← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 176

Sashe 7

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta taɓe baki tayi ciki abinta. "kai kasan abunda kace, ni dai nafi ƙarfin zagi da yaren bature. Na ɗauka yau ɗin zaka tafi na baka saƙo ka kaiwa Nuratu".

Jin ta ambaci abar ƙaunarsa yay saurin cewa,"ki bada yau zan koma".

Tace,"na fasa ai". Sannan ta dubi Aliyu tace,"kai kuma É—an zaman kashe wando idan zaka tafi karka bar min tv a kunne ka kashe min".

Yusuf na fitowa yay part ɗin Ammi mahaifiyarsa, har ya shiga parlon sai ya fito sakamakon murɗawa da cikinsa yay, ya koma part ɗin Hajiya Falmata da suke kira da Umma. Step sisters ɗinsa ya tarar a parlon su biyu, Salma da Kursum. Ya ƙarasa shiga ciki ya zauna kan kujera suka gaishe shi, Salma ta miƙe tana faɗin,"bari na kira Umman".

Tare suka dawo da ita, Salma na gaba ita tana baya da waya kare a kunnenta tana bada sallahun da za'a taho mata da shi daga kano.

"yanzu ka shigo?". Ya kalli Umman da tayi masa magana yace,"na É—an jima ina wajen Inna Wuro".

Tace da shi,"aiko ga breakfast É—inka can ina ga ma yay sanyi". Ta kalli Kursum tace,"je kiyi warming abincin Yayanku".

Within 3mints Kursum ta dawo ta janyo center table ta É—ora plate É—in abincin a kai. Yana ci su na magana da Umma, tana sanar masa tafiyar Nameer da yay a É—azu, ya samu aiki a wani company da ke can taraba state.

Bayan ya sauke spoon daga bakinsa yace,"Nameer É—in yace min Daddy bai yarda da zuwansa can ba".

tace,"da ƙyar Alhaji Saleh yay conviecing ɗinsa ai, shi ne Nameer ɗin ya wuce yau da wuri".
"to Allah ya taimaka ya bada sa'a".

Umma ta amsa da amin. Sauri sauri Yusuf ke yi wajen cin abincin dan gaba É—aya hankalinsa na can wurin Ammi, fatansa ma Allah sa Yusrah bata faÉ—a mata ya shigo ba.

Yana gamawa ya miƙe yana yiwa Umma Sallama. Ta tambaye shi,"when zaka koma?".

Yace,"may be da yamma ko kuma gobe".

Umma tace,"Nuratu tayi min complain jiya da mu kai waya...".

Tun Umma bata ƙarasa maganar ba yay murmushi tare da cewan,"tare zamu tafi insha'Allahu".

Itama tayi murmushin tana cewa,"sai ka dinga haƙuri da rigimar Nuratu, musamman yanzu da ba ita kaɗai bace".

Fitowarsa daga part ɗin Umma na Ammi ya wuce, a parlo ya tarar da ita su na magana ita da yaranta, ya ƙaraso ciki kansa a ƙasa gabansa sai faɗuwa yake.
Ammi kam ko iskar da ta ɗebo shi ta kawo shi bata kalla ba, maid ɗin da ke riƙe da trolley ɗin Ammi ta durƙusa ta gaishe shi ya amsa.

Sai da ya bari Ammi ta gama magana da yaranta sannan ya gaisheta, tai banza da shi tamkar bata ji shi ba.
ta zo fita ne ma ta tuna da ƙararsa da Yusrah ta kawo mata sannan ta dakata daga fitan, ta dawo tayi tsaye akansa.

"idan ka wulaƙanta ni nayi maka shiru ba zan yarda ka dinga saka min yara kuka ba ka aje wannan a ɓangaren tunaninka...idan ba haka ba wallah ba zamu kwashe ta daɗi da kai ba, ba ruwanka da sabgar ƴaƴana ka fita a harkarsu".

