Sashe 35
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a bakin ƙofar suka tarar da Turaki wanda jin za su fito yay saurin matsawa daga jikin windon da yake tsaye a wajen tun ɗazu. su na ƙoƙarin durƙusawa ƙasa su gaida shi ya dakatar da su.
"dan Allah Kaka bana son kuke tsuguna min irin haka, ni fa jikanku ne, ku daina kallon wani matsayi da nake da shi, mutum nake kamar kowa".
Yami tace,"ranka ya daÉ—e kallon matsayi ai ya zama dole kam. kai É—in ne dai ka fita daban da sauran da suke da irin matsayinka. kuma muna godiya a gareka bisa kyautata da mutumtawa, Allah ya haÉ—aka da mace ta gari".
Kaka ta matsa daga bakin ƙofar tana basa hanya.
"ka shiga ciki yallaɓai bismilillah, ai tama farka tun ɗazu, jiki da sauƙi kam".
idonsa na kan handle yace,"to masha'Allahu, Allah ya ƙara lafiya...ina dai daɗa bada haƙuri Kaka".
Kaka dai bata kallonsa tace,"kai haba ranka ya daÉ—e wane mutum, aimu wannan tsautsayin abun farin ciki ne garemu. in banda haka ina ma za'a ganta?, da yanzu muna cikin tashin hankali".
bai ce komai ba ya kama handle ɗin ya buɗe ƙofar, su Kaka kuma suka wuce bayan sun ce masa zasu je ɗaya ward ɗin ne zasu yo dubiyar wata Ƴar Ƙawarsu da aka yiwa aiki ta haihu ɗan yazo babu rai, yayi musu a dawo lafiya sannan suka wuce shi kuma ya shiga room ɗin.
Maijidda nata fama da Fillo kan taci abinci amma taƙi, bai maida ƙofar ya rufe ba, kawai ya tsaya yana kallon Fillo kamar ɗazu da ya tsaya. yana kallonta ta window sanda suke abinsu ita da Maijidda. shi mamaki ta basa sosai bai yi tsammanin ma yarinyar na magana ba, da sakewa irin haka, zatonsa a tsorace take ko da yaushe irin yanda ya saba ganinta.
idanunsa suka nuna masa irin ramewar da ta ƙarayi, ƙasusuwan jikinta tsab zasu lissafu, idonta ya faɗa yayi loko kamar yanda yaga nasa yayi da ya na duba madubi ɗazu.
basu san ya shigo ba sai da Maijidda ta miƙe tana faɗin,"kiran Amir zanyi na faɗa masa kinƙi cin abincin, shi kya ji maganarsa tunda kinfi sonsa".
ta harareta tace,"ku kuma da banji maganarku ba bana sonku kenan?".
Maijidda ta É—aga kafaÉ—arta,"alama ta nuna hakan".
Fillo tayi shiru ta maida ƙafafunta kan gadon ta jingina da pillow, sai lokacin Turaki ya tura ƙofar ya rufe ya ƙarasa shigowa.
dukansu suka kai idonsu bakin ƙofar, gaban Fillo ya faɗi, taji wani tsoro ya kamata. ta wutsiyar ido yake kallonta, kuma yaga wannan tsoron a idonta wanda bai gani ba a ɗazu da take tare da ƴar'uwarta.
da sauri Maijidda ta aje abincin da ke hannunta ta durƙusa tana gaishe shi, ya amsa muryarsa bata fitowa sosai. ta miƙe ta ɗauki kujera daga gefen gadon Fillo ta kai masa, amma sai bai zauna ba.
