← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 176

Sashe 135

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jakar laptop ɗinsa ya ɗauka ya fita a room ɗin, daidai bakin ƙofar room ɗin Fillo ya tsaya, ƙofar a buɗe take, ya tsaya yana tunanin ya shiga ko kar ya shiga, a ƙarshe zuciyarsa ta yanke masa yay tafiyarsa kawai, tun da har ta iya barin ɗakin nasa taji sauƙi kenan.
yana saukowa parlo ƴan aiki suka fito da sauri daga kitchen, suka durƙusa suka gaida shi, hannu ya ɗaga musu ba tare da ya amsa da fatar baki ba, har ya kai bakin ƙofa idonsa ya sauka akan dining, flask ne guda biyu a ajiye sai na tea flask, ya kalli Sakina da ba ta koma kitchen ɗin ba ya ce,"ta sakko ne?".

kanta a ƙasa ta ce,"a'a ranka ya daɗe bata sakko ba kwatakwata".

yay É—an jimm sai kuma ya ce,"ita tace kuke yin girki?".

ta ce,"a'a ranka ya daÉ—e, mun ga dai hakan na cikin aikin mu ne".

ƙaramin tsaki kawai yayi ya zuge glass ya fi ce, Sakina ta bi shi da kallo tana riƙe haɓa da jinjina kai.

Hannatu na ganinta ta ce,"lafiya?, me kika guntso?".

"uhmm ke wannan me gidan bai da sauƙi ko kaɗan, babu ma alamar mutunci a tare da shi, ni da ma tun ranar farko naji bai yi min ba sam, gaskiya matarsa na haƙuri da shi, irin mazan nan masu shegen girman kai da izza, fuska gaba ɗaya babu annuri".

Hannatu ta ce,"wani abu kika gani hala".

tayi maganar da irin suffa ta ƙwanƙwararrun munafukai.

"ke kin ji yacca yake tambayar wa ya saka mu yin girki, kamar fa zai kawo min duka, babu wani irin taushi girmamawa ta É—an adam acikin muryarsa".

sai kuma ta taɓe baki,"ni da ma na faɗa miki tun ranar da muka zo na san ba zaman lafiya ake a gidan nan ba, ba ki ga ita kanta kamar ba ta da miji ba, sai dai ta sauko tayi kallo taci abinci ita ɗaya ta koma, tabɗijam ni kuwa dai duk kuɗin namiji wallahi ba zan yarda da rashin mutuncinsa ba, ke ni ba zan ma yarda da wani auren dole ba, ba zan iya namiji ya takani ba gaskiya".

"ke ma dai Sakina ai da ma da gani ba auren soyayya akai ba, ni itace ma ta ke bani tausayi tun da naji ance tayi aiki a gidansu, wataƙila ƙarfi aka nuna musu aka aura ma ta shi dan anga ba su da hali, ni tausayi ma take bani kina kallonta kin san bata jin daɗin zaman, ko da yake babu komai zamu ɗaurata a hanya, naga ba ta da girman kai za ta sake da mu, zamu ba ta shawarwarin da zata saita mishi zama".

Sakina ta nufi cooker gas tana faɗin,"ke yanzu dai buɗe firinjin nan ki ɗauko mana kazar nan da naji ta ɗan fara yami, mu gyara muci abarmu in ba haka ba a banza za'a barta ta lalace, naga matar gidan ba wani wayewa tayi da cin kayan daɗi ba, duk gata nan a ƙanjame ai. Allah na tuba ni ina da wannan uban kayan daɗin ma me zai sa in damu da takaicin ɗa namiji, ai ɗaukarka zanyi in bawa banza ajiyarka, kai ita ma dai wallahi anyi lusara, ko da yake wasu sun ɗaukaki soyayyar namiji fiye da jin daɗi, kuma kin san Allah duk yanda akayi ganinta ƙashi da rai yasa yake ma ta wulaƙanci, babu gaba babu baya kyace me cutar S, kai Allah dai mun gode maka, kuma banza da ita ma kawai ta jefa shi a kwandon shawara ta bawa jikinta ingantattun kayan da zasu farfaɗo da ita, ba dai gidan jin daɗi da hutu ta zo ba, wallah wata guda yay ma ta yawa ta murmure".

Hannatu tai Æ´ar dariya tana fito da gasashshiyar kaza a freezer,"Sakina ko dai ko dai, kawai...".

bata ƙarasa ba Sakina ta juyo tana yi ma ta wani kallo,"ko me?, ni da wannan miskilin mijin?, ba dariya ba murmushi babu fara'a?, azaba!, Allah ya kiyaye wallahi, ai ranar farko zan bakawa gidan nan wuta dan ba zan iya da mugun halinsa ba, dukanta fa yake yi".

Hannatu ta riƙe baki,"kai don manzon Allah?".

"mtswww ke sai shegiyar gulma ba kya sa ido a abu, jiya baki ganta tana kuka ba?, to da daddare ma lokacin da ya shigo na hau saman ina jinsa a É—akinta yana zazzaga mata masifa ita kuma sai kuka takeyi, ke Allah yasa ma ba sakinta yay ba dan naga yau gaba É—aya fa ba ta sakko ba".

Hannatu tayi dariya,"wallahi yana sakinta zan shiga daga ciki, wa ye zai so rabuwa da wannan gidan da aka aje daula, aljannar duniya, ita ma É—in dai shashasha ce kawai, ni fa yana burge ni sosai saboda yana da kyau kamar ka sace shi ka gudu, kuma da yardar Allah sai ya zama rabona". ta faÉ—a tana jujjuyawa,"kalle ni fa da kyau, kissar Æ´an aiki zanyi kawai a wuce wurin".

buɗar bakin Sakina za ta yi magana suka ji sallama a parlo, da sauri suka fita a tare, ganin Yami yasa suka ƙarasa da sauri su na yi ma ta sannu da zuwa, Yami na yi musu fara'a ta amsa musu, ta zauna akan kujera tana tambayarsu ya aiki.

