← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 176

Sashe 5

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ɗauko chips ɗin zai kai baki sai ya dakata saboda Zaytuna da ta faɗo a ransa, duk da cewar tana cikin ransa a kowacce bugawar daƙiƙa. To amma dai a yanzun ba ya jin zai iya saka komai acikinsa idan har itama babu abunda taci.
Wayarsa ya É—auko ya kira lambarta, kira na farko bata É—auka ba sai ana biyu shima sai da ya kusa yankewa.

"Hellow Hammah nah". Ta kira sunan nasa cikin muryar bacci.

Yatsun hannu basu isa sun ƙirga adadin farin cikin da ya shiga ba da jin muryarta. Ya sauke numfashi sannan yace.

"ba za ki daina wannan malalacin baccin naki ba ko Zaytun?".

"Hammah nah jiya bamu kwanta da wuri ba ne, ka san Boɗejo tazo...to ta tsaremu da wannan hirar tata mara ƙarewa bamu ankarewa ba sai gani mukai lokaci ya wuce".

"yayi muku kyau ai, kuyi ta biye mata tana hanaku baccin kirki, bayan ita ta riga tayi nata tun yarinta".

Zaytun tayi murmushi me ƙarfin sauti ba tare da tace komai ba, kasancewar ita ɗin ba mai yawan magana bace.

Turaki ya ƙara cewa,"dama i just call to check on you, I hope all is well?".

"komai lafiya Hammah nah".

Yay ɗan jim before saying,"idan kinyi breakfast let me know...amma yanzu fa za ki tashi bana son zama da yunwa, ki kalla time ki gani ƙarfe nawa".

Ba tare da ta duba komai ɗin ba tace,"Yanzu fa Safiyan yay Hammah". Tayi maganar a shagwaɓe.

"shafo cikinki sai ki faÉ—a min yanda yake".

Ta kai hannu kan stomach É—inta sannan tace,"Hammah yana nan yanda ka san shi a shamule".

"to kinga alamar yana buƙatar abinci kenan, i keep telling you babu namijin da zai ɗauke ki alhalin yasan cikinki da bayanki a haɗe suke, he will be thinking you can not bear him a child".

Tabbas ya faɗi maganar ne to entertain her, kuma hakan ce ta kasance, dan sai da tayi dariya sosai har baccin da bai bar idonta ba ya saketa lokaci ɗaya, ta miƙe zaune akan gadon tana ɗora pillow akan cinyarta, fuskarta cike da annashuwa tace da shi.

"ni da nake so ko da Allah bai azurtani da ƴaƴa da yawa ba, ya bani guda ɗaya tilo da zan saka masa sunan Hammah nah. Dan haka dole na tashi naje naci abinci ko da banyi niyya ba...ni Hammah idan ma kaga ana tallan maganin da ke ƙara tumbi ka sayo min kawai".

Turaki yay siririyar dariya da cewar,"wasu na neman ragewa mu kuma muna neman na ƙari".
Yay maganar yana mai duban agogon hannunsa sannan yace,"zan wuce office na kusa late".

Daga haka su kai sallama cike da kewar juna.

*After 10minutes, Growth Stack Software.*
*Zone 5, 1st Floor Novare Central, Dalaba St, Wuse 900285, Abuja.*

Motarsa ta shigo cikin company ta ƙarasa zuwa wurin da aka tanadarwa ma'aikata domin aje motoci. Tun kafin ya ƙarasa buɗe murfin motar wani tsoho ya ƙaraso wajen cikin sassarfa.

"sannu da zuwa ranka ya daÉ—e".
"yauwa Baba sannunmu". Ya faÉ—a yana fitowa daga motar ya rufe.

Tsohon ya buɗe bayan motar ya ɗauki ƴar ƙaramar jakar laptop ɗinsa, sannan yay cikin office ɗin da ita. Shi kuma Turaki ya mara masa baya, tunda staffs ɗin wurin suka ganshi suke ta rissinawa su na gaida shi matsayinsa na Managing Director a ma'aikatar.

