tunanin da naira miliyan bakwai da rabi kacal zasu iya sakin yarinyar, sun jima suna kidnapping su yanke kuɗaɗe masu uban kauri, amma basu san me yasa akan wannan yarinyar ba suka buƙaci kuɗi kaɗan.
cike da rashin imaninsa yasa ƙafa ya ta-ke ƙafarta yace,"ka san menene yaro?, ko iyaka motan gidanku da muka ƙwamusoka daga wajen da muka ganka ranar idan siyar da shi za'ai ya haura sama da miliyan asirin, saboda haka ku daina ce mana baku da shi. for the last time zamu kira waya ka faɗa a gida kace aciko mana miliyan uku, ana cikawa mu kuma munyi alƙawarin zamu sake ka".

cikin tsananin azaba da wahalar da take ji tace,"ni Kakata kawai nake da ita a duniya, bayan ita banda kowa. wannan motar ba tamu bace ta gidan da nake aiki ce, dan Allah ku taimaka min, na tabbata Kakata duka gadonmu na wurin mahaifiyarmu ta siyar aka sami wannan kuɗin, a yanzu kuwa na san babu wani abu da zata ƙara ɗagawa ta siyar, kuyi min rai dan Allah".

shirunta yay dai² da shigowar wani mutum dogo kamar sanda, ya ƙaraso gaban ƙaton mutumin yana miƙa masa waya yana cewa,"oga ka duba news ka gani".

Ogan ya shiga kallon shafin facebook da yake nuna masa yana karanta bayanan dake jiki na ɓatan Fillo ƴar aiki a gidan Judge Alƙali Dikko, da kuma hotonta a ƙasa sanye da hijab.
sai ya bushe da dariya yana sa ƙafa yayi fatali da kujerar dake kusa da shi, ya mayarwa da mutumin wayar yana faɗin,"ashe kamu muka yi me soka bamu sani ba, har muna ɓata lokacinmu wurin amsar 5million only".

sai yay shiru yana ƙara sakin dariya yace,"Hardo kaje ka nema mana numban waya na gidan Alƙali, wannan yaro yana da taurin kan jaraba ba zai bamu wani number ba...kayi sauri ka kawo min in the next few minutes, yanzu ba miliyan 10 muke nema ba, miliyan 200 zamu karɓa".
ya faɗa yana miƙewa daga kan kujerar yana ƙara sakin dariya cike da nishaɗi.
sannan ya ƙara kallon ɗaya acikin yaran nasa yace,"Jibril, ka siyo kaza ka bashi yaci, domin ina sha'awan wannan yaro, ina so na huta da shi. a siyo masa kayan gina jiki a bashi yaci kafin nazo na biya buƙatana akansa, tun a ranar farko naji ina sha'awan budurci nasa, i know by that time uban Alkalai ya kawo mana 200Million namu, sai muna sakinsa yana tafiya".

Kalmar Virginity yay wani duka a ƙwaƙalwar Fillo da yasa taji ta girgiza gaba ɗayanta, her virgin?, kamar dai bata fahimci maganar tasa ba da kyau, sai kuma taji wanda aka barta da shi na faɗin,"kash Oga banji daɗi ba kana riga ni shiga daɗin wannan kyakykyawan yarinyar, nima ina ta kwaɗayinta tuntuni, amma da zarar ka sha naka rabon daɗin nima zan sha nawa kafin a sallameta". yaja igiyar ƙafarta ya ƙara ɗaurewa da kyau yana cewa,"kai Budurci yana da daɗi, gaki da ganinki za ki daɗi ƴan mata".

