Sashe 94
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaka ta fashe da kuka tana cewa da Fillo,"Fillo ashe dama Amir ne ya É—auke ki, ashe yaron nan ba mutumin arziÆ™i ba ne, ashe Amir azzalumin bawa ne, ashe duk wannan kyawun halayyar tasa yardararmu yayi saboda cimma wata manufa tasa, ashe baÆ™in *BIRI* ne shi ya *LULLUÆE* kansa ta yanda ba zamu shaida mugun Æ™udurinsa ba, Allah ya isa tsakaninmu da shi, ko yafiyarmu kaÉ—ai ta ragewa Amir shiga aljannah ba zan yafe masa ba, sai Allah yay mana hisabi da shi, kuma insha'Allah sai yaga sakayya, sai ubangiji ya bi mana hakkin cutarmu da yayi tun anan duniya. yanzu muna kan hanya Khalil ya É—auko mu ance an kawoki asibiti rai hannun Allah muka ji sanarwar an kama waÉ—anda sukai garkuwa da ke, wallahi tallahi ban shaida muryar matsiyacin ba sai Yami ce ta shaida, sai kuma da naji an ambaci sunansa, yanzu haka ance gobe za'a kai su kotu Hajiya Madina tace sai yayi zaman gidan yari".
sai ta fashe da kuka sosai tana ƙara cewa,"yasa na siyar duk da wani abu da ku ka mallaka a wajen mahaifiyarku, sai da ya tsiyatamu tass Fillo, biyar ɗin kanmu bamu da ita a yanzu, yasa muka ɗauki dukkan yarda da amana muka ba shi?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, gaba ɗaya tsoron kowa nake yi Fillo, ta ya yanzu zaka iya tantance fuskar mugun mutum da ta mutumin kirki bayan mugwayen na amfani da fuskar mutanen ƙwarai?, Allah ya tawarwatsa rayuwar mutane irinsa a duk inda suke, adu'ata ɗaya Allah yasa bai lalata miki rayuwa ba".
Fillo ta zame daga jikinta, tasa hannu ta goge hawayenta tace,"bai ida mugun nufinsa ba Allah yaɓullo min da hanyar guduwa, Kaka bana son kukanki dan Allah ki daina, ki manta da zaluncin da Amir yay mana ki barsa da Allah, indai duniya ce ga shi gata nan, yau ba ranar kukan baƙin ciki ba ce ranar kukan farin ciki ne, irin wannan hawayen nawa nake so kiyi ba irin wanda nayi a sanda na san cewar Amir Birin da ya lulluɓe kansa da mayafin da ba mai iya ɓata shi bane. Ummi ta dawo Kaka, Allah ya bayyana mana ita, dan haka ki kalla gabas ki yiwa jalla wa'azza godiya".
Kaka bata bar kukan ba tace,"ke wai kina hauka ne, a ina kika ga wata Ummi?".
Ummi dake riƙe da Kaka ta gefe ta kwanto a kafaɗarta tace,"gani Dada".
"Halimatu". Kakan ta kira Ummi da mamaki matuƙa. "na'am Dada". sai Kaka ta rungumeta tana hawayen farin ciki itama,"Halimatu ina kika je?, dama kina raye Halimatu?, ƴata na yafe miki domin nasan ba komai ya saki barin gida ba sai baƙin cikin mugun miji, amma tsayin wannan lokaci ina kika shiga Halimatu har na ganki haka lafiya ƙalau?, kai Allah maji roƙon bayinsa".
Ummi tace,"tashin farko Kawu Nasir ne ya bani goyon baya harma ya ɓoye ni a gidansa, daga nan labarin da yawa, amma waɗan can mutanen da kike gani ɗansu ne ya tsince a sanda na faɗa cikin wani hali, kusan shekara yanzu suke bani duk wata kalar kulawa".
nan da nan kuma duka Families biyu sai suka manta da damuwar da ake ciki, a shiga babin farin ciki. dan kamar yanda su Hajiya Madina suka mance da lamarin su Fillo haka suma su Kaka suka manta da lamarinsu, dan suma waje suka samu suka zauna, Kaka sai kwarara adu'a take yi da godiya ga su Yusuf, tunda Ummi ta shiga faÉ—a mata irin alkhairan da suka yi mata.
da ƙyar iyalan Dikko suka safafawa Hajiya Ramla suka bar jikinta, ta bisu da kallo tana cewa Hajiya Madina,"ranki ya daɗe yanzu duka waɗannan yaranmu ne?, har waɗannan samarin?". ta faɗa tana nuna Khalil da Sameer.
