← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 176

Sashe 170

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta buɗe baki a hankali tace,"ko kai fa Baban biyu, please you take good care of our kids, ko babu ni na san kai uba ne na gari, na san yaranmu ba za su yi kukan maraici ba, kayi musu dukkan gatan da uba yake yiwa ƴaƴansa, ka ba su wadataccen ilimi, kaja su a jikinka ta yanda zaka dinƙa jin damuwar kowannen su, ka kula da tarbiyar su, tarbiyar su da iliminsu!, tarbiyarsu da ilimin su don Allah Jannaty".

furucin nata yasa yaji kamar zai yi kuka, ya ƙanƙameta yana faɗin,"bana son magana irin wannan, you promise me that we will be together forever, so why talking like this?".

"Allah ya baka haƙuri ba zan ƙara ba daga yau, ka yafe min".

taja hancinsa laɓɓanta na motsa da murmushin ƙarfin hali tace,"i love you Turakin Fulani".

sai kawai ya miƙe tsaye, ya manta da nurses ɗin da ke tsaye a gefe, ya manta da su Mum da ke tsaye su na kallonsu, ya manta da mutanen dake giftawa, yasa hannu ya ɗagota, ya haɗe bakinsa da nata yana kissing har tsawon minti biyu, kafin daga baya ya shiga kissing ko'ina na fuskarta sannan ya rungumeta tare da furta,"i love you morethan you do Fulanin Turaki".

a lokacin ne kuma Dr ya bawa nurses umarnin cewa su wuce da ita É—akin tiyatar.
sai taji hannun Turaki na zamewa daga cikin nata, muryarsa na fito a mugun karye, yana yi mata adu'ar Allah yasa ayi cikin sa'a, Allah yasa ta fito lafiya.
sai kawai ta rumtse idanuwanta gam, tana jin nurses ɗin na tura gadon nata suna barin wajen, tana jin kamar tana so tace musu su ƙyaleta ba sai an ciro yaran ba.

Turaki yabi ta da kallo yana ganin yacca hawaye ke sauka ta gefen idonta, hawaye na farko da zai cewa ya gani a tare da ita tun a ɗazu da ta fara naƙudar.

"don Allah kar kuyi min allurar bacci, ku yi min idona a buÉ—e, ina son ganin a yacca za'a fito min da Babies É—ina".

ta faɗa idanunta na kallon likitocin da ke kanta tare da nurses, a lokaci ɗaya sai taji tausayin bawan Allahn da rayuwarsa take tamkar a nannaɗe da tata, Turakinta! Mijinta!, uban ƴaƴanta, wanda ta san a duk lokacin da tata rayuwar ta ƙare, lokacin da ta zama bata cikin rayuwarsa, to tabbas bata san ya duniyarsa zata kasance ba.

sannan tausayin ƴaƴan da zasu fito daga cikinta yay mugun matse zuciyarta, bata san ya rayuwarsu zata kasance ba a yayin da babu ita, bata san ya tasu ƙaddarar rayuwar zata zama ba, bata san irin jarabawowin da za su fuskanta ba, duk da ta san babbar jarabawa a gare su shi ne na rashinta, za su taso ba tare da uwar da ta kawo su duniya ba, za su ta so ba tare da sun san wannan ɗumin jikin na uwa ba, za su taso babu wannan kulawa da soyayyar da yake a wurin uwa ba kaɗai.

"bismillahir-Rahmanirrahim, bring the knife".
haka taji likitan da ke tsaye akanta ya faÉ—a, kuma bayan wannan zata iya cewa jinta ya É—auke na É—an wani lokaci kafin ya dawo.

a san da aka fara aikin, idanun Fillo a jiƙe suke sharkaf da hawaye, hawayen da ya hanata ganin komai sosai. a wannan lokacin dukkan tunaninta ya gama hargitsiwa da kowanne motsin dake faruwa a cikin ɗakin tiyatar, tana jin yacca sautin zuciyarta ke bugawa da ƙarfi acikin kunnenta.
lokaci ɗaya taji sautin wata ƙara ta fita a jikinta, sautin da ta tabbatar na yanka ne, cikinta ake yankawa!, sai taji zafin ciwon da take ta daurewa ya ƙaru, zafinsa na ƙaruwa sosai da sosai, zafin da har ta kai ga kasa tantance cikinta ake yankawa ko kuma ruhinta ake zarewa.

hawaye ya bi ta gefen fuskarta, ta ji kamar ta ɗago tasa hannu ta danne wajen da aka yanka ko zata sami sassauci, sai dai babu abin da zata iya, bata da ƙarfin motsi ko kaɗan, tamkar matacciya take.
tsawon lokaci babu wani abu dake wanzuwa a cikin É—akin tiyatar sai fafutukar da likitoci ke yi wajen ciro yaran daga cikin mahaifiyar su.

kunnuwan Fillo sun ji lokacin da aka ciro Baby na farko, Babyn da taji Dr na cewa da nurses su yi ƙoƙarin su wajen ganin yayi kuka, sai taji wani farin ciki ya ratsata, farin cikin da taji tamkar an yi mata bushara da gidan aljannah.
so take taga yaron da aka ciro, don haka cikin ƙarfin hali da dauriya ta karkata kanta gefe domin kallon jaririn da cibiyarsa kaɗai take iya hangowa, kuma a san da nurse ɗin ke juyowa zuwa sashinta, lokacin sabuwar azaba ta ƙara ratsata, tayi saurin rumtse ido tana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

ambaton nata ya haÉ—e tare da kukan Baby na biyu da aka ciro, kukan da ya cika É—akin gaba É—aya, kukan da zata ce kamar ta tsinci sunan da take ta muradin ta haife su taji sun kirata da shi, Ummina!.
a san da Babyn yay shiru sai taji jikinta ya tsaya a lokaci ɗaya, yay sanyi ƙalau, numfashinta mai nauyi na cigaba da fita, yayin da zuciyarta ke bugawa a hankali, hakan yasa ta fahimci cewa hargitsin azabar ciwon da take sha yazo ƙarshe, ƴaƴa biyun da ke cikinta an fito da su duniya, ta zama uwa, dukkan fatanta da burinta ya gama cika, atleast ta samu masu yi mata adu'a a kowacce daƙiƙa a yayin da komai ya riga ya kai ƙarshe.

