Sashe 95
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Turaki dai sai yabi Fillo da kallo, ba wai ya manta da ita bane, tun ɗazu hankalinsa na kanta, kawai dai ba zai iya barin Mum bane, amma Allah Allah yake yaga Dr Yusuf yazo wajen. ji yake kamar yaje ya sunkuceta ya ɗauketa ya kaita inda zai zama daga shi sai ita, silent place ɗin da ba za'aji sautin komai ba sai na dariyarta, dan tabbas zai ƙara yalwata wannan annurin da yake gani shimfiɗe a saman fuskarta. zai ajiyeta akan cinyarsa yayi mata godiya da irin salon da ba'a taɓa yiwa wani mahaluƙi shi ba duk girman matsayinsa da mulkinsa kuwa.
Mum ta dubeta tace,"zo nan Æ´ata". Fillo ta isa wurinta zata tsuguna tace,"a'a zo nan". ta faÉ—a tana yi mata nuni da kusa da ita, yayinda take kallon Turaki tana cewa,"Babana matsa".
Turaki ya matsa Fillo ta zauna, Mum na kama fuskarta tace,"how are you feeling now dear?, ina ke miki ciwo?". tace,"feeling much better Mum". ta faɗa da ƙyar saboda yacca take jin babban yatsan Turaki na ƙafarsa na yawo akan ƙafarta. ga shi yana matso da fuskarsa saitin kunnenta kamar baya ganin kowa da komai a wajen, ita al'amarunsa tun before ya tafi suka fara bata tsoro, kuma kawai sai ji tayi ya ratso da hannunsa ta baya ya matsa cikinta, ta ɗanyi zillo tana jin kamar ta fashe da kuka.
a hankali ta yanda ko kaÉ—an Mum ba zata ji ba balle ta gane yace,"tanks immeasurably".
ta ɗan kallesa kaɗan ta ɗauke idonta. a sannanne suka jiyo guɗa ta karaɗe cikin asibitin, Boɗejo ce ta taho sai rawa takeyi, take kuma wuri ya ƙara kacemewa da murna.
Inna Wuro dai na gefe da sakakken baki cikin ranta tana faÉ—in ashe haka aljanu ma suke da haÉ—in kai. daga bige musu Æ´a har sunyi cincirindo haka da wannan uban daren, sai dai babu hankali sam dan taga kamar murna suke yi.
ta ratsa ta gefen su Kaka da suke tsatstsaye da Æ´an gidan su Yusuf, ta tafi da sauri zuwa reception, ta sami wasu nurses su huÉ—u a zaune suna hira, tayi musu sallama suka gaida ita.
tace,"ku ana can anata haska film kunan zaune da farin kaya kamar sabababbin gawa, a'a to ni dai da ku ka ganni kujerar zama nazo ɗauka. wata ƴar arziƙin tazo ta kai min kujera dan Allah in samu wajen zama tunda naga abin bana tsayuwa ba ne".
Nurse ɗaya ta taso tana cewa,"Hajiya kawo Babyn". ɗayar kuma da mamaki tace,"film kuma Hajiya! a asibitin?". Inna Wuro ta gyara zaman mayafi tana riƙe Farha da kyau tace,"a'a babu zancen wani in kawo Baby, sunanta Farha ba Baby ba, kuma yanzu ina ni ina baki jaririya alhalin ban sanki ba?, inje ki cuceta in shiga uku, to wallah uwarta a kotu take yin aiki tsab sai ta iya sawa a ɗaure ni ba mutunci ne da ita ba, a hannuna ta san ƴarta haka kawai in baki ki yiwa ƴar allurar tetanus ki jamin jafa'i, yo banda ma tana can tana kallon Film ina zata bar min ita, ai basa bani ita nima kuma bana karɓa saboda sunan Zainabu Yusuf ya saka mata, ummm wai ko dai sunan uwarsa yasa bacin yasan Uwar ba mutumiyar ƙwarai bace, Allah yasa ma dai kar ƴar ta yo gadon hali, dan naga goshinta iri ɗaya da na Zainabun".
