← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 176

Sashe 61

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

idanuwanta a lumshe ta ƙaraso ƙofar ɗakinsu, lokacin Maijidda ta fito daga ɗakin suka yi karo da juna. Maijidda ma taja hanci tana shaƙar ƙamshin tare da cewa,"kai Fillo wannan ƙamshin fa?".

****
BoÉ—ejo dake zaune kan kujera a babban parlon Mai Martaba tace,"ah tou ni É—in dai na gama magana...idan kuma kun lalace ne to sai naji, amma batun auren Ilham da ÆŠan'uwanta wancan kumburarren babu wanda ya isa ya hana sai dai ko bayan raina, sai in kuma ikon me sama".

Mai Martaba ya sauke numfashi yace,"amma Hajjah...". da sauri ta katse shi,"Hashim kai kaɗai ne me shegen taurin kan da ba zaka tuba ka daina kirana da Hajja ba ko?, kasan Allah karka bari raina ya ɓaci akanka, ya nazo ina batun haɗa yara aure kana ce min ba haka ba yanzu kuma kana ƙara kirana da sunan da kasan bana so".

cikin kwantar da murya Mai Martaba yace,"kiyi haƙuri".
Boɗejo ta ƙara haɗe rai tace,"ka riƙe haƙurinka. muyi batun da ya kawoni wajenka, ba tun yau nake faɗa ba sai dai zan ƙara nanatawa ina so ku haɗa Muhammadu da Rumana aure, in kuma ban isa ba sai inji".

Baffa ya É—ago kai ya kalleta yace,"balle ma kin isa BoÉ—ejo, sai dai kawai ya kamata ayi duba a lamarin, tunda bamu san ba ko su yaran nan zasu so haÉ—a su auren da za'ai".

Mai Martaba yace,"abinda nake so ki fahimta kenan Mama, zamanin yanzu ba ɗaya bane da na da, yanzu ba'a haɗa yara aure gudun abinda ka iya zuwa ya dawo a zamantakewar tasu muddin babu soyayyar junansu, amma kuwa idan aka tabbatar da yaran nan suna son junansu shikenan salamun alaikum mu kanmu ba ƙaramin farinciki zamu yi da hakan ba".

Boɗejo ta tafa hannu tana salati kafin tace,"na shiga uku, Hashim yanzu al'adar tamu zaka rushe?, kai kasan a yanda akayi aurena da ubanku kuwa?, tabɗijam, to da kasan ta yanda aka laliƙa min ubanka na aura da baka zo min da wannan ƙabali da ba'adin ba...shashashan sarki kawai, kai idan akai hakan ma ba ƙarfafa zumunci akayi ba, amma kana batun wani idan basa son junansu, a'a to da ƙiyayyar junansu suke yi?, ko an faɗa muku su irin ƴan'uwan mahaifinku ne kafin su tuba, kai gaskiya Hashim kana da gurɓataccen tunani, wai idan basa son junansu!, maganar nan naka har ga Allah yayi min zafi, to karka ƙara wallahi, don ni dai kaf jinina babu me mugun hali, kowa son ɗan'uwansa yake yi...tsakani da Allah ina Turaki zai ce baya son Ilham ƴar'uwarsa?, kuma itama ta ina zata ce bata sonsa yarinyar da kullum zancenta akansa yake, babu fitowar rana da faɗuwarta da ba zata ambaci sunansa ba, dan ma dai waccan uwar tata me baƙin hali da mugun nufi na hanata zumunci da shi, to a gaskiya indai ana so aga dai-dai abi umarnina kawai, auren nan yinsa za'ai babu wani zaman tuntuɓe-tuntuɓe balle asa jinina ya hau".

Mai Martaba zai yi magana ta É—aga masa hannu,"a'a dakata, dakata ba sai kace komai ba. É—aga waya kawai ka kira min Hakimi yazo yanzun nan, ban sani ba ko haÉ—e kanku kuka yi kuke so ku nuna min kune kuka haifi yaran nan, ni banda wani hurumi da su, in haka ne kuwa sai in kama gabana na barku da halin bijirewa maganata".

Baffa ya tausasa murya yace,"ba bijire miki zamu yi ba BoÉ—ejo, zamani muke so ki duba. kuma muma fa bamu ce ba za'ayi hakan ba, ce muka yi a fara jin ta bakinsu tukunna, idan sun amince da junansu mu abin farinciki ne a wurinmu wallahi".

Boɗejo ta jijjiga kai ta harɗe ƙafafu tace,"to bara kaji Dikko, tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin Ubanku ba sai a ranar da aka kirani akai min zancen aurenmu da shi...ina zaune lafiya daga zuwa na gaida mahaifiyata zanyi kwana uku a wurinta sai Kakanku yasa Babana ya doka min kira wai inje fada ana nemana, kai kasan tashin hankalin da mahaifiyata ta shiga a dalilin wannan kiran kuwa?, saboda kiran fada bai cika zama alkhairi ba, ina zuwa ga Babana Waziri ga Mai Martaba ga Ubanku a zaune aka ce ga mijin da akayi min, kuma a gobe za'a ɗaura mana aure. yo da ike ni me biyayya ce ban bijire ba daga ni har shi uban naku, hasalima shi tausata yake yana cewa muyi haƙuri mubi umarnin iyaye zamu ga ribar hakan, to dana aure shi Dikko mutuwa nayi ko me?, gashi nan dai ku huɗu na haifa jeras tare da shi, idan bana sonsa zan bari a haife ku ne?. sai akan ƴaƴanku zaku ce ba haka ba, Turakin ma da wancan algungumar Azimar ta raine shi, Turaki fa har goya Ilham yayi, to banda dai rashin tsoron Allah irin naku ina ku ina cewa baya sonta?
ku dai ku ke kyautata zato akan abu, ba wai kowa yake hasashe mara kyau ba. na tabbata babu abinda zai sa yarannan suƙi amincewa muddin kun nuna musu kuna so, banƙi ba shi ɗan naka ya iya botsarewa to amma shima na san na ƴan mintina ne tunda yana da ladabi, kana cewa haka kake so ba zai ja ba zaice ya amince, sai dai idan kuma a munafurce ni a hure musu kunne".

