← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 163

Sashe 23

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Teemah taga kamar mummyn nata dagaske take sai tace" Mummy kinsan mugun halin yayan kuwa, nidai kibari Habibu ya kaini dan Allah mummy"!

"Ai na riga da nagama magana nikam Teemah, inba iskanci ba da Abbas d'in da habibun miye banbancinsu wato dan kinga kin raina Habibun shiyasa kike son shi ya kaiki ko?

"a a fah mummy yah Abbas d'in ne ni kawai bana so ya kaini"

"Ai shine dai-dai ke Teemah gara yana yin maganin kin ai inkuwa ba haka sai ki zamanki agida ba lallai ba dole"

Zatayi magana mummy ta dakakar da ita da fad'in idan fah bazaki ba babu dole nace kuma nasan kinjini, ni bazan canja magana ta ba"

Ai tana jin hakan ta mik'e dan bata so tayi missing d'in zuwa wajen.

"Bari inje in shirya toh, ai da babu gara ba dad'i .

"Daya fi miki kam" mummy tace mata.

Daganan ta tashi da gudu ta nufi d'akinta da niyar shiryawa.

Tana shiga ta hau cire kayan da ke jikinta sai data ciresu gaba d'aya kafin ta nemi towel ta d'aura.

Kayan da ta cire d'inma sai ta tattare su ta ninke ta bud'e ma'ajiyar kayan wankinta ta jefa su aciki.

Tana juyowa daga wurin sai taci karo da k'adangare mai jan kai a tsakiyar d'akin. Jikinta take yafara k'yarma tafara rawan baki awurin.

Shi kuwa k'adangaren kansa asama yana wani jijjigawa alamar da warginsa ya taho

Aikuwa sai ya d'an motsa daga inda yakrn sai akayi rashin sa'a inda ya nufa d'in anan Teemah take tsaye.

Wani ihun da Teemah ta saka sai da ya firgita duk ahalin gidan gaba d'aya.

Abbas da shigowansa kenan daga masallacin sallar la'asar yana k'ok'arin shiga d'akinsa sai yajiyo ihun ta.

Fasa shiga d'akin nasa yayi ya dawo ya isa main parlourn gidan,inda shigowansa yayi dai-dai da 6acewar mummy daga parlourn itama bin bayanta yayi shima ya nufi inda yaga tabi, hanyar da zai sada mutun da d'akin Teemah sukayi.

Tana tafiya yana binta abaya batare data sani ba, isowan mummy sai yayi dai-dai da fitowan Teemah daga d'akin nata arikice sai sukayi karo da mummyn takuwa k'ank'ameta jikinta sai rawa yakeyi takasa cewa komai.

Ko fad'an damuwarta ma ta kasayi illah rintse idanunta da tayi da k'arfin gaske.

mummy duk ta shiga damuwa sai tambayarta take ta faman yi amma ko amsa d'aya bata samu ba daga Teemahn ba..

Abbas na isowa sai ya wuce d'akin nata ya shiga, anan yaga k'adangaren shima anan inda Teemah ta ganshi har yanzu bai motsa ba, sai ya tsaya kallonsa da mamakin ta inda ya shigo d'akin.

Har ya fara rarraba idanunsa a d'akin.
Ai kuwa take ya tuna da ranar dayaga windown ta a6ud'e harya mata magana akan tana rufewa.

Tunowa da yayi da hakan yasa ya d'aga kansa ya kallo 6angaren da windown yake, ga mamakinsa sai kuwa ya gansa a bud'en yauma, hatta net d'in ma ta zuge tabarshi a bud'eko miye fa'idar hakan oho.

Zuwa yayi ya bud'e wurin datake ajiye kayanta da niyar d'auko wani abinda zai kama k'adangaren dashi sai kawai ya d'auko wani farin vest d'inta ya je ya d'au k'adangaren dashi .

Ta windown data bud'e d'in ya jefa k'adangaren tare da vest d'in gaba dokin yasan ya tsaji a aiki , sannan yaja ya rurrufe glass da net d'in sannan ya sake labile.

