← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 176

Sashe 22

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"tom Maama, sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya ya dawo daku lafiya"
har bakin mota tai mata rakiya, Khalil ne zai ja motar dama, ta shiga tana tambayarsu,
"ina Hammanku da Nihal?".
Sameer yace,"Hamma ba lallai yasan mun fito ba, amma naga Nihal tayi wajensa da nake fitowa".
"kira min shi".

Sameer ya É—auki waya ya kira shi, sai dai kamin ta kai ga yin magana ma yace gashi nan fitowa.

Fillo kuwa tana komawa key ta ɗauka ta fito ta wuce ɓangaren Turaki, ɓangarensa dake jikin na Baffa. tana shiga parlon taji maganarsa na tashi a parlon.
tayi saɗaf ta ɓoye ta wajen wani corrido, dan har ga Allah ita ba so ta ke suke haɗuwa ba saboda bata son wannan tsawar da yake sakar mata, yana sakata tana tunawa da moment ɗin da ba son tunawa da shi ta ke ba.

kuma har zuwa wannan lokacin tana ƙyale shi ne kawai saboda darajar mahafiyarsa, banda haka da tuni ta nuna masa tafi ƙarfin ya dinga zaburar da ita dan kawai tana aiki ƙarƙashin arziƙinsu.

shi da Nihal ne wadda taji tana roƙonsa akan dan Allah ya bawa Maama haƙuri. maganar ta ke tana karyewa saboda kukan dake fita daga bakinta. ta leƙo taga Turakin na tsaye ne ya harɗe hannayensa ta baya yana fuskantar gabas, kansa a sama kamar me tunani. ita kuma Nihal gwiwoyinta na zube a ƙasa a gabansa. kafin ya juyo gareta yaci gaba da magana bayan shirun da tayi.

"arziƙi da talauci duka na Allah ne, idan Allah ya baka arziƙi ba yana nufin kafi kowa bane acikin bayinsa, kuma ba wai an baka dama ba ne dan ka wulaƙanta wanda bai da shi ba, shima idan Allah yaso yana iya ba shi nasa rabon, ko kuma ya ƙwace daga hannun kai da kake wulaƙanta talaka ya bawa wanda ka raina...but kin san me nake so ki fahimta?".

Nihal ta ɗago da kanta tana kallonsa, sannan ta girgiza kanta alamar a'a. shi kuma yaci gaba,"Mama uwa ce da yau ba zata so ace ƴarta ta shiga gidan da zata wahala ba, wannan haka yake ga kowacce uwa...burin iyaye ne ace ƴaƴansu sunyi aure sun zauna a inda zasu ji daɗi, dan haka Maama bata hana alaƙarki da shi ba ne saboda yana talaka ba...".

tun bai kai ga ƙarasawa ba ta katse maganarsa,"Allah Hammah tace makusarsa a wajenta shine talaucinsa, banda haka babu abinda zai hana ta barina mu'amala da shi...kuma ni wallahi Hammah ina sonsa, shi kaɗai zuciyata ke da muradin aure".

ya kai hannu ya shafo wuyansa yana mai lumshe ido ya buÉ—e. "ba za'a hanaki aurensa ba dan kawai yana talaka, idan har na gari ne to ba shi da wani aibu a idon Baffa...saboda haka ki kwantar da hankalinki, ta shi muje".

ta miƙe ya kama hannunta suka fita. Fillo ta sauke ajiyar zuciya, duk yacce ta ke tunanin mutumin nan ba haka yake ba. shi ɗin me kyau ne, kuma ta fahimci yana da kyan zuciya.

contact 08024976578
[8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

*13*
Hakimi wato Alhaji Babba zaune akan royal chair ɗin da ke tamfatsetsen parlon da ya gaji da tsaruwa da kayan alatu, duk wani kayan jin daɗi na mo re rayuwa an zuba a wannan parlon, haka idan har kai farin shiga ne a zuwa gidan, to tabbas zaka iya rantsewa ba'a ƙasar nigeria kake ba. farin rawani ne akansa, kana masa kallo ɗaya zaka san jinin sarauta ya gama ratsa shi.

