← Book details Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 176

Sashe 64

Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya ɗaga shoulders ɗinsa yace,"and so?, hannun matar fa da zan aura na riƙe shi kuma munafiki ina ruwansa?...kinga bar batun ma na sakar miki hannu dan ba zan iya ba, watanni bakwai ɗin dana ɗauka bana tare dake Allah ɗaya yasan baƙar wuyar dana sha, dube ni fa kiga yanda duk na fige na lalace, duk wanda ya ganni ya ga wanda yay jinya ba ƙarama ba, cin abinci da ƙyar bacci kuma sai ɓarawo. but you". ya faɗa yana sa ɗayan hannunsa ya ɗago fuskarta,"hankalinki kwance har da wani kumatu kinyi, kinyi haske abinki alamun baki da wata matsala balle damuwa. lallai yau na yarda ni ɗaya nake kiɗa da rawata, Allah sarki ni Amir ashe son maso wani nake yi".

Fillo ta kauda fuska gefe tace,"ai kaima kasan abinda kayi min baka kyauta ba, da farko na rame sosai saboda jin ciwon abinda kayi min, amma da na cireka daga raina gaba É—aya sai na sami salama, in yi baccina hankali kwance ba tunaninka balle na damu. kuma ni ka sakeni kar wani ya ganmu, this is not a privacy place".

Amir ya ware idonsa sosai akanta yana kallonta da mamaki yace,"Halimatuna am i hearing well?, english fa naji kina yi".
ta juya ƙwayar idonta tace,"da ka barni ai ba wulaƙanta nayi ba, yanzu haka lesson teacher na bai jima da tafiya ba".
mood ɗin Amir ya sauya, yana niyyar fizgota jikinsa ta cije tana ƙwacewa daga hannunsa har sai daya saketa.

ta bisa da kallon sauyawar mood ɗinsa tace,"lafiya?". without looking at her yace,"please and please, i beg you for the sake of Allah, let by gone be by gone. bana son tuna baya, karki ƙara cewa na tafi na barki, if not kuma Allah zan miki tafiya me gaba ɗaya, dan zanje na tunkuri mota gaba da gaba tabi ta kaina".

tayi far da ido tana haɗe hannayenta a ƙirjinta tace,"tom ba zan ƙara ba insha'Allah. am sorry, ina Innah?".
ya ɗan kalleta yay mata harar wasa, harar da tasa Fillo ƙyalƙyalewa da dariya sosai wanda duka haƙoranta na gaba sai da suka bayyana.

cikin nishaɗin da take jin kanta aciki tace,"ɗan ƙara yi na gani". fuskarsa na washewa da dariya ya kai yatsansa zai ɗalli fuskarta tayi saurin kauda fuska still tana dariya.

Amir yay ƙwafa yace,"zaki bayani, nima sai na rama kukan da kika sa na dinƙa yiwa Innah". ya sauke numfashi yace,"Innah na gaida ki, ƙila gobe tazo ko jibi, zasu zo da kayan sa ranarki. Halimatu nan da next 2months nake so na mallakeki matsayin matata. na sami aiki a wata makaranta yanzu haka ni ne Director a school en, last month ma na saya wancan machine ɗin da kike gani".

tace,"wow congratulations". yanda ta faÉ—a kace wata baturiyar gaske, kawai sai ya waigo yana kallonta da burgewa da sha'awa. yace,"Halimatu yanda kike da kyau da burgewa haka komai naki yake, kinji ko in kika yi english kamar a bakinki aka yisa, ina irin americans É—in nan na cikin tv masu news?, wallah fa kamar haka, taya hakan ya kasance?".

ta basa labarin komai tare da cewan,"kuma Adda Zaytuna da Maama ma totally bama hausa da su yanzu, wurin da nayi mistake zasu gyara min".
Amir yace,"masha'Allah, Allah sakama mutanen gidan nan da alkhairi, but".

