Sashe 129
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fillo na murguɗe murguɗe da harare harare ta nufi hanyar toilet za ta shiga, yay amfani da sautin muryarsa wajen buga mata tsawa akan ta tsaya, duk ta yanda taso ta dake ta nuna rashin firgitarta sai da ta tsorata ta ƙame a wuri ɗaya jikinta na kyarma.
ya ƙarasa shigowa ciki ya ja stool ya zauna akai, ya saita kira akan lambar Maama, sannan ya ɗago yana kallonta yaga har yanzu rawar jiki kawai take kamar me jin sanyi tama ƙi buɗe idanuwanta, hawaye na sauka a kuncinta. yay tsaki na ban haushi da takaici, ya miƙa hannunsa ya fizgota sai gata ta wancakalo bakin gado kamar sandar da aka janyo, abunka da mara ƙiba sam sam.
"buɗe idonki". yanda yayi amfani da sautin muryarsa abin ya bata tsoro, kuma da ta buɗe ido ta kalle shi tsoron sai ya ƙaru fiye da misali, dan rikiɗewa ya ke yana komawa kamar ba mutum ba.
muryarta na breaking ta ce,"tafiya zan yi".
ya danna kiran Maama ya jefa mata wayar a jiki, niyyarta ta miƙe wayar ta tarwatse a ƙasa, amma sai taji Maama na magana, sannan ne ta ɗauka tana magana ta yanda Maama ba zata fahimci kukan da take yi ba a muryarta.
*comment, share and vote.*
[9/5, 19:45] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*48*
"Daughter nah". Hajiya Madina ta kirata da sabon sunan da ta raÉ—a ma ta tun a ranar da aka kawo musu ita.
"na'am Maama".
with much care Maama ta ce mata,"ya jikin naki?, da sauƙi ko kuwa?, kina shan magani?, yanzu ya kike ji?, mene yake ya damunki?".
waɗannann tarin tambayoyin yasa ta kallon Turaki ta gefen ido, idonsa na kan ɗaya wayar da ke hannunsa, fuskarsa kamar baƙin hadarin da ya haɗo, ta rufe ido ta ce,"Maama lafiyata lau, shi ne kawai yace miki ban da lafiya". ta faɗa kamar zata sa kuka.
furucin nata yasa Hajiya Madina murmushi, ko ba komai ta san da gaske jikin nata da sauƙi kamar yan da yace, ta furta alhamdullahi sannan ta ƙara cewa,"kina cin abinci sosai ko?".
ta ce,"ina ci".
"to Allah ya ba ki lafiya Daughter, Allah ya sa kaffara, ki daure ki dinƙa shan magani kinji, becx bana so na ji wani abu yana taɓa min ke, zan zo anjima na duba ku, Allah ya yi muku albarka".
a hankali Fillo ta ce,"Maama Ummina fa?". ta faɗa muryarta na ɓallewa da kuka.
zaton Hajiya Madina ko tana so ta ganta hakan yasa tace mata,"za ki je kiga Ummin ki very soon, ni da kaina ma zan kai ki".
kamar ta faɗawa Maama komai sai kuma tayi shiru, ita tambayar da tayi saboda Maama ta ce zata haɗa su a waya ne, in yaso sai tace da Ummi azo a ɗauketa dan ba ta fatan ta ƙara kwana acikin gidan da ba zaman aure take yi ba.
ta sauke wayar da ga kunnenta bayan Hajiya Madina ta kashe, ta waiga tana kallon Turaki ta ce,"ka ba ni lambar Kaka ko Ummi please".
