Sashe 175
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta kalli agogo taga ƙarfe tara da rabi a lokacin, ta miƙe ta wuce ɗaki, ba jimawa sai gata ta sakko sanye da hijab. ta kalli yaran tace,"idan Babanku ya dawo kuce masa na tafi wurin Mami. ku faɗa masa ina ta kiran wayarsa taƙi shiga".
su ka amsa mata,"to, a dawo lafiya".
"Allah yasa". ta faɗa tana nufar ƙofar fita, maganar Maama ta dakatar da ita,"Anty ko za ki tafi da tebar?".
ta kalleta tace,"Mum ce tayi?".
"ehh".
"Maama ba zan iya ci ba, ku cinye idan kuna so. akwai pancake a kitchen na ajiye muku, ba kwa buƙatar wani abu?".
suka haɗa baki wajen faɗin,"ba ma buƙatar komai Anty".
ta kalli Ayan tace,"saura ka sakata kuka".
yay Æ´ar dariya yace,"Anty wai haka kawai nake sakata kukan?, sai fa tayi min ba daidai ba".
tayi murmushin ƙarfin hali kawai ta fice ba tare da ta ƙara ce musu komai ba.
sai wajen goma Turaki ya dawo gida, yana shigowa parlo ya tarar da Ayan akan Maama yana zazzaga mata masifa.
"dilla Malama bani abu na, na rantse da Allah daga yau ma kika ƙara taɓa min kaya sai na faffasa miki baki, kin dai ji na faɗa miki".
ya faɗa yana sakin ƙwafa me ƙarfi, sai kuma ya saka hannu ya dungure mata kai glass ɗin idonta ya faɗi, a rikice ta durƙusa tana neman glass ɗin.
ta lalubo shi da ƙyar ta saka, ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tana hura hanci tace,"kuma wallahi idan Abi ya dawo sai na faɗa masa".
tana ƙoƙarin raɓawa ta gefensa ta wuce, ya fincikota yana faɗin,"ɗauko min kayana ki bani".
ta fizge tana faÉ—in,"ba zan É—auko ba É—in".
a zuciye Ayan ya É—aga hannu zai mareta muryar Turaki ta dakatar da shi.
"Ayan!". ya kira sunansa da ƙarfin sauti wanda hakan yasa Ayan ɗin nutsuwa.
"me ta taɓa maka da ma?, kai da baka da haƙuri, na faɗa maka bana son wannan zafin zuciyar taka, idan ƙanwarka bata taɓa abinka ba na wa kake so ta taɓa?".
Ayan na faman huci yace,"to Abie ita ce komai ta É—aukar min sai ta lalata, kalla fa yanda ta fasa min sabon earpod É—ina, kuma shekaranjiya da Uncle Bello yazo ya ban shi".
yay maganar yana nunawa Turaki.
"kuma shi ne saboda rashin tunanin akan abun duniya zaka É—aga hannu kace zaka mareta?, ranar da bana raye a haka zaka kula da ita?".
Ayan yay shiru bai ce komai ba, ya kumbura yayi fam yana tunanin abin da zai yiwa Maama ya huce.
"garin ya kika fasa masa abun sa?".
"Abie ba na sane Allah, nazo sakkowa daga upstairs na zame shi ne ya faÉ—i daga kunnena".
Turaki ya jefawa Ayan key É—in motarsa yace,"ka je mota ka É—auko nawa".
yana rufe baki Maama ta ce,"Abie ni fa?, Farha ta karɓi nawa aro kuma ba zan iya cewa ta ba ni ba".
