Sashe 157
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Maama daga wurin Mum É—in fa nake tace Adda ta taho da kayan nan".
Zaytuna ta ce,"nawa kawai na ɗauko na bar miki naki acan, kiyi sauri kije ki duba in ba haka ba a ɗauke, kin san ɗakin Mum wasarairai take da shi, na nemi sarƙata sama ko ƙasa na rasa".
cikin sauri Samha ta fita bayan ta ce da yaran su biyota da kayan da ta ba su.
Nihal ta matsar da bakinta kusa da kunnen Hajiya Madina tace,"Maama gulma zan miki, kin san me Hammah yaywa Fillo kuwa?".
Hajiya Madina tayi saurin mayar da hankalinta gareta. sai kuma Nihal É—in ta tashi da sauri tana cewa,"kai ba ruwana, ba za'aji mutuwar sarki a bakina ba".
ta faÉ—a tana saurin ficewa ta bar É—akin.
Hajiya Madina tabi bayanta da kallo, kafin ta mayar da hankalinta kan maganar da Mama Bilki ke yi mata.
"Zaytuna za'a fara kaiwa kenan?".
"ehh ita za'a kai gobe, jibi akai Samha sai gata mu karɓo amaryar Khaleel, ita anan zata zauna tare da mu, wancan matar ta me Babban sunan kuma yau za su kawota".
Tana faɗa ta miƙe ta fita ta bar ɗakin, don hankalinta bai kwanta ba da maganar da Nihal ta fara yi mata, duk yanda akayi an sami wani misunderstanding tsakanin Turakin da Fillo, dan ta lura tun jiya da aka mayar da aurensa ya zama wani kalar masifaffe, da asuba ma tana jin Khaleel na complain ɗin faɗan da ya kama yi musu na babu gaira babu dalili, to tsoronta kar ya sauke fushinsa akan baiwar Allah, ita da ba ita tasa aka mayar da auren ba, wacca ita ta ma fi shi takaicin mayar da auren, don ta lura da hakan a tare da Fillo, kawai don dai yarinyar na da haƙuri yasa bata nuna ba, sai ka ɗauka ma ko bata san ciwon kanta ba shiyasa take ta hidimarta ko a gefen yatsarta.
fatan ta É—aya Allah yasa ba BoÉ—ejo ba ce taje ta kunna musu wuta a gida. ko kuma halin jiya ya maimaita musu, don ance jiya ma kafin É—aurin aure kusan rufe Fillo da duka yayi.
****
"yauwa bayan kin auna fulawanki sai ki zuba butter, ki kwaɓa yeast ɗin da ruwan ɗumi kuma da shi za ki kwaɓin gaba ɗaya. yauwa to miƙo min gishirin can, if you like you can add sugar".
bayanin da Nuratu ke yiwa Fillo kenan a kitchen É—inta, a yayin da take koya mata yanda ake alkubus, tun san da suka dawo suka zo gidan taci taji daÉ—insa tace zata koyi irin nata.
Fillo ta ɗauko roban sugar da gishirin kamar yanda Nuratun tace, ta ajiye tana ci gaba da kallon yanda take yin kwaɓin da kuma sauraron bayanin da take yi mata.
wucewar wasu mintuna Nuratu ta kalli Fillo jin tayi shiru, ta girgiza kanta kawai tare da jin tausayinta, kafin tace mata,"kin san mene?, wallahi tallahi cutar kanki za kiyi muddin za ki ɗauki damuwa kisa a ranki har haka, ke wa ya faɗa miki yanzu ana nuna damuwa da kishiya?, kina ƴar ƙaramarki haka?, amma...".
ranta a ɓace ta ɗauki tukunyar da ta rufe ta bar kitchen ɗin.
Fillo ta bi bayanta da kallo kafin ita ma ta bar kitchen É—in, parlo ta wuce ta zauna, ta É—auko Farha da ke cikin keken wasanta, tana cikin yi mata wasa Yusuf ya shigo, bayan sun gaisa ya ke ce mata.
