Sashe 56
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsawon mintina biyu suna ahakan, motsi Teemah tafara sanadiyyan gajiya da 'kafafunta suka yi dayake lan'kwashe su tayi ta zauna akansu, zogi taji sun fara yi mata take sai ta sake yamutse fuska tare da daidaita su yanda zata 'dan ji dama-dama.
Motsin data yin ne ya'dan ankarar dashi daga zuba mata idanun da yayi, sai da ya 'dauke idanunsa ya kawar gefe kafin daga bisani ya dawo da kallon shi gareta.
" kina jina"
Ya tambayeta.
Sai itama ta bashi amsa daidai da yanayinta a'kasan ma'koshi ta amsa masa da " uumm" tare da 'dagowa a'dan sace ta dube shi.
Bata san meyasa ba amma wani 6angare acikin zuciyarta na kwa'daita mata son kallon fuskar sa yayin da 6angare 'dayan kuma tsoro ya rinjayar shi kuma sai tsoron yafi mata tasiri saboda idanun ya Abbas tsoro sosai suke bata ayau 'din aduk lokacin da yake yanayin da ba dai-dai ba ko ada ma da take masa iskanci son ranta dan be ta6a ritsata bane shiyasa, amma duk da haka de sai da ta 'dan saci kallon san wannan karan dan yadda yayi mata maganar cikin natsuwa sai yasata har ta samu 'kwarin gwiwan 'daga kanta ta kalleshi, idanunsa 'kur akanta ita kuwa bazata iya sar'ke idanuwanta acikin nashi ba dan haka sai tayi gaggawan maida idanuwanta ga tafukan hannunta dake kan cinyarta luguden da zuciyarta ke yi mata ma ka'dai ya isheta.
_" dagaske ne wai aure zakiyi Angel 'din daddy"?_
Muryarsa asanyaye yayi maganar cikin nutsuwa sai kace bashine ya daka mata uban tsawa 'dazu ba, sai ta 'dago da kanta ka'dan itama amma bata kaiga fuskarsa ba sai ta sau'kar da idanun nata akan hannunsa 'daya dake ajiye akan hannun kujera, a irin yanayin da yayi maganar itama sai tace
_" Daddy ne nima ya_ _fa'da min haka"._
_" toh meyasa ni baki 'kirani kin gaya min ba a lokacin"._
Sai tayi saurin bashi amsa da fad'in " _Wallahi Yayah mantawa nayi kayi ha'kuri"._ Ta 'karashe maganar da karkata kanta gefe harma ta daure ta sanya idanunta cikin nashi.
Yanda tayin ba'karamin birgeshi tayi ba sai kawai ya tsaya yana kallonta kamar baze sake magana ba.
Ita kuwa har godiya takewa Allah dayaga yayi shiru yana kallontan, _"Allah kasa ya ha'kura ya barni na tafi"_
duk zaton ta laifin da tayi masa kenan shiyasa yayi maltreating 'dinta 'dazu har tana tunani aranta " ashe dama akan 'dan wannan abin ne, toh ai in de wannan ne harda kai a laifin, kaima ai baka ta6a 'kirana ba, toh ni meyasa zan 'ki......
Tana cikin tunanin taji ya sake fa'din " _kin_ _manta kika_ _ce_ "?
Ga mamakinta wannan karan atsaye yake hannunsa 'daya cikin aljihunsa harma ya juya mata baya kamar me shirin barin 'dakin.
Mamakinta be wuche na har yaushe yabar nan 'din ba batare da tasani ba.
_" Fatima toh dani kika manta ko kuma da 'kirana a waya?_
Yana gama fa'dan hakan ya juyo ya fuskance ta ga dukkan alamu amsar tambayarsa yake bu'kata gamsashshiya daga bakinta.
Ita kuwa rasa abin da zata ce masa yasa tafara in ina domin ta kamamman abinda zata furta wanda bazai zama laifi ba take so dan ta kar ta 'kara yi masa wani tunda tasamu ya sau'ko, kuma sai tarasa, sai da 'kyar tasamu ta furta _" da wayar"_.