maganar tata sai ya zama tamkar da dutse tayi, yay banza da ita ban da ma waya da ya kara a kunnensa yana amsa sallama, bata ɗauke idonta akansa ba taci gaba da kallonsa, hotunan kasadar da ta dinƙa yi wurin ceto rayuwarsa yana haska mata a ido, sai a yanzu ne ta yarda da cewa ɗan adam butulu ne, ita ba wai don ya saketa ba, a'a irin wulaƙanci ma da yake mata na nuna da ita da banza da wofi ɗaya, kuma ƙila duk yana mata haka ne saboda sanin mahaifinta da yay, da ma sai da ta faɗawa Ummi cewa wallahi bai aureta ba saboda abubuwan da ya faɗa sai don ya wulaƙantata, a lokacin Ummin ba ta yarda da ita ba hasalima faɗa suka haɗu suka dinƙa yi ma ta ita da Kaka, but yanzu ta san dole za su yarda da abin da ta ce, kuma ko ba komai ta san Turaki zai ga ishara akan aurenta da yay ba don komai ba sai domin ya tozartata.
maganar da yake yi a cikin wayar ta shiga kunnenta.
"no ba haka ba ne Faruq, bana fatan na ƙara maimaita kuskure, this time around ba zan yi gaban kaina ba, ba zan ƙara yiwa kaina aure ba sai da sanin iyayena, kai ba ma aure ba kawai, dukka wani abu na rayuwata, gaban kaina da nayi banji da daɗi ba, ni ɗaya na san halin da na shiga, but da na rabu da kowacce yanzu komai ya zamar min normal, ina cikin farin ciki da kwanciyar hankali".
_na rabu da kowacce._ kalmar ta maimaitu a cikin kan Fillo, kenan har Ilham ma ya rabu da ita?, ita kuma me tayi masa?, wai wanne irin mutum ne shi É—in?, kenan shi ma yana sahun mazan da basa mutunta aure, burinsu su aura su saka?.
ta yiwa kanta tambayar da zuciyarta ke ba ta amsa, tunaninta ya tsaya cak san da taji yana cewa,"sunanta Aisha Æ´ar sarkin kano ce, insha'Allahu gobe nake so naje na gana da iyayenta, zan fara neman izininsu before na kai maganar gaban su Baffa, ita ba ni da matsala da ita becx ita ta fara cewa tana so na, so pray for me kar na sami matsala da Baffa, dan nima ina son yarinyar sosai...".
cak maganarsa ta katse dalilin ƙarar fashewar abu da yaji, yay saurin ɗago ido yana kallon wurin da Fillo ke tsaye tana ƙoƙarin saka hijab, sai kuma idonsa ya kai kan wayarsa da ta tawarwatse a ƙasa, ta yi ragaga tamkar tayar mota ce ta bi ta kanta.
bai san lokacin da ya miƙe ba yana bin ƙasan tiles ɗin da kallo, yana kallon kowanne pieces na glass ɗin wayar da ya barbaje.
Muhimman abubuwansa da suke kan wayar!, hakan ya gimla a zuciyarsa, lokaci ɗaya ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, ya dunƙule hannu ya ɗago kansa a fusace yana kallonta wacce ke shirin ficewa, da zafin nama ya janyo hijab ɗin nata ya dawo da ita gabansa yana cewa,"are you mad?". ya ɗaga hannu sama a zafafe zai sauke mata kyawawan mari tayi saurin yin ƙasa da fuskarta, take jinkinta ya ɗauki rawa saboda yacce take jin hucinsa na cika ɗakin.
babu shiri taja da ba ya tana rarraba ido, sai da ta kai jikin bango tukunna ta sami damar ɗago da kai tana kallonsa, tayi mugun tsorata da yanda ƙwayar idonsa ta sauya kala, da yanda taga kamar yana huruwa yana sacewa, tsananin tsoron abun da zai iya aikata ma ta yasa ta ɓallewa da kuka tana faɗin,"to ai bana sa ne".
ta faɗi hakan dan ba ta tunanin kalmar haƙuri za ta iya fitowa da ga bakinta zuwa gare shi.
