← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 176

Sashe 103

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Bello yaga ransa ya ɓaci sosai sannan ya juya ya fita, yana faɗin,"sannu me mata". Turaki ma yabi bayansa da sauri yasa key ya rufe ƙofar.

yana kallon Bello tsaye ta ƙasan ido yace,"maye kawai".

Bello yay ƙwafa yace,"ka buɗe ɗakin sai in nuna maka ƙarshen maita a gaban idonka".

Turaki yaja tsaki yay gaba bayan yace masa,"mahaukaci, kuma ka bar min ƙofar ɗaki in ba haka ba na dawo na sameka Allah sai na ji maka ciwo".

ana idar da sallah ko cikakken azkar bai yi ba ya baro masallacin, kuma tun bai shigo gida ba ya kira Zaytuna yace ta kira Ummi ta faÉ—a mata Fillo zata kwana a wurinta.
Zaytuna da É—an tsoro tace,"but Hammah kasan at any time Mum zata zo É—akinka ko".

yace,"zance mata zan kwana office saboda wani aiki".
yana faɗar hakan ya kashe wayarsa yaci gaba da tafiya a gaggauce, a parking lot ya sami Bello ya fito zai tafi, bai ko tsaya ba ya wuce shi fuskar nan babu ko annuri kamar bai taɓa sanin Bello ba, Bello ya bisa da kallo yana dariya sosai.

sai da yay me isarsa sannan ya É—aga wayarsa ya kira Turaki, yana picking yace masa,"in tafi?".

Yace,"ehh tafiyarka". daga yanda yake maganar a daƙile yasan haushinsa yake ji.
yace,"baka buƙatar shawarar tawa kenan?".
yace,"ehh bana buƙata". ya faɗi hakan yana kashe wayar.

tun a masallaci hankalinsa ke kan Fullo, yana tafiya yana haɗa hanya saboda rashin ganin hanyar da kyau, hoton fuskarta kawai ke haska masa, a yanzu ma da zai buɗe ɗakin hannunsa duk rawa yake yi. yana buɗewa ya ganta tsaye a bakin ƙofar dama jira take yi a buɗe, ganin tana neman saka kai ta fice yay saurin tura ƙofar ya saka key ya kama hannunta ya kaita bakin toilet yace,"shiga ki alwala".

ya faÉ—a yana tamke fuskarsa dan yaga kamar sai yayi hakan tukunna zasu dai-dai da ita.

kuma bata musa ba ta shiga toilet ɗin jikinta sai kyarma yake, ba jimawa ta fito tana kyaɓe fuska kamar zata yi kuka tana yarfe hannun me ciwo, ya kamo hannun ya dinga hura mata iskar bakinsa me ɗumi har sai da ruwan wajen ya tsane tukunna ya ƙyaleta. ya riƙe hannunta yaje ya shimfiɗa mata darduma ya buɗe closet ɗinsa ya ciro sabon hijab da Granny taje saudiyya ta taho dasu ta raba musu tace suyi kyautarsa, shi kuma baida wanda zai bawa hakan yasa ta ajiyarsu suna nan kusan guda biyar.

Fillo taƙi karɓar hijab ɗin har hannunsa ya ƙage, ya ƙara ɗago da hannun ya miƙa mata taƙi karɓa, shi dai ya san mayafinta na mota balle tace da shi zata yi.

ita ko ta bisa da kallo da mamakin zuwan hijab cikin kayansa, zuciyarta taji tana neman dasa mata wani banzan tunani tayi saurin kawarwa, itama ta haÉ—e rai daidai da yanda ya haÉ—e nasa ta turo baki ta bar kusa da shi ta tafi kan dardumar tana kunce É—ankwalin kanta ta yafa.