ƙwayar idon Fillo tun ɗazu ƙafe take a wuri ɗaya, tun bayan fitar wancan mutumin take so ta fahimci abinda ya faɗa kafin ya fita, kuma bata gane komai ba sai a yanzu, sai yanzu ta fahimci abinda yake nufi daga shi har wannan, suna maganar zasu amshi budurcinta ne kafin ta fita daga hannunsu.
da sauri ta shiga jujjuya kanta da ke barazanar tarwatsewa, hawaye masu zafin gaske na daɗa biyo kuncinta, ta jinginar da kanta jikin bango tana jin ƙirjinta yay mata wani irin nauyi tamkar an ɗora dala da goron dutse akai, a hankali ta shiga ambaton sunan Allah tana fashewa da wani kuka me ƙarfin sauti cikin fitar hayyaci.
ta jima tana kukan tana kiran sunan Allah, bata ma san time ɗin da mutumin da aka barta da ahi ba ya fita ba. zuwa yanzu ta san ruwan hawayenta sun ƙare, ƙazaman maganganun mutanen ke tayi mata yawo acikin kanta.
ta sa ni shikenan tata kuma ta ƙare, dan haka ta sallama da rayuwar gaba ɗaya, kanta ta buga ajikin bango tana addu'ar,"Allah ka ɗauki raina kafin waɗannan azzaluman su cimma burinsu akaina, Allah ka ɗau raina ayanzu ko na huta da wannan bala'in".

tsananin tausayin kanta ya lulluɓeta, babu ta yanda ta-ke tsammanin zata iya guduwa daga wajen nan, dan tayi attempting sau ɗaya suka kamata, shine tun daga ranar suka ɗaureta basu ƙara ƙunceta ba har zuwa yau, jini har ya gaji da daskarewa waje ɗaya a jikinta.
idanuwanta a rufe taji kamar mutum na taɓata, a mutuƙar firgice ta buɗe ido tana sakin ihu cikin ƙaraji da bala'in tsoro, da sauri farin mutumin dake gabanta yasa hannunsa ya toshe bakinta.

ta ƙwalolo ido waje tana kallonsa, ta san shi sosai kullum shine yake kawo mata abinci. a hankali taji yace,"ki shiru zan taimaka miki ne ki fita daga wajen nan, ki yarda da ni wallahi ba zan cuceki ba saboda haka karki yi ihu"
ya sauke hannunsa a bakinta, cike da tsoro dan bata tunanin za ta yarda da shi. ya miƙa mata plate na abinci gabanta yace,"ki fara cin abincin tukunna".
tace,"dan Allah karka yi min komai".
yace,"wallahi tallahi banda niyyar cutar fa ce taimakonki, amma kici abincin ko kaÉ—anne kinji".

tana ta kallonsa tace,"ba zan iya ci ba. dan Allah ka taimaka min".
yace,"zan taimaka miki amma in har ba kiyi wani yunƙuri na tona min asiri ba".
da sauri ta jijjaga kanta tana cewa,"zan bi duk ubarninka in har ba wanda zaka cuceni ba".

yasa hannu ya kunce ɗaurin igiyar ƙafarta, sannan ya kunce ɗaurin na hannu, amma sai dai bai warware ba.
yace,"kowa ya fita daga gidan nan, ni kaɗai ne amma zuwa nan da minti goma zuwa sha biyar Babban Oga zai iya zuwa saboda haka ba zan ce miki ki fita nan da wuri ba. kawai dai kiyi hankalin da ba zasu gane cewar wannan igiyar a kwance ta-ke ba, idan kika ta shi akwai ƙofa ta nan baya kusa da parlo da aka cire ki jiya, kibi ta nan ki fita. kina fita za ki hango wata ƙofa a wurin sai kiyi saurin buɗewa ki fita, za ki ganki cikin daji karki tsaya a kusa-kusa sai kin tabbatar kinyi nisa sosai da babu me iya riskar ki".

yasa hannu a aljihu ya ɗauko ƙaramar waya yace,"ga wannan kina iya kira gida ki faɗi inda kike ko da za ki kasa gane hanya".
tabi ƙaramar wayar hannun nasa da kallo kafin ta ɗago ido ta kallesa tana nazarinsa.
yay mata murmushi yace,"ni dai har ga Allah iyakar abin zan miki kenan, ya rage naki kuma ki kuɓutar da kanki ko kuma ki zauna su cuceki tun kina ƙaramarki. dan wallahi ina mai tabbatar miki sai sun mayar dake yarinyarsu after sun gama talauta danginki, ƙarƙari ki kasa juriyar ɗaukarsu ki mutu su jefar da ke, dan Babban Oga bai da imani wallahi".

