Sashe 1
Lullubin Biri Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[8/5, 18:59] Halimahz: *LULLUÆIN BIRI*
*©ï¸Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Na fara da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW._
*1*
*APRIL 20th 2021.*
*American Hospital Dubai, 2:30pm.*
_"hey don't move, we are us navy seals...God! Damn it...we have a tango in the north wing every week. stop! stop! stop!...great team work guys, yeah we will mark you for the assist on this one."_
sautin da ke fitowa kenan daga cikin ƙatuwar plasma ɗin da ke manne a bangon ofishin, cikin wani american film me suna Steel Brigade. dai-dai lokacin da sojojin suka kama mutumin da ke sanye da mask, dai-dai lokacin Yusuf da ke juyi akan kujerarsa yasa tafukan hannunsa duka biyu ya shafo fuskarsa tare da fitar da iska daga bakinsa. "ohh dammm it".
"ai na faɗa maka sai sun kama shi". Kalid wanda har yanzu bai ɗauke idonsa daga kallon tv ɗin ba ya faɗa a sa'ilin da duka haƙoran gabansa ke bayyana a waje alamar yayi farin ciki da abinda ya faru.
Yusuf ya ƙara juyawa akan kujerarsa zuwa gefe guda sannan yay guntun tsaki yace,"ko waye producer ɗin nan sam bai iya tsara film ba".
"hhh to ai hakan shine dai-dai, kai kana kallon sojojin nan kasan bana banza ba ne...kuma gwara a kama shi tun a farko, wasan zai fi tafiya dai-dai".
"kuma wataƙila ya suɓuce masu ba".
"ta ya ya?, macece fa ai da kamar wuya ta iya ƙwacewa".
"wannan ai ba mace ba ce".
"bari su buÉ—e fuskar zaka gani, ai yanayin gudun kaÉ—ai zaka fahimci macece, itama ba me kamar maza ba".
shirun Kalid É—in ya haÉ—e da sanda sautin maganar film É—in ta ci gaba da tafiya, nan sukai shiru suna ci gaba da kallon.
_"get the mask!!...there is no harmful in the air we already checked, expect for the thorpe's breath."_ ɗaya cikin sojojin yay maganar a tsawace inda a take ya fizge mask ɗin daga fuskar mutumin, kuma lokaci ɗaya zaton Khalid ya bayyana, hakan kuma ya wanzar da dariya a fuskarsa, nan ya juyo ya kalli Yusuf dake aikin jan gajeran tsaki babu ƙaƙƙautawa alamun ba hakan yaso ba.
lokacin da Yusuf ya buɗi baki zai yi magana lokacin ƙofar ofishin tayi ƙara, aka turota a hankali inda wata matashiyar budurwa ta bayyana hannunta riƙe da wasu takardu, jikinta kuma sanye da unifom na ma'aikatan jinya. ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin ofishin tana ƙarasawa gaban tebirin da Yusuf ke zaune kan kujera yana juyawa gefe zuwa gefe a hankali.
cike da girmamawa ta rissinar da kanta tare da aje fayel É—in hannunta akan teburin tana tura su zuwa gaban Yusuf. "Ranka ya daÉ—e ga result É—in da aka samu". ta faÉ—a sanda ta ke harÉ—e hannayenta zuwa baya.
"ta farka ne?". Yusuf É—in ya tambaya a sa'ilin da ya buÉ—e fayel É—in yana dubawa.
"ehh ranka ya daɗe ta farka wajen ƙarfe ɗaya da minti goma sha biyu, amma bata fi sakan huɗu ba ta koma, da alamu dai har yanzu da saura kamin ta dawo hayyacinta".
shiru ya biyo bayan maganarta, idon Yusuf ta cikin farin gilishin da ya manna na bin rubutun da ke cikin fayel ɗin, karantarsu yake da fahimta, wucewar daƙiƙa 1,2 Yusuf ya ɗago kansa akan fayel ɗin, ya kai hannu ya shafo goshinsa sannan ya jinginar da kansa jikin kujera yana mai sauke gajeran numfashi.
