← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 176

Sashe 89

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma kamar gimlawar Jinnu haka Hajiya Ramla taji maimacin furucin da Fillo tayi acikin kanta. ta dafe ɓarin kanta tana ta ambaton Allah har sanda taji wani abu na tafiya acikin kanta yana fitowa yana barin jikinta. lokacin kuma ta saki ƙara tana dafe kan sosai tana ƙara ambaton Allah.
wucewar daƙiƙa biyu ta buɗe idonta ta sauke su a wurin da ta-ke, hankalinta da tunaninta da suka dawo dai-dai suka fara tambayar a ina ne nan ɗin?.
magana ta farko da ta fara tunawa kamin gushewar hankalinta itace,_"ni Fulani Azima ni ce nayi miki asiri Ramla, saboda kin aure min farin cikina, dan haka kamar yanda na rasa Dikko kema kin rasa shi har abada domin asirin dake kanki har ki mutu ba zai barki ba, Æ´aÆ´anki kuma zan saka su a tafin hannu dan suma sun shiga gonata tun da har ubansu yay kuskuren haifarsu da wata ba ni ba"._

wannan furucin na Azima shine furuci na ƙarshe da zata iya cewa ta tuna kafin hankalinta ya bar jikinta gaba ɗaya, ta rufe idonta tana tuna amintar dake tsakaninta da Fulani Azima tun suna Oxford University.

sai kuma tayi hanzarin buɗe ido ta maida kallonta kan Fillo wacce wahala tasa tayi laƙwas sai nishi kawai ta-ke saukewa. ta kamo hannunta jikinta na karkarwa tace,"ina ne nan ɗin muke?, kuma ke wacece?, sannan ina Babana da Zaytuna?, aina zan gansu?".

Fillo tace,"Mum suna gida ki tafi kije ki samesu, ni ƴar aikin gidan ce". tayi maganar da ƙyar tana jin ƴaƴan cikinta kamar zasu fito saboda masifar yunwa da ƙishiryawa.
Hajiya Ramla ta É—agota jikinta tana faÉ—in,"ta ya zan tafi na barki bayan kin taimake ni, ke ya akai kika tsinci kanki a wannan halin?".
tambayar ta kawo zubar hawaye me zafi akan kuncin Fillo tace,"kidnappers ne suka É—auke ni".
Hajiya Ramla tace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yi haƙuri ki daure ki tashi muje kinje, kin san hanyar da zamu bi muje asibiti?, domin kina da buƙatar ganin likita ƴata".

Kuka ya kubcewa Fillo tace,"Mum ai ba zan gane hanya ba, ban san nan É—in ina bane dare yayi sosai".
Hajiya Ramla tace,"kamar kin ban waya É—azu ko?".
kai kawai Fillo ta iya ɗagawa dan ƙarfinta ya ƙare bata jin akwai sauran yawu da ya rage a bakinta da zata yi magana.
tasa hannu a rigarta ta zaro wayar Hajiya Ramla ta karɓa, ta danna 0 tana ƙoƙarin tuna lambar Baffa ko ta Maama amma sai taji ta kasa, tai ta trying taji ba zata iya rubuta duk wata lamba da taɓa sani ba".

tace,"Æ´ata na mance lambar kowa da na sa ni, amma naji kina ta ce min Babana da Zaytuna banji kina min maganar Madina da Khalil ba, dan Allah suna ina?".
Fillo ta kasa magana kwata-kwata. Hajiya Ramla ta yunƙura ta miƙe tare da kamo hannunta tace,"yi haƙuri ki daure mu bar wajen nan, idan muka isa titi Allah zai kawo mana mafita". Fillo ta ɗaga kanta kawai.
"mu nufi gabas insha'Allahu sa'a ce zata fitar da mu".