Fillo dai da bata san ma shi ya kaɗeta ba, dan ba'a faɗa mata ba. tana dai cike da mamakin waɗanne irin mutanene su, ita ba kowan komai ba garesu amma sai zuwa suke su na dubata, taji su Kaka sun ce jiya da yau ne kawai Hajiya Madina da Baffa da Boɗejo ba su zo ba, amma hatta Hakimi kansa sai da ya zo, kuma shima Mai Martaba sai da ya aiko iyalinsa suka zo. ƙwarai kirkinsu ya wuce tunanin mutum, kuma la shakka ba zasu taɓa faɗuwa a rayuwa ba sai dai cigaba. ba tayi zaton ma Turaki zai iya zuwa dubata ba tunda wanda bai sonka ba ya sonka, no matter what happen to you ba zai nuna tausayinsa akanka ba.
zuro da ƙafafuwanta tayi daga kan gadon zata sauko ta gaishe shi, sai taji muryarsa kamar a saman kanta yace,"ki sauko kiyi me?".
bata É—ago ta kalle shi ba tace,"zan gaishe ka ne".
Idonsa har lokacin na kanta yace,"wa ya farlanta miki hakan?".
Bata ce komai ba tayi shiru sai wasa da yatsun hannunta take ta duƙar da kai.
shi kam kallonta kawai yake, ta wani natsu kamar wadda taga mutuwa, kamar ba ita ta gama surutu É—azu ba harda dukan wata.
É—akin yay shiru Maijidda na daga gefe har yanzu a tsugune, ya maida kallonsa kan abincin da Maijiddan ta aje yace,"ki kawo mata abincin".
Maijidda ta ɗauko plate ɗin da ke ɗauke da tuwon semovita da miyar agusi da naman ganda akai, ta miƙawa Fillo wacca tuni idonta ya cika da ruwa sai aikin ɓata fuska take.
da mamakin Maijidda babu tirjiya balle musu Fillo tasa hannu ta karɓa, kallon abincin kawai take ba don tana jin zata iya ci ba. bakinta babu taste ɗin komai hakan ne yasa ba zata iya cin komai ba, kuma bata ma jin yunwar.
wucewar daƙiƙa biyu Turaki yace mata,"wa kike jira yazo ya ci miki?".
ba tsoronsa take ji ba, ita kawai yana yi mata kwarjini ne, ko bata kalle shi ba indai yana waje sai taji girman kwarjininsa ya cika wurin.
ba don tana so ba ta gutsiri tuwon da spoon ta kai baki, ta tauna ta haɗiye da ƙyar kamar me tauna magani, tana yin spoon huɗu sai ga amai ya yunƙuro, Turaki yay saurin ɗauke idonsa daga kanta ya kauda kai gefe yana jin zuciyarsa na tashi, Maijidda ta kamata suka wuce toilet, duka ta amayar da ɗan guntun abin da taci, ta wanke baki suka fito har sannan yana tsaye sai dai yanayin fuskarsa ya sauya.
sai sauke numfashi takeyi tana maida ƙwallar idonta, ta ƙasan ido take ta kallonsa, tana ce sannu yazo yi mata?, shi bai yi ba kuma bai tafi ba ya tsaya kamar wani sandar ba'are, Allah ya sani ji take kamar akanta yake a tsaye, da zata iya da ta buɗe baki tace masa ya tafi kawai.
a bakin gadon ta zauna. kuma tana zama taji ya ƙara cewa,"ki ɗauka ki ƙara ci, sai ki ƙara zuwa kiyi wani aman, ki dawo ki ƙara ci kije ki amayar haka har ki cinye shi".
wannan karon ba ita ta kalle shi ba Maijidda ce, tana masa kallo É—aya ta É—auke idonta ta koma can kan É—aya gadon da ke cikin É—akin, room É—in 2patient ake admiting acikinsa amma ko da Baffa yazo sai ya biya kuÉ—in É—aya gadon dalilin da yasa take zaune ita É—aya kenan.
jin an turo ƙofa Turaki ya kai idonsa wajen, Dr Yusuf ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. duk da cewar tun ɗazu da Turaki ya baro masallaci yana office ɗinsa hakan bai hana su daɗa yin musabaha ba. as usual fuskar nan tasa da murmushin da ba ya yankewa.
"ya me jikin ranka ya daÉ—e?". Dr Yusuf ya tambayi Turaki.
"gata nan maganin gardama ya rage ku bata before ku sallameta".