kamar yanda tarihi ya gabatar, an kafa Masarautar Gombe a shekarar 1804 a lokacin jihadin Fulani wanda Buba Yero mabiyin Usman ɗan Fodio ne. Buba Yero ya mai da Gombe (Abba) hedikwatarsa ​​domin yaƙin da ake yi da matsugunan Jukun na Pindiga da Kalam, daga nan kuma yayi ta kai hare-hare har zuwa Adamawa da ke gefen kogin Benue.

a lokacin sarki Alhaji Bukar Dukku shi ke riƙe da sarautar garin gombe, bayan rasuwarsa ne kuma babban ɗansa Hashim Bukar Dukko ya karɓi sauratar, wanda ya riƙe sarautar tsawon shekaru masu yawa.
Sarki Hashim Bukar ya ajiye ƴaƴa a ƙalla guda takwas kuma dukansu maza, kuma duk su takwas ɗin sun fito ne daga tsatson mace guda ɗaya Sarauniya Falmata, wacca a lokacinsu ne aka kafa tarihin sarkin daya zauna da mace ɗaya tal a karagar mulkinsa har rayuwarsa ta ƙare ba tare daya mallaki ko da ƙwarƙwara ba.

cikin ƴaƴa takwas daya bari sune Adam, Ishaq, Lateef, Harun, Ibrahim, Yusuf, Isma'il, Shu'aib. akaf cikin yaran babu wanda ya samu kulawa me girma da gata daga wurin mahaifinsa irin babban ɗansa Adam, kasancewar tunda Sarauniya Falmata ta haife shi sai da ta shafe shekaru shida kafin ta ƙara samun wani cikin, lokacin har sun yanke tsammani da samun wani rabon, kuma daga haihuwar Yarima Ishaq shikenan ta shiga jero haihuwar ƴaƴa har sai da ta jera 8 gaba ɗaya.

duk da ƙarancin shekaru da Yarima Adam ke da shi a wancan lokacin, hakan bai gaza fahimtar cewar shi wanene ba, ya san daga tsatson daya fito, domin a ko da yaushe mahaifinsa na faɗa masa cewar gaba da bayansa shi ɗan sarauta ne dan ko mahaifiyarsa ma ƴar sarki ce.
bayan tarin ƙauna, soyayya, gata da kulawa wadda Yarima Adam ya samu a wurin mahaifinsa da mahaifiyarsa, sai kuma na ɓangaren al'umma. waɗanda suke ƙasƙan da kansu a gare shi matsayinsa na ɗa ɗaya tilo a wurin Mai Martaba da suke jin basu da tamkarsa.
hakan kuma ya haifar da aƙida ta girman kai da gadara a wurin Yarima Adam, har ta kai ga yana nuna ƙasƙanci ga na ƙasansa, hatta ga hadiman dake kewaye da Sarki kuwa.

tun kamin ayi masa ƙanne ya haddace wani furuci dake fitowa daga bakin al'umma na kirarin da suke yi masa da Yarima Sarkin Gobe, kai ɗaya ne Yariman da akai babu irinsa, bayanka sarauta gabanka sarauta.
amma tun daga lokacin da mahaifiyarsa ta ƙara haihuwa sai yaji salon wannan kirarin ya sauya, kuma bai gyaru ba har zuwa lokacin da ta tsaya da haihuwa, kirakiran ya tashi daga kansa shi ɗaya ya koma har ga sauran ƴan'uwansa.

dalilin da yasa zuciyarsa tayi baƙi kenan akan ƴan'uwansa, dan yana ganin silarsu zai iya rasa wasu tarin nasarori daya rubuce su a tafin hannunsa. da tafiya tayi tafiya sai ya zamana sam Yarima Adam baya ko da raɓar inda ƴan'uwansa suke, tsakaninsa da su nisantar juna, basa samun fuska a wurinsa matsayinsa na babbansu.
tun zuciyarsa na raya masa wani abu wai shi ƙiyayya har hakan ta tabbata akan ɗan'uwansa Yarima Lateef, wanda ya ƙwace duk wata fada da yake da ita a wurin mahaifinsu, wannan soyayyar da gata da dukkan komai da ya samu lokacin da yake shi ɗaya daga wurin mahaifinsa gaba ɗaya sai ta koma kan Yarima Lateef, hatta da soyayya da girmamawar da al'umma suke ba shi.