Hajiya Madina tace,"ƙwarai kuwa". nan da nan ta shiga nuna mata su Nihal tana faɗa mata sunayensu, tai mata nuni da Ilham dake gefe ɗaya ta rakuɓe sai kallonsu take tana murmushi.
tace,"ga inlaw É—inmu can". Mum tace,"really?". Maama tace,"ga zahiri na kunya nan kina gani". ai nan da ko Mum ta buÉ—e mata hannu tace ta taho gareta, ta rungumeta da tsananin farinciki sai saka mata albarka take yi.
kuma sai a lokacin Mama ta lura da rashin Zaytuna, sai ta miƙe tana dube dube dan dama tuni ta san da ƙullatar da Zaytuna tayi da Mum.
ta ganta tsaye can gefe ta haɗe rai fuskarta a gefe ɗaya, ranta ya ɓaci sosai taji tama kasa magana, hakan ne yasa Hajiya Ramla fahimtar komai musamman da ta ɗaga ido ta kalli photocopy ɗinta, ba sai an faɗa mata ba ai tana kallonta tasan itace jaririyarta da ta tafi ta bari.
Turaki ma ya dinƙa kallon Zaytuna yana tuna lokuta da dama da take ce masa,"ka daina damuwa da ita Hammah tunda ai itama bata damu da mu, ni fa Hammah Allah ko ace ta dawo inda take ba zan kalla ba balle na raɓeta".
sai kawai ya miƙe ya nufi wajenta, yana jin Maama cikin muryar ɓacin rai tana cewa,"wannan ba itace tarbiyar da na baki ba Zaytuna, kuma ko ki ɗago ƙafa kizo mahaifiyarki tasa miki albarka ko kuma wallahi in ƙaraso nan inyi miki duk abinda zuciyata ta sani, dan ba ki isa ki lalata mana farin cikin da muke ciki ba".
Tayi shiru a sanda Turaki yaje gaban Zaytuna ɗin ya kamo hannunta, har ta cije tana neman ƙwacewa, ban san me ya faɗa mata a kunne ba yasa ta biyo shi.
suna zuwa gaban Mum Turaki ya zube duka gwiwoyinsa a ƙasa, yaja hannun Zaytuna da ta tsaya ƙiƙam itama ta zube nata gwiwoyin, dama wannan ranar ya daɗe yana jira, dama wannan lokacin yake ta jira, dan haka kawai sai ya haɗe hannayensa duka biyu alamun neman yafiya cikin amon sauti me mugun ban tausayi yace,"Mum dan Allah dan Annabi ki yafe mana, ki yafe min dan girman Allah, wallahi tallahi ban san ta yacca akayi wutar ta kama ba, da sanina ba zan haddasa gobara ba Mum kema kin san banda fitina, amma ina neman yafiyarka dan Allah Mum".
yay maganar hawaye na sakko masa hoton komai na wancan lokacin na haska masa musamman a sanda yabi Mum ta hankaɗo shi ta rufe ƙofa ta tafi ta barsu.
Hajiya Ramla ta fashe da kuka, kukan da ya tafi ya shiga kunnuwansu ya daki zuciyar Turaki da Zaytuna, suka yi saurin ɗago ido suna kallonta, a ɗazu zai faɗi duk wani saukar hawayenta da sunan hawayen farin ciki, amma wannan kukan da ta kasa riƙe ƙarfin sautinsa na shaida masa so take ta yishi iyakar gwargwado, ta yanda zata samu ta rage raɗaɗi da baƙin cikin wani abu dake ranta. to me ya kawo hakan?, shi da yayi mata laifi.
kuma kafin ya gama karantar dattin baƙin cikin dake saman fuskarta sai yaga ta sauko daga kan kujerar, itama ta zube nata gwiwon a ƙasa ta rungumo su jikinta tsam. tana kukan sosai tana faɗin,"Babana babu abinda ka yi min, baka min laifin komai ba Babana. ni ce nayi muku laifi wanda har ba zan yafewa kaina ba sai in kun yafe min, dan Allah, dan Annabi Babana kai da Zaytuna ina baku haƙuri, ina roƙonku ku yafe min da nisanta daga gareku da nayi, sharrin shaiɗan ne".