tace,"but what?". ta tambayesa ƙwayar idonsa na shaida mata kishin dake ransa, tai murmushi tace,"teacher ɗin ma fa inyamuri ne, duk ya zama jagwal, shi ko kallo ma bai da shi".

ya lakuce mata kumatu yace,"time É—in da zai kalle ki ai ba sani zaki yi ba. gwarama muyi auren ni naci gaba da koya miki".
ta ware ido,"Maama ai tace zan zana waec na wuce UNI".
ya fincikota gabansa yace,"UNI É—in da zaki je ta wuce gidana".

sai da suka kusa 1hour tsaye a wajen suna hira kafin hankalin Fillo ya dawo jikinta, don gaba É—aya Amir yayi amfani da salon soyayyarsa ya kawar da duk wani fushi da take yi akansa, kuma ita kanta bata san sanda salon soyayyar ya É—ebeta ba ta manta da komai, har ta sake da shi suka koma kamar ba suyi faÉ—a ba.

tana leƙen agogon hannunsa tace,"Amir time, tausa fa nake ma Boɗejo na taso. kuma haka nace yanzu zaka tafi, ni duk naji ma ina jin kunya dan wannan tsohuwar sai ta ɓaro ni".

yay murmushi me sanyi yace,"shikenan ki koma ciki, amma zan dawo da daddare bayan kin koma aiki, ban gaji da ganinki ba gaskiya".

su kai sallama zai tafi yace,"i love you so much Halee". tace,"thank you, bye bye. ka gaida Inna". ta faÉ—a tana juyawa don barin wajen.

ai da sauri ya riƙo hannunta ya koma gabanta yana faɗin,"Allah sai kin faɗa".
ta shagwaɓe fuska tana cewa,"zan faɗa but not now, not 2day". yace,"ai kinji na rantse". sai da ta kulle idonta tukunna ta iya cewa,"i love you too". ta faɗa Amir na jin wani mugun daɗi acikin ransa, ya kama hancinta ya ɗan ja sannan ya saki hannunta asking her me take so ya taho mata da shi anjima, tace duk abinda yaga ya dace da ita.

ya juya ya tafi yana É—aga mata hannu, itama cike da kunya take É—aga nata.
sai da ya hau machine É—insa ya tafi sannan ta nufi gate.

daga Amir har Fillo cikinsu babu wanda ya lura da motar da tai parking daga can gefensu, tun fara hirarsu ba jimawa, haka yanzu ma da ta zo shiga gidan bata kula da motar ba, so tana zira ƙafarta cikin gate taji an mugun danna horn kamar za'a tashi duniya, ta juyo a tsorace tana kallon bayanta.
ba tare da gama tantance motar waye ba ƙarar horn ya kuma shiga kunnenta tana jin kamar dodon kunnen zai mutu.

ta ɗan yatsine fuska tana shigewarta tunda ba huruminta bane na me gadi ne, bata taɓa ganin kalar motar ba acikin gidan balle tace ta gidan ce.
ta shige da saurinta, kiciɓis suka yi da mai gadi ya fito daga banɗaki riƙe da buta a hannunsa sai sauri yake yi. yace,"ƴar nan Allah sa ba Alhaji bane".

Fillo tace,"wallah ban sani ba Baba, amma motan kamar bana gidan ba, ban dai sani ba". Me gadi ya fice da sauri, ganin ba motar gidan bace yasa shi ƙarasawa don ganin waye.

Turaki ya gani aciki fuskarsa kamar an aiko masa mutuwa, ya tabbatar da AC kunne a motan amma yana ganin yacca zufa ta tsatstsafo a goshinsa.
Me gadi ya rissina yana faɗin,"ranka ya daɗe ashe kaina, kayi haƙuri na shiga banɗaki ne. motar kuma ban shaida ta waye ba shisa, bari inje in buɗe".

da ƙyar Turaki ya iya buɗe baki saboda yacca yake jin kansa kamar zai fashe yace,"ba gate zaka buɗe ba, yarinyar da ta shiga yanzu zaka kira, da sauri".
cikin sauri me gadi ya koma, lokacin Fillo na dab da entrance na side ɗin Boɗejo taji me gadi na ƙwala mata jira.

