Sashe 139
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai saurari abin da take faÉ—a ba ya haÉ—eta da jikinsa yana hugging É—inta very tight, ya ware duka five fingers É—insa a gadon bayanta, gently yake shafa very soft skin É—inta, lokaci É—aya yaji yanayin jikinsa na sauyawa gaba É—aya, a hankali ya sunkuyo da fuskarsa yana neman lips É—inta ya haÉ—e da na shi ya tsotsa, kamar wanda aka tsikara kuma sai ya fasa ya É—ago kansa yana girgizawa, ya buÉ—e idanuwansa da suka fara rinewa yana kallon yacca duk jikinta ya É—auki rawa sai kuka take yi masa a hankali.
ya sarƙe yatsunsu wuri ɗaya yana ɗora goshinsa a nata goshin, murya a kasalance yace,"sorry".
ta gyaÉ—a kanta kawai tana ce masa,"ni É—akina zan tafi".
ba tare da ya buÉ—e idonsa ba yace,"bana so ki tafi, ki zauna anan yau muna tare".
sai ta buÉ—e ido tana kallonsa, yanayin yanda yake maganar kamar ba muryarsa ba.
bata san lokacin da bakinta ya suɓuce da tambayarsa,"menene?".
a sannan ya buÉ—e lumsassun idonsa ya kaÉ—a ma ta kai,"nothing".
ya faÉ—a yana sauke numfashi,"me za kiyi a É—akin naki?, ko can zamu koma?, ni bana son zama ni É—aya".
tana ƙifta idanu ta ce,"tsoro kake ji?". ya ɗaga mata kai alamar ehh tare da cewa,"da kika shiga wanka naji kamar za'a kama ni".
sai ta turo baki gaba ta ce,"ba wani nan".
ya matsa hannunta ya ce,"me kike nufi?".
ba ta ce da shi komai ba sai kare ƙirjinta take yi da ɗayan hannunta.
yana riƙe da hannunta suka isa bakin mirrow, ya zaunar da ita akan stool, ita dai sai kallonsa take ta cikin mirrow ɗin yanda yanayinsa ya koma kamar na mara lafiya, ya ɗauko lotion ɗin da yake shafawa ya ajiye mata, baya tunanin zai iya aikin shafa mata dan za'a iya samun matsala, ba yanzu yake so komai ya kasance ba, zai ci gaba da daurewa zuwa lokacin da ya ɗaukarwa kansa.
ta ga ya bar wajen ya isa gado ya ɗauko babban kwalban humra ya jiye a saman mirriow ɗin, tafin hannunsa a saman haɓarta ya juyo da fuskarta yana ma ta nuni da kan gado ya ce,"your dress".
sai kawai ta bi kayan da ido kafin ta gyaÉ—a masa kai, ba tare da ce komai ba, kuma ba tare da ta kalle shi ba.
tana kallonsa ya fice daga ɗakin jiki a saɓule kamar mara lafiya ko wanda aka yo aiken mutuwa, duk sai taji kamar yana neman bata tausayi, ko me akayi masa oho?.
sai da ya fita sannan ta iya ɗaukar man ta shafa, tana mita ƙasa-ƙasa ta ɗauki humrar ta shafa, kawai yaje ya ɗauko mata sabuwa alhalin ga buɗaɗɗu nan har guda uku a ajiye, tana gama shafawa ta wuce kan gado, tunaninta ɗaya pant da pad, kuma da mamakinta tana ɗaga kayan sai ga pad ɗin haɗe da sabon pant, wata uwar kunya ta lulluɓeta, yaushe ma ya san tana period ɗin?.
tana murguɗa baki ta shiga toilet ta saka, garin ɗauko brezier ɗinta ta zame ta faɗa cikin bathtube ɗin ta jiƙe, ta rumtse ido kawai ta fito bayan ta shanya, cikin sauri ta ɗauki kayan ta saka gudun kar ya dawo.
tana saka rigar taji kamar ta kurma ihu, ya san kuwa kayan da ya ɗauko mata?, ita kam bata jin zata iya saka kayan nan alhalin yana nan, duk rigar tayi transparent, kuma iyakar gwiwarta fa, hannun ma irin na vest, kuma ma ko ya haɗo mata da brezier, sai kawai ta doki ƙafafu a ƙasa da ƙarfi kamar tiles ɗin sun mata laifi.
