← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 163

Sashe 99

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tura 'kofar Ummah tayi ta ri'ke ahannunta batare da ta 'karasa ciki ba ganin kowa na sabganshi a'dakin tamkar sun manta da batun fitan da zasuyin gashi har yamma ta kawo kai basu tafi ba.

Sukuwa 'karan bu'de 'kofan ne yasa dukkansu hankalinsu ya kai gurin 'kofar afirgice domin basuyi zaton mutun ba sai suka ga ashe Ummah ce
Cewa tayi
" _har kunje kun dawo ne_ ?

Hannah ce tayi saurin bata amsa da fa'din " _ba Yayah ya hana mu ba, wai sai gobe zamu_ "

Murmushi Ummah tayi cikin nuna halin ko'in kula tace " _toh Allah_ _ya kaimu goben_ "!

Zaburowa Hannah tayi tace " _haba Ummah kema haka zaki ce kuma?_

" _Toh me kike so in ce Hannah bayan lokacin daya hana ku fitan baku zo kun sameni ba, yanzu da lokaci ya 'kure kuma me zance in banda Allah ya kaimu goben_ "!

Kwafa Hannah tayi tace
" _Allah Yayah yaban haushi Ummah, kuma fah shi ya ri'ke Teemah da aiki har sai da yaga_ _lokaci ya 'kure tukunna_ "

Teemah kam ko 'kala bata ce ba dan kwata-kwata ma bata san me zata furta ba ita.

'Karasowa ciki Ummah tayi ta zauna akan stool 'din dressing mirror sannan ta dubesu tace.
" _kuyi ha'kuri ai inda rai gaben ma kamar yau ne karku damu kunji?_

Kallonta ta mayar kan Teemah tace
_Fateemah kiyi ha'kuri kinji halin Yayan naku ne_ _sai a hankali_ "

Murmushi Teemah tayi itama ta sunkuyar da kai 'kasa yanzun bata jin yin magana ne.

*****
Washe gari kuwa dawuri suka gama shirin su tun 11am, saboda su samu su sake sosai sun gama tsara cewa yau 'din sai sun sha yawo sosai kafin su dawo duk da suna tsammanin ayau 'din bazasu fasa ba.

Hannah ce ma data tsaya waya da Bilal ita ce ta 'dan 6ata musu lokaci, dan Bilal baya 'kasar shi kuma ba ko da yaushe suke samun damar yin waya ba sai lokaci zuwa lokaci saboda abubuwan dake gabansa hakan yasa duk lokacin da ya 'kirata hirarsu bata yankewa da wuri, Teemah haushi kamar ta 'kwace wayar ta jefar ganin har kwalliyarsu na shirin dusashewa amma basu fita ba, musamman idan taji yanda Hannah ke 'ko'karin lan'kwashe muryarta idan tana waya da Bilal 'din sai haushin Hannah ma ya 'kara kamata tace ai duk da laifinta ma tunda take biyeshi gashi sai 6ata musu lokaci yake abanza.

Ba ita ta 'kare wayar ba sai 11:28am wanda tana cire wayar akunnanta Teemah taja tsaki tare da banka mata harara.

Hannah murmushi tayi tace mata " _ya haka ne 'yan mata, let me be please ko dan ke baki san so ba ko? yes na_ _tabbata hakane, shiyasa ma naga kike wani banka_ _min harara..._ "

Dakatar da ita Teemah tayi cikin jin haushi da fa'din " _ban san so ba kika_ _ce_ ?
_Karki manta fah har aure nayi kinga kuwa 'karshen sanin so kenan ko_ "

Dariya ka'dan Hannah tayi idanunta akan wayarta tace
" _wancan ai is different, aure kikayi amma ba soyayya ba, na tabbata duk ranar da soyayya ta kamaki zaki gane cewa nawa wasa ne, wancen auren kin ai bashi da bambanci da babu,_
_ehh toh kuma, bansani ba kam ko kafin ya rasu ya koya miki soyayyar shi, kuma fah ba mamaki dan yanda naga kika_ _rin'ka kuka kina damuwa da rashin san nan ze yiwu son mijin naki ke damunki......._

Mi'kewa tsaye Teemah tayi tace
" _Ya isa dan Allah Hannah kitashi mutafi ni surutun ya ishe ni haka_ "
Tayi maganar tana 'ko'karin 'daukar mayafinta.