Nurse É—in tai murmushi kawai. Inna Wuro tace,"yanzu dai É—aukar min kujerar muje, ko kuma sai an biya kuÉ—in É—aukar ne?".
Nurse É—in tai Æ´ar dariya tace,"a'a Mama, kula daku ai aikinmu ne, muje". ta faÉ—a tana É—aukar kujerar.
Inna Wuro tace,"a'a in ma kince sai an biyaki ai sai a biyaki, albashin da ake baku dudu nawa yake, kuɗin fa abincin rana ɗaya ne da Amadu yake kashe mana, muje wallahi sai in sa ya baki wani abin ai ɗana yana da kuɗi, shisa ma kaf nabi Malaman duniya nace suke masa adu'a kar a sawa kuɗin ido su ƙare da wuri mu shiga uku mu gantale acin ɗumamen safe, shayi kuma ba madara balle isassan sikari".
Nurse ɗin tayi gaba tana ƙunshe dariyarta, Inna Wuro na lura da hakan tace,"a'a wallahi dawo ki ajiye in ɗauka da kaina, sam bana haɗa hanya da ƴan banza irinku, shisa kaf ƴaƴan Amadu da Kursum ce bama shiri saboda irin wannan munafukar dariyar, sai inyi magana a wani ƙunshe dariya saboda ga taɓaɓɓa na magana ko?, to Allah ya isar min dan ba yafe miki zan ba, yanzu tsakani da Allah wani yazo wucewa ya gani ai sai yace min sannu, to sannu ina lafiya ƙalau ai zagi ne da cin mutumci, gaskiya ajiye kujerarki bana so na ɗauka da kaina, dama ku yaran asibitin nan duk ƴan banza ne sam baku da mutumci wallahi, kullum sai mutane sun kai ƙararku radiyo tsabar ba kwa so ku gama da duniya lafiya, to wallahi ni babu ruwana a lahira kuna kallo zan yi gaba in shige aljannah salin alin ku kam kuna baya ana ramawa talakawa abinda ku kayi musu".
Nurse ɗin tace,"yi haƙuri Mama bada ke nake ba".
Inna Wuro ta haɗe rai tayi mata wani kallo tace,"wato ke harda halin ƙarya irin na Aliyu kina da shi kenan, ina ganinki da idona kina ce min bada ni kike ba, to kawai na barwa Allah abar zancen bana son sabuwar fitina bacin wadda nake ciki". tasa ƙafa tayi fatali da kujerar, ta nemi wata ta ɗauka tayi gaba sai masifa take yi.
sai da zata bar wajen kuma sai ta dawo murya ƙasa-ƙasa tace,"ba zaku zo kallon ba ne?, ai ko dai zaku yiwa kanku dan zaku rasa na ɗorarwa, kunga yanda jama'a suka cika wajen akayi maƙil da ƙyar ake numfashi, to dai za'ai babu ku wallahi indai baku zo ba dan faɗan aljanu da mutane ne, ɗana Aliyu ne ya kashe musu ƴarsu suka zo cin Uwassa Zainabu, ni dai du Allah kuzo ina gayyatarku kallo, ku taho da kujeru kuma ku sami na takawa dan anyiwa wajen rumfa nima sai na taka zan hango abinda ke faruwa, dan baku ga yacce suka zo da makamai suka yiwa wajen ƙawanya ba, ni yanzu so nake ma suce ba akan Aliyu zasu ɗau fansar ba akan Zainabu zasu ɗauka, ni dai da nayi sati ban bacci ba saboda tsabagen murna".
jiyo tashin hayaniya ta tafi da sauri,"kai kai kai na tafi kar ayi babu ni, kar a shanye ƙafar Aliyu banga ta yanda akayi ba in kasa bada labari".
