Sashe 97
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daga haka suka yi sallama. su kai shiru daga Ilham har Mai martaba kowa yana jin ransa ba daɗi, in ace suna da iko kwana ɗaya tal ba za'a ƙara ba Fulani Azima zata warke, to amma lamarin ba nasu bane na ubangiji ne, sai dai su roƙe shi ya warkar da ita ba tare da tayi doguwar jinya ba.
suna zaune kusan minti goma sai ga Sarauniya Mabruka wato matar Mai Martaba ta farko, ita da ƴaƴanta uku suna biye da ita tare da masu kula da su mutum uku. tun a washegarin ranar da Fulani Azima tai accident aka taho da ita Philippines domin ƙwararrun likitoci su dubata, dan Mai Martaba yana ganin kamar likitocin nigeria ba zasu iya ba, duk da cewar asibitin fada ma ba ƙanan likitoci bane acikinsa, kusan duk ɗinsu a ƙasar waje suka yi karatu, amma shi yafi ganin su taho nan ɗin.
kuma families da dama sun so su biyo bayansu Mai Martaba yace a'a su É—an dakata tukunna, ita kanta Ilham sai da aka kwana biyar sannan suka taho ita da su Hajiya Shema'u da Turaki, kuma shi ranar da yazo ranar ya koma bai zauna ba.
kuma sai a yau da suka kwan 21days sannan mai martaba ya bar iyalinsa suka taho, don farko duk bai zaton za'aja haka ba, da zarar an mata aiki a ido shikenan zata dawo normal, to kuma likita sai yazo musu da bayanin duk da ya girgiza su. Sarauniya Mabruka ce ta fara sauka sauran biyun duk suna baya suma tare da nasu ƴaƴan. ta zauna kusa da Mai Martaba tana ɗago da Ilham daga jikinsa ta kwantar da ita a nata jikin, hadiman dake tare da ita suka watse suka tsaitsaya daga can gefe, Yarima Abbas da Yarima Lateef da Yarima Bilal suka zauna kusa da mahaifinsu ta ɗayan ɓarin.
Sarauniya Mabruka tace da Mai Martaba,"ya jikin nata?".
idonsa na tsaye ƙyam akan wata ƙofa cike da nazari a bisa faruwar accident ɗin ya bata amsa da cewar,"da sauƙi irin na malam bahaushe, zuwa anjima zasu ƙara shiga da ita theater za'aiwa ɗaya idon aiki, shima tana kukan bata gani da shi sosai, sai maƙogaronta da akai hoto akaga still akwai glasses na mota da suka farfashe mata aciki".
"Allah ya sauƙe ya bata lafiya don nabiyyurrahmati". ta faɗa tana saka hannu ta goge hawayen da ya sauko mata. lamarin duk yasa jikinsu mutuwa, sosai suke tausayin Fulani Azima domin ita ɗin mutum ce a garesu, duk wanda zai buɗi baki ya faɗi aibutunta to sai dai idan maƙiyinta ko kuma wanda basa shiri.
duk cikin su huɗun ita ɗaya ce babu ruwanta a yanda take nuna musu, ko irin kishin nan ma na rashin haihuwar ɗa namiji ita bata yi sam bata ɗaga hankalinta ba, hasalima kama nasu ƴaƴan take kamar nata, nan kuwa duk basu san tana bi musu ta ƙarƙashin ƙasa ba ne, fir'auna ce a zuciya Allah a fili.
suka miƙe gaba ɗayansu suka wuce zuwa room ɗin da take, duk me cikakken imani kallo ɗaya zai yiwa Fulani Azima yaji saukar hawaye a fuskarsa, kwance take kan gadon kana kallon idonta na dama zaka san bata gani da shi kwatakwata, sai kallon kowa take yi da ɗayan shima kuma dusudusu take gani, ga karaya a hannayenta duka biyun banda ta ƙafarta guda ɗaya, kallon kowa kawai take tana hawaye masu zafi.
ita so take ma tayi magana amma ta kasa, tun washegarin ranar da abun ya faru taso ta buɗi baki ta nemi yafiyar Hajiya Ramla a sanda suka je dubata, amma tayi tayi tai magana sam ta kasa, ga shi duk ta yanda taso tayi wata alama da zaisa a fahimci tana so tayi magana da Hajiya Ramla ta kasa, kuma daga yanda taga fuskokin familyn Dikko tasan ko kusa Hajiya Ramla bata tona mata asiri ba, akwai tabbas ɗin bata faɗawa kowa komai ba, wanda hakan ya ƙara haifar da danasani da kuma dama nadama a tare da ita, tana ji tana gani ko da bata mutu ba tata rayuwar dai ta ƙare, ita da matacce marabarsu numfashi kawai, babu abinda take biɗa a yanzu sama da ta kalli Hajiya Ramla a gabanta ta nemi yafiyarta, sannan taga Jakadiyya da Drivern da ta kashe suma tace su yafe mata, to amma ba zata samu duka wannan damar ba, haka zata tafi lahira da tarin zunubi da kuma hakkin waɗanda ta zalunta, shikenan ita kuma tayi biyu babu, babu nan duniyar babu can lahirar, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
sosai take kuka idonta guda ɗaya na hawaye, inama ace a dawo da baya, da tayi amfani da damarmakin da take da su ta gyara lahirarta, to sai dai hakan ba zai kasance ba, lokaci ya riga ya ƙure mata, yanda kowa ke ganin saukar hawayen nata babu wanda ya fahimci me take buƙata, sai tausayinta da kowa yaji yana roƙo mata lafiya a wurin Allah.