"ki bari zan siyo miki wani Maama".
washe gari da safe wajen ƙarfe takwas hayaniyar yaran nasa ta tashe shi daga bacci, ya tashi ya shiga toilet yay wanka, bayan ya fito yazo ya tsaya jikin window yana hango su.
a field suke su na buga basket ball, Ayan na ta yawo da ball ɗin yana dariya, ita ma Maama na ta yawo wajen ganin ta kare ball ɗin daga shiga cikin raga, sai dariya take yi tana cije leɓenta, motsi kaɗan sai ta gyara zaman glass ta karyar da wuya alamun ta fara gajiya.
duhun garin kuma ya fara hanata gani sosai duk da medical glass É—in da ke sanye a idon nata.
ta durƙusa tana nishi, Ayan ya jefa mata ball ɗin ta ƙwalu a saman kanta, ya kwasa da gudu yana faɗin,"idan kin isa ki biyo ni ki rama ƴar makauniya".
haka yake yi mata sau tari, sai suna waje suna wasa sai ya tsokane ta ya gudu in dai yasan akwai hadari.
zafin ƙwala ball ɗin yasa Maama miƙewa ta ɗauka ball ɗin, ta ƙanƙance ido ta cikin glasses ɗin sannan ta saita Ayan da ya juyo yana yi mata gwalo, ta ɗaga ball ɗin ta jefa masa, ai ko cikin sa'a sai ga ball ɗin a fuskarsa, ta buga tsalle tare da ihu tana faɗin,"wooo ai dai na rama".
shi kuma ya dafe goshi yana faɗin,"yasin sai na faɗawa Abie ciwon idon ƙarya kike yi, ya daina asarar kuɗinsa a siyan glass kina gani tarr".
lokacin kuma hadari ya ƙara ɗinkewa, lokaci ɗaya garin yay baƙiƙƙirin, sai ya zamto Maama bata iya ganin komai hatta da gabanta, hankalinta ya tashi ta ɗaga hannu ta shiga laluben gabanta tana kiran Ayan.
"Ayan please ka zo, kar ruwan ya sauko, bana gani fa".
tana rufe bakinta taji ana yi mata cakulkuli ta baya, tai saurin juyowa don kama shi, sai dariyarsa ta jiyo yana ƙara yi mata cakulkuli ta bayanta da ya ƙara zagayawa.
"yarinyar ki bar min agogon da Ummi ta bar miki sai in taimaka in yi miki jagora".
"to ai tace nawa ne ni É—aya".
"to shikenan sai ki taho da kanki".
taji yayi shiru babu motsinsa, taita ƙwala masa kira yana gefenta a tsaye yay mata shiru, sai kawai ta fashe da kuka tana ta ƙwala masa kira.
Turaki dake hango su yana murmushi, ya faÉ—a tunanin wani moment na su shi da Fillo.
kamar haka suna tare a field ɗin suna yin wasan ƴar burin burin, ya ɓace mata tana ta kiran sunansa yay shiru yaƙi amsawa, kuma a sanda ta kunce ɗaurin idon taga bata gansa ba sai ta saka kuka.
kamar dai yanda Maama ke yi a yanzu, sai ya tuna yacca ya dinƙa jin sautin kukan nata na dukan zuciyarsa a lokacin, amma duk da haka bai fito daga ɓoye mata ɗin da yay ba sai da ta shiga parlo.
ta hau upstairs ta gama lalubensa a can baya nan sai ta dawo ƙasa, shi kuma a lokacin ya shigo parlon, suna haɗa ido da ita ya kwashe da dariya sosai ganin yacca hawaye duk ya ɓata mata fuska.
kuma ganin nasa yasa ta ɗauki pillon kujera ta biyo shi, suka shiga zagayen kujerun parlon tana faɗin,"Allah ni ka tsaya in ƙwala maka".
ya tsaya daga bayan babbar kujera yana haki yace,"saboda me to?, wannan ai mugunta ce, kawai sai ki kama ƙwala min pillow bayan kin san da zafi".
"ni dai sai na ƙwala maka".
ta faɗa tana turo bakinta gaba cikin shagwaɓa, tare da dukan ƙafafu a ƙasa hawaye na sakkowa ta ido ɗaya.
sai ya kama ƙugunsa yana kwaikwayon yacca take yi da idanu, hakan ya daɗa tuzurata ta sa kukan shagwaɓa sosai.
cikin dabara ta dinƙa matsawa zata zagaya ta bayan kujerar da yake tsaye, fahimtar hakan yasa shi barin wajen da gudu dariyarsa na ƙaruwa sosai.