Zaytuna ta fashe da kuka tana shigewa jikin Mum ɗin sosai, cikin muryar kuka suka haɗe baki ita da Turaki suka ce,"Mum ke fa Uwa ce akan me za kike neman yafiyarmu bayan baki yi mana komai ba. to ma idan kinyi ɗin menene ai girmanki ne da cancantarki, balle ma har duniya ta naɗe ba za ki taɓa yi mana abinda zamu kallesa a matsayin kin mana laifi ba".
furucin nasu sai ya zama kamar haɗin baki ko kuma tun can dama sun tsara hakan. sukai shiru suna barin jikinta, Turaki yasa hannunsa na hagu a gefen fuskarta ta ɓarin da yake, itama Zaytuna haka.
suka ƙara haɗa baki da faɗin,"muna miki tsananin so, farin cikinki shi ne muce mun yafe ko?, to mun yafe miki Jarumar mata".
sukai kissing nata a goshi suna jin wani irin shauƙi na daban da basu taɓa jinsa ba mara misaltuwa na bin jinin jikinsu.
gaba ɗayansu kuma har Mum ɗin sai suka saki murmushi me faɗi, har haƙoransu duka na bayyana a waje. Hajiya Madina da su Neehal sai suka koma ƴan kallo, dukkansu sai murmushi suke yi, kuma har sannan Hajiya Madina bata bari Baffa ya sani ba saboda sanin irin fushin da yake da Hajiya Ramla, ta bari ne kawai sai dai ya gansu a gida.
Zaytuna taƙi sakin mahaifiyartata tace,"Mum yau a jikinki nake so na kwana, yau ba zanyi bacci ba Mum zan zauna inta kallonki".
suka riƙo hannunta ta miƙe ta koma kan kujerar ta zauna, sannan ne ta kalli Hajiya Madina da zolaya tace,"Madam kisa ƴaƴanki su sakeni in tafi wurin sabuwar ƴar da nayi".
aiko karaf Neehal tace,"ki tafi ina Mum?". ta faÉ—a tana turo baki tai saurin zagayowa ta zauna kusa da ita tana kama hannunta da cewar,"ai mu daga yau kina manne wajenmu kuma".
bata bar murmushi ba tace,"to zanje in duba patients É—ina, a ban izini dan Allah". Kusan duk a tare suka haÉ—a baki wajen faÉ—in,"patient kuma Mum?".
tana kallon Hajiya Madina tace,"wata yarinya ce da ta taimaka min muka fito daga cikin jeji mota ta bigeta, tun É—azu munfi 1hour amma shiru, tace min Æ´ar aikin gidanmu ce, dan tunda ta ganni ma take cewa muna kama da Zaytun".
a lokacinne kuma sai ga Fillo nan tazo wajen kamar tasan zancenta akeyi, tana riƙe da hannun Ummi ta ƙaraso da kumburarriyar fuskarta da taƙi barin murmushi. ta saki hannun Ummi ta nufi wajen Hajiya Madina wacca ta buɗe mata hannu, ta shige jikin Hajiya Madina ita kuma tana rungumeta tare da faɗin,"hasken gidan Alƙali Dikko, haƙiƙa ke ɗin haske ce a tare damu Fillo".
Fillo tace,"Maama nima ga Ummina na gani, ashe bata mutu ba". ta saketa tana faÉ—in,"haba dai". tabi Ummi da kallo kafin ta isa wajenta da sauri tana gaisheta suna yiwa juna barka da farin cikin da suka tsinci kansu a ranar yau.