yana gama faɗar hakan ya miƙe ya fitar ya barta, tabi bayansa da kallo kafin ta dawo da idonta kan wayar da ya bar mata. jin kamar motsi tayi saurin ɗaukar wayar ta tura acikin rigarta, Allah ya taimaketa kuwa tana sawa ana turo ƙofa a shigo.
jere ta gansu duk kusan kansu ɗaya, zata iya cewa bata taɓa ganinsu ba duk da cewar fuskokinsu a rufe yake da mask irin wanda take gani a film, suka wuceta suka shiga ciki, in ta lura da kyau kamar harda mace, na ƙarshen ya duƙa gabanta ya mammari fuskarta yana wani makirin murmushi yace,"zamu huta sosai da kai".
da faɗin hakan ya miƙe yabi bayan sauran.

taji sabon hawaye ya taho mata, ta rumtse ido sosai tana rasa ma me take ji a ranta.
dai-dai nan taji mutumin ɗazu ya dawo can ƙasa da muryarsa yana cewa,"you got the chance, zasu yi zaman meeting yanzu and atleast they will take up to 30minutes kamin su gama, babu wanda zai ji motsinki har ki fice, karki yi wasa da wannan chance ina daɗa jadadda maki if not wallahi a yau ko ba'a ɗau gawarki ba sai kin mugun raina kanki, dan kaf wannan mutane da kike gani sai sunyi amfani da ke".
yay saurin ficewa gudun kar wani ya fito ya gansa tare da ita.

*A dai-dai wannan lokacin.*
wayar Hajiya Madina da ke riƙe a hannun Nihal tayi ringing, tai saurin miƙa mata sanda ta ke tambayarta,"waye?". tace,"ba suna a jiki".
Hajiya Madina da jikinta yake a sanyaye ta karɓi wayar, dai-dai kuma da katsewar kiran, ta sauke numfashi jikinta duk a mace saboda halin da Kaka ke ciki, tun ɗazu suka zo asibiti amma har yanzu bata dawo hayyacinta ba, a sannan likita ya shigo ɗakin yana cewa,"Hajiya meet me in my office".

da hanzari Hajiya Madina tabi bayansa, nan kiran lambar ɗazu ya ƙara shigowa, ta ɗaga tana yin sallama tana ci gaba da bin bayan likitan. daga can ɓangaren taji wata gwandareriyar murya na faɗin,"Hajiya mune kidnapper na ƴarku".
tsabagen rikicewa sai wayar ta suɓuce daga hannunta tana tsaya daga bakin ƙofar tana haki kamar wadda tayi tsare, saura ƙiris wayar ta kai ƙasa Allah ya shigo da Turaki yay saurin riƙo wayar yana dubanta.

"lafiya Maama?". da shi da kowa na É—akin suka tambayeta a tare suna yowa kanta. tsabar gigita tama kasa cewa komai sai nunawa Turaki wayar ta ke da hannu. ya kalla screen É—in wayar yana kallon yacca call ke tafiya, ya kara wayar a kunnensa yana cewa,"Salamu Alaikum".

cikin ɗaga murya aka ce masa,"karku ƙara yi mana sallama ba ita muke buƙata ba".
mamaki ya bayyana akan fuskar Turaki yace,"wake magana?".
aka ce,"wanda suka yi garkuwa da yaro naku ne, kuna san yaron naku a raye ko kuma mu kashe shi mu aiko muku da namansa?".
Turaki bai san lokacin da yaywa hannu Maama wata muguwar damƙa ba da yasata yin ƴar ƙara tana faɗin,"Me Babban suna zaka karya min hannu".
Chapter 84 · 0% Book details