← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 176

Sashe 146

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai ta saka facemask ta fesa turare sannan ta fuskanci gaba ɗaya windon, tace da ita,"na san kina ta so ki buɗi baki ki nemi yafiyar abin da kika yi min ni da ɗana, kamar yanda kike so ki buɗe baki ki faɗi mugwayen abubuwan da kika aikata. ban da masaniyar ko Allah zai baki aron wannan damar, but ki sani ko da bayan raina kika sami damar magana, karki tsammaci za ki ambaci sunana da roƙon na yafe miki, karki saka sunana acikin waɗanda zasu yafe miki, Azima ba zan taɓa yafe miki abin da kika min ni da Babana ba, sai mun tsaya a gaban ubangiji ni da ke, sai Allah yayi mana hisabi. but just keep in mind da bakina dai ba zan taɓa faɗar abin da kika aikata ba, idan Allah ya nufeki da yin magana kafin mutuwarki kya bada labarin zaluncin da kika aikata, duk da bana fatan Allah ya baki aron wannan damar, gwara ki tafi da tarin alhakin mutane ta yanda za ki ɗanɗani abinda kika shuka tun a ƙabari kafin ranar tsayuwa a gaban ubangiji, Azima insha'Allahu har mutuwarki babu me yafe miki abin da kika masa domin ke ɗin azzaluma ce".

tana gama faÉ—ar haka ta bar bakin windon tana kuka.
hango tahowarta yasa Zaytuna fitowa daga mota tazo ta kama hannunta.
Hajiya Madina ta kalleta ta girgiza kai tace,"your excellency".

Mum ta É—aga kai ta kalleta, sai Maama tasa tissue tana goge ma ta hawaye.
"don Allah ki daina zubar da hawayenki ga wacca bata kamaci a zubar ma ta da hawaye ba, duk da irin tsananin halin da take ciki, masu imani ake yiwa kuka ba azzalumai irin Azima ba".

sai kuma ta numfasa ta ƙara cewa,"in dai ina raye Allah har Azima ta mutu ba za ki ƙara zuwa inda take ba, balle ki dinga zubar da hawaye haka a banza, ba gwara ki tara mana hawayen ba idan abin farin ciki ya same mu ki yi".

"na daina ma daga yau, ba zan ƙara ɓarnatar da hawayena ba akanta".
"better!, ki godewa Allah da ya saka miki tun daga nan duniya".

da sauri Hajiya Ramla ta É—ago tana dubanta da mamaki.
Hajiya Madina tayi murmushin da ya tsaya a iyakar leɓenta sannan tace,"ban da masaniyar wanda yay miki asiri kika bar gida, but haka ɗaya nake jin zuciyata ta kasa aminta da Azima, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya amma ni dai ita nake zargi, shiyasa ko kaɗan bana tausaya ma ta, wallah in har itace silar asirinki da na me babban suna da yardar ubangiji sai tayi mutuwar wulaƙanci".

tayi shiru tana rufe idonta na sakanni sannan ta buÉ—e, sai kuma ta juya topic É—in da cewa,"yanzu me babban suna suka shigo, ba ki gansu ba gwanin sha'awa sunyi kyau sosai, sai naji kamar ni É—aya nai sa'ar haihuwar É—a me kyau da kuma dacen balarabiyar sirika".

Hajiya Ramla tayi murmushi. "ai ce nake ba za su zo ba, dan É—an naki yayo halin kafiyarki".
"yanzun ma na faÉ—a musu sannu ce kawai ta kawo su, da zarar sunyi ma ta sannu ko ta amsa ko bata amsa ba suyi tasowarsu su tafi".

Hajiya Ramla ta girgiza kanta,"da ba ki ce musu haka ba ai".
"hakanne ma yasa na hanasu zuwa wurinki nace su wuce wurin BoÉ—ejon kai tsaye, kana tausayin me tausayinka ne, haka kana mutunta me ganin mutuncinka".

