Sashe 126
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bakinta ya suɓuce da tsakin da ba ta san dalilin yinsa ba, ta koma upstairs ta buɗe jakar da Dadda ta ce an ajiye ma ta kuɗi, ta zaro 10k, hijab ta ɗauka ta sa ta fito ta sa mu mai gadi, ta durƙusa har ƙasa ta gaisar da shi yana amsawa da fara'a tare da saka ma ta albarka. sai taji nauyinsa, ba ta jin zata iya aikensa dan ya haifeta, idan bai girmi Abbanta ba tabbas za su yi sa'anni, ta yi shiru tana juya kuɗin a hannunta har sai da ya katse shirun na ta da cewa,"da akwai abunda ki ke buƙata ne?".
ta ce,"Baba don Allah ko za'a sami almajiri a waje?".
ya ce,"aike ne?".
ta ce,"ehh Baba". ta faɗa kanta na ƙasa.
kamar kuwa yanda zuciyarta ke raya ma ta taji ya ce,"ai kin san layin namu babu almajirai, sai dai ki kawo bari naje na siyo".
ta na girgiza kai ta ce,"a'a Baba ka bar shi ba zan iya baka aike ba gaskiya".
yay murmushi yana jin har ransa ta burgesa, da kuma yabawa da tarbiyarta da hankalinta, ya tuno san da Ilham tana nan, a rana ba'a aike shi ba a aike shi sau uku, kuma a gadarance da nuna isar mulki.
"kawo ƴata babu komai ai sai aje a siyo miki, ai ba aikena kika yi ba, a matsayina na uba zan fita siyo miki abun da ƴata take buƙata saboda kare darajar aurenta".
ta ɗago ido tana kallonsa, taji tausayinsa sosai a cikin ranta, ta miƙa masa kuɗin ta ce,"na gode Baba. da ma golden morn za'a siyo min babban ledan, sai madara na gwangwani babba, sai sugar rabin kwano, sai cornflask kwali biyu. za su isa kuɗin ko Baba?".
zai ƙirga kuɗin ta ce,"dubu goma ne ban san yanda kuɗin na su yake ba".
ya ce,"ehh tou nima gaskiya ban san yanda kuɗin yake ba, amma yanda za'a yi, bara idan naje in akwai ciko sai na karɓo miki lambar akawunt ɗinsa sai ki tura masa tunda da ma mun saba da shi, nima na kan yiwa iyali cefane acan".
tayi ɗan jimm kafin ta ce,"bara dai na ƙaro in ya zama da sauran canji ko ma sun kai shikenan".
ta faÉ—a masa hakan tunawa da tayi bata da waya balle wani account.
5k ta ƙaro, ta ba shi ta ce ya yi har na mota, dan indai ba'a tafiyarta ba tasan layin nan nasu kaf babu wani kanti.
da ga fitowarta ta farko, da komawar da tayi ta ƙara fitowa duk a idon Turaki da ke tsaye a balcony na sama, hannunsa riƙe da mug da alama tea yake sha, ya bita da kallo san da ta koma ciki yana ji zuciyarsa na ƙirga masa girman laifin da ta aikata.
sai bayan ta shiga kuma kawai sai idonta ya sauka acan dining area, adon wurin ya yi bala'in burgeta hakan yasa ta tafi, tana zuwa ta tarar da manyan warmcoolers na abinci guda huÉ—u da babban tea flask, tana kallonsu ta shaida su, coolers É—in kitchen É—in Maama ne da sai Baffa yana nan kawai ake amfani da su.
ta buɗe ƙaramin coolern taga irish ne da miyar hanta da soyayyan ƙwai, ƙamshin ya ziyarci hancinta har sai da ta lumshe ido, ai ko bata jin yunwa sai taci balle kuma uwar yunwa na ƙwazafarta a ciki, mamakinta ɗaya ne da yaushe aka kawo abincin?, zuciyarta ta faɗa mata tana can tana bacci.
ta ɗauko plate ta fara zuba abinci sai taji ana knocking, adu'arta ɗaya ne a lokacin Allah yasa su Dadda ne suka zo, ta miƙe da sauri taje ta buɗe door sannan ta zuge glass, idanuwanta suka sauka akan Bello da ke tsaye hannunsa ɗaya a aljihu ɗaya kuma yana maƙale da waya a kunnensa.
taja da ba ya tana ba shi hanya tare da yi masa sannu da zuwa, ya shigo yayin da yake amsawa, ya wuce ya zauna kan kujera ita kuma ta durƙusa har ƙasa ta gaida shi, ya amsa ya ɗan kallonta da son fahimtar wani abu, sai dai ya gagara fahimtar komai ɗin.
tana tsugune tana jan yatsun hannunta har wucewar daƙiƙa biyu sannan ya kalleta ya girgiza kai ya ce,"MT bai ta shi ba ne?".
tai ɗan jimm tana nazari, kamar ta ce bai tashi ba kamar kuma ta ce masa ya fita, a wannan shirun na ta Bello ya samu amsar tambayarsa, tausayin yarinya ya kama shi, a irin hallacin da tayi masa sam sam ba ta kamaci wani abu wulaƙanci a wurin Turaki ba balle tozarci, dan babu tozararci irin sakin da ya yi mata tana ƙarama da ita, ya miƙe yana cewa da ita,"idan ya dawo kice masa nazo, ina ta kiran wayarsa bata shiga ya yi ƙoƙarin kirana".
ta amsa da,"toh". sannan ta ce,"ba ka sha ruwa ba, ga tea zan kawo maka". bai kalleta ba amma yanda voice É—in ta ya fito ya tabbatar ruwan hawaye sun cika idanuwanta, kuma so ta ke ta zubar da su, ya sauke numfashi ya koma ya zauna tare da cewa,"oak kawo min tea kawai, kisa nescafe idan ba takurawa".
