← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 176

Sashe 160

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ɓangaren Ilham kuwa tana can tana shan mugwayen shawarwari, an cika mata kai fal da abubuwan da muddin ta ɗauke su ba zata jima ba Turaki zai ƙara saita mata hanya.
wajen ƙarfe takwas da rabi na dare, Fillo ce a ɗakinta tana shirin kwanciya bacci, wayarta tayi ƙara, waƙar da ke tashi wajen ringing ɗin ya shaida mata Turaki ne, hakan yasa bata ko matsa daga inda take ba balle taje ta ɗauka.

har sau biyu kiran na shigowa ya katse bata ɗauka ba, tana gama shiryawa ta haye kan gado ta kwanta, ta dunƙule a waje ɗaya, idanuwanta na ta hasko mata yacca Turaki zai kwana tare da wata yau ba ita ba.
tayi nisa cikin wata duniya ta daban Turaki ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya kunna fitila ya bita da kallo, ƙarasawa yayi gaban dressing mirror da ya hangi wayarta akai, ya ɗauka ya kunna, sai yaga a silent take, hakan ya tabbatar masa da cewa ba da gangan taƙi ɗaga kiran nasa ba.

ajiye wayar yayi ya shiga taɓa ƙafarta, tana jinsa amma tayi masa banza, ta rufe idonta kamar me baccin gaske.
zama yay a gefen gadon kafin yasa hannu ya yaye blanket É—in da ta rufa da shi, ya rumtsa idonsa a lokacin da idanuwansa suka sauka akan cikakkun breast É—in ta da ya kwan biyu bai haÉ—u da su ba.

Fillo ta buÉ—e ido a lokacin ta zabga masa harara tare da faÉ—in,"lafiya?". ta faÉ—a murya a sama kamar ba ita ba.

ba tare da ya kalleta ba ya miƙe tsaye, ya zuba hannayensa cikin aljihu sannan yace da ita,"ki sauko ƙasa ki same ni, ina so zan yi magana da ku".

taja blanket É—in ta gyara kwanciyarta kamar bata ji me yace ba. ya juyo yana kallonta,"ba magana nayi miki ba kika koma ki kwanta?, me kike ji da shi ne yanzu?".

ta ƙara jan blanket ɗin ta rufe har kanta, yana tsaye yana ta kallonta yana ƙoƙarin sarrafa ɓacin ransa, ya fi ƙarfin minti uku a tsaye Fillo bata ko motsa ba balle yasa ran ma zata tashi ne, ya jijjiga kansa ya fita ransa a mugun ɓace.
yana sauka ya tarar Ilham ta shigo a lokacin, tana tafiyar yauƙi ta wuce ta zauna kan kujera, sai kallon parlon take yi tana taɓe baki kamar wacca taga kashi, mamaki take yi sosai har cikin ranta, bata taɓa zaton kaya masu shegen kyau da tsada ba ne aka zubawa Fillo.

kusan zata ce kuÉ—i daidai ne da nata, kuma in har ba son zuciya ba colour É—in funitures É—in Fillo sun fi nata kyau sosai ma.
sai da aka kwashi kusan mintuna goma kafin Fillo ta sauko, sanye take da hijab har ƙasa, fuskarta wasai kamar bata da damuwar komai, sai ma bacci da ya fara nuna alamarsa a fuskartata.

tun da ta taho Ilham ke kallonta idanuwanta kamar za su faɗo ƙasa, zuciyarta tayi mugun bugawa da wani masifar kishi, ta haɗiye yawu da ƙyar a maƙoshinta, dama har haka Fillo ke da azababben kyau bata sani ba?, a yau dai ba zata so zuciyarta ba kam Fillo ta ci uwar ubanta a kyau, kyan nata har tsoro ya bata, yarinyar ta koma kamar ba ita ba, ta ƙara fresh da kyau me matuƙar ɗaukan hankali, sai ƙyalli take yi, ga shi kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana ɗauke da ciki, bata san lokacin da wani uban gumi ya wanke mata wuya ba, ta damƙe hannunta a jikin kujerar tana ji kamar ta tashi ta bar parlon.