ƙafafun Turaki suka shiga cikin parlon kafin na Babyn roba su bi bayansa, ya kama hannun Fillo da ke rakuɓe a bayansa suka shiga ciki.
su ka zauna da ga É—an nesa inda BoÉ—ejo tasa wata hadimarta tayi musu nuni, tun da akace ma ta su ne ta sunkuyar da kanta, har suka zauna kuma ko É—ago kai bata yi ta kalle su ba don bata tunanin iyayensa ma sun isheta kallo balle shi kansa da wata sillan karan matarsa.

Fillo ta kalleta taga tamkar bata san da shigowarsu ba, sai taji wani abu me kama da tsoro ya kamata, ta kalli Turaki suka haɗa ido, cikin bin umarnin da yay ma ta da ido ta buɗi baki ta ce,"Boɗejo ina yini, ya sauƙin jiki?, Allah ya ƙara miki lafiya yasa kaffara".
ta haÉ—e duka maganarta a lokaci É—aya, dan ta san abu ne me kamar wuya BoÉ—ejo ta amsa ma ta, ile kuwa kamar yanda tayi tsammanin uffan ba ta ce ma ta ba.

Turaki ya kama hannunta ya riƙe wanda yake jin yana rawa a jikinsa. ransa ya ɓaci sosai, daraja ɗaya Boɗejo zata ci haifar Baffa da tayi, ya rumtse idonsa ya buɗe, ya danne abin da yake ji yana taso masa a zuciya ya ce,"tsohuwa ashe ba kiji daɗi ba, na san ba komai bane sai kewata ko?, to ai gani na zo kuma naga sai wani ciccin magani kike yi, ko ba'a maraba da ganin nawa?".
ya faÉ—a cike da tsokana dake tsakaninsa da Kakar tasa.

ta ɗago tayi masa wani kallo me cike da ban haushi ta ce,"munafiki, mara mutunci, wanda ya kunyata ni akan kucakar ƴar aiki, wanda ya fifita mace akan bin umarnin mahaifinsa, kai har kana tunanin muryarka ma ina ƙaunar ji ne, ai tuni na sallamaka acikin jikokina, saboda haka ka bar bin wata hanyar shishshige min, ranar da Amaryarka ta koma ɗakinta wataƙila ma iya shiryawa in akwai rabon hakan".

yay murmushi me faɗi har da sauti yace,"ashe zamu shirya ɗin dai, yanzu dai ya jikin naki kin ji sauƙi ko ya?".
ta galla masa harara,"ina ruwanka da lafiyata, ka ga tun kamin raina yay mugun ɓaci tashi ka fita ka bar min waje, idan ba haka ba na ƙwala ihu yanzu na ƙalawa wannan ƴar banzar yarinyar sharrin da babu wanda zai iya ƙwatarta duk duniyar nan".

fuskar Turaki ta washe da murmushi ya ce,"yo ba tana da Allah ba, shi ai zai ƙwaceta, yanzu dai ban gaji da ganinki ba kya bari in gama kallonki tukunna sai ki kora ni, ke kawai daga yi miki kishiya duk sai bi ki zama fitinanniya, wannan kishin naki yayi yawa".
ta jijjiga kanta ba tare da tace da shi ƙala ba.

Fillo ta miƙe ta ɗauki manyan ledojin da suka shigo da su guda biyu, taje gaban Boɗejo ta tsuguna ta ajiye, muryarta ta fito very cool da cewa,"ga wannan ba yawa, Allah ya ƙara miki lafiya".

ta numfasa, ta ɗora hannunta akan ƙafar Boɗejo, cikin taushin murya tace,"don Allah kiyi haƙuri, Allah ya huci zuciyarki, da ni da shi duk bamu da laifi, zanen ƙaddarar mu ne ya zo a haka, tun kafin zuwanmu duniya ubangiji ya rubuta cewar zamu kasance a inuwa guda ɗaya, Allah ya rubuta hakan a lauhul mahfuz, dan haka ni ko shi ko wani babu wanda ya isa ya sauya abin da Allah ya rubuta zai faru, illa kawai mu roƙe shi ya juyar da abinda zuciyoyin mu basa so su zama alkhairi a gare mu, ya kuma saka mana haƙuri da dangana mu karɓi lamarin a yanda yazo mana".