Koda ya fito su mummy basa inda ya barsun sai kawai ya wuche parlourn mummy, anan yatarar dasu dukkansu Teemah tawani shige jikin mummy kamar me shirin komawa cikinta.

Zama yazo yayi shima agefen su sai mummy tajefo masa tambayar" wai miye ad'akin ne Abbas inata tambayar ta tak'i tabani amsa tun d'azu sai rawar jiki takeyi"

Amsa ta yayi atakaice da fad'in
"K'adangare ne mummy"

Baki mummy ta kama sannan tace ikon Allah nikam garin yaya kuma ya shiga har cikin d'akinta?"

Baiyi magana ba illah d'aga idanunsa dayayi ya kalleta sai yaji ta matuk'ar bashi tausayi, musamman yanda yaga duk tayi laushi, idanunta a lumshe yake hakan yasa ya k'are mata kallon da kyau sai dai daya lura ba kayan kirki bane ajikinta sai ya kauda kansa gefe tare da korar shaid'an azuciyarsa.

Tambayar dayake so yamata ne yasa shi adole badan yaso ba ya sake kallonta ahakan " _Fateemah_ " ya k'ira sunanta asanyaye ta bud'e idanunta batare da ta amsa k'iran daya mata d'inba.

Sanin datayi cewa shine yak'iratan yasa ta sauk'e idanunta akansa.

"Ban ta6a cewa ki rufe windown d'akin kinnan ba? ya tambayeta

K'asa tayi da idanunta dan tasan taurin kantane yasa tak'i rufewa ba komai ba.
"Tambayarki nakeyi fah!
Da kyar ta bud'i baki tace "ehh kafad'a yayah"

" Owk ban isa inyi magana kiji bako "
Yafad'a ad'an harzuk'e.

Jin hakan yasata jijjiga kanta alamar "a'a".

Sai yanzun mummy takar6e maganar da fad'in "ai in juninki taurin kai ne kuwa kina tare da wahala wallahi, ashema dagangan kike barin windown kenan kuma har amiki magana amma bazaki ji ba, yanzu toh wa gari ya waya?!

Ran mummy a6ace yau tketa sababi ta inda take shigaa bata nan take sauk'a ba sai da Abbas ya ga kamar ran mummyn k'ara 6aci yake yi kafin ya fara bata hak'uri musamman daya lura akalar fad'an naso ya canja gaba d'aya.

Dan mummy duk tana masifar ne akan rashin bin maganar Abbas d'in data k'iyi ne bawai dan shigar k'adangaren d'akin ba.

Teemah kuwa tun fara fad'an mummy take zubda ruwan hawaye dan tun d'azun batayi kukan komai ba tun faruwar al'amarin sai yanzu sai hawayen yak'i tsayuwa abin sai ya zame mata biyu.

Sosai jikin Abbas yayi sanyi sai yaji ba dad'i,dan kana ganin hawayen zaka san cewa kukan daga zuciyarta yake fitowa.

Tausayinta yakeji na k'aruwa masa a zuciya sosai da sosai kuma saboda hakanne yasa yayi wa mummyn magana akan tayi hak'uri.

Sai da yaga komai yayi normal ne kafin yace Teemahn tatafi tasa kaya ajikinta aikuwa tak'i taje fir sai ma k'ara shigewa jikin mummy data keyi.

Ganin hakan yasa mummyn cewa "aww bazaki partyn bane ko kin fasa"

Sai kawai ta jijjiga kanta " mekenan?
Mummyn tasake tambayarta dan bata fahimci takamammiyar manufar wannan amsar ba wato jijjiga kai d'in da Teemahn tayi.

Sai Teemahn ta bud'i baki tace "zani ban fasa ba mummy "

murmushi mummyn tayi kafin tace " ai kuwa dai sarkin yawo babu fashi da yake fita unguwa neai, sai Teemahn ta sake 6oye fuskarta a jikin mummyn ita nan wai taji kunya.