Fillo ta wuce ta kashe tv, sarai ta san Turaki kallon news É—in yake yi, ya bita da kallo, tun É—azu yake a hasale da ita, ya lura ta É—auki salon rashin mutunci, dole zai taka mata burki tun kafin akai ga nisa, don ba zai É—auki wannan banzan halin ba, har ta dawo ta zauna kusa da shi bai É—auke idonsa akanta ba, so yake ya karanci ma'anar murmushin da yaga tana yi tun da ta sakko.

"i'm sorry Jannaty, haɗewa nayi da shaf'i da wutri shiyasa na ɗan ɓata lokaci, i hope hakan bai ɓata maka rai ba".
tayi maganar tana kallon Ilham ta ƙasan ido, wacca ta cika tayi fam tana kallon yacca Fillo ta wani maƙale a kusa da Turaki.

Turaki ya sauke numfashi ya dube su gaba ɗayan su, ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga yi musu nasiha akan zamantakewar su, ya faɗa musu yacca yake so zaman su ya kasance, ya faɗa musu abubuwan da yake so su kiyaye gudun ɓacin ransa da na su.
daga ƙarshe kuma ya tsara yadda kwanakin kowacen su zai kasance, sannan ya ba su damar jin ta bakinsu, Fillo na wasa da yatsun hannunta ta ce,"duk yanda ka yanke Jannaty ni kam yayi min".

ya kalli Ilham, wacca ke kallonsa fuskarta na bayyana rashin amincewarta akan hakan, sai da ya É—aga mata gira ya ce,"ehen, ko kina ciwon baki ne?".

ta kawar da kai gefe guda tana cin nagani ta ce,"da dai ka ƙara, kwana biyu sai kace a zamanin da, ko gidan ƙawata kwana huɗu ake yi musu su da suka fi mu jimawa ma kenan".

Turaki yay mata mugun kallo kafin ya ce,"to kwana biyun na yanke ba zan ƙara ba, nan gidana ne ba gidan ƙawarki ba ne".

ya danne ɓacin ran da ke ingizo shi, ya ci gaba da yi musu nasiha sosai, irin nasihar da kowaccen su sai da taji a zuciyarta, bayan nan yay musu adu'ar zaman lafiya, kafin nan ya rufe taron na su da adu'a.
cikin ƙarfin hali Fillo ta danne bala'in abin da ke taso mata ta ce,"Allah ya amsa dukkan adu'oin da kayi mana ranka ya daɗe, insha'Allahu ta ɓangarena ba zaka taɓa samun wata matsala ba, zan kiyaye dukkan abin da baka so, haka zan yi ƙoƙarin aikata duk wani abu da kake so domin farin cikinka, na yi maka alƙawarin hakan muddin numfashina".

sai kuma ta kalli Ilham tace,"abokiyar zamana ina yi miki barka da dawowa, ina fatan zamu haɗe kanmu mu zauna lafiya kamar yanda mijinmu ke so, ni dai ta ɓangarena ba ki da damuwa na ɗauke ki tamkar ƴaruwa ta jini. bismillah gaisuwar musulunci".
ta faɗi hakan tana miƙawa Ilham hannu don su gaisa, but sai Ilham ɗin taƙi miƙa mata nata, ta yi mata kallon sama da ƙasa tare da jefa mata wani irin wulaƙantaccen kallo.

É—an runtse idanun Fillo tayi tare da yin murmushin takaicin da babu wanda zai fahimta, bata san cewa ita ma ba har zuciyarta ba, yanda bata so ta haÉ—a hannu da ita haka ita ma, don ko ace ma ta amince su gaisa É—in cikin dabararta zata aiwatar da abin da zai hana hakan, ai ba don Turaki a wajen ba kallo bata isheta ba.
Ilham ta miƙe a zafafe zata fita ta bar parlon Turaki ya dakatar da ita.