tayi ƙoƙarin ɓoye kukan dake shirin ƙwace ma ta. "don Allah don Annabi kiyi haƙuri ki daina fushi da kowa, duk mun san munyi miki laifi, babu wanda yaƙi bin umarninki, babu wanda zai so abin da ba kya so, kawai dai babu yanda zamu yi da lamarin da Allah ya shirya dole zai faru ne. don Allah Boɗejo ki daina fushi da Maama da Mum, haka ki daina fushi da mijinmu".

ta ƙarashe maganar su na haɗa ido, sai Boɗejo taji wani abu da bata san menene shi ba ya tsarga mata akan Fillo, abu ɗaya ta sa ni kamar yarinyar tana da wani girma na kwarjini wanda ba zaka san da hakan ba zai ka kalli ƙwayar idanuwanta, haka kuma akwai hikimar zance a bakinta wanda samun hakan shima babbar baiwa ce.

duk sai taji ta kasa yi ma ta cin mutuncin da tayi niyyar yi ma ta a duk ranar da tayi tozali da ita, alwashi ne da ta ɗauka, so tayi duk ranar da suka yi ido huɗu sai ta yiwa Fillo abin da zai sa ta bar gidan Turaki da ƙafafunta, tayi tafiyar da ba zata taɓa dawowa gare shi ba.
idanuwan Fillo suka manne akan mirrow ɗin da ke fuskantarta, murmushi ya suɓuce a saman leɓenta wanda ita kaɗai ta san tayi shi, hatta Turaki dake kallonta ba zai ce tayi ba.

Boɗejo ta haɗe rai tana ɗauke hannun Fillo akan ƙafarta ta ce,"Malama ta shi ki bar kusa da ni, kuma ki ɗau tsiyarki, ki kai can ƙauye inda ake yunwa, amma ba nan inda aka fi ƙarfinsa ba".

Fillo ta marairaice murya ta ce,"tuba nake ranki ya daÉ—e, ina barin kusa da ke ne kawai idan har an dubi girman laifin da na aikata an yafe min ba, hakan kaÉ—ai zai sa in sami sukuni da salama. Kaka bata fushi da jikokinta, ko da tayi hutu ne ta É—auka saboda ta huta da rashin jinsu, ranki ya daÉ—e namu hutun ya isa haka a tausaya mana".

mamaki ya hana Boɗejo cewa komai, ƙaramar yarinya kamar wannan ta iya zaro zancen tsari irin haka, zancen da tana da tabbacin ba har zuciyarta take yi ba, tsabar kissa ne kawai.

"ka taso ka dawo nan".
muryar Fullon ta fito ta wuce kai tsaye zuwa cikin kunnuwan Turaki, ya rufe bakinsa da ya buɗe yana kallonta tun ɗazu, ta sakar masa wani kyakykyawan murmushi da ya sa shi tasowa babu shiri, sannan nata murmushin ya ƙaru a sanda ta kuma yin tozali da madubin.

ya zauna kusa da ita, ya kama hannunta guda yana murzawa, tare da kai hannu ya É—auki apple dake cikin plate, ya gatsa sannan ya kai bakin BoÉ—ejo ya ce,"Uwar gidana".

ta mangare hannun nasa, ta taso masa cikin masifa har sai da Fillo ta ƙanƙame shi saboda tsorata ba tare da ta san tayi hakan ba. shi kuma yay saurin kewayeta da hannunsa yana cewa da Boɗejo,"yi a hankali tsohuwa Baby bata son hayaniya".

sai ya É—an narkar da murya yace,"kin ga kin tsorata min ita ko, haba don Allah BoÉ—ejo wannan wanne irin fushi ne haka da ba'a hucewa, ce nake tun da har yarinyar nan ta riga ta tare shikenan komai ya wuce".
Chapter 146 · 0% Book details