← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 163

Sashe 106

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce*😍

[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir rahmanir raheem*

_No man succeeds without a good woman behind him......either Wife or mother, if it is both, he is twice blessed indeed_🤞🏻

🅿 *76*

Haka a gida ma da yawan mutane na farin ciki da wannan aure sai faman sanya albarka akeyi.

An shirya Teemah cikin wata doguwar riga mai kyan gaske kalar touqoise blue da ratsin golden, rigar ta kama ta sosai daga 'kirji 'kasan rigar kuwa abu'de yake ba 'karamin fito da kyaunta rigar tayi ba.

Hannah kam yau ba ta jin gari, tunda aka 'daura auren ta fara 'kiran Teemah da suna _amaryar_ _Yayah_ , Teemah tun tana mitar bata so har ta ha'kura tayi shiru balle da taji kanta yafara sara mata ai tuni sai ta nemi 'dakin da aka sau'kar da Mummy ta shiga da niyyan hutawa.

Mummy kam korota tayi tace maza taje cikin 'yan uwanta ta zauna bata son zama shirun nan.

Fuskar shagwa6a tayi tace
" _Allah Mummy kaina ke ciwo ne shi yasa_ "

Mummy tace taje yanzu ta 'dau maganinta tasha ba jiya an siya miki magunguna ba, hayaniya ne ke saki ciwon kan ba komai ba.

Fita tayi taje 'dakin su nan ta samu Hannah da 'kawayenta sai ihu sukeyi, haka ta zauna agefensu tayi shiru bata kula su amma duk yadda Hannah tasan zata takalo ta tasata magana sai tayi.

'Karfe uku nayi duk suka wuce gidajensu da sunan zasu je kowa ta yo shirin walima su dawo.

Hannah ma kasuwa ta shiga aka bar Teemah ita ka'dai.

Taji da'din raguwar hayaniyan amma kuma sai ta ringa jin zazza6i na son taso mata.

Zama tayi a'dakin nasu ta'ki zuwa ko'ina kuma ta'ki shan maganin ma .

Kafin yamma kuwa zazza6in Teemah sabo fil ya dawo ga jiri dake faman 'diban ta har bata iya tsayuwa da kanta sai ta kama abu, gaba 'daya ta fita a hayyacinta.

Anty ne tazo neman ta dan afara shirin yi mata kwalliyar yamma ta zuwa walima, gagarumin walima ne da Daddy da kansa ya shirya shi.

Sosai Anty ma tayi 'ko'kari dan kuwa duk wasu kaya da Fateemah tayi anfani dasu da ma wa'dan da zata sa agaba duk Anty ne ta 'dau nauyin yinsu tare da 'dauko wata shahararriyar mata wacce ta 'kware a fannin kwalliya na zamani domin ta ringa yiwa Teemah make'up har biki ya 'kare.

Ko yanzun ma da kanta ta shiga duba Teemah sai ta tarar da ita kwance ta du'kun'kunu a cikin blanket.

Da sauri ta 'karaso tazo gareta tana tambayar ta "me ya faru?

Tayi saurin fahimtar abinda ke faruwa ne sanadin zafin da taji jikinta yayi ga kuma ha'duwan da ha'koranta keyi.

Fita tayi da sauri da niyyan 'kiran Mummy sai kuma tariga ha'duwa da Ummah tun kafin ta kai ga Mummyn.

Ummah kam ganin hankalin Anty atashe yasa tayi saurin barin maganar da takeyi ta taho ta tareta da tambayar meke faruwa ne?

Bayani Anty tayi mata atakaice tun kafin tadasa aya kuwa Ummah ta furta " _subhanallah_ " sai tayi gaba, tare suka 'dunguma zuwa 'dakin su Teemahn da Anty da wasu mata guda biyu.

Ganin yanayin Teemah yasa Ummah fa'din " Fateemah sannu ko, sannu Allah ya sauwa 'ka!