Fillo ta daure da ɗan sauran kuzarin da ta-ke da shi suka ci gaba da gudu, sanda suka fara hango titi dai-dai lokacin ne kuma mota ta shigo layin da wani mahaukacin gudu irin tuƙin ƴan wiwi, tsoro yasa su kasa kaucewa gaban motar, haka ma Aliyu dake driving rikicewa yasa shi rasa yanda zaiyi, ganin motar tayo kansu gadangadan babu ta yanda zasu kuɓuta Fillo ta ture Hajiya Ramla daga kusa da ita, dai-dai lokacin kuma Aliyu yabi ta kan Fillo ta gangara gefe ɗaya.
cikin tsananin tashin hankali, ɗimauta da gigita Hajiya Ramla ta ƙwala ihu tana ɗora hannu akanta ta kurma salati, kafin tayi kan Fillo a guje tana ɗagota zuwa jikinta, ganin uban jinin dake zuba yasa ta fashewa da matsanancin kuka tana ƙara ambaton innalillahi.

Aliyu ya fito daga mota a hargitse yana furta,"innalillahi wa'inna ilahi raji'un".
Inna Wuro ma ta fito daga bayan motar ta taho da sauri tana faɗin,"shikenan ka shiga uku kai ɗaya Aliyu dan ban dani wallahi, yanzu ai kaga amfani jin maganata ni da kake ɗauka a watse, tuƙin mutuwar da nake hanaka kana maida ni gantalalla kana ƙara wani akai ga shi nan yau yaja maka masifa ka bige aljanu".

tayo wajen da Aliyu ke tsaye ya rasa abinyi, jinin dake zuba jikin Fillo ya rikitar da shi tashin hankalinsa É—aya kar ace ya kashe rai.
ya zaro wayarsa a aljihu ya kira wayar Ammi, tana ɗagawa cikin dauriya da ƙarfin hali irin namiji yace,"Ammi ki fito na kaɗe wata yarinya, kuma kamar ta mutu Ammi".

Hajiya Ramla kuwa sai kuka take yi tana jijjiga Fillo akan ta tashi, Inna Wuro ta ƙaraso wajen da Hajiya Ramla ke zube a ƙasa da Fillo akan cinyarta, ta tsaya daga ɗan baya tace,"bayin Allah aljanu kuyi haƙuri dan Allah, ni wallahi babu ruwana, saukata kenan daga saudiya ko awa ɗaya banyi ba, aka tura wannan gantalallan yaron yaje ɗauko ni, alhalin tuntuni na faɗawa ubansa ya daina aika shi taho da ni tunda baida hankali, to da yake dai nayi rashin sa'ar haihuwar ɗa me jin maganata sai ta ƴaƴansa, in gaya miki sarauniyar aljanu tun daga iya fat Aliyu yake fafara wannan tuƙin mutuwar da ni, ina ta roƙarsa Allah Annabi ya tsaya yaƙi tsayawa saurarena saima ƙara wani da yake yi, yanzun ma ina ta ce masa zai buge mutane yaƙi jina ashe da rabon manyan zai shafce, rashin jin maganata yasa ya buge ƴar sarkin aljanu dan ba tsautsayi bane yana sane, dan haka wallahi kuyi masa duk abunda kuga dama baida kirki ko kaɗan, ko ƙafarsa ce ma ku shanye ta yanda zai daina tuƙa motar, kuyi haƙuri aljanu ni dai banda laifin komai Aliyu ne ku kumbura masa ciki wallahi tunda ya kashe muku ƴarku".

duk wannan maganar da take idonta rufe yake, sai yanzu ta ɗan buɗe ɗayan kaɗan tana kallon Mum, ita tsakaninta da Allah ta-ke maganarta aljanu suka bige, saboda yanda taga yalwataccen gashin Mum har kusa da ɗawawu, ga shi duk da uban dafewar da tayi hakan bai sa tsananin hasken fatar da ta-ke da shi ya dusashe duka ba, hakanne ya ƙara tsorata sosai ta-ke zaton aljanu ne musamman da taga dare ne yanzu, mai lafiya dai ba zai fito a yanda suke ɗin nan ba duka babu ɗankwali gasu a hargitse kamar sababbun kamu.