Bai shiga office É—insa ba kai tsaye ya wuce zuwa ofishin Manager, ya É—auki kusan 5minutes sannan ya fito ya wuce nasa office É—in bayan Manager ya shaida masa ya tsayar musu da lokacin da zasu shiga meeting É—in.

Zamansa kenan akan kujerarsa sai ga Saktariyarsa ta shigo, ta aje record book ɗin da ke hannunta a saman table ɗinsa, ya janyo shi zuwa gabansa yay rubutu ajiki sannan ya ƙara miƙa mata. Ta ɗauka sannan tace da shi.

"ranka ya daÉ—e PWC sun shigo tun aroud 8:30".

Ya ɗago daga kan computernsa ya kalleta, yana mai ɗan ƙanƙance idonsa cikin yin nazari kafin yace da ita.

"dama muna da Appointment ne da wasu this week?".

"a'a ranka ya daÉ—e, nima dai nayi mamakin zuwansu..to amma da suka ce min daga ofishin Manager suke sai na tsammaci shi ya turo su wurinka".

Ta faɗa tana buɗe wani file na daban da ke hannunta ta ciro wani envelop a ciki, sannan ta miƙa masa. "sun ce na baka wannan".

Duk a cikin harshen turanci ta ke maganar. Ya miƙa hannu ya karɓi envelop ɗin ya buɗe, cikin seconds ɗin da ba su haura 10 ba ya gama karanta abin da ke jikin takardar. Bayan ya gama ya miƙa mata tare da cewa.

"ki kai office É—in Manager, zamu yi waya da shi yanzu".
Ta rissina tare da karɓa sannan ta fita daga office ɗin.

Don Allah share to other groups🙏

Youtube Channel-NISHADI MULTIMEDIA
[8/7, 18:42] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*

*5*
Fitarta da minti biyar akai knocking É—in door, ba tare da ya É—ago kansa daga kan system ba yace,"yes come in".
Muryar nasa ya fito a hankali yayin da hannunsa guda ke dunƙule a gefen bakinsa.

Bello ƙaraye ya shigo cikin office ɗin ya zauna akan kujera, ya fuskanci Turaki da har yanzu bai ɗago ido ya kalle shi ba yace da shi.

"sai yanzu ka ga damar fitowan?".

Turaki na typing a Laptop yace,"kai ma dai kasan ba mata gare ni ba balle na sami me tashina da wuri".

Bello Ƙaraye yay masa wani duba yace,"tun yaushe ake cewa kayi auren kaƙi. ni na rasa ruwan idon uban me ka tsaya yi da har yanzu ka rasa macen da tayi maka".

Turaki yace,"Lokacina ne bai yi ba, ko kaga nayi girman da za'a dinga tarata da maganar aure ne?".

Bello ya harare shi yace,"sannu motsin gado".
Turaki yace,"Yauwa, don haka sai a barni na sarara".

Bello ya ƙara cewa,"yanzu Asma'u ɗin ma bata yi maka ba?".
"yes, she is not beautifull enough, and you know me well bana son abu mara kyau...idan kana sonta ka ƙara ata biyu na bar maka".

Bello dake masa wani kallo yace,"Ba ka da hankali...let close the charpter kamin ka ɓata min rai. kuma bari na faɗa maka, ka daina discouraging mutum akan abunda kai bai yi maka ba alhalin shi yayi masa, Ishaq told me you were telling him to get rid of that girl after all kasan yayi magana da iyayen yarinyar nan...tsaya ma! just because you think the girl was too local shikenan sai akace ba za'a aureta ba?".

Turaki yay guntun tsaki yace,"ka zo muyi magana akan aiki ne ko kuma zamu tsaya kan shirmen zancenka ne, da baku da aiki sai zancen soyayya, mace, aure".