Juyawa tayi ta kalli 'dakin tace "wai ni har yanzu Hannah bata dawo bane?

Wata Antyn su da suka zo daga Gombe ce ta bata amsa da fa'din " inaga de bata dawon bane 'kila"

Ummah dialling no. tayi ta 'kira shiru tsawon seconds bakwai sannan ta furta
"Ameen wa alaikassalam"

"Jama'ah Alhamdulillah"

"Fateemah ba ta jin da'di ne nace ko zaka aiko doctor adubata "

"Ok, toh shikenan"
tafa'da tare da yanke wayar.

Iya abinda kowa yaji kenan kuma babu wanda yasan da waye tayi magana.

Sai da ta cire wayar a kunnanta kafin tayi musu bayanin cewa " Abbas zaizo yanzu 'kila ya taho da likita ko kuma ya kaita asibiti ban san wanne zaiyi ba"

Fita tayi tace "bari tana zuwa yanzu kafin ya iso"

15mins be cika ba sai gashi ya bayyana a'dakin cikin wata arniyar shadda sky blue mai kyan gaske wanda ya dace da yanayin jikinsa.

Da sallamar sa ya shigo tare da gaida wa'danda yagani a'dakin.

Sake tambayar Anty yayi abinda ke damun Teemah Antyn sai tace dashi " _inajin zazza6in ne ya dawo dan jikinta ya dau zafi gaskiya sosai_ "
Tayi maganar tare da kaiwa hannunta zuwa jikin Teemah.

Abbas kam tana gama bayani sai ya kallo inda yaga maganin ta jiya, aikuwa sai yagansa still agurin, zuwa yayi a hankali ya isa inda yake ajiyen ya duba sai ya ga tun wanda ya 6alla mata jiya ne bata 'kara shan wani ba.

Sai yanzun yakai dubansa kan Fateemah da tun safiyar yau yake mararin ganinta amma be ganta ba sai yanzun.

Jikinta arufe ruf illah kanta ne yake iya kallo dan fuskarta yana 'daya bangaren ne ta juya musu baya.
Tuni 'daurin da aka mata ya zame ya koma gefe ya bar iya gashinta dake kwance gwanin sha'awah awaje yana ta she'ki.

Takawa yayi a hankali zuwa bakin gadon yasa hannu ya ta6o fuskar tata sai yaji zafi gau be 'dauke hannun ba sai da ya shafi gashin kanta da ya 'dau hankalinsa yanda babu wanda zai lura cewa dagan gan yayi.

Juyawa yayi ya fara tafiya yace da su akaita motansa zai same su acan, yace gara muje hospital adubata yafi"
Yana gama fa'din haka ya bar 'dakin.

Wasu su biyu ne suka kama kafa 'dunta zuwa inda ya fa'da 'din Anty na binsu abaya.

Anan ya same su ri'ke da ita an lullu6a mata mayafi akanta wanda yarufe jikinta da kyau, hakan kuwa ba 'karamin da'di yaji aransa ba, sai daya iso ya bu'de motan kafin ta shiga da taimakon Anty sannan shima yashiga tare da furta _bismillah_
don zatonsa ko da 'dayansu za'a.

"Sai kun dawo, Allah ya tsare ya bada lafiya in gantacciya"
Anty ne tafa'di haka kafin ya amsa kuwa har sun juya masa baya.

Ganin sun juya kuwa yasashi sakin hamdala azuciyarsa dama shi ba son rakiyar yake ba dan sai ya cire babbar rigar dake jikinsa ya wulla ta baya dama duk ta takurasa ha'kuri kawai yakeyi da ita na yau ka'dai.

Jan motar yayi suka bar haraban gidan, sai da ya hau titi kafin ya juya ya kalleta sai yaga ta kwantar da kanta ajikin cinyoyinta ta takura guri guda ga dukkan alamu sanyi takeji sosai.