ƙofa ta nufa zata fita sai dai tana zuwa taji ƙofar a rufe ya saka key ta waje, ta cije leɓen ƙasa ta juya ta koma toilet ɗin, ta ɗauko brezier ɗin sai dai ba zata saku ba don sosai ta jiƙe.
fitowa tayi tana hawaye, gado ta nufa ta durƙushe a wajen ta kifa kai tana kuka, can jimawa taji an buɗe ƙofar, bata ko ɗago ba dan ita haushinsa take ji, shi ma kuma da ya shigo ɗin kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, ya wuce ya ajiye basket ɗin abincin dake hannunsa, ya fito da cooler ɗin ciki ya ajiye akan table.
bakin gadon ya dawo ya zauna, ya É—agota ya É—aurata saman cinyarsa tare da zagayeta da hannayensa ya ce,"kukan na menene?, me Fulanin Turaki ke so?".
ta É—ago da kanta, tana matse idanu tamkar baby Æ´ar 2years ta ce,"ni É—akina zan tafi".
É—an murmushi yayi yace,"naji to za ki koma can É—in but tare zamu tafi ko?".
tai saurin girgiza masa kai, ya ƙara cewa,"why?".
"to ai kaima ga naka, kowa ya zauna a nasa ai".
ya buɗe ido yana kallonta sosai kafin ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana shaƙar ƙamshin humrar da ke fita a jikinta.
da wani irin murya yace,"to ni yau tsoro nake ji, ba zan iya kwana ni ɗaya ba, in kin yarda na bi ki ɗakinki, na yarda ko a ƙasa ne zan yi shimfiɗa, but please karki tafi ki barni ni ɗaya bana so wani abun yazo ya kamani, ba zan iya ƙwatar kaina ba".
Fillo ta dinƙa kallonsa kafin ta ce,"kai ne ɗin kake jin tsoro?".
ba tare da ya É—ago kansa dake kafaÉ—arta ba ya É—aga mata kai kawai. sai kawai ta tsinci kanta da kama hannunsa ta ce,"to amma jiyan nan ai kaine ka kori abun da yake biyo ni".
"to ai jiya kika ce, yau indai yazo to sai dai ya cinyemu dukanmu, kuma da ma jiyan ma ai ƙarfin hali nayi na zama jarumi saboda bana so wani abu ya taɓa ki".
tayi shiru ba ta ce masa komai ba, ya É—ago kansa ya kalleta ya ce,"shikenan ma kawai, zan tafi gidan su Bello".
ta kalle shi suka haɗa ido ta girgiza masa kai da sauri, sai kuma ta sauke idonta ƙasa tana jan yatsunta.
"ai dare yayi yanzu".
hannu yasa ya ɗago haɓarta ya ce,"look in to my eyes".
sam taƙi sai ma ido da ta daɗa rumtsewa. idanuwansa na neman lumshewa ya zura hannunsa cikin rigarta, tana jin hannunsa a ciki tayi saurin buɗe ido ta zabura zata miƙe ya riƙeta, flat tommy ɗinta ya shiga shafawa yana faɗin,"na san wannan shafaffan cikin na buƙatar abinci ko?".
magana yake yi duk yay wani collapse.
ta É—aga rigar ta fito da hannunsa tana cewa,"ni ka bari".
yay knooding ma ta kansa, ɗaukarta yay zuwa kan kujera ya ajiyeta, ya buɗe cooler ɗin abincin, nan da nan ɗakin ya karaɗe da ƙamshin ƙwai. ta bisa da kallo a sanda yake ɗauko plate ya zuba soyayyar doya da ƙwai da kuma miyar souse, bayan ya gama zubawa ya juyo ya fuskanceta, da hannunsa ya ɗauki doyan ya kai bakinta.