"jiya sai nake jin zancen an mayar da auren abokiyar zaman ki".
wata ƙwallar ciwo ta tararwa Fillo a ido kafin tace,"ehh Yaya".
"to Allah ya baku zaman lafiya, ayi ta haƙuri kin ji ko".
"insha'Allahu Yaya, na gode".
sai ya ƙara cewa,"amma ba ki da wata matsala ko?".
"babu Yaya".
"to masha'Allahu, kar fa kice za ki sakawa ranki damuwa kinji ko, kinga ba isassar lafiya gare ki ba. ya zancen karatun ki kuma?".
tasa hannu ta goge hawayen da yay nasarar gangaro ma ta kafin tace,"lokacin da muna Ausburg har ya nema min addimission acan, to kuma da muka dawo sai yake cewa wai na haƙura kawai, to ban san me dai yake nufi ba, gaba ɗaya zan haƙura da karatun ko kuma wancan admission ɗin zan haƙura da shi".
Yusuf ya sauke numfashi yay É—an jim kafin yace,"ki ba shi lokaci tukunna, zuwa gaba sai kiji koma menene dai, amma karatun naki yana da muhimmanci sosai".
ya miƙe daga kan kujerar da yake zai wuce ɗaki Farha tasa kuka, ya dawo ya karɓeta ya tafi da ita.
wayar Fillo dake kan cinyarta tayi ƙara, ta ɗauka ta kara a kunne tare da amsa sallamar Maijidda.
"ke na zo kuma na tarar ba kya nan".
"ehh wallahi naje gidan Yaya Yusuf ne".
"lallai ma ke ɗin nan, kuma kika ce na zo na raka ki ƙunshi, kin san za ki fita za kisa na zo, ko don kawai dai kin raina min hankali, wannan ai rashin mutunci ne".
"Allah ya ba ki haƙuri maida wuƙar, ba jimawa zan yi ba yanzu ma fa nake shirin tahowa. sanin halin ɓata lokacinki yasa nace bari kawai in je in dawo, don Allah ki zauna yanzu gani nan a hanya".
"sai kin dawo, idan da mota kika fita ki yiwa Allah ki samo min mangoro a hanya".
"to uwar biyu".
Maijidda tayi dariya sosai tare da cewa,"rufa min asiri maza su kaini ba mata ba, uban wa na aura da har zan zama uwar biyu, ke É—in dai".
su kai Sallama Fillo na miƙewa ta nufi ɗakin Nuratu, samunta tayi tana haɗa wasu magunguna a leda da dukkan alama maganin mata ne.
Fillo ta zauna bakin gadon tana cewa,"Anty tafiya fa zan yi...". kuma bata ƙarasa ba ƙarar wayarta ya katseta, ganin sunan Maama yasa tayi saurin ɗagawa.
daga ɓangaren Hajiya Madina tace da ita,"Daughter lafiya ba ki shigo ba?".
"Maama naje gidan Yaya Yusuf ne".
"zuwa yaushe za ki dawo?, ko acan za'a yi miki ƙunshin?".
"a'a wallahi Maama, wadda muka yi zata zo ɗin da safe ta kirani an yi musu rasuwa, wai da zata turo sister ɗinta but tana faɗa min bata ƙwarai sosai kamarta ba, shi ne nace ta bar shi kawai".
"ok to ki taho yanzu, nasa a kira wacca ta yiwa amare tazo tayi miki, bana so ki ƙara zama haka babu lallai, da ɗaurin aure an ga ba kiyi ba mutane sai su fara zaton ko baƙin cikin damuwar kishiyarki yasa".
"to Maama yanzu zan taho".
"to shikenan sai kin dawo, yauwa kar ki manta ki taho min da ajiyar nan da na ba ki, ga dai Nihal nan zata ja da duk alamu É—inkinki na gobe ma babu".