Ganin ko motsi Hannah batayi ba yasa Teemah taja tsaki ka'dan tace " _Haba dan Allah kina gani ko Hannah lokaci na tafiya salan Yayah ya sake hanamu fita ko me_ ?

Tana gama fadin haka ta nufi gaban mirror tasake duba jikinta ganin batada matsala yasa ta dauki turare kawai tasake feshe jikinta dashi.

Sai lokacin Hannah kuma ta ajiye wayar tata
ta sau'ka a agadon tana dariya tare da fa'din " _da kin barni na fa'di gaskiya ai yarinya_ "

Juyawa Teemah tayi tace
" _Ni dai muje dan_ _Allah, inkin gama ki sameni wajen Ummah._ "
Teemah ta fa'di tare da barin 'dakin gaba daya.

Hannah kam Teemah na fita ta janyo wayarta tacigaba da chat 'din da takeyi da Bilal.

Tana isa parloun ta hango Ummah zaune akan kujera nesa ka'dan da kujerar dake gefenta kuma Yayah Abbas ne zaune suna 'dan hira.

Kallo 'daya Teemah tayi masa sai ta 'dauke kanta, sanye yake cikin black trouser da wata longslip ash colour me zanen ba'ki layi-layi ajiki, sosai kayan sukayi masa kyau suka kar6eshi.

Kirjinta taji yana bugawa wanda hakan yayi sanadin rage mata speed 'din tafiyarta, ahankali ta 'karaso har inda suke 'din ta zauna gefen Ummah, sai da ta iso ma sannan taji mahaukacin 'kamshin turarensa mai da'di ya bigi hancinta, daya ha'du da nata 'kamshin kuwa sai ya riki'de ya bada wani 'kamshi me 'kayatarwa, Ummah ce ka'dai zatayi iya bayyana hakan saboda ita ce atsakaninsu.

Abbas kam yi yayi kamar be ganta ba, amma Allah ne ka'dai yasan yanda zuciyarsa ta yaba da yarinyar, sosai yaga zallan kyaun ta ayau 'din dan purple atamfar data saka ba 'karamin fito da ita yayi ba.

" _Har kun gama_ _shiryawa ne_ ?
Ummah ta tambayeta bayan ta maida dukkan hankalinta zuwa ga Teemah.

Kai Teemah ta 'daga mata alamar " _ehh_ "
Kasancewar sun gaisa da Ummahn dasafe Abbas ne kawai basu gaisa ba dan shi ba'a zuwa 'dakinsa haka kawai dan gaisuwa idan ba shine yanemi mutun ba toh sai de inya fito ka gaisheshi, hakan yasa ta 'dan 'dago kanta ka'dan tace
" _ina kwana Yayah_ !

Be amsa ba sai da ya 'dago shima ya kalleta kafin ya amsa da fa'din " _lafiya 'kalau_ ."

Bata 'kara wata gaisuwar ba dan tasan ko tayi ma ba sake amsata zaiyi ba.

Abbas kam yanzu kasa 'dauke idanunsa yayi akanta Allah ma sai ya taimakeshi Ummah ba shi take kallo ba hankalinta nakan Teemah ne, Teemahn kuwa kanta na kasa shiyasa ma yasamu chance 'din kare mata kallo hankalinsa kwance.

" _Dan Allah Fateemah inkun je_ _karki biyewa Hannah kinji, nasanta iyayi gareta gashi inta fita shopping tana da'dewa kafin ta dawo kamar zata na'do komai pls_ _karki biyeta Fateemah ku dawo_ _da wuri kinji Antynki ma tana hanya yau zata zo_ ?
Ummah ce tayi maganar cikin sigar lallami.

Kai Teemah ta 'daga mata alamar " _toh_ " Tana murmushi dajin cewa Anty na hanya sai de gaba 'daya jitake ta takura da zaman, hakan yasata lafewa ajikin Ummah kamar wata 'yar yarinya 'karama.