daga Baffa har Mai Martaba babu wanda ya ƙara yin magana, Boɗejo ta tafa hannu wani bafade ya shigo parlon yana zubewa a ƙasa.
tace,"maza kira min sarkin gida". fitarsa babu jimawa sai ga sarkin gida ya shigo, ya zube agaban BoÉ—ejo tace,"É—au waya ka kira min Hakimi".

Sarkin gida ya kira wayar Hakimi da wayar Mai Martaba, bugu ɗaya biyu ya ɗaga. yay saurin miƙawa Boɗejo. ta karɓa tasa a kunne, bayan sun gama gaisawa tace,"kana jina?".
a ladabce yace,"ina jinki ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon rai". tace,"amin, Allah yayi maka albarka...dama magana zanyi da kai".

kamar yana gabanta saboda tsananin ladabi yace,"tom shikenan, É—azu ance min kin fita, gidan Dikko zanzo ko fada?".

tace,"a'a yi zamanka akan kujerarka. dama batu ne na aure nazo maka da shi, ina so a haɗa auren Turaki da Ilham, ba kuma na so ya wuce wata guda tunda da arziƙinmu, wata gudanma saboda zan gyara jikata ne banda haka cikin sati ɗaya za'ai komai a gama".
Hakimi yace,"tom shikenan ranki ya daÉ—e, za'ayi yanda kika ce. Allah ya tabbatar da alkhairi".
tace,"amin ya Allah". da haka suka yi sallama, da yake a handsfree ta saka duk conversation É—insu su Mai Martaba sunji.

"da akwai wanda zai ja ne?". ta faÉ—a tana kallon su duka. a tare suka haÉ—a baki wajen faÉ—in,"a'a, Allah yasa albarka ya kuma tabbatar da alkhairi". tana nuna musu fushinta na gardarma da suka yi mata a farko tace,"kai Dikko ka kira min Falmata yanzu a waya".

Baffa ya ɗau wayarsa ya kira Falmata ya miƙawa Boɗejo, sallamar Falmata kawai ta amsa tace da ita,"anjima za'a kawo Ilham gidanki, ki gyarata gyara na ban mamaki Falmata, gyaran da ba zai sa Turaki ƙara kallon wata mace da sunan sha'awa ba har mutuwarsa, irin gyaran da ba zai so Ilham ta matsa a kusa da shi ba".

Inna Falmata ta amsa da,"tom ranki ya daÉ—e".
BoÉ—ejo ta dubi Mai Martaba bayan gama wayar tace,"sai kuma me?".
ya rissinar da kansa yace,"ya kamata a sanar da Fulani Azima da kuma Madina".
BoÉ—ejo ta haÉ—e rai tace,"ashema ba so nake auren ya tabbata ba. gwara ma in Madina kace, amma wace wata Fulani Azima?...to maganar aure dai cikin sirri nayi ta, ko yaran ba zasu sani ba sai ranar É—aurin aurensu, magana daga ni sai ku nayi ta, idan naji ta a wani waje kuma wallahi tallahi akwai Allah".

tana gama faɗar hakan ta miƙe. "Dikko tashi muje gidanka zan wuce".

*Comment, Share and Vote.*
[8/28, 10:43] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

_not edited._

*28*
washegari da safe Fillo ta gama shiryawa kenan sai ga Yami ta faÉ—o É—akin kamar an jefota. fuskarta a haÉ—e take kallon Fillo, ita kuma tana ganin hakan tasha jinin jikinta.
Yami ta miƙa mata wayar hannunta tana faɗin,"ungo nan, idan ta kama ki tafi da ita can, abu ɗaya kawai na sani shine ki tabbatar kin ɗaga kiran Amir kunyi magana da shi, ki kuma basa damar zuwa idan ya buƙaci hakan".

idon Fillo suka ƙanƙance tana kallon Yami da ta ɓata rai, ƙirjinta taji yana bugawa da sauri sauri domin bata tunanin zata iya bin umarnin Yami.
Yami ta doka mata tsawa,"kin karɓa ko saina hamɓare ki". tuni jikinta ya hau kyarma tayi sauri ta karɓi wayar tana duƙawa a wurin ta fashe da kuka.

Kaka tace,"to dama ni dai da naga ba kiyi magana ba yasa nayi shiru, zatona ko baki san komai ba".
Yami tace,"ai ina sane, na zuba mata ido ne naga iyakar gudun ruwanta. sai naga rashin hankalin nata da gaske ne, to banda ma dai É—an Adam butulu ne dan ubanki ina ke ina juyawa Amir baya, duk abinda Amir zai yi miki a rayuwa ai ke me iya shanyewa ce ba wai kiyi zuciya da shi ba, wane irin alkhairi ne yaron nan bai yi miki ba, wane kalar halacci ne bai yi miki ba, ke inda baya sonki da gaskiya har yace yaji ya gani ya aminta zai aureki sanda ake hure masa kunne da cewar ke Æ´ar gaba da fatiha ce. amma saboda toshewar basira irin taki har ki iya É—aukar fushi da shi na tsawon wata da watanni, gaskiya kin bani kunya da mamaki".
cike da takaici Yami ta ƙarasa maganar.
Chapter 61 · 0% Book details