Har yay shiru sai kuma ya ƙara cewa,"to for what reason ma yana da degree har biyu zai je ya ɗauko yarinyar da she didn't even finish secondary school".

"to kai ina ruwanka?, shi ai yasan da hakan yaje ya É—auko ta ko".

Turaki yay tsaki, Bello bai ce da shi komai ba ya fiddo laptop É—insa daga cikin jaka. Yay danne danne ya juyar da fuskar laptop É—in yana nunawa Turaki.

"Na sami number'n contractor É—in, zanyi waya da shi zuwa dare".
Turaki ya faɗa sanda ya gama karanta rubutun da ke jiki, sannan ya miƙe daga kujerarsa zuwa gaban wata drower da tarin takardu suke a cikinta.

Bello Ƙaraye na binsa da kallo har ya taka steps, hannunsa ya kai cikin drower ɗin yana fito da wani file ƙunshe da takardu fal a ciki. Ya dawo kan kujerarsa yana duba takardun cikin file ɗin. Bayan yay musu ɗai-ɗai ya kwashi wanda zai amfani da su ya wuce cikin madaidaicn parlon cikin office ɗin, daga bisani Bello ya mara masa baya.

Tsaye ya tarar da shi yana fuskantar gilashin windo, ya harɗe hannunsa guda ɗaya ta baya. Idanunsa na kafe ne akan glass ɗin kamar mai son ɗakko wani abu ajiki. Bello ya zauna kan kujera yana ƙarewa tsayuwar Turaki kallo, tsayuwar nan tasa mai cike da ƙasaita da taƙama, kana kallo zaka san an gaji sarauta cikin jini da asali.

Sanyin Ac yasa idanuwan Turaki lumshewa, muryarsa a kausashe yace, "tunda naji ana talking of billions tunanina ya bani da akwai wata a ƙasa".

Ya faÉ—a sannan ya juyo ya zauna kan kujerar da ke fuskartar Bello, ya shafo fuskarsa da duka tafukan hannunsa biyu kamin yace,"dole ne ma ba zamu yi aiki da wannan company É—in ba".

Bello ya dube shi da mamaki yace,"saboda me?".

"yanzu Accounter suka fita shi da mutanen nan".

"ta ina kai ka gansu?".
"a bakin gate suka tsaya, shi kuma ya fita da mota ya É—ebe su".

Ya faɗa ƙwayar idonsa na haskawa da dimbin ɓacin ran da ke ciki, ya ɗora ƙafafunsa kan table ɗin na tsakiyarsu, sannan ya koma ya jingina da kujerar da yake zaune.

Idanunsa a kulle yake cewa,"rayuwa cike ta ke da marasa halacci, ko kaÉ—an bana son mutum mara gaskiya".

"So now how are we going to tackle this problem?".
Bellon ya faÉ—a shima in astonishing at what Turaki had said.

"na san yanda zanyi tackiling É—in abun, let's get out of the meeting first".

*Gombe, Dukku.*
*Alh. Ahmad Alfindiki Residence, 8:30am.*

"Kaima ai ka sa ni, it's either na kwana gida ko kuma na wuce gidan Khalid, na tsani kwana a hotel if not necessary".

Yusuf ke magana a wayan da ke maƙale a kunnensa, yasa key ya rufe motan sannan ya wuce ɓangaren Inna Wuro wato Kakarsu, har lokacin da ya shiga parlonta bai gama wayar ba.

Inna Wuro na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun parlon ta kalli Yusuf da ya duƙa yana cire takalminsa, ta taɓe baki ta ɗauke kai taci gaba da kallon tv da ta ke.

"yes kusan 2 weeks ma kenan, but i think i will be coming back next tomorrow by God willing. Becox akwai patient É—in da nake da ita acan".

Yaci gaba da wayar yana ƙarasowa ya zauna kan 1 seater. "alright i will you call before then insha'Allah".
Chapter 5 · 0% Book details