← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 163

Sashe 9

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummyn ce ta k'ara da cewa "fushi takeyi wai yanzun da yayanta,amma inaga abin kowa ma bai tsirah ba."

Murmushi sukayi dukkan su,daga nan suka ci gaba da sabgoginsu akitchen d'in suna yi suna d'an ta6a hira jifa-jifa.

Basu k'ara had'uwa ba sai bayan isha'i,dasuka zo cin abincin dare,Nan ma mummy tace taje maza tak'ira shi.

Tana jin abinda mummy tafa'da ta fara bubbuga k'afafu ak'asa,tana fad'in "haba mummy shi wai bazai zo da kansa ba sai ank'irasa"?

Tsawa mummy ta daka mata "bana son rashin kunyah Teemah,aiken nawa ne bazaki ba ko kuwa shid'inne kika fi k'arfin ki k'irashi"

Tana jin haka ta juya ta fara tafiyah zuwa d'akin nasa,

"mthww" mummy taja tsaki biyan tajuya d'in, ita kuwa haushi kamar ya kasheta sai mita takeyi k'asa-k'asa ahankali "wlh mummy duk so take yi ta zubar min da ajina agun wannan mutumin😅,so take ya raina ni gaba d'aya.(kujimin yarinya fah🤔😏)

Bakinta kuwa kamar na 6era tsabar yanda ta turo shi gaba.

Duk da ran mummy a6ace yake,amma bata kasa fahimtar yanayin Teemahn ba,kuma duk tasan bazai wuce akan abinda yafaru d'azun bane,take wannan abun.

Haka taje k'ofar d'akin ta tsaya daga waje tana knock in d'in k'ofar,jitayi babu wanda yace mata ko cikanki ne,sake bugawa tayi da 'dan k'arfi,amma still shiru taji, babu alamun ma anjita.
Hakan yasa ta tura k'ofar azuciye,tashiga cika batare ma da sallama ba.

Gani tayi yanzun d'akin da haske ba kamar d'azu da ta zo ba.

Ta6e baki tayi tare da rarraba idanu ad'akin dan bata ga alamar mutun ba aciki.Komai nakin tsaf dashi tagani,babu gurin data isa ta kushe ad'akin,sai uban k'anshin turarensa mai dad'in shak'a.

Ita kuwa dan iskanci sai ta d'aga hannunta ta toshe hancinta da su,harda ta6a fuska,adole wai turaren bai mata ba ita.

Dai dai shima yabud'e k'ofar d'akin ya shigo,ga mamkinsa sai yaga tana toshe hanci,k'arasa shigowa yayi a mamakance idonsa na kanta,so yake yaji menene dalilinta na toshe hanci a muhallinsa,tunda yasan bai bar komai ad'akin da zai sa har aji wani abu makamancin wari ba,dan ko bayin dake cikin d'akin ma atsaftace yake,ko abinci inta kama sai ka iyah ci aciki,balle ma shi bayaga wanka babu abinda ya had'a sa da bayin tunda yazo gidan sai ko alwala.

Bin d'akin ya sakeyi da kallo akaro na biyu sannan ya kalleta, wuri-wuri tana rarraba idanu,taku yad'anyi kad'an zuwa inda take,tana ganin haka tayi baya itama da sauri,ganin haka sai ya tsaya a inda yake d'in.

"Wani isakanci ne yasaki toshemin hanci ad'aki?"

Dan sosai abin yaba shi haushi,ba k'aramin cin fuska bane yin hakan ga wani,babu wanda zai so ace anji wani abu da ya danganci hakan a inda yake rayuwa,balle mutun irin Abbas da tun tashinsa da tsafta aka sanshi,tun yana yaro ya tsani k'azanta.....................

"Ba tambayarki nakeyi bane"

Ya fad'a atsawace dan jin bata amsa masa tambayar farkon ba.