"ki zo da sauri yallaɓai ne ke kira". ita da yace yallaɓai sai tayi zaton ko Baffa yake nufi. don haka ta ɗago ƙafa tana cewa,"tom". shi kuma yana ƙara cewa,"yace kije da sauri". Fillo ta ƙara saurin tafiyarta har tana jin kaman za tayi tuntuɓe.

tunda ta fito jajayen idon Turaki ke kanta har ta ƙaraso ta ɗayan glass ɗin, ya sauke glass ɗin ba tare da ya waiga ya kalli ko da inuwarta ba.
dan a yacca zuciyarsa ke tafarfasa zai iya shaƙota ya shigo da ita ta cikin glass ɗin.

Fillo ganinsa yasa gaba ɗaya ta tsure, da ƙyar ta tattaro yawun bakinta tace,"gani".
ta faÉ—a kamar me koyon magana, bala'in tsoro na kamata saboda yanayinsa da ta gani, ita ko babu yanayinsa ma tana jin tsoronsa.

"buÉ—e ki shigo". haka taji amon muryarsa tamkar saukar aradu aka.
zata tsaya tunanin maganar tasa taga ya juyo a fusace ya zuba mata rikitattun idanuwansa da suka koma kamar na tiger.

babu shiri ta nufi ƙofar baya zata buɗe a tsawace taji yace,"kika shiga nan babu abinda zai hanani ɓalla ƙasusuwanki na zubar a wajenan".

take ruwan hawaye ya sakko mata ta dawo tana buÉ—e gaba ta shiga da tsananin ruÉ—ewa, duk ta firgice ta gigice.
ta rufo ƙofar motar tana kifa kai akan cinyarta ta fashe da kuka. Turaki ya dinƙa kallonta babu ko ƙifta ido, a hankali kuma ya mayar da ƙwayar idonsa kan hannun hagunta da Amir ya riƙe for morethan 2tyms, yaji zuciyarsa ta ƙara tamkewa, trying his best to be very calm gudun kar ya illata ƴar mutane, ya damƙo tsintsiyar hannunta dake rawa yana mata mugun riƙo kamar zai karya ƙashin wajen.

ta ɗago da kanta a gigice tana kallonsa da tsananin jin zafin riƙon. cikin muryar kuka tace,"me nayi maka?". tambayartata yaji kamar ya tsinka mata marin da zai yi sanadiyar ɗaukewar jinta da ganinta gaba ɗaya, wataƙila hakan yasa tasan laifinta.

acikin rishin kukan da take yi tace,"jiya fa kace ka haƙura, amma tunda baka haƙura ba i will give you half of the money now, ending month sai na cika maka sauran".

shi dai kallonta kawai yake yi yana tunani iri iri cikin ransa, tana batun ta basa 25k now, aina ta samu 25k?, wanda ya tafi ne ya bata?, me tayi masa ya bata?. sai ya rumtse ido gam yana ƙara damƙe hannun da mugun ƙarfin da yafi na ɗazu har sai da ƙashinta yayi ƙara, idan ce masa akayi an ganta da wani ba zai taɓa yarda ba don ba tayi kama da wadda zata tsaya da namiji ba, amma with his own 2eyes ya ganta tsaye da namiji a inda babu kowa sai su kaɗai, ƙofar gidan da babu masu wucewa, sama da rabin awa suna hira cikin nishaɗi har tana wage masa all her 32teeths.

which kind of purnishment did he supposed to give her?, shin ya ɗimautata da sanar da ita cewar akwai igiyoyin auren wani akanta guda uku reras?, ko kuma yayi mata abinda ba zata ƙara kallon wani namiji ba a rayuwarta?, balle harta bari ya riƙe mata hannu har tai masa dariya har ta barsa yaja hancinta.
Chapter 64 · 0% Book details