← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 176

Sashe 36

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kana gani kasan tura tuwon kawai takeyi, bata ko tsayawa ta gama cinye na bakin zata ƙara saka wani, tunda take bata taɓa cin malmalar tuwo me girman wannan ba, kai abincin kansa bata cin da yawan hakan, shi yasa Yami kullum ke mata tsiyar taƙi ci tana ta bushewa.

yana zaune yana shafa wayarsa amma indonsa sam ba akan wayar yake ba akanta yake, tun lomar farko da ta kai baki. ba ƙaramin ba shi dariya tayi ba ya danne yana cije leɓe murmushinsa na fita saboda dariyar ba zata dannu duka ba, yanda take ta tura abinci cikin sauri, har yunƙurin amai tayi amma tayi maza ta maida shi, ga jikinta ma gaba ɗaya rawa yake kamar mazari.

cikin mintunan da ba zasu haura uku ba plate ɗin ya zama babu komai, ta cinye tas sai nishi take yi, ta sauko taje ta wanke hannu ta dawo. ta kalle shi taga ma hankalinsa bai kanta, wayarsa kawai yake dannawa, kamar tayi magana ta roƙe shi suyi haƙuri sai dai tayi shiru, ta kama yatsun hannunta sai jansu take kace tana lazimi. idanuwan nan da suke loko sai ƙifƙiftasu take. Turaki duk yana kallonta, har maganar da bakinta ke son yi yana kallon yanda ɗan ƙaramin leɓen ke motsawa. shi gani yake ma kamar ƙunƙuni take tana zaginsa.

su na haka aka murɗa ƙofa, tana jin hakan gabanta yay mugun faɗuwa ta haye kan gadon gaba ɗaya a zabure, ta takure ƙafafuwanta tana shirin sakin kuka.
muryarta na karkawa ta cewa Turaki,"tun ɗazu na cinye abincin dan Allah kuyi haƙuri".

tana rufe bakinta sai taga ashe su Kaka ne ba Dr Yusuf ba kamar yanda ta tsammata. hakan yasa ta saki ajiyar zuciya tana bin Kaka da ido, taga fuskar Kakan a haɗe alamar ɓacin rai.

"sannu fa me babban suna".

Turaki ya tashi ya amsawa Kaka. "yauwa Kaka sannunku da dawowa. ya me jiki?".

tace "da sauƙi...kayi zamanka mana".

yace,"a'a Kaka dama ina niyyar tashi ai".
tace,"ni dai da ka zauna wallahi, bana jin daɗi idan kana ƙin zaman nan saboda mu".

ya kalli tsohuwar da jin tausayinta a ransa, sosai suke kama da Fillo kawai dan ita ta tsufa ne. ba ya son musu da babba saboda haka dole ya koma ya zauna.

bayan ya zauna Kaka tace,"muna daÉ—a godiya fa me babban suna, babu abin da zamu ce sai Allah ya saka maka da gidan aljannah. kai da iyayenka kuna kulawa damu Allah ya biyaku da alkhairansa".

yace,"amin Kaka na gode".

ta sake cewa,"Maijidda ce taje take faÉ—a mana abin da ke faruwa na za'a shiga da ita tiyata, shi ne muka taho. nace ai hakan ma wani gata ne akai mata".

Yami tace,"Allah yasa dai ayi a sa'a".

ya sosa girarsa leɓensa na fitar da murmushi yace,"ehh likitan ne dama ya bada shawarar hakan".

karaf Fillo tayi saurin cewa,"a'a ba shi bane kaine ka fara faɗa masa. ni dan girman Allah Kaka kuyi haƙuri indai abinci ne zanke ci".

Kaka tayi mata banza, Yami tace,"to ai magana ta ƙare tunda har likitan ma yayi shirinsa. kiyi adu'a kawai Allah yasa ayi miki a sa'a, hakan ai gata akayi miki Fillo kinga yanzu cikinki ga dinƙa samun abincin kirki. magana kuwa kya dinƙa nuna abunda kike nufi da hannu".