Muryarsa na razana ta amma,dan jikinta har rawa ya fara,amma haka ta dake ta bashi amsa da

"d'akin yana wari ne"

Ranshi a6ace yake amma baisan sanda ya zaro idanu waje ba tsabar mamaki,

"Wari kuma.......?
"Warin me toh?
Ya tambayeta.

" *Turare* "
Ta bashi amsa kanta tsaye.

Tsabar takaici kasa yin magana yayi,illah kallon daya bita dashi,amma dai yad'an ji nutsuwa datce warin turare ne,abin takaici kuma har yanzu bata bar toshe hancin ba.

Gani da yayi still tana rufe da hancin ta ai sai ya yunkura zai kamota,tana ganin ya nufota kuwa ta juya baya,dagudu tabar d'akin,cikin sa'a ma abud'e tasamu k'ofar,dan mamakinta ne yasa daya shigo ko k'ofar bai mayar ya rufeta ba,shiyasa tasamu sauk'in gudu,fit ta fice abinta batare da ta tsaya jan k'ofar ba.

Sai da ta tsaya wani lungu ta daidaita numfashinta kafin ta isa wurin mummyn,
"Mummy wai yana zuwa"

"Uhm" mummyn tace sannan ta k'ara. Da fad'in yakin da'de,

"Bansame shi ad'akin bane mummy" tafad'a kamar wata mumina, dan ji take ranta wasai yanzu dalilin wannan abin data yimasan.

Shikuwa bayan fitar ta ad'akin sai yaje ya tura k'ofar tare da fad'in "useless kawai" sanin da yayi wa kansa, k'anshi ko wari ko yaya suke kuwa sai ya jiyosu indai wad'annan abubuwan ne,bata isa ta nuna masa jinsu ba.

Dawo wa yayi cikin d'akin yatsaya ya sake k'arewa ilahirin d'akin kallo,sai kuma yayi murmushi,
"zan had'u da ke ne yarinya"
afili ya fad'i hakan sannan ya ka'rasa bakin gado ya ajiye wayarsa.

Shima ya zauna ya fara 6alle botiran rigarsa,
har ya kusan 6allewa sai kuma ya tuna k'ila aikota akayi,
tunda yanzu lokacin cin abincine agidan kamar yadda yasani tun ada,
take sai ya mik'e ya fice daga da'kin.
Ya nufi main parlour.................

Drop ur comment pls readers🤞🏻,inkuna son ku faranta min🙈

*Salmerhn* 😍 ku ce 👌🏻
[10/2, 5:53 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Dedicated
2
_Friendy like no_ _other_ .......
( *Mamee Hafsat* *Ndahi) I hrt u baby* *girl* ._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Ego is just like a dust in the eye ….... without clearing the dust you can’t see anything clear........,. *so clear* *the ego* *and see the world.*

🅿 *10*

A dinning ya same su gaba d'ayansu har daddy amma basu fara cin abincin ba har yanzu,da alamu jiransa suka tsaya yi.
Teemah na ganinsa tafara zare idanu tayi k'asa da kanta sarai tasan tayi masa laifi kuma bata kyauta ba,don babu wanda zai so a kushe masa muhallinsa ballantana ma ita na raini tayi.
Ko kallon inda take ma baiyi ba yaja kujera ya zauna tare da yiwa su daddy barka da gida.

Amsawa sukayi daganan suka yi bismillah auka fara cin abincin su.

Teemah yau kam har mamaki ta bawa iyayenta ganin yanda ta ke cin abincin,ita kuwa cin k'arfin hali ta ke yi,don so take ta riga kowa barin kan table d'in tagudu d'akinta ta kulle kafin yah Abbas ya cafkota.

Kusan duk kaiwa spoon d'inta baki toh sai ta kalleshi,amma ko sau d'aya basu ta6a had'a idanu ba.

Taci abincin yakai rabin plate sannan ta tashi awurin tsam ko sallama bata musu ba.

Babu kuwa wanda yah tankata dan mamakin da ta cika su dashi,Abbas kuwa ko ajikinsa,cin abincinsa yake yi cikin kwanciyar hankali,