_"huuuuhh"._ hucin iska ta fita daga bakinsa. *"EXOGENOUS DEPRESSION".* ya faÉ—a cikin amon sauti na tausayawa haÉ—e da kulle murfin idonsa. furucin nasa kuma yasa Kalid maido da kallonsa gare shi.
"tana cikin matakin biopolar kenan?".
Yusuf ya jijjiga kansa tabbacin hakan ba tare da ya ce komai ba, na tsawon wasu sakanni ya ɗaga ido ya kalli Nurse ɗin yace,"kuma iyaka binciken da jami'an tsaro suka yi babu wani danginta a ƙasar nan?".
"ƙwarai ranka ya daɗe sun bada tabbacin hakan...ni kaina lamarinta na ɗaure min kai".
Kalid yace,"gaskiya da sake a wannan lamarin, su ƙara bincike domin idan ba zaman ƙasar nan take ba to wa ya kawota ya ajiyeta kuma ya tafi ya barta cikin wannan mawuyacin yanayin?".
Yusuf ya ƙara fitar da iska daga bakinsa kamin yace da nurse din,"Ƙarƙashin kulawar wa ta ke?".
"Ranka ya daɗe tana ƙarƙashin kulawar Dr Nameer, sai dai gaskiya tana fuskantar matsala".
"wanne irin matsala?".
"Dr Nameer yana da zafi, so kuma shi yace muddin babu wani nata ba zai bata wani kulawan da ya dace ba...infact yanzu ma yaƙi rubuta alluran da suka kamata ayi mata saboda wai ko ya rubuta bata da me saya mata".
karo na babu adadi Yusuf ya ƙara girgiza kansa tausayi fal ransa, sannan ya ɗauki ƙaramar takarda yay signing a jiki ya miƙa mata tare da fayel ɗin.
"kije Pharmacy Sumayya, ayi dukkan abinda ya dace akan matar nan, zan saka maki kuɗi a account, dan Allah ki kula da ita ni kuma nayi miki alƙawarin biyanki da kauri".
ta rissina ta É—auki fayel É—in tana yi mishi godiya sannan tayi musu sallama ta fice daga ofishin.
bayan fitarta da wucewar minti uku Yusuf ya miƙe yana kafa hular zanna bukar a gashin kansa, fuskarsa na bayyana ainihin damuwar da ke cikin ransa.
"tashi mu tafi Kalid".
"a'a ba kana da sauran aiki ba?".
"ba zan iya komai ba Kalid, kaina ciwo yake. zan yiwa Dr Yusrah magana".
Kalid ya miƙe tsaye shima, suka nufi ƙofa yana cewa da Yusuf. "Dr ka rage saka damuwar wani a ranka...". kuma bai ƙarasa maganar ba Yusuf ya tari nunfashinsa da cewa.
"Kalid idan har matar nan tana da miji a raye to ya cika azzalumi, idan ma yana raye ne ko ya mutu to tabbas Æ´aÆ´anta salwantattu ne, basa neman albarka kwata-kwata, basu san darajar uwa ba, domin ko kaffara ba zanyi maka ba ta dalilinsu ta shiga wannan bala'in rayuwar, kuma duk san da nayi tozali da wani É—a nata sai nayi shari'a da shi". maganar yake cikin zafin rai kamar zai kaiwa bango duka.
"tabbas ba zai wuce takaicin miji ko na Æ´aÆ´anta ne ya zama silar wannan ciwon nata ba...amma ni abun mamakin ace tana cikin wannan mawuyacin halin kuma babu kowa nata a tare da ita".
Kalid yay maganar a sanda suke sauka daga kan steps su na ƙarasowa cikin reception kamin su sa kai su fita gaba ɗaya daga asibitin. kuma har suka isa bakin mota cikinsu babu wanda ya sake magana.
on their way to hotel wayar Yusuf tayi ƙara, ya kai hannu ya cirota daga aljuhunsa, ya ɗaga vedio call ɗin da ya shigo yana mai raba hankalinsa gida biyu, ɗaya ga tuƙin da yake, ɗaya kuma ga fuskar matarsa da ta bayyana a cikin wayar.