"to wai me nayi miki za ki ƙwala min abu?".
ta É—age gira duka biyu ta ce,"ba kai ba ne ka gudu ka barni ka saka ina ta nemanka ban ganka ba".
"to sai ki bari naki turn ɗin yazo sai ki rama, amma ni dai ba za ki ƙwala min wannan pilon me zafi ba".
"ni dai Allah sai na ƙwala maka ko kuma ka ban haƙuri".
"tabɗijam sannu sara me baƙar takashi, kawai sai in kama ba ki haƙuri kina ƴar ƙarama da ke, bayan in da nayi haihuwar ƙauye da nayi jika da ke".
abin da ya faɗa yasa ta cije leɓe tana tunanin abun da zata yi masa, bata ankara ba taji ya ƙwalo mata pillow a saman ka.
ai kuwa sai ta ƙara fyallawa da gudu zata kamo shi, suka ci gaba da zagaye parlon cikin guje gujen su, shi yana ƙyalƙyala dariya ita tana cewa Allah sai ta rama, har sai da ta koma roƙonsa da Allah ya tsaya ta rama.
sai ya tsaya yana haki yace,"to naji za ki rama, amma kar kiyi min da zafi".
"ehh naji a hankali zan maka".
ta faɗa tana jijjiga ƙafa ɗaya.
sai ya sake yin dariya yace,"habawa yarinya ni za ki yiwa wayo".
yana faɗar hakan iska tayi blowing laluben parlon ya rufe masa fuska, kafin ya buɗe tayi tsalle ta dira akansa, ta cukwikwiye shi suka faɗa kan kujera tana ƙwaƙwƙwala masa pilon, sai da ƙyar ya iya kama hannayenta ya riƙe a cikin nasa.
"sai ance kin iya mugunta kice ke ba haka ba".
"ai har sai ka ban haƙuri zan ƙyaleka".
"ni fa ba zan bawa ƴar ƙaramar yarinya haƙuri ba".
suka shiga kokayawa har sai da tayi nasarar gantsara masa cizo a kunne, zafin cizon ya ratsa shi ya ƙwala ƙara yana faɗi,"i am sorry".
ta ƙara kai masa cizo a hanci tana cewa,"ba haka ba, sai kace don Allah".
ai kuwa ya ƙwalla ƙara da ƙarfi yace,"Don Allah kiyi haƙuri Fulani Nah, haba Fulanin Turaki ƴar albarka".
"waye yay nasara?".
"kece Anty Fulani".
ta É—aga shi tana dariya sai haki take yi, tana tafa hannu tana cewa,"yau na zama Anty Fulani".
sai kuma ta faɗa saman ƙirjinsa ta tura hannu cikin rigarsa tana yawo da shi akan ƙirjinsa.
cikin muryarta mai sanyi da ratsa dukkan jijiyoyin jiki tace,"Jannaty idan muna wasa karka ƙara ɓace min irin haka, tsoro yana kama ni, bana so in ji bana tare da kai".
ta faÉ—a tana kifa kyawawan idanuwanta cikin nasa, idanun da suke É—auke da guntun ruwan hawayen kukan da tayi.
"ba zan ƙara ba insha'Allahu Fulani nah, am sorry kin ji, i will always be with you".
sai ya rumtse idonsa yana tunawa da kyakykyawan murmushin da ta sakar masa a lokacin, ya tuna yacca ta shigar da jikinta jikinsa ta ƙanƙame shi tare da faɗa masa kalmomin da a duniyarsa yafi so yaji sun fito daga bakinta.
"i love you Jannaty, ina yi maka son da har bar san irinsa ba Jannaty, Allah ya barmu tare har abada".
lokaci É—aya yaji idanunsa sun cika da ruwa, ya dafe saitin zuciyarsa da yaji tana yi masa zafi.
ya tuna bayan rasuwar Fulani sai da yay watanni kafin ya dawo cikin hankalinsa, hatta deppression sai da ya kama shi, ban da ma Allah yasa ta bar masa yaran nan da tuni zuciyarsa ta buga shima ya mutu.