kawai sai ya tsaya yana kallonta da mamaki baki a buÉ—e yace,"a hakan za ki sallar?".
ta ɗaga masa kai kawai, abinma sai ya kusa basa dariya, ya tafi yaje ya tsaya ta gabanta yana ƙare mata kallon mamaki da kyau, bilhaqqi da wannan guntun ɗankwalin zata yi sallar tunda gashi har kabbara tayi, mamakinsa bai ƙare ba kawai yaji ta fashe da kuka tana cewa,"to ni ba zanyi da wannan hijab ɗin ba".

ya kalli hijab É—in ya kalleta sannan yace,"ba'a sallah da irinsa ne?". ya tambaya da gaskiyarsa saboda irin me kwalliyar nan ne na saudiya.

taja majinar hancinta tace,"ni kawai ba zanyi da shi ba".

ya ƙara gyara zaman hannunsa a ƙirji yace,"saboda?".
tace,"to ai ban san na waye ba".

Yace,"aina kika ga na É—auko?".
ta É—an kallesa tace,"to me ya kawo kayan mata cikin kayanka?".

Yace,"sawa nake idan zan fita".
bata kulasa ba kawai ta tsuguna ta É—auki dardumar ta bar wajen ta sauya wuri, zata tayar kawai taji ya saka mata hijab É—in yana gargaÉ—inta akan,"Allah kika yi gigin cirewa sai na ji miki ciwon da yafi na É—azu".

Ta kallesa tace,"da ma kana sane?".
ya bar wajen yana faÉ—in,"ehh ina sane sai ki rama".

tayi masa shiru ta tayar da sallar, saboda bata son lokaci ya ƙure mata shisa ma bata sa masa darun sai ya buɗe mata ƙofar ta fita ba. tana idarwa ta yasar da hijab ɗin a wajen ko adu'a bata tsaya yi ba ta nufi ƙofa, ta dinga murɗa handle taji ta kasa buɗewa, sai tayi ƙasa da murya ta shiga roƙonsa tana cewa,"dan darajan Allah kazo ka buɗe min, Maama ce fa ta kirani kuma ko wurinta banje ba, kaje ka ɓallo min yatsuna, kuma ni Allah bana so kake min irin haka, na faɗa maka bana so babu kyau kana kawo ni ɗakinka ka kulle, babu kyau kana taɓani, kuma ai yanzu kai ba yaro bane tunda ka yi aure ka daina irin haka".

ya É—aga ido yana kallon yanda ta rufe ido tana ta maganar kamar me shirin sa masa duka, yaci gaba da buÉ—e ledar kazar da ya É—auko yace,"zan buÉ—e miki amma sai in kiyi duk abinda nace".

tace,"ai nasan halinka".
yace,"wane hali gare ni?".

tace,"ai ko nayi ba zaka buÉ—e ba". yace,"ki ci gaba da saka ni magana kici gaba da zama anan, tunda nace miki zan buÉ—e ai zan buÉ—e, but in kinyi abinda nace".

tana hararsa tace,"to rantse da Allah". kamar ƙaramin yaro yace,"Allah da gaske". tl
Tace,"to me zan maka?". ta faɗa still tana tsaye bakin ƙofan, ya kalleta yana ɗan ƙunshe dariyarsa yace,"to anan zan saki aikin?". ta turo baki gaba ta taho kamar mara laka, har ta ƙaraso inda yake bai ɗauke idonsa akanta ba. ta tsaya ƙeƙam akansa yace,"hau saman kan nawa sai ki tsaya da kyau".

ta shiga dukan ƙafa a ƙasa tace,"wai mene hakan?". 
ya jawo ledan fruite ɗin yana yanka abarba yace,"abinda yay hakan shi yay hakan,  sai an tambayeki tare aka haife ku da Kuka kice ba haka ba".

yaci gaba da yankan lemonsa yana kallonta ta gefen ido, ganin zata bar wajen yace,"dawo".
ta tsaya ya É—ago yana mata nuni da gefen gadon yace,"zauna". kamar za tai masa musu sai kuma ta zauna tana aikin kumbure-kumbure.

zai kama hannunta ta janye tana neman fashewa da kuka tace,"nace maka babu kyau, Allah zan faÉ—awa Mum".
ya ɗaga gira ɗaya yace,"i will escourt you". ta langaɓar da kai cikin wata iriyar shagaɓar da bata san sanda tai ba tace,"Allah to sai in faɗawa Baffa".

da sauri ya zaro ido waje yace,"kice masa me?".
tace,"ince masa Turaki yana taɓani kuma har kulleni yake a ɗakinsa".