"You Excellency what am i seeing on your face?, whats wrong?, are you oak?, wani abu ya faru ne?, what is the problem?". tarin tambayoyin da suka fito daga bakin Nuratu kenan zuwa ga mijinta, cikin kiÉ—ima da bayyanuwar tashin hankali na farat É—aya, dalilin damuwar da ta gani a tare da shi ta haddasa ma ta ruÉ—ewa na neman fitar hayyaci.
kallo ɗaya na yanayin da take ciki zaka yi kasan macece mai tsananin so da ƙaunar mijinta, gami da tausayinsa, wanda bata so ko da ƙuda ɗaya ya taɓa mata shi, kan kace kwabo hawaye sun fara reto akan kuncinta, cikin ƙanƙanen lokaci kuma ta fashe da kuka, kukan da ya haddasa wani duka a ƙirjin Yusuf.
"Sweety". sai a yanzu laɓɓansa suka buɗe da kiran sunanta, ta ɗago kanta da ta duƙar tana kuka ta zuba idonta cikin nasa. sai kawai ya sakar ma ta wani kyakykyawan murmushi, irin murmushin nan da zai tsayar da kukan nata. amma me? kamar yanda ya riga ya sani ba zata yi shirun ba, hasalima kamar ya ƙara tunzurata ne, dan kawai ɗora hannu tayi akan fuskar ta ƙara fashewa da kuka, kuka sosai kamar ƙaramin yaro me neman shan nono, sautin muryarta na fita cikin kuka na shagwaɓa da damuwa take ƙara cewa.
"ni ba irin wannan ba, bana son wannan ka jefar da shi. indai murmushin ƙarfin hali ne a tare da kai your Excellency bana ƙaunarsa, kuma ba shi zai sa na sami sassaucin raɗaɗin damuwar da na riska a tare da kai ba".
tuƙin yake amma gaba ɗaya attension ɗinsa ya koma gareta, kyawawan idanuwanta na kan wuyansa tana bin wani dunƙulallan abu da ke wucewa ta maƙogoronsa, muryarta ta ƙara narkewa tana cewa.
"please tell me what is the problem?, Did you do something that you did not succeed on it?".
ta riga ta san waye mijinta, yawancin damuwarsa na ta'allaƙa ne akan rashin cimma nasararsa akan abu musamman ma ta ɓangaren aikinsa, amma da mamakinta sai taji yace,"keep calm Sweety". voice ɗinsa ya fito very cool.
sai ta gwaɓe kamar ƙaramar yarinya tana cewa da shi. "to ni dai ka dawo gida idan Allah ya kaimu gobe. ka bar komai da kake yi ka dawo, otherwise i will keep on crying".
"Sweety isn't a big deal faa, please don't bother your self kinji".
"ni ban yarda da kai ba".
sai kawai ya tsarate da wani kallo da ya sa ta saki wani murmushi da ya fito da annurin fuskarta, sannan kamar sai a yanzu ne ma ya lura da irin shigar da ke jikinta wanda yasan ta kira ne dan ta nuna masa, dan haka ya kanne mata ido guda ita kuma sai ta cije gefen leɓenta kaɗan.
gaba ɗayansu sai murmushinsu mai ƙarfin sauti ya fito a tare. wucewar daƙiƙa 2 su na aikawa junansu saƙo ta irin kallon da suke ma juna kamin Nuratu ta ɗan cukule fuska tace da shi.
"this time around idan ka dawo sai nayi shari'a da Kalid".
yanda tayi maganar da gaskiyarta yasa shi yin murmushin da ya bayyanar da haƙoransa, Kalid da ke gefe yana charting ya saki dariya yana faɗin. "yi haƙuri Madam tuba nake".
"i will not accept your apology tunda kai dai har yanzu ka kasa koyon yanda zaka kula da amanar da aka baka".
"wani abu ya faru ranki ya daɗe?". ya tambayeta cike da zolaya da kuma son ƙara kunnata.