"ina matar gidan fa?". Yami ta tambaye su.

Sakina ta yi saurin cewa,"bari a hau a kirawota yau ba ta sakko ba gaba ɗaya, ƙila ba ta tashi ba".

Maijidda ta cire hijab ɗinta ta ajiye tana cewa,"ƙyale ta bari na hau na sakko da ita".

ta faÉ—a tana nufar upstairs, kuma duk da haka Sakina sai da ta bi ta saboda taje ta yo munafurci.

“Aa lafiya dai?” Maijidda ta tambaya lokacin da take ɗora ƙafafunta akan steps.

Sakina ta ɗan sosa gefen fuskarta ta ce,“Aa da ma wai...”. dakatar da ita Maijidda ta yi kana ta ce,“Aa Kika ce bata sakko ba ko, na ce miki to zan je na gani ko lafiya, ina ga ai babu kuma buƙatar sai kin biyo baya na ko kuwa?. Kije kiyi aikin gaban ki”.

Haka kawai ta tsinci kanta da fad’a mata wad’annan maganganun ba tare da sanin dalili ba.

but still sai da Sakina ta bi ta ɗin bayan ta haye, kuma tana hawa ɗakin Turaki ta buɗe a hankali ta shiga, tai tsaye daga bakin ƙofa tana yi masa kallon tsab, ganin kan gadon ba'a gyare ba yasa ta riƙe baki tana jijjiga kai, ko me ta saƙa a ranta oho, da sauri kuma ta fito tana barin wajen ta nu fi ɗakin Fillo.
Maijidda kuwa tana isa ta ga ƙofar d’akin Fillo a bud’e, bata yi mamaki ba sanin cewar Turakin baya nan, kai tsaye ta saka kanta ciki d’auke da sallama. Bata ji alamun za'a amsa ma ta ba don haka kawai ta kutsa kanta ciki, a karo na biyu ta ƙara yin sallama saboda son ta samu izini kamar yadda Manzon Allah (SAW) yay mana umarni da mu yi.

Sai da tayi sallama uku babu amsa hakan ya sa ta ƙarasa ciki tana kuma ƙara yin sallama, rufe bakinta ke da wuya sai ta jiyo kamar shesshek’ar kuka, hakan ya bata damar yin sauri ta isa bakin gadon tana fad’in,“hasbunallah wa ni’imal wakil, na shiga uku ni Hauwa, Ke! Meye ka faruwa meye damuwan?, Wani ya mutu bani da labari ne?.”.
kawai sai itama ta fashe da kukan, da ma itama gwanar hawaye kamar Fillon, ganin hakan Kuwa ya ba ma Fillo damar ‘kara fashewa da wani matsanancin kuka cike da shagwab’a da iya shege gami da zallar wawta.

Sakina dai na laɓe bakin ƙofa ta kasa kai da kunne, ta rufe baki tana fito da idanu waje.
Maijidda tayi saurin kai hannu ta janyo Fillo jikinta, da tsantsar kulawa da damuwa irin ta ƴan'uwantaka take fad’in,“wai don Allah me aka yi maki?, don Allah ki sanar da ni meye wai ni don Allah?”.

Da k’yar Fullo ta bud’e baki ta fara magana, leb’en sama da na k’asa su na had’uwa su na faman luguden kuka,“wai wai ni fisabilillah haka kawai..”.

Maijidda ta zabura tana k’ara fad’in, “wai Ke me?, don Allah ki min bayani inji?, kin san kuwa duk yanda gabana ke faɗuwa?".
“to wai ba Turaki ba ne haka kawai shi kullum ya gagara ya fahimce ni sam, sai yay ta faman ji da kansa, kullum sai yay ta ƙin kula ni yana share ni, ko kallona ma ba yayi, sai dai fa yay ta hararata, kuma idan nayi magana sai yay ta min tsawa yana ɗaga hannu zai mareni, ni sai yay ta min abu kamar ba mijina ba, da ma sai da na faɗa muku ba ya so na, ni kawai gida zan koma, ki kira min Ummi a waya please".

kukanta ya ƙaru a san da take ƙarasa maganar.

damuwa ta bayyana fal a fuskar Maijidda, cikin sanyin jiki da murya ta ce da ita,"kuma kina yi masa biyayya?, kina sauke duk hakkinsa da ke kanki?, kuma ba laifi kika yi masa ba?".

tasa hannu tana goge hawayenta ta ce,"ai ni bana kula shi ma".

Maijidda ta ware ido,"ba kya me?, kwatakwata ba kya kula shi kike nu fi ko kuwa da ku ka yi faÉ—an ne?, ni ban gane rashin kulawar ba".

"ni kawai ba na kula shi ai baya so na?".

Maijidda ta raɗa ma ta abu a kunne, Fillo ta ɗago daga jikinta tana faman ɓata rai,"ni nace miki komai ma bana kula shi, sai jiya ma na fara ganinsa a gidan, ni dan Allah ki kira min Ummi a waya azo a tafi da ni".

"Allah me girma da É—aukaka, yau ina ganin iya shege, da ma Fillo har haka kika kai ba kiyi hankali ba?, mijin naki za ki ce sai jiya kika gansa bayan sati guda da aure?, kuna cikin gida É—ayan?, to wa kika barwa shi?, É—aya matar tasa ko kuma Æ´an aikin?".

kuka ya ƙara zuwar ma ta,"to ai shi ne baya zuwa inda nake, kuma da yazo sai ya fara min tsawa alhalin ya san bana so".
Chapter 135 · 0% Book details