ta durƙusa a ƙasa tana yin alamar roƙo tace,"me girma aljana kiyi haƙuri ki daina tunanin yanke hukunci da ni, ki sunkuci ƴarki ku ɓace kuyi nahiyarku dan Allah. idan kuma ba za ki haƙura ba wallahi na goyi da bayanki kici uban Aliyu dan ko kaɗan baida mutumci, ga gidansu can ubansu shine ɗana ni na haife shi da cikina, amma ba kiga yanda ake wulaƙanta ni ba a gidan, matansa biyu ɗaya me mutunci ɗaya watsatstsiya, amma duk su ɗin sai suka haifi gantalallun yara ba kiga yanda suke bani wahala ba wallahi har kuka sai kin yi min idan kinga a yanda nake zaune a gidan, ni kuma kamar mayya na kasa barin gidan saboda duk cikin yarana gidan Amadu ne kaɗai kullum ake shan shayi da ƙwai da naman ganda da safe, sauran gidajen ƴaƴan ko daga ɗumame sai koko babu ko sikari aciki, to ba zan mutu a wahala ba na dawo gidan Amadu ake ban kayan daɗi ana gani min azaba".

Mum ta É—ago jajayen idonta tana kallon Inna Wuro, hakan yasa Inna Wuro zabura taga da baya tana faÉ—in,"wa'innahu min sulaimana wa'innahu bissimillahir Rahmanir Rahim".
Mum na kuka sosai tace,"yanzu ba zaku taimaka min ba sai na rasa Æ´ata?".
Inna Wuro na adu'a a bakinta tace,"ku kuwa kuna da taurin kai mutanen ɓoye, kawai kiyi siddabarunku ta tashi shine har sai anje asibiti salon dai aja kuɗin ɗana Amadu, kuma na faɗa miki indai Aliyu ne ku tafi da shi can nahiyar taku kawai kuci ubansa wallahi, ƴaƴan Amadu da yawa ba shi ɗaya ya haifa ba".

Mum na kuka ta kalli Aliyu da duk yake a ruÉ—e, shima tsoron ya fara kama shi yana ganin kamar ta bakin Inna Wuro aljanun ne.
adu'a kawai yake yana ƙara kiran wayar Mum da bata ɗagawa, Hajiya Ramla ta miƙe ta sunkuci Fillo da ƙyar zata goyata a lokacin ne Daddy da Ammi da me gadi suka iso wajen cike da tashin hankali.

Aliyu yace,"ban san garin ya ba Daddy, nayi ƙoƙarin ƙwacewa na kasa".
Daddy ya ɗago yayi masa wani kallo, sannan ya doka masa uwar tsawa yace,"dan uwarka baka da hankalin da zaka iya ɗaukarsu zuwa asibiti ne da har sai ka kira?, ko baka ga jinin dake zuba daga jikin yarinyar bane shashashan banza, comon zo karɓeta ku sata cikin mota".

Aliyu ya taho cikin mutuwar jiki suka kama Fillo shi da me gadi suka saka a mota.
cikin hanzari Daddy ya shiga driver seat sannan Ammi ma ta shiga gaban motar, Aliyu da Mum kuma sauka zauna da Fillo a baya, Daddy nata bawa Mum ɗin haƙuri, Ammi dai ta kasa cewa komai dan duk a ruɗe ta-ke.

Daddy yace,"kiyi haƙuri Hajiya ki daina kukan kiyi mata adu'a, insha'Allahu matsalar ba babba bace".
Inna Wuro ta ƙwanƙwasa glass tace da Daddy,"buɗen bus ina kwaso kayan jaririyar Yusuf da na yo mata tsarabarsu, da tsada na siyo dubu sha biyar duk guda ɗaya".

Daddy yace,"kiyi haƙuri mu dawo tukunna kinga a condition ɗin da yarinyar nan ta-ke kar jininta ya ƙare".

ta zabga salati tace,"Amadu yanzu har Æ´ar sarkin aljanu ta fini matsayi a wurinka, saboda kana tare da aljanu ba zaka iya jin maganata ba, to kaje ni dai ba abinda zance wallah sai dai Allah ya saka min".
Chapter 89 · 0% Book details