Ya ɗago ido ya kalleta ta ɗauke nata daga kallonsa, muryarsa a ƙasa yace,"ita Yusran me tace miki dama?, babu wanda ya duketa balle zagi, kayan da zata fita da su ne basu dace ba akace ta sauya shikenan sai ta ɓare baki...".

Ammi ta wurga masa wani kallo tare da cewan,"ni rufe min baki, ina ruwanku da shigar da tayi, ina ce ai ba tsirara zata fita ba ko?...da ƴaƴan waccan Matar ne da kake kallonta da gashin ido ai ba zaka ce da su ƙala ba, sai nawa ƴaƴan da aka raina shi ne za'a bi a takura musu...to da gatansu tunda ban mutu ba saboda haka a bar takura musu, na faɗa maka. itama kuma Kakar taka ka faɗa mata...shima Aliyun zai shigo ya same ni".

Ya girgiza kansa kawai, kamin yace,"kiyi haƙuri".

Tana ƙoƙarin fita maganarsa ta tsaida ita,"Ammi dan Allah ki kwana ɗaya kawai".

Tace,"tunda takarda aurena a hannunka ta ke me zai hana Yusuf".

"dan Allah Ammi, wallah idan ki kai nisa da yawa gidan ba ya daÉ—i".

Tayi murmushin takaici,"har yaushe asirin da ke kanka ya kunce daka fara sanin muhimmancina acikin gidan nan?...kaima ka zama mace ka iya makirci kenan, to ni ba zaka yaudaren ba, ko É—azu baka san ina kallonka ka shigo ka fita ba ne saboda kana tsoron kada uwarka ta tsine maka...".

Yusuf yay saurin katseta da cewan,"Ammi don Allah ki daina irin wannan maganar...".

Itama bai ƙarasa ba ta katse shi da faɗin,"an riga an shanyeka ai duk gaskiyar da zan faɗa a iska zaka dinga jinta".

Yay shiru bai ce komai ba, ta ƙara cewa,"ka tashi ka kaini airpot". Yay saurin miƙewa yana karɓan jakar hannunta suka fita tare.

Tunda suka shigo motan babu wanda yay magana, har ga Allah Yusuf naso yay hira da mahaifiyar tasa amma yana tsoron ta balbale shi da faÉ—a, dan yanzu da abunda yake na faÉ—a da wanda ba na faÉ—a ba duka na faÉ—a yake zamar mata indai tsakaninta da shi ne.

Tunda yazo ma yake son mata albishir da cikin Nuratu amma yana tsoron abunda hakan zai haifar, dan bata ƙi ma tai muguwar adu'a ba tunda ba son auren nasu ta ke ba, ita duk abunda ya shafi Falmata to shikenan ta ɗaura gaba da shi, yasan da ace Nuratu ba jinin Falmata bace Ammi zata ɗan rangwanta masa akan ƙin zaɓinta da yay.

Maganarta ta kutsa cikin tunaninsa. "yarinyar da na so na haɗaku ce za'ai bikinta. Da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai ya haɗata da wanda ya fika. Ɗan governor ɗin Jigawa ne, yaron ance a ƙalla ya mallaki sama da miliyan 500. Shi ɗaya ne a wurin mahaifinsa, babarsa ita ɗaya ce for morethan 35years da suke tare da mijinta...ba irin Babanka ba da shekara 15 muka ɗauka tare yaje ya ɗauko min annoba".

Yusuf yace,"Allah sanya albarka a auren nasu".

Aciki ta amsa masa, yana kallon yanda ta ke hararsa ta cikin window, tunda yake da ita ba su taɓa fita tare ba ta shiga back seat ba sai yau, tunma bayan auren nasu dama bata yarda ta shiga motarsa, hanya ma bata so su haɗa da shi.

"Ammi Nuratu ta kwan biyu bata da lafiya". Ya faÉ—a cikin kwantar da murya.