"ta wurinki zan fara samun matsala kenan ko?".

Fillo ta miƙe ta ce,"zan wuce ɗaki, Allah ya bamu alkhairi ya tashe mu lafiya, sai da asuba ranka ya daɗe".

tana faÉ—a ta wuce upstairs cikin natsuwa, Ilham ma ta bar parlon kamar wacca iska ke tunkuÉ—awa.

tun da Fillo ta koma ɗaki taji bacci ya ƙara ƙauracewa idanuwanta, ta gaza danne abin da take ji a zuciyarta don ta samu ta saita kanta, gaba ɗaya zuciyarta a cunkushe take, bata taɓa zaton zafin kishinta ya kai har haka ba sai yanzu, tayi saurin faɗawa toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah.
salloli tayi ta jerowa, gani take kamar idan tayi kuskuren sallamewa zata iya yiwa kanta rauni.

bayan ta idar tayi zamanta akan dardumar tana tasbihi, lokaci zuwa lokaci sai ta sharce ƙwallar da ke sakko mata..
zuciyarta zafi take yi mata sosai, hatta kanta jinsa take yi tamkar zai rabe gida biyu, gaba ɗaya jin duniyar take babu daɗi sam, wataƙila in ace yau ba zata yi kwanan gidan nan ba da zata iya samun sassaucin raɗaɗin da take ji a zuciyarta.

a can ɓangaren Turaki kuwa tun komawarsa ya tarar Ilham ta rufe ƙofa, bai ko bi ta kanta ba ya wuce ɗakinsa, sai dai tun da ya koma zuciyarsa ta gaza yi masa daɗi, tazara!, irin tazarar nan da bai taɓa zaton zata kasance tsakaninsa da Fillo ba, ko da sukai shariyar juna ya kan shiga duk dare yaga sleeping beauty face ɗinta.
ya zata ji yau zata kwana a ɓangarenta ita ɗaya ba tare da motsinsa a sashin nata ba?, sai yay shiru kawai tare da rufe idonsa, haka kawai ya ji ya damu sosai akan halin da yasan babu makawa tana cikinsa yanzu.

ya san yay mata rashin kyautawa, bai kamata ya shareta ba har ya canja mata ya zamar mata wani kalar mutum na daban da bai raineta akan hakan ba.
tabbas tana buƙatar rarrashinsa ko ya ne, tana buƙatar kulawarsa da rarrashinsa a wannan daren ko zata samu bacci, don kamar yanda ya san kayarsa ne daren yau ba lallai ne ta iya bacci ba.

wajen sha biyu saura aka turo ƙofar ɗakin a hankali, tun bata ɗago kai ba ƙamshin turarensa ya daki hancinta. ta ɗago domin ganin shigowar ko ta lafiya ce, kallo ɗaya tayi masa ta watsar.
kallo É—ayan da tayi masa ya fuskanci tayi kuka ne har ta godewa Allah, don idanuwanta sun yi mugun kumbura, sai kawai ya tsinci kansa da matsanancin tausayinta a ransa.

ƙarasa shiga yay, ya zauna a gefen dardumar, ya dinƙa kallonta yana ganin yacca taƙi ɗago ido ta kallesa, kenan bata ko ƙaunar ganinsa a yanzu?.
kafin ya buɗe baki yay magana yaga ta miƙe, taja dardumar ta jefar da rabin ƙafarsa da ke kai, ta ninke sannan taje ta kashe fitilar ɗakin ta haye saman gado.

ji tayi ya biyota kan gadon, tayi saurin miƙewa zaune tana cewa da shi,"ka tashi ka fitar min a ɗaki".

ta faÉ—a murya a karye, yayin da hawaye ke sakkowa saman kuncinta, hawayen da yake jin su har cikin ransa tamkar ana hura huta a zuciyarsa.
ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa, sai taji ta kasa ƙwacewa, kawai ta kifa kai akan gwiyarta, tayi kewarsa har bata san iyaka adadinta ba.
Chapter 160 · 0% Book details