Turaki ya rumtse idonsa gam for few minutes yana so ya taushi zuciyarsa, ya buɗe ido yana furzar da iska daga bakinsa, ya watsa mata wani mugun kallon da ya ƙara hargitsata, cikin ɗagowar murya ya ce,"zo ki ɗauko ki ban".
hakan bai sa ta ko motsa da ga in da take ba, illa ma haɗe rai da tayi tana juyar da kanta gefe guda, Turaki ya daɗa fusata yay taku ɗaya ya isa gabanta, ya shaƙi wuyanta ya manna kanta da bango.
ya zaro mata idanuwansa waje ya ce,"ke wacce kalar halitta ce ne da babu ƙwalƙwalwa a jikinki?". ya faɗa da wani amon sauti da ba nasa ba, zai iya rantsewa tun da yake ba'a taɓa ɓata masa rai ba irin yau, fashewar wayar ba shi ne damuwarsa ba, crucial documents na office da yay saving a phone storage, jiya ya gama ɓata lokaci wajen saving wani document na contract ɗin da suka karɓa, Bello kawai yake jira ya zo ya tura masa, yanzu shikenan ta jiƙa masa aiki, kwana yayi yana typing bai ko runtsa ba, haka ya dinƙa aikin babu daɗi saboda ya baro laptop ɗinsa a office.
ya cije leɓensa na ƙasa yasa ƙafa zai fyaɗeta ta kife a ƙasa sai kuma ya fasa, ya buga mata tsawa da cewa,"wuce ki ɗauko ki ban".
tuntuni ta daina tsoronsa, sai dai ta rasa dalilin da yasa ta kasa daina jin tsoron tsawarsa ba, tana tafe yana bin ta a baya.
ta durƙusa sai kyarmar jiki takeyi ta ɗauko wayar ta ba shi, yasa handky ya karɓa gudun kar glass ya soke shi, ta yi tsaye tana zumɓura baki, ta ƙara jin saukar tsawar muryarsa da cewa,"tattaro glass ɗin".
zata wuce ɗauko tsintsiya ya fincikota. "hannu za ki saka". ta kallesa taga babu alamar imani tare da shi hakan ya sa ba shiri ta durƙusa ta shiga tattara kwalban, idonsa ƙyam akan hannunta da ke zubar da jini dan tun a ɗauko wayar kwalabar ta soketa.
sai da ta gama tattarawa ya wurga ma ta ɗayan handky ɗin, ta ɗauka ta zuba glass ɗin a ciki ta miƙo masa, ya karɓa yana nunata da yatsa cikin kakkausar muryar da ke shaida kashedi me girma ya ce,"kar ki kuskura, kar kiyi saken da zan dawo cikin gidana na sameki, in har kuwa na dawo na tadda ke ki tabbatar da cewa alƙiyamarki ta tsaya, dan sai kin ƙwammace ba ki taɓa sanin zuri'ar Alƙali ba balle kuma ni, and ki san da cewa sai kin biya ni wayata".
yana faɗar haka ya fice fuuu ya bar ɗakin, ta bi bayansa da kallo kafin ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka sosai, babu abin da take ji a zuciyarta sama da danasanin saninsa, sai da ta daɗe a haka sannan ta miƙe tunawa da kashedin da yayi mata, ta ɗauki jakarta ta fita daga ɗakin tana jin zuciyarta kamar zata buga, jiri ne ma yake neman zubar da ita dan da ƙyar idanuwanta suke kallon gabanta, tana sakkowa da ga benen ta faɗi kanta ya ƙumu da ƙarfen benen, cikin ƙarfin hali ta tashi tana daddafa bango ta iso har ƙofa ta buɗe.
daidai da zuge glass ɗin ƙofar da Hajiya Madina tayi, karaf idonta ya fara sauka akan hannun Fillo da ke zubar da jini, ta zaro ido waje tana ambaton,"subhanallahi".
sai kuma ta kalli Fillon taga tana hawaye ga shi kamar ba ta cikin hayyacinta, tai saurin kamota ganin tana neman faÉ—uwa.
"Daughter lafiya?, wannan jinin fa da ga ina?"