Murmushin takaici yayi inda murmushin ya tsaya masa a iya saman la66ansa sannan ya juyo ya dawo kusa da ita kanta ya 'dago zuwaga kallonshi wannan karan kam jitayi zata iya kallon idanunsa tunda taji ya 'dan sau'ko daga masifar da 'daina shayin ha'da ido dashi aikuwa takalleshin idanun su suka 'sarke cikin na juna
_" ki gaya min gaskiya, ke ma kina son auren nan ko?._
Ita kanta bata san lokacin da har kanta ya motsa ta bashi amsa ba saboda wani bug...bug take jin zuciyarta kamar zata fa'do waje.
_" Fatima kina son Mahmud"_?
Ya sake tambayarta.
Yanzun kam shiru tayi masa sai da ya sake maimaitawa da 'dan 'karfi kafin ta sake 'daga masa kai alamar _"ehh_"
Yagane me take nufi amma dan yasake tabbatarwa yace mata be fahimceta ba dolenta ta bu'di baki ta bashi amsa da " _ehhh"._
_" kin tabbatar "?_
kai ta 'daga masa yanzun ma dan ji tayi bakinta yayi mata nauyi koda zai doke tane bazata iya bashi amsa da bakinta ba.
Yana gama fahimtar ta take sai yasake mata kanta ya koma ya zauna da kyau akan kujera ya lumshe idanunsa tare da jingina bayansa tsawon mintina biyu.
Tashi yayi cak kamar an mintsine shi ya nufi 'kofar fita daga 'dakin, yanda ya buga 'kofar ma ka'dai abin ka juya ka kalleshi ne domin da 'karfinsa ya bugata tamkar tayi masa babban zunubi.
Teemah tana inda ya bartan har ya bar 'dakin bata iya 'daga ido ta kalleshi ba, tana zaune tamkar mutun mutumi, bata san me yasa take jin kamar bata kyauta ba haka kawai sai take jin rashin nutsuwa ga kuma damuwa da tausayin kanta da bata san tushensu ba na ratsata ta ko'ina hakan sai ya 'kara kashe mata jiki tare hana ta motsi agurin banda gudun da hawayen ta ke yi babu abinda ke motsi ajikinta.
Yana fita daga 'dakin sai su kaci karo da Hannah da ta taho da saurinta itama ta nufo dakin, dan tun 'dazu tun fitan Teemah take cikin bayi bata san da labarin zuwan shi ba koda ta fito kuma 'kawayen Teemah basu tuna sun sanar da ita 'kiran da Ummah take yi musu akan lokaci ba, sai da ta 'bata lokaci awurin yin shirin tagama kafin Naanah ta tuna da cewa an'kirasu tun 'dazu.
Koda taje gun Ummah kuwa masifah tafara yimata akan wai ina ta zauna tun 'dazu bata je sun gaisa ba alhalin tasan baya da'dewa akan hanya yake, ha'kuri tabawa Ummahn tare da fa'din ai batasan shine yazo ba"
Mummy ce ta tari maganan da fa'din je ki sameshi ku gaisa kafin ya tafi yana can 'dakin.
Toh ita da suka zo jiya Teemah duk tabi da ita ta nunnuna mata ko'ina agidan da 'dakunan yayun tan, hakan yasa da mummy tace mata yana 'dakinsa sai ta nufi 'dakin da Teemah ta nuna mata jiya amatsayin 'dakin sa, amma sai bata ga alamar ma anbu'de shi ba ( ashe ita kuma mummy key 'din 'dakin Mahmud ta bayar aka sau'keshi aciki), ita kuma sai Hannah tayi tunanin ko bata gane lissafin bane tace bari ta dubo 'dayan tagani tukunna ( abinda ya sa tayi delay 'din zuwa da wuri kenan).
Tana zuwa kuma sai ta ha'du dashi harya fito, _"ah ah_Yayah _har tafiya zakayi_ __ne_ _bayan bamu ha'du ba?
_"Sauri nake yi Hannah lokaci zai 'kure min"._
"_Toh yayah kaci abinci ne ?_ "
Duk maganannan da sukayi akan tafiya suka yi ta, Abbas be tsaya ba koda ya gantan sai yaci gaba da tafiyarsa, itama tana binsa abaya take ta faman jero masa tambayayoyin, ganin kamar zata takura shi. Sai ya ce
_" Hannah naci jeki fito da sauran suna ciki"._
Yasan in ya fa'di haka zata koma tayi abinda yace dan yasan Hannah bata ta6a musanta masa magana kowacce irice.
Illai kuwa hakanne, dan yana fa'din haka ta tsaya cak daga binsan da takeyi, ta bi bayansa kawai da kallo daga bisani kuma sai ta juya ta koma 'dakin domin fito da ragowar abincin kamar yadda ya ce da ita.
Tana shiga sai ta hango Teemah a zaune tana zubda hawaye, da sauri ta 'karasa inda Teemahn take tayi zaman dirshan a gaban ta arikice take tambayarta abinda yafaru.
Teemah kuwa bata san da shigowan Hannah ba sai kawai taganta agabanta lokaci guda.
Hawayenta ta fara 'ko'karin gogewa ita adole kar Hannah tagani.
Duk 'ko'karin da Hannah tayi dan taji meyasamu Teemah tayi amma takasa samun gamshashshiyar amsa ko guda 'daya ne daga wurin Teemah.
Data gaji da tambayar sai tace mata
_" nasan me ya faru ai kawai baki san sanar dani ne"_
Shiru Teemah tayi kawai tana kallonta ita kanta so take taji abinda yasame ta so take taji daga bakin HANNAH, dan idan zata tambayi kanta da kanta ma bata san meke damunta ba bata san mezata ce yafaru tsakaninta da Yah Abbas ba.
_" wannan sojan ne nasani, nasan shine yasaki kuka domin shi ne ka'dai naga yafita daga 'dakin nan kuma nasan sarai zai iya"_
Hannah tayi maganar tare da mi 'kewa tsaye ta nufi inda taga tray 'din abincin.
_" gaskiyarki ne Hannah, Yah Abbas ne !,toh amma me zance yamin har nake kuka"?_ azuciyarta tayi wannan tunanin, sannan itama ta mi'ke tabi bayan Hannah zuwa gurin abincin.
Hannah sai da ta zauna kafin tafara bu'de su 'daya bayan 'daya tana gani.
_" 'kila ya tsaya yi miki mugunta ne ma shiyasa ko abincin be saurara ba harda wani cewa wai inzo in kwashe_ _sauran ashema ko bu'dewa beyi ba"_ tayi maganar dai dai tana 'ko'karin rufe plate 'din daya kasance na 'karshe data bu'de " _muje sai na tambayeshi ai laifin me kika masa da har yasaki kuka, innayi sa'a shi zai gaya min tunda ke kin'ki sanar da ni, problem 'din ma miskilancin tsiya gareshi da 'kyar ma yakulani idan yaga dama, amma nasan me zanyi ai in ya'ki bani amsa Daddy zan 'kira infa'dawa ince in yazo nan dukanki yake yi kullum kafin yatafi "_
Suna kan tafiya Hannah take ta jero bayananta batare da Teemah ta fa'di ko kalma 'daya ba sai da Hannah ta dasa aya sannan Teemah tace
_" ke nifah bance miki ya Abbasa ya doke ni ba"!_ awani tsare tayi maganar tamkar wata jaruma.
Turus Hannah taja ta tsaya
_"Toh yah akayi? fa'damin_ "!
_" ayaya kika sameni"_ ?
Sai da Hannah ta 'dage gira tukunna tace
_"Azaune mana kina_ _kuka"!_
_"Toh abinda yasame ni kenan, gajiya nayi da zaman kuma kafata ta ri'ke sai zogi takemin nakasa ko motsa ta shiyasa ni kawai nafara kuka"_
_" shikuma yatafi ya 'kyaleki ahakan"_?
_"Sai da ya fita sannan na fara jin zafin"_!
_" kin ma rainawa kanki hankali yarinya amma da nazo 'din waye yataimaka miki kika mi'ke?"
Da sauri Teemah tace _" ai lokacin 'kafar ta daina zafi"_
_" kuma hawayen kasa tsayuwa yayi ko"? ,_