kuma hakan ya samo wuri ne dalilin banbancin halayya, cikin kaf su takwas ɗin da Mai Martaba ya mallaka babu wanda ya ɗauko kyawun halayyarsa da ɗabi'unsa sai Yarima Lateef, shine yasan darajar mutane, saɓanin sauran da suke nuna ƙasƙsanci ga mutane, haka shine kaɗai mai sauƙin kai amma kaf sauran suna da mummunar ɗabi'a ta girman kai, kuma shi ɗaya ne mai son mutane da yi musu fara'a, gaba ɗaya Yarima Lateef kan manta da cewar shi ɗin jinin sarauta ne kasancewar ba'a gabansa take ba, amma ƴan'uwansa sarautar itace abar alfaharinsu da tunƙahonsu, a karan kansu sukan ji tamkar su mutstsuke juna saboda girman izza, kowannensu mulki da muƙami kawai yake wa hari a rayuwarsa amma banda Yarima Lateef.

shakarun Yarima Lateef 24 a duniya mahaifinsa ya aura masa Æ´ar gidan wazirinsa me suna Rumana, itama kuma sai ta samu matsuguni na soyayya a wurin Mai Martaba ta dalilin É—ansa da take aure, dan tunda akayi auren Mai Martaba da Sarauniya Falmata suke kiranta da gimbiya.

a wannan lokacin Yarima Lateef yayi auren biyayya ne kawai ba don yana son Rumana ba, sai bayan auren kuma ya gane cewar zaɓin mahaifinsa kyakykyawan zaɓi ne a gare shi, kuma dama abinda yasa baya son auren ganin cewar yayyansa Yarima Adam da Yarima Ishaq basu yi aure ba, sai yake ganin kamar babu dacewar ace shi ya riga su yin aure.

wannan aure na Yarima Lateef shi ya ƙara janyo masa baƙin jini a wurin ƴan'uwansa musamman Yarima Adam.
kuma auren nasa babu jimawa shima Yarima Adam É—in ya bijiro da nasa inda ya kawo Æ´ar gidan gomnan garin gombe a matsayin wacce zai aura, bayan zugo shi da Jakadan Sarki yayi akan cewar muddin yana son kujerar mahaifinsa to yayi aure tun mahaifinsa na raye, idan kuwa ba haka ba wannan burin mulkin nasa da saurautar zasu ta shi a tutar babu ne, dan zai kasance abu me wahala a ba shi saurauta alhalin baida iyali.

shi kuwa a sanda Jakada ke ba shi wannan shawarar ji yake da zai iya kashe Lateef ba tare da kowa ya sa ni ba da babu abunda zai hana shi, to tsoronsa ɗaya ne, ya riga ya sa ni abu ne me sauƙi Mai Martaba yasa shima a kashe shi ko kuma ya kashe shi da hannunsa.
dan Mai Martaba kan mance da kowa da komai akan Yarima Lateef, kuma yasha tarasu ya faÉ—a musu cewar zai iya yin komai akan Lateef.

kuma bayan rasuwar Sarki Hashim Bukar anyi tata ɓurza wajen naɗa magajinsa, don har sai da ta kai ta kawo duka Yaran sun fito da abunda yake zuciyoyinsu ƙiriƙiri, rigima ta ɓarkewa junansu kowa na ganin ya cancanci a basa wannan sarautar. majaifiyarsu Sarauniya Falmata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa akan babban yaƙin dake shirin ɓarkewa, Lateef shi ɗaya ne me ƙoƙarin ganin ya kwantar mata da hankali domin har sai da ta kai ga ya ɗauketa daga ƙasar ya fitar da ita da matarsa me jaririn yaro a lokacin, saboda komai zai iya faruwa hatta ga rasa rayuka kuwa.
Chapter 22 · 0% Book details