Muryar Abbas suka jiyo yana fa'din " _wai Ummah ina zasu ne ba fah na son yawon nan ni_ "

'Dagowa Teemah tayi da mamaki ta kalleshi suna ha'da idanu kuwa sai ta kauda kanta gefe tare da turo baki aranta tace _lallai ma Yayan nan, bacin shine jiya ya hanamu fita yace sai yau kuma da_ _yau 'din tayi sai_ _yawani ce be san da_ _zancen ba_ .

Ummah tariga tasan halinsa na nuna ko'in kula akan abubuwa shiyasa ma bata meda zancen baya ba duk da tasan yasan da batun fitan amma sai kawai tace masa " _Shopping zasu je ko_ _zaka kaimin_ _su_ "

" _Ni kuma Ummah? Inada inda zani fah_ "

" _Nasani ai Abbas naga akn hanya shiyasa_ " ummah ce ta fa'di hakan tana kallonsa.

Yana so yace ina driver amma sai yaji bakinsa yayi masa nawi, kawai sai ya koma baya ya ha'da jikinsa da jikin kujera yayi wa Ummahn shiru, minti 'daya be cika ba sai ga Hannah ta fito cikin 'dan sauri-sauri ta nufo su.

Sai da ta gaida Yayan kafin tace da Teemah su tafi.

Dayake alraedy Ummah ta sallame su inda ta tura ma Hannah ku'din shopping 'din a account bata basu cash ba.

Tashi Teemah tayi suka yiwa Ummah sallama ,
Ummah nata yi musu addu'ar Allah ya bada sa'a suka amsa da (Ameen) kafin suka nufi 'kofar fita.

Abbas ma tashi yayi ya bi bayansu yana wannan 'kasaitacciyar tafiyar nan tasa me birgewa.

Ahanya yazo ya wuche su Teemah nayi mata gulmar wai shi ai zai kaisu.

Haushin ha'da su da Ummah tayi Hannah taji dan tasan ba barinsu zaiyi su sake ba.

Koda suka isa jikin motar ma Hannah 'kin shiga gaba tayi dan har yanzu basu gama da Bilal ba chat sukeyi dashi shiyasa ma bata son shiga gaban don tsoro takeji kar Abbas ya kamata.

Muhawara suka tsaya yi dan Teemah ma 'kin shiga gaba tayi sai da ya daka musu tsawa kafin kowa tayi saurin bu'dewa tashiga.

Koda ya kai sun kuwa 'kin barin su yayi sai da yaga sun gama yabiya ku'din kafin yasako su agaba suka dawo gida.

Shopping sosai sukayi dan suna da ishashshen ku'di a account 'din Hannah shiyasa ma suka saki ransu suka jidi tarkace harda na banza, cikin sa'a kuwa sai Abbas ma ya biya bill 'din.

Koda suka isa gida kowa 'diban kayan yayi, Hannah ce tafara 'diba ta wuche ciki, koda Teemah ta 'diba ta fara tafiya kuwa kasawa tayi sai da ta ajiye dan wanda Hannah ta bar mata sunfi yawa.

Numfashi take sau'kewa ahankali tana watsa hannu ga dukkan alamu zafi suke mata.

Tana 'ko'karin sake 'dauka ta tsinkayo muryarsa yana fa'din " _idan bazaki iya ba dole sai kin 'dauka duka lokaci 'daya ne_ ?

Sai lokacin ma tunanin hakan yazo mata dan haka sai ta raba kayan ta 'dauki ka'dan ta nufi ciki inda ta bar sauran awurin akan inta dawo ta 'karasa 'dauka.

Tana cikin tafiya taga yazo ya wuche ta hannunsa da ragowar kayan, bin bayansa tayi sai ya kasance kusan tare tafiyar tasu take.

Yana shiga parloun kuwa itama ta 6ullo sai ya kasance atare suka shigo.

Anty na saitin 'kofa ne dan haka ita tafara ganinsu take kuwa taga dacewar kasancewarsu a inuwa 'daya, zata so Fateemahn tasamu jajirtaccen namiji irin Abbas wanda zai kula da rayuwarta ba kamar yanda ta so cin zarafinta abaya ba.
Chapter 99 · 0% Book details