ba wai yana yin yunwa ba ne, a'a kawai ba zai iya ƙin tayan da tayi masa ba, dan sosai shi dai yake bala'in tausayinta.
ta wuce cikin sauri ta ɗau mug anan kan ƙaton family dining table, ta cika shi da ruwan tea sannan ta ɗauki plate ɗin da ta zuba irish da miyar hanta taje ta kai masa, shi ya tayata janyo center table gabansa dan yaga kamar mug da plate ɗin da ke hannunta suna neman rinjiyar waɗannan sillan karan hannayen nata, kar yaje ata dalilinsa ƙashin ƴar mutane ya karye.
ta na kallon carpet ta ce masa,"nescafe É—in ne dai babu sai na bayar an siyo, kuma mai gadi ya fita bai dawo ba".
da mamaki Bello ya ce,"sai an siyo?".
ta É—aga masa kai kawai tana sa hannu ta goge hawayenta. yay ta kallonta da mugun tausayinta ya ce,"kuma kin duba ko'ina a kitchen É—in babu?".
ta yi shiru, sai taji ya ƙara cewa,"tsaya tukunna!, faɗa min gaskiya kar ki ɓoye min komai, ke ɗaya kika kwana a nan ko?".
da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. yay guntun murmushi na takaici ya ce,"kar ki rufawa MT asiri, ɗan banza ne bai da hankali ko kaɗan, tunaninsa ba irin na mutane ba ne, gwara ma ki fayyace min komai dan ko kin ɓoye min shi ba zai ɓoye min ba. ki faɗan gaskiyar amsar tambayar da nayi miki".
hawaye su ka ƙara zubo ma ta bata ce da shi komai ba, a wannan hawayen ya karanto duk wata amsar tambaya da yake son yi ma ta.
ya sosa girarsa yana tunanin ta yacca zai shawo kan wannan lamarin, tun jiya yake tunanin ta yan da zai yi convincing Turaki akan ya mayar da aurensu, shikenan su zauna lafiya salin alin babu wanda ya san anyi, to amma ya san shegiyar gardama da rashin ɗaukar shawara irin tasa ba lallai ya amince ba, shi abun da yake gudu ma kar silar zaman nata a gidan azo a aikata kwaɓa, yay guntun tsoki ya ƙara trying lambar Turaki amma bai samu ba.
ya ce da ita,"ƙofar tsakiyar nan anan kitchen ya ke, ki kawo min nescafe ɗin".
sai ta juya tana kallon ƙofar da ta buɗe ta shiga ɗazu har tafi ƙarfin minti uku tsaye a ciki, ta ƙara juyo da kanta gare shi ta ce,"babu ai kitchen ɗazu duk na duba".
yay gajeran murmushi ya ce,"ai na zaki dinƙa girki idan babu kitchen?, ko kin taɓa ganin gida babu kitchen?".
ta ce,"a'a ƙila haɗe mana yayi da ita, anjima na ke son zuwa part ɗin nata".
Bello ya kaÉ—a kai,"kina uwar gidan zai tafi bangaren wata yayi kitchen?, to ba haka ba ne, kowaccenku da nata kitchen É—in, duba in da na faÉ—a miki".
ba ta iya jayayya da Babba ba, amma ita ta san babu wani kitchen, ta tashi taje ta buɗe parlon, yana ta kallonta a san da ta shiga ta tsaya daga bakin ƙofar, yay smiling ya ce ta buɗe ƙofar ciki, ta ƙarasa shiga ciki ta isa wa ta ƙofa da ta gani ta buɗe, jimawa kaɗan sai gata ta dawo riƙe da ƙaton gwangwani na nescafe, ta ajiye masa ta koma dining ta zauna, yana shan ruwan tea ɗin yana ɗan janta da hira sama-sama, har da tsokanarta wai an bata award na amaryar da tafi kowacce amarya kyau tun da aka fara aure a nigeria.
ita dai murmushi kawai take yi, kuma sai taji hirar tasa na yi mata daɗi musamman da yana bata labarin yarintarsu, irin yanda suke faɗa akai akai kamar ƴan tsaki, da yacca Baffa ke cin ƙaniyarsu, har ya ce yana basu purnishment ɗin yin dariya da haƙori ɗaya ko su ciji hancinsu in ba haka ba a dafa su a bawa mage ta cinye, sai suyi ta kuka suna bada haƙori in Baffa yaƙi haƙura sai su ɓuya a lambu, sun sha kwana acan yafi a ƙirga saboda basa son faɗan Baffa da dukansa ko kaɗan.
sai ta sami kanta da yin dariya sosai, sai da ya É—eba mata kewa tukunna yay mata sallama ya tafi, bayan tafiyar tasa duk sai taji babu daÉ—i, ta dawo ta koma upstairs tai kwanta zuciyarta cike da son ganinta a gida, yanzu ta san su Dadda sun É—au hanya, tana ta so ta yi waya da Umminta taji muryarta, tun da ta tashi take mugun kewarta.
ban da tunane tunane babu abin da takeyi har ƙarfe goma, sai lokacin ta tuna da aiken da ta bawa Baba, hakan yasa tayi saurin saukowa ta fita, tana fitowar kuwa ta tarar da Baba me gadi yana isowa entrance na ɓangarenta, ta tafi da sauri dan karɓar masa kayan, sai dai kamin ta ƙarasa Turaki ya rigata, ta ƙaraso wajen Baban a sanda Turaki ke miƙa masa hannu alama na ya ba shi kayan ba tare da ya ce masa komai ba.