Ganin da gaske take maganar yay saurin cewa,"Allah ya baki haƙuri".
ya faÉ—a yana dawowa gabanta ya gutsuro kaza ya kai bakinta,"wannan za ki cinye sai in barki ki tafi".
ta kallesa ta kalli gudar kazar sannan tace,"duka?".
ya girgiza kansa,"a'a iyaka yanda likita yace kici".
ya faɗa yana kama hannun ciwon da ƙara cewa,"wai sai kinci iyakar yanda fatar nan da ta loma zata ciko".

ta kalli yatsunta da fatarsu ta shafe sannan ta kai hannun hagunta zata karɓa ya janye yace,"kafirai ke cin abinci da hannun hagu, kawai ki yarda in taimaka in baki tunda dai baki da hannun musulmai".

ba yanda ta iya haka ta dinga amsar naman da ya gutsuro yana bata, tun tana kawar da kai tana ƙin karɓa har ta gaji ta dinƙa karɓa a dole tana ci, bai ƙyaleta ba sai da yaga taci da yawa sannan ya ɗauko madarar kwali ya bata itama sai da tasha rabi sannan ya yarda ya barta, ya bata ayaba da kankana suma tasha tana jin kamar zata yi amai saboda ƙoshi, ita dai kallonsa kawai take yi tana jin wani irin abu tare da ita.

ya tattare komai ya kaisu gefe sannan ya ɗauko jakar uban choculates ɗin ya ɗauko ɗaya ya buɗe ya kai bakinta, ta kauda fuska tana yamutsa fuska tace,"na ƙoshi fa, zanyi amai".
ya É—auke yana faÉ—in,"ashe ba ki shirya fita a É—akin nan ba".

da sauri ta janyo hannunsa ta kai choculate ɗin bakinta ta gutsura sai ɓata fuska take yi, a haka sai da ta shanye guda ɗaya tass tukunna ya kafeta da ido yana kallonta da wani sihirtaccen murmushi.

bata hanasa kamo hannunta me ciwon ba, ya tmbayeta,"yana zafin ko ya daina?".

Tace,"yana zafi sosai dauriya kawai nake yi, kaine ina ta maka alama ka datse min hannu kaci gaba da masifarka, dan Allah ka mayar dani wajen likitan ya yanke min su na huta, kuma dan Allah ka rage masifa in ba haka ba wataran zaka iya ɓallani gaba ɗaya".

ya shafo wuyansa yana wani irin murmushi da yake jin yana motsa ilahirin jikinsa da wani feelings na daban.

sai taga ya sauke daga kan stool da yake zaune ya zauna gaban ƙafafunta, sannan ya ɗora kansa da hannunsa ɗaya kan ƙafafunta yace,"idan aka yanke kuma da wanne za kike wa mijinki ƙunshi yana kallo yana jin daɗi?, a barsu dai insha'Allahu zuwa safiya zasu daina zafin".

ta ture kansa da É—ayan hannun tace,"ka É—agani ba kyau".
ya riƙe hannun ya mayar da kansa yana cewa,"naji, Allah kuma kika ƙara ce min ba kyau sai kin kwana a dakin nan yau".

tai shiru tana sakin kukanta mara sauti, ya ɗago kansa haɓarsa kan gwiwarta yana kallonta sosai yace,"ai dama ranar nan kince min ni ke saki kuka, dan haka yi me isarki tunda yau Allah ya haɗa mu".
Chapter 103 · 0% Book details