Nurses ɗin na dariya suka biyo bayanta da sauri suma, ita dai sai jan kujera take tana ɗaga ƙafarta me ciwo da ƙyar, ɗayar nurse ɗin ta dage sai da Inna Wuro ta tsaya ta bata Farha, ta bata ita tana cewa,"ni da ace da jakar goyo ma sai ku ara min in sakata aciki kar inje tashin hankali yay tashin hankali nayi ta kaina in yasar musu da ƴa a wajen ban sani ba".
suka gimtse dariyarsu Nurse Raliya tace,"zan riƙe miki ita Mama".
tace,"aiko dai Allah rabaki da sharrin zaurawa ya haÉ—aki da saurayi me irin zuciyar É—ana Amadu, ya rabaki da sharrin samarin zamani masu munin hali irin na Aliyu".
ta amsa da amin. tana tafe sai faman sauri take tana cewa nurses ɗin,"amma fa kuyi shiri ku riƙe takalmanku a hannu dan da zarar an fara sare-sare ta kaina zanyi in barku, dan ba zan tuna ma ni na gayyatoku ba, ku taho da sauri dai kar ayi a gama babu mu".
kuma duk bakin room ɗin da Inna Wuro tazo wucewa sai ta leƙa tace,"jama'a ku fito ana faɗan aljanu da mutane ana can ana faman shanye ƙafafu, dan Allah ku fito jama'a ku taimaka mana kar a kashe jikana Aliyu, wayyo na Annabi ku taimaka jikana yana cikin masifa ya kashe ƴar aljanu, ku kawo mana ɗauki dan Allah, jama'a da yawa sun taru an rasa yanda za'ai da su kowa yabi su da kallo ana zazzare ido".
jin wannan yasa mutane aka dinƙa fitowa ana ta faɗin subhanallah da innalillahi, dama tun ɗazu suna ɗan jiyo hayaniyar, kan kace me wannan wuri ya ƙara ɗinkewa da mutane kamar cinema, Inna Wuro ta rasa wajen ratsawa ta wuce sai ta tsaya daga gefe ta ƙwalla wata razananniyar ƙara da tasa a lokaci ɗaya akayo kanta.
kamin a rufeta tayi saurin jan kujerarta tabi ta gefe ta wuce ta samu wurin da zata bawa idonta hakkinsa, ta zauna tana ɗaga kai sai kalle-kalle take tana kiran,"ƙawayena masu farin kaya da na gayyato kuna ina?, gani anan tsakiya idan kun jini ku ɗaga hannu in zo in shigo da ku, ga sarauniyar aljanun nan duk an rungumeta ku hasko waya ku ɗaukarwa duniya".
wani takaici ya turnuƙe Dr Yusuf, ya dinga kallonta yana jin kamar ya kai mata duka, Aliyu da ya dawo hayyacinsa ya ɓata rai yazo yana ce mata,"wai ke dan Allah mene haka?, jifa yanda kika tarowa mutane jama'a, ke ko ina akaje sai kin yarfa mutane, kinga tashi kawai mu tafi gida kamin ki gama ɓararwa da Daddy mutunci".
ko kallonsa bata yi ba tasa hannu tana turesa gefe. "yo Aliyu tunda dai ba naka mutuncin zan ɓarar ba me kuma ya shafeka". ganin yaƙi matsawa ta zabga salati tana nuna masa can gefe da cewar,"mun shiga uku ga Zainabu can ta yanke jiki zata faɗi". Aliyu yay hanzarin matsawa yana wurga idanuwa, ta kallesa tai dariya tace,"ɗan ƙwal uba addababbe".
ta buɗe idanuwa duka tana ƙara kallon su Hajiya Madina da su Kaka waɗanda a yanzu suka haɗe wuri ɗaya, waje ya zama kamar gidan biki, Hajiya Madina na rungume da Fillo tana cewa,"tabbas ke ɗin alkhairi ce, kin zama haske a cikin rayuwarmu tunda kika kusance mu, insha'Allahu nayi ɗamarar faranta miki Fillo har ƙarshen rayuwata".
Daddy ya ƙaraso inda Inna Wuro take zaune tayi ƙyam da ido a waje ɗaya tana ta aikin kallon bidirin da har yanzu bata fahimci kansa ba ma. in zaka yanka wuyanta ba zata ce ga abu ɗaya da taji an faɗa ba tun ɗazu, balle tace maka ga akan ainihin abinda yasa ake wannan murna, ita dai abu ɗaya ta barwa kanta dukansu aljanu ne kuma uban Aliyu suka zo ci.