"wa ye ya dafa abincin?". taji bakinta ya suɓece da yi masa tambayar.
"Zaytun nasa ta kawo mana, i know ba ki da lafiya, and ba ki iya girki ba, so na roƙeta alfarmar take dafa abinci tana kawo mana before na kai ki catering school ki koya".
ta tsuke fuska tana kallonsa ta ce,"ni ce ban iya girki ba?, wancan ranar da na dafa indomie ai kace na iya dafawa".
ya ce,"amma ai bance yayi daÉ—i ba ko?".
ta turo baki gaba ta kauda fuska gefe,"Allah na iya girki nima, kuma ka tambayi Maama kaji, Baffa ma da yaci wainar masar da nayi sai da yace yayi daɗi Allah yay min albarka, Adda Zaytuna ma indai zata yi baƙo in tana asibiti tana sawa nayi mata, kuma ka tambayi abokinka ɗin kaji, kuma ma ka tambayi Kaka kaji tun ina ƴar ƙarama nake yin girki".
ya dinƙa kallon bakinta yana murmushi, har tayi shiru bai yi magana ba, jin shirunsa yasa ta juyowa tana kallonsa ta ce,"Allah na iya girki".
ya rufe ido ya buɗe ya ce,"ai tun kina ƙarama kika ce".
tai saurin cewa,"a'a nufina tun ina ƴar ƙarama nake yi, ko time ɗin ma da muna masarauta ina yi".
"ohhh yanzu kenan ke babba ce?".
kamar jiran tambayar take yi ta ɗaga masa kai, murmushinsa me sauti ya fito yana cewa,"to ni ban ga girman ba, you are still a Baby in my eyes, dan haka ni ba zan ci abinci ƴar ƙarama ba babu daɗi, rabi ya dahu rabi bai dahu ba, ko yay ta ƙauri, ko a cika gishiri".
su ka haÉ—a ido ta haÉ—e gira waje É—aya ta murguÉ—a masa baki, yasa yatsa ya É—alle bakin nata.
"oya ba rigima na ce ba, abincin za'a ci, buÉ—e bakin".
saboda yunwar da take ji ta buɗe bakin tana karɓa, sai da ya gama bata sannan ya matso kusa da ita sosai, ya ce shi ma ta ba shi hannunsa ya gaji zai karye, yay ta narke ma ta yana koma ma ta ƙaramin yaro, da taƙi ya ta shi zai bar wajen yana cewa ya fasa kira ma ta Ummi ɗin, babu shiri ta ɗauka plate ta kamo hannunsa ya dawo ya zauna ta shiga ba shi, kuma yaƙi yarda ta ba shi da spoon dole sai hannu ta saka, duk kaiwa ɗaya sai ya cije hannun nata, har ta gama ba shi bata yarda sun haɗa ido ba kanta na ƙasa, sai dai tana ta murmushin da ta rasa dalilinsa.
duk yanda Fillo ta cije ta noƙe akan ba zata bi shi toilet ba sai da yaja ta suka tafi tare, da kansa yay mata brush, sannan shi ma yay nasa, su ka fito yana ɗauke da ita rungume ajikinsa, ita kuma tayi laƙwas ta lafe a jikin nasa kamar mage, ya wuce yay switching light off sannan ya kunna deem light, tukunna ya wuce kan gadon, ita dai duk sai kunyarsa take ji.
ko a kan gadon ma a jikinsa ya kwantar da ita, murya can ƙasa ya ce,"Fulani nah".
ta ce,"uhmm". ya shafo gashin kanta da yake jin laushinsa da santsinsa na shiga jikinsa ya ce,"mu bari sai Allah ya kaimu gobe sai a kira Ummi ko?".
ta girgiza kai da sauri,"a'a yanzu dai".
"to ai dare yayi, kar tayi tsammanin wani abu ne ya faru".
kamar zata yi kuka ta ce,"ni dai don Allah yanzu".
ya sauke numfashi ya ɗauko wayarsa ya bata, ta miƙe daga jikinsa tana cewa,"remove the password".