Dr Yusuf yay Æ´ar dariya yace da Fillo,"ya kike jin jikin naki?".
Tace,"naji sauƙi".
yace,"to Allah ya ƙara lafiya. yanzu cin abinci yay miki saura shi ne za ki samu ƙwarin jikinki".
tace,"to".
ya juya ya karɓi file daga hannun nurse ɗin da ta shigo ɗakin yanzu, yay rubuce-rubuce sannan ya rufe ya bata.
ya fuskanci Turaki yace,"insha'Allahu by wenesday zamu sallameta. komai normal babu wata matsala".
Turaki ya kalleta ya kalli tuwon yaga ko rabin cinsa bata yi ba, yace da Dr Yusuf.
"Allah ya kaimu. amma babu yacca za'ai a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan?, tunda bakinta nayi mata wahalar cin abincin".
da murmushi a leɓen Dr Yusuf yace,"babu matsala sai ayi hakan. bari yanzu sai mu fara preparation ɗin shiga da ita ɗakin tiyata...sai dai kuma fa idan za'ai irin wannan aikin dole sai a ɗinke bakin mutum gaba ɗaya ya zamana mutum ya dawo ba ya magana, wurin da za'a yanka a cikin nasa shi ne zai koma yagar bakinsa, abinci da ruwa ne kawai za'a dinga zubawa a ciki".
Turaki ya sosa girarsa sannan yaja kujerar da ke kusa da shi ya zauna.
"ayi abinda ya dace kawai Dr".
sai ya kalla agogon hannunsa yace,"nan da minti nawa za'a shiga tiyatar?".
Dr Yusuf yace,"in the next 5minutes, office kawai zan shiga na fito, ita dai yanzu a shiryata".
Turaki yace,"alright a fito lafiya".
Dr Yusuf ya fita Nurse na biye da shi, wacca take ta dariya ƙasa-ƙasa da zancen da akai, ta lura sosai maganar ta tsorata Fillo. Maijidda ma na gefe a tsaye, itama dariya take ƙasa-ƙasa farkon da akayi zancen farka ciki, saboda yanda taga Fillo ta tsure tana raba idanuwa, amma daga baya da taga kamar maganar da gaske ne sai tayi jugum tana dai ta kallon Turaki ta gefen ido, tana kuma jin tausayin Fillo na tsarga mata.
_"amma babu yacca za'ai a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan?"_
maganar ta Turaki ta daɗa maimaituwa acikin kanta. farko da ya faɗa bata razana ba, amma da ta shiga bin fuskokinsu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sai ta tsorata ainun, dan ko ɗigo babu na alamar wasa a yacca fuskokinsu ke nunawa, hakan ya tabbatar mata lallai da gaske suke, farke mata ciki za'ai sannan kuma a ɗinke bakinta ta daina magana har a abada. idan da abinda yafi tashin hankali wannan maganar tasa ta shiga ciki, hangota take babu bakin magana kuma cikinta a yage, ta haɗe murfin idanunta da suke neman zazzagowa ƙasa, dan tunda aka fara maganar suke a waje.
jikinta rawa yake sosai, ƙatuwar malmalar tuwon take ta kallo, lissafi take yi, lissafin yanda za'ai ta cinye shi acikin miniti biyar kafin a shiga da ita tiyatar da suka ce. ta ɗago ido ta kalli Maijidda da ke kallonta, yanda take a tsorace haka Maijiddan ma. cikinsu biyun kowa ya kasa cewa komai, tsoron Fillo ɗaya ne! tace zata basa haƙuri ya sakar mata wannan uwar tsawar da bata so, dan taga kamar hakan yake jira, dalilin da ya sa bakinta mutuwa kenan.
Maijidda tayi sum sum ta fice zuwa kiran su Kaka, tana fita Fillo ta sakko a kan gadon ta wuce toilet, Turaki ya bita da kallo har ta dawo. ta koma gefen gadon ta zauna, ta saka hannunta da ta wanke ta fara cin tuwon tana kai ƙatuwar lomar da ta fi ƙarfin bakinta.