Ammi ta dakata daga danna wayar da ta ke yi ta É—ago ta dube shi, kamar ba zata ce komai sai can kuma a hankali tace,"bata da Æ´an'uwa ne?".

Ya rumtse idonsa sosai kamin yace,"tana da su mana Ammi".

"ohh tou kuma kazo kana faÉ—a min bata da lafiya, ai su zaka je ka sama bani ba da ban haÉ—a dangi da ita ba".

Bai ƙara cewa komai ba yay shiru, Sani Abacha International Airport ya ajiyeta, bai baro wajen ba sai da jirginsu ya tashi tukunna. Yana kan hanya abokinsa Dr Huzaifa ya kira shi, saboda haka ya yanke hanya ya biyo ta shongo estate.

Slowly yake driving ɗin, Idonsa na kallon left side yana kallon wani gini da ake ƙarasawa, idonsa ya sauka akan yashin da tifa ta juye yanzu ta bar wajen.
Kamar wanda ya tuna wani abu sai ya waiga yana daɗa kallon wajen da ya bari, hoton wannan yarinyar ya haska a cikin idonsa a wancan lokacin da ya taɓa wucewa ta wajen.

Tana zaune a gefen yashi ta ƙudundune tana rera kuka a hankali, ta riƙe siririyar doguwar ƙafarta tana kallon wajen da taji ciwo cike da tashin hankali. Gaba ɗaya ciwon ba wani babba bane, amma kace wadda akace ƙafartata ce ta ruɓe za'a yanke saboda kawai jinin da ya fito a wajen ɗan kaɗan.

sai yaga kamar yanzu ne abun ya faru, dan bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba tunawa da yay da irin dramar da suka sha da ita akan kawai ta bari ya saka mata bandage akan ciwon da taji.

_"jinina zai ƙare"._ Haka ta faɗa masa a lokacin da ya tsuguna gabanta yana tambayarta me ya faru, cikin muryar kuka, kuma duk da cewar muryar tata ɗauke ta ke da kukan da tasha, hakan bai hana daɗin muryarta fitowa ba.

Ta runtse ido ma ta kasa kallon ciwon, ya koma mota ya ɗauko first aid amma ko da ya dawo sai ya tarar bata wurin, abun yay matuƙar bashi mamaki a sannan, dan zatonsa ma ko aljana ya gani ko kuma aljanu suka buɗe masa ido yau, saboda kyan yarinyar ma yafi kama da na aljanu. Kuma sai can zai bar wajen ya hangeta ta ɓoye a bayan bulo, ashe first aid box ɗin da ya ɗauko ne yasa ta guduwa.
[8/8, 00:57] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

*6*

Yau ya kasance juma'a. Ƙofar gidan na Judge Dikko Habib cike yake da ɗumbin mutane masu zuwa karɓan sadaqa, yara da manya musamman ma magidanta marasa ƙarfi, haka gidan yake kasancewa a duk wata juma'a, zaka ga mutane babu masaka tsinke tun an idar da sallar asubahi sun bi layi su na jiran fitowar Mai gidan.

Judge Dikko Habib babban alƙali ne wanda ake damawa da shi a manyan shari'ar da ta shafi cikin ƙasa da wajenta, kuma alƙalin da gwamnatin tarayya keji da shi. Dattijon ƙwarai mai halin dattako da nagarta, Yawancin zamansa a america yay, karatunsa ma tun daga secondry har matakin phd duka acan yayi.

Matansa Biyu Hajiya Ramla da Hajiya Madina amma ainihin sunanta Aina'u, Ƴaƴansa 6, uku maza uku mata. Kuma kaf cikinsu babu wanda ke karatu a nigeria duka waje yake fitar da su. Turaki ne ma kawai yayi secondry a nigeria kamin ya fita US yay degree da masters ɗinsa acan.
Chapter 7 · 0% Book details