Ilham ta ƙwace daga hannun Sauraniya Mabruka ta isa gadon ta faɗa jikinta ta fashewa da wani irin kuka, kukan da duk sai da ya saka kowa dake ɗakin hawaye babu shiri.
*Dubai Quarters, Gombe State, Nigeria.*
daga ɓangaren kudu, gida na tsakiya me lamba 20, flat house ne ɗan tsakiya me ɗauke da milk gate da abuja brown paint, sai flowers dake zagaye da ƙofar gidan, daga yanda wajensa yake da kyau zaka shaida cikinsa ma me kyau ne.
daga cikin gidan Fillo ce a É—akinta kwance akan madaidaicin gadonta, ba bacci takeyi ba idanuwanta a rufe suka kawai hawaye na bin gefen fuskarta. ta tashi zaune tana saukowa akan gadon ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah, tana cikin sallar Ummi ta shigo, ganin tana sallar yasa ta ce mata,"idan kin idar ki fito muci abinci".
bayan Fillo ta idar ta kalli agogo taga har biyu saura, dan haka bata fita ba sai da ta saka uniform na islamiyarta tukunna, ta ajiye hijab É—in da jakar akan gadonta ta fito cikin sauri.
Kaka da Ummi na zaune a ƙasa kan carpet suna kallon tashar arewa 24 ana maimaicin kwana casa'in, ta zauna gefen Ummi sannan su kai bismillah suka fara cin abincin, bai fi spoon biyar Fillo tayi ba ta miƙe, Kaka da Ummi suka bita da ido har ta shiga ɗakinta.
wucewar minti biyu sai gata ta dawo riƙe da jaka da hijab a hannu, ta zauna kan kujera tana kallo tv tana ji tana neman kasa riƙe hawayen dake yunƙurin zubo mata.
sai bayan da su Ummi suka kammala cin abincin sannan Kaka na dubanta tace,"kinga, kinga Fillo ki kiyaye ni, na faɗa miki ki cire batun cutarwar da Amir yay miki a ranki amma kinƙi ji ko, haka kawai kina ƴar ƙarama dake kisawa kanki damuwa salon kija mana masifa, ke bama abin farin cikinki bane tunda har aka sami bayin Allahn da suka tsaya miki hukuma tabi miki hakkinki".
take kuwa hawayen da take ta riƙewa suka zubo, ta kifa kai da gwiwa tana fashewa da kuka, Ummi na kallon ƴartata da tausayawa tace,"Auta zo nan". ta taso ta dawo kan kujerar da Ummi take ta kwanta a jikinta.
Ummi na shafa kanta tace,"kina so na koma inda ba xaki ƙara ganina ba?". da sauri ta girgiza kanta da cewar,"a'a Ummina".
tace,"to ki daina kuka haka nan ya isa bana so, ki manta da duk abinda ya zama past ki focusing akan rayuwar gabanki, babu abinda zai fishsheki yanzu sama da ki mayar da hankali akan karatunki shine kawai gatanki har zuwa ranar da Allah zai kawo miki miji na gari kiyi aurenki".
bata daina kukan ba tace,"Ummi har yanzu abin yana yi min ciwo sosai".
Ummi tace,"sai ki godewa Allah da ya tona asirinsa tun bai aureki ya miki cuta me gaba É—aya ba, ki kuma gode masa da ya kareki daga sharrinsa a iya zaman da ku kai da shi".
tayi shiru bata ce komai ba, idonta na haska mata hoton jiya sanda suka je kotu ita da su Maama akan case ɗin Amir da aka ƙarke a jiyan, tana tsaye a bayan Mum taji Turaki ya kama hannunta ba tare da sanin kowa ba suka bar wajen, kuma duk ta yanda taso ta raba hannunsa da nata ta kasa har suka shiga wani ɗaki inda aka kai Amir shi da tawagarsa, kallo ɗaya tayi masa ta saurin ɗauke kanta gefe dan a duniya idan da mutumin da bata ƙaunar gani bai wuce shi ba.
kuma tsabar rashin kunya irin da azzalumin bawa wai har yake zubewa a gaban ƙafafunta yana roƙonta Allah da Annabi akan ta yafe masa abinda yay mata, sannan ta roƙar masa alƙali ya sassauta masa hukuncin da aka yanke masa na zaman prison tsawon shekara goma sha biyar, har da wai in ya fito yayi mata alƙawari zai tuba ya koma mutumin arziƙi ya aureta.
wannan maganar kuma ita tayi mata zafi bata san lokacin da ta ɗaga hannu ta wanke shi da maruka har biyu ba, Turaki kuma ya karɓi kulki a hannun police ya bata, ta dinga buga masa a fuska har sai da taga jini yana zuba ta hancinsa tukunna ta ƙyale shi tayi saurin fita daga ɗakin, in ba haka ba tsab zuciya zata iya sata ta rarumi duk abinda zai kai Amir Lahira ta buga masa.
Kaka na kallon Ummi tace,"Halimatu kinga duk inda Hamid yake yana nan hankalinsa na kanki da tunanin halin da kike ciki, fushin fa da kike da mahaifinsa ba zai fa shafe shi ba tunda ba shi yay miki laifi ba".
fuskar Ummi ta juye zuwa ɓacin rai tace,"Dada zan nemi Hamid amma ba yanzu ba, akwai lokacin da nake jira, dama in ace ma zan ƙara waiwayar gidan Hayyo to ace Auta na hannunsa ne, yanzu kuwa da bata wurinsa banga dalilin da zaisa in taka ƙafata a ƙofar gidansa saboda ina da wata ajiyar a gidansa ba, Hamid namiji ne baya buƙatata kamar yanda Auta ke buƙatata".