Fillo tayi Æ´ar dariya.
Maama ta ƙara cewa,"ga baƙi nan an ƙara yi, su na ta tambayar uwar gidan Turaki, idan kin zo duk zan miki bayaninsu, ƴan uwana ne na Kano, babu wanda ya taɓa zuwar min sai yanzu da bikin ƴaƴansu ya tashi".
bayan sun yi sallama Nuratu tace,"to ke ko anan ma ba sai ki godewa Allah ba, iyayen miji na sonki miji na sonki, danginsa su na sonki to kuma dan me na damuwar don ya mayar da matarsa?, auren nan fa biyayya ce kawai zai yi ba wai don baya sonki ba, ko a haka matsayinki da nata ai ba É—aya ba, matar so kike, ita kuma matar shige".
"Anty Nuratu wallahi ni abin da nake tsoro raini da wulaƙanci".
ta faÉ—a cikin rauni da muryan ban tausayi.
Nuratu tayi guntun murmushi me sauti.
"me zai sa ta raina ki?, a wanne dalili Fillo?, wurinki fa daban wurinta daban, ko za ku shekara dubu a gidan nan sai kun so za ku haɗu da juna. kinga look, ni fa ko a yanda na ɗauka ma sai ka yi abin da za'a rainaka ɗin tukunna ake samun damar rainaka, as far as kin kiyaye waɗan nan abubuwan wallah ko da me kishiya ke ji bata isa ta raina ki ba. na farko karki kuskuren saka mata Ido a lamarinta, kar ki ke kai ƙaranta, saurin faɗa da ita shi ne babban abin da ke janyo raini, da kuma ɗaukar zuga, in har kishiya ta fuskanci kina ɗaukar zugar mutane to billahi ta gama rainaki, haka zalika kar ki yi gigin dinga shiga kowanne lamarinta ko da ita da kanta ke cusa ki aciki, baya baya dai...".
Fillo ta tari numfashinta,"Anty Nuratu to ni ina ma nake da lokacin waɗannan abubuwan akanta. ina miki batu ne na tana ganin ita ƴar sarki ce, ta fini ilimi, ta kuma fini wayewa, kuma tana da aikin yi, sannan zata dinƙa min kallon cewar ni ba kowa bace face ƴar aikin da aka tausayawa aka auro, Anty Nuratu dole ta raina ni".
"to ai ƴar aikin ta fita tun da har tausayin ma yasa aka iya auro ki, ita da ba'aji tausayin nata an aurota ɗin ba fa sai cusata da aka yi?, mtsww kin ga don Allah ni kar ki bayar da ni, ko wayewar ma ai bata fiki ba, wayewar shiga jami'a kawai ta fiki, amma ban da ta gidan miji, ko kin manta tsawon watanni da kika shafe a ƙasashe da dama kina durzar amarci ke da mijinki, ita ta sami wannan damar ne?, bata samu ba kuma ba zata samu ba".
sai kuma ta miƙa mata ledar da ta gama zuba kaya aciki,"ga waɗan nan ɗin, ai duk nayi miki bayanin yanda za kiyi amfani da su".
"to na gode sosai, Anty Nuratu sai garin kunun, don Allah a ƙara yi min, naji daɗinsa sosai wallahi, sometimes idan na kalli kaina sai inga kamar ba ni ba, ji fa kumatun da na tara".
ta faɗa tana ƴar dariya me kama da ta ƙarfin hali.
"wai ke zatonki kunu ne kaɗai ya saka ki wannan ƙibar, to har da Babyn mu".
"hmm ni fa banda wani ciki. haka jiya Ammi ma da naje sai adu'a take wai Allah ya raba lafiya, ni dai nayi murmushi kawai. kafin mu taho test nawa aka yi duk ba ciki ba ne, ni kam ma ba yanzu zan haihu ba sai kamar nan da 2years lokacin na ƙara girma".