ta riga ta san abin da yake cikinta tuntuni, macece da na namiji ne ba sai an faɗa mata ba a yanzu. tana jin yacca motsin yaran da ake ta aikin gyarawa ke mutsutsu acikin kunnenta, tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da son su da ƙaunar su, sannan a hankali ta fara jin komai na zamewa daga cikin kanta yana barin ƙwaƙwalwarta, cikin ranta tana adu'ar,_"Ya Rahman if you decide to take my soul at this time, i beg you Allah to give my husband and my childrens the strength to bear it, Allah kaji tausayin ƴaƴana, ka tausayawa maraicin su ka basu tamkar Hajiya Madina a matsayin wacca zata kula da su"._

da ga wannan furucin dake cikin ranta, sai kuma bakinta ya shiga maimaito kalmar shahadar da taji tana wanzuwa acikin kanta, hakan yasa idanuwan likitocin da ke É—akin ya manne akanta, akan murfin idonta da ke barin kan twins É—in da ake nuna mata amma ta kasa kallon su.
kuma wucewar sakanni biyar komai ya zama ya ƙare, komai ɗin dake rayuwar Fillo, shikenan wa'adin da ubangiji ya ɗiba mata ya cika, alƙalaminta ya riga ya bushe, ubangiji yayi hukuncinsa.

bayan wasu mintuna Turaki da ke tsugune a ƙofar ɗakin tiyatar yaji an buɗe ƙofar, bai motsa ba dan bai san ta yanda zai motsa ba, yana so dai ya buɗe idonsa yaga abin da ke wanzuwa, so yake ya buɗe ido ko ya samu zuciyarsa ta daina bugawar da take yi.
acikin wata fargaba da ke tare da shi yaji an ɗora hannu akan kafaɗar sa, sai ya ɗan buɗe ido kaɗan yana kallon nurses guda biyun da ke tsaye akansa tare da likita, ba zai ce ga lokacin da ya miƙe ba, ya dai tsince shi ne tsaye akan ƙafafunsa yana kallon jariran dake hannun nurses ɗin, bai san me yake ji a zuciyarsa ba, amma dai ya san bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa hannu ya fara karɓar namijin, sakanni uku yana kallon yaron me kama da shi sak kafin ya miƙa shi ga Dr Yusuf da ke tsaye a kusa da shi, sannan ya daɗa karɓar macen da ita ce ƙarama, kuma a lokacin da ya ɗora idonsa akanta a lokacin Doctor ɗin yace da shi,"I am very sorry to tell you that your wife is no more, Allah yayi mata cikawa, ina yi maka ta'aziyya Allah yaji ƙanta da rahamarsa".

a maimakon rufewar da idanun Turaki ke shirin yi sai yaji sun maƙale akan jaririyar da ke kuka a hankali, jaririyar da yake hasko fuskar mahaifiyarta a fuskarta.
sai kawai yaji furucin likitan na maimaituwa acikin kansa,_"your wife is no more"._

sai yaji kalaman likitan suna ƙara tafiya a hankali, yayin da yake ji suna barin cikin kunnensa har zuwa cikin kansa da zuciyarsa in da suka samu masauki, don ya kasa gane ta yadda zai karɓe su balle har su yi ma'ana a cikin ƙwaƙwalwarsa.
Fulani ta mutu?, yana nufin Fulaninsa ta mutu, Fulani ta mutu!, Fulanin da suka yini tare yau, to ta ya zai yarda da hakan?.

sai kawai ya kutsa ta tsakiyar mutanen da ke gabansa ya faɗa cikin tiyata room ɗin still yana riƙe da jaririyar, yana shiga ya hangota an rufeta, rufewa tana nufin lulluɓewa har fuska, irin lulluɓewar da ya gani akan Maamansa sati biyu da suka wuce, irin lulluɓewar da yasan mamaci kawai ake yiwa, irin lulluɓin nan da ake yiwa gawa kaɗai.
Turaki ya tsaya cak tamkar mutum mutumi, idonsa na kallon gawar, yaji guiwoyinsa sun yi sanyi ƙalau, irin sanyin da suka kasa cigaba da ɗaukarsa, don haka sai ya nemi bango ya dafe gudun kar ya faɗi jaririyar da ke hannunsa ta cutu, haka ya dinƙa jan ƙafa yana dafe da bangon har ya ƙarasa gaban gawar, a lokacin ƙafafunsa suka kasa ci gaba da ɗaukarsa ya zube a wajen, ya damƙi mayafin da aka lulluɓeta da shi, a hankali ya shiga adu'ar.

"Allah ba yanzu ba, Allah ko don waɗannan jariran, zuwansu duniyar kenan Allah, Allah ka sauya musu wannan ƙaddara ya zama ka ɗauke ni ba mahaifiyar su ba, sun yi kaɗan da irin wannan jarabawar, Allah don Allah ka dawo da Fulani ka ɗauke ni,  Allah kar kasa Fulani ta tafi ta barmu, Allah ka tausaya mana ba zamu iya ɗauka ba,Allah ka tausaya mana don masoyinka fiyayyan halitta, Allah don son da kake yiwa Annabi Muhammadu SAW".
Chapter 170 · 0% Book details