"Tashi maza kije ki shirya toh inyaso sai yayankin ya kaiki"
Cewar mummy
Sai da Teemah ta tashi ta zauna kafin ta ce " mummy toh kiraka ni ".

Duk wannan dramar Abbas na zaune yana kallonsu fuskarsa tallafe da hannayensa amma baiyi magana ba.

Mummy ce ta kalleshi wannan karon batare data amsa maganar da Teemah tayi mata ba, sai ta dawo da kallonta ga Abbas tace masa " kayi hak'uri dan Allah ka kaita wai zata je birthday partyn k'awarta ne a _Abbah ibrahim_kuma idan na had'ata da Habibu ba dawowa da wuri zatayi ba kasanta da rashin kunya shiyasa na keso kai ka kaita"

"Ai bakomai mummy taje ta shirya d'in sai tazo kawai mu wuce"

" yauwa d'an albarka ai nasan bazaka k'i ba"

Daga nan ta dawo da kallonta ga Teemah sannan tace "tashi muje toh ki shirya"

Tashi tayi tafar tagiyah sai mummy ta biyo bayanta suka wuce d'akin nata da mummy sai da aka kusan isa d'akin kafin taja ta tsaya mummyn ce ta wuce gaba tare da yin tsaki dan tasan manufar yin hakan domin duk cikin salon tsorone irin na Teemah.

Da d'ari-d'ari ta shirya suka fito daga d'akin, mummy naganin ta sa kaya sai tayi hanyar waje itama sai ta kwaso mayafinta da takalminta tabiyo bayan mummy dagudu sai suka fito atare.

Dariya ne wannan karon yaso kwacewa Abbas ganin yanda Teemah take tafiya tana waiwayen bayanta.

Aparlourn tak'arasa shirinta sannan taje d'akin mummynta ta d'auko kayan make up d'in ta tazo ta yi kwalliyar aparlourn sannan suka fito atare da Abbas d'in bayan sunyi sallama da mummy akan cewa sai sun dawo.

Sosai Teemah tayi kyau acikin shigar datayin sai ta zama tamkar tauraruwa mai haskaka zuciyar............(mamuda)lolz😜

Abbas har satan kallonta yakeyi tsabar yanda yaga tayi shar da ita,sai da suka hau titi taga ya nufi Gashua road sai alokacin tace masa " yayah kawuce fah Abbah ibrahim zamu"

Ko kulata baiyi ba yaci gaba da tuk'insa........

_comment and share_ _pls_

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 5:58 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 dukkan masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs.Nagode da_ _irin k'aunar da kuke min da kuma kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai ni da ku mutu ka raba _ 😍

Sister safiyyah Ina tayaki murnar kammala littafinki *(BA JINSUN MU* *BACE*) hak'ik'a wannan littafin ba k'aramar karantar damu yayi ba Allah ubangiji yasaka miki da mafificin Alkhairi ya kuma biyaki....up
up
up❤

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

For those da suke rubuta jamb Allah ubangiji ya baku sa'a yasa daga wannan ba k'ari an wuce kenan.

🅿 *23*

Cikin gari ya wuce da ita shikanshi da farko baisan inda zashiba,sai da yaga ya shigo cikin garin kafin ya yanke shawarar zuwa bayan tasha.

Koda suka isa bayan tashan
guri ya samu yayi parking sannan ya bata umarnin fitowa daga motar.

Kamar bazata fitoba sai kuma taga ya k'ureta da kallo fuskarsa ba alamun walwala sai kawai ta bud'e motar ta fita bakinta kamar zai fad'i k'asa tsabar yanda ta turo shi gaba, dan ita bata san mai yake nufi da hakan ba, inda akace ya kaita daban inda kuma ya kawo ta daban, haushi ne ya sake cikata data tuno irin rok'on data tayi kafin mummy tabarta zuwa birthday party d'in sai gashi kuma wannan mutumin yakama ya yi wani guri da ita.

Tafiya kad'an suka yi sai taga ya shiga cikin wani babban shagon kayan make-up.
Chapter 23 · 0% Book details