Yami na yin shiru Fillo ta fashe da kuka tana kifa kanta a gwiwarta, ta sani babu wanda zaiji tausayinta, kuma babu me jin kukanta tunda bata da uwa bata da uba a raye.

Turaki ya É—auke idonsa akanta, zai fita Kaka tace,"a'a me babban suna tunda dai sa hannunka ne a yin aikin nan to ka É—an jira likitan yazo a É—auketa a gabanka. mu ba jin maganarmu take ba,".

Tana faÉ—in haka suka fice su duka suka bar Maijidda a tsaye, itama sai ta fara hawayen.
bayan fitar su Kaka ya jawo kujera sosai gaban gadon sannan ya zauna, ya aje wayarsa akan gadon, sannan ya sarƙe yatsunsa wuri ɗaya.

yace da ita,"haƙura za'ai da farka cikin ko kukan za ki ci gaba?".

kalmar farka cikin ita ke É—aga hankalinta, tayi saurin É—agowa fuskarta tayi sharkaf.

"dan girman Allah karka sa a farke min ciki, zan dinga cin abinci kullum, ai kana kallo na cinye na É—azu. dan son da kake yiwa Maama da Adda Zaytuna kace ba za'ai min ba".

mamaki yasa kawai ya tsareta da ido, ta ya akai tasan yana ƙaunar mutanen nan guda biyu?, ta ya tasan zai iya yin komai akansu?, wa ya faɗa mata ana roƙonsa da su ya aikata abin da bai niyya ba?.

ya sauke numfashi sannan yace,"an fasa".

a hankali tace,"na gode, Allah ya kareka daga sharrin maƙiyanka".

ta faÉ—a tana goge hawaye da É—ankwalinta da ya zame. suka haÉ—a ido tayi saurin É—auketa nata, ya kalli gashin kanta yace,"É—aura É—ankwalin ki bani amsar tambayata".

Ta ɗaura ya ƙara cewa,"to ki cire tsoron ki nutsu".

ta haÉ—iye wani irin yawu tana saita nutsuwarta. taji yace,"É—ago idonki ki kalle ni".

tayi yunƙurin yin hakan amma sai ta kasa, yaci gaba da kallon siraran hannunta da suke ta karkarwa, sai kawai ya miƙa hannunsa ya haɗe hannayenta biyu ya riƙesu cikin nasa guda ɗaya, sai dai da mamakinsa duk da hakan basu bar karkarwar da suke ba kamar ma ƙaruwa abin yayi, cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi wannan rawar da jikin nata yake yi bana lafiya ba ne.

jin yanda ya riƙe hannuwan nata yasa ta kulle ido wani abu na wucewa ta maƙogoronta. kuma kafin ta buɗe idon taji yace,"me ya kai ki wannan wurin a wancan ranar?".

ta buɗe ido ta sauke a saman sumarsa tana jin numfashinta na ƙoƙarin katsewa.

****
Yusuf na zaune a office yana operating computer wayarsa tayi ringing, ya kai hannu ya É—auki wayar, yana duba sunan me kiran yaga Inna Wuro, ya katse tukunna yabi bayan kiran.

Inna Wuro na É—aga kiran ta maka salati,"innalillahii wa'inna ilaihi raji'una. Yusuf kana ina?, kaiwa Allah kazo da sauri babu lafiya".

tun salatin farko da ta ja ya miƙe daga kan kujerarsa, tana cewa babu lafiya bai jira komai ba ya kai bakin ƙofa, yabar office ɗin cikin sauri hankalinsa a tashe.

daga parlon Inna Wuro ta soke wayarta a gefen zani bayan kiran wayarsu da Yusuf ya katse. ta kalli Nuratu wacce ta tattare carpet ta kwanta a ƙasan tiles, sai yamutsa fuska take yi hannnunta riƙe da tulun ƙasa ƙarami da aka zuba yashi acikinsa, acikinsa take tofa yawu.

"ina dalili, gwara ya baro duk abunda yake yi yazo aiwa tufkar hanci, ba zan iya rainon wannan cikin nasa me shegiyar ƙazanta ba. ba ni nayi ciki ba dan haka ba zanyi wahalarsa ba, azo duk abi a dinga tofe min ɗaki da yawu yana ƙarni...yanzu fa fisabillahi ji wani abu, anyi shara kin ɗage min carpet salon dai ayi baƙo a tafi anayi da ni a duniya bana gyara wajena, alhalin ba haka nake ba, kai da gyara wani can da baku haɗa komai da shi ba yazo ya ɓata maka...kuma ni dai gaskiya nake faɗa miki kwanciyar ƙasar nan illa zata miki, inda rabon kin haifo ɗan da sanyi yayi ƙatutu a jikinsa ne ni ba abin da ya dameni ba ne".

ta ɗau mayafinta da ke kan kujera ta fita daga parlon, ɗan ƙaramin durstbin na shara ta ɗauka a ƙofar parlon sannan ta wuce ta nufi can inda incilerator yake zata zubar da sharar sai mita take yi.

"yanzu ni ba abin na faɗawa Amadu irin cin kashin da ƴaƴansa suke min ba yaga kamar ina tukura musu alhalin nazo ina cin arziƙinsa, Zainabu ta ƙullace ni tace zan haɗa ƴaƴa da ubansu. gwara nayi shiru na haƙura watarana sai labari, amma tsakani da Allah ni ba daɗin hakan nake ji ba, kawai dai dan babu yanda zanyi ne, amma cuta kam ana cutata".

ganinta mai gadi ya taso da sauri. "Inna ina za ki haka da kanki?".

Ta tsaya tana gyara mayafi tace,"ni ko wa nake da shi da zai min bacin na ƙarfafa jiki na yiwa kaina".

ta ɗaga ƙaramin durstbin ɗin sharar tace masa,"kaga dai yanda kwandon nan ya cika ko?".

ya É—aga kai yace,"na gani".
tace,"to billahi ina faɗa maka ko dattina ɗaya babu a ciki, bar ganin daga ɓangarena ya fito".

Mai gadin yace,"to fa garin ya haka kuma Inna?".

tace,"kar ka tsammaci aljanu ne, wallahi ko ɗaya basu da hakki, mutanene marasa tausayin tsoho. Ƴaƴan Amadu ne wallahi, haka suke zuwa su cika min ɗaki alhalin ubansu yayi musu nasu, to ba za su zauna a nasu ba dole dai sai anzo wajena an ɗauki magana. ni kuma bana biye musu kasanni da haƙuri, ban iya ɗaukar magana ba saboda bana son tashin hankali. kuma dai naga gidan na ubansu ne arziƙinsu nake ci shi yasa na iya zamana da su banda haka kullum sai anji kanmu...yanzu fa ka duba ka gani wannan sharar daga safiya zuwa yammacin nan aka tarata, da ci banza ci wofinsu aka mayar min da ɗaki kamar bola. yo ni kuwa me zanyi wanda ya wuci Allah ya isa".

Mai gadi yace,"a'a dai Inna haƙuri za'a ci gaba da yi, banda dai Allah ya isan kinga ai jikoki ne".

tace,"yo abunda ba ni na haifa ba balle bakina ya bisu su gantale, barni nayi kayata ni dai kam ai Allah ya isar min kawai. kai ai baka san wani abu ba ma, Allah ya isa ai sun saba da ita, dan jiya yaron nan Aliyu ce min yay wai babu wajen shigar tawa, daga nan na sallama nace Allah ya isa kam yanzu na fara har sai tawa ta sami shiga... yanzu ka duba ka gani banda dai rashin tausayi ina uwar me ƙaton gidan nan da kai shara, ko da yake rayuwa ce kowa yay na gari kansa...haka zanta haƙuri har dai Allah ya kawon mafita, ko kai haka iyalinka ke Uwarka?".

Mai gadin yace,"a'a Inna".
tace,"kaga inda arziƙi yake, banda gidan Amadu inda Ƴaƴan ba kyau matan ba kyau".

Mai gadin ya karɓi basket ɗin yace,"kawo na zubar miki, ai ba kyaje wurin can da kanki ba yamma tayi".
Chapter 36 · 0% Book details