Be yi mata magana ba hannu yasa kawai ya kashe AC gaba 'daya sannan yaci gaba da tu'kinsa.

Koda aka gwada ta ma ba komai ke damunta ba zazza6in ne kawai sai stress daya mata yawa amma bakomai, kuma ciwon na 'kara 'karfi ne sanadin rashin cin ishshen abinci da batayi.

Yau kam cewa yayi ayi mata allura dan bata son shan magani ma yace ko najiya ma 'kin sha tayi.

Kuka tafara tare da ro'konsa akan dan Allah yayi ha'kuri bazata sake 'kin shan magani ba.

Kau da kai yayi yace da nurse 'din ta ha'da injections 'din yace kuma bata son cin abinci ma doctor.

" _Yayah plz kace ta bari Allah zan rin'ka shan magani kullun_ "!

Yi yayi kamar beji ta ba sai ma yace da doctor ta hanzarta please.

" _Wallahi ni bana son alluran nan, kuma sai na gayawa Ummah da Anty da Daddy ma_ ".

Murmushi doctor tayi aranta take mamakin irin dramar wa'dannan Yayah da 'kan wan suna matu'kar birgeta ita kam.

Dakansa ya ri'ke ta tana fiffisgewa amma sai da aka mata har biyu sannan ya saketa.

Zamewa tayi ta 'dora kanta ajikin 'kafafunsa taci gaba da kukanta daya ga haka sai yace ta koma kan sofa 'din dake office 'din ta kwanta, itama sai tayi kamar bata jishi ba, murmushi yayi ka'dan yasan haushinsa takeji yanzu dagangan sai yace da nurse 'din " _doctor inajin fah alluran be isheta_ _ba_ "

Tana jin haka ta mi'ke ta koma inda ya fa'din ta kwanta shiru tana sau'ke ajiyan zuciya, dayaga kamar zatayi bacci ne sai yace su tafi gara taje ta huta gaba 'daya a gida.

*****
Can gida kuwa already shirye-shiryen walima ya kankama kowa nata faman shiri, lokacin da suka iso gidan ma 'dakinsu yayi niyyan kaita amma jin hayaniyar Hannah da 'kawayenta a 'dakin dole sai ya maida ta 6angarensa dan so ya ke ta huta sosai zuwa lokacin kuwa bacci yariga yaci 'karfinta gaba daya.

Suna isa tazame ta ta 'dora jikinta akan gadonsa sai kuwa bacci ya 'dauke ta ahakan sai sakin ajiyar zuciya take yi na kukan da tayi 'dazu.

Abbas kam tsayuwa yayi akanta yana 'kare mata kallo ba 'karamin kyau ta masa ayadda take 'din ba, ahankali yadawo da idanunsa saman la66anta da suka 'karayin ja sosai.

Da sauri ya kawar da mugun tunanin da yazo ransa tare da fa'din " a _uzubillah_ "

Gani yayi kamar kayan da ke jikinta sun mata nauyi dan haka sai ya 'dauki wayarsa yakoma parlour, layin Hannah ya'kira amma bata 'daga ba, daya sake 'kira kuwa sai ta 'daga amma bata jin sa tsaban hayaniyan daya yi yawa agurin da take.

Take yayi tsaki ka'dan tare da yanke 'kiran.
Dama so yake ya sanar da ita ta kawo wa Fateema kaya marasa nauyi amma hakan be samu ba ganin bajinsa zatayi ba, sai kawai yafara tunanin wata mafitar daban.

Baifi 5mins a parlour ba sai ya tashi ya koma bedroom 'din tare da 'daukan stool yakoma gaban gadon ya zauna ya zuba mata idanu.

Ahankali yakai hannunsa zuwa bayanta ya zuge zip 'din doguwar rigan da ke jikinta wanda yakamata 'dam ya zauna sosai.

Ahankali ya zare rigar zuwa 'kasa har ya cire ta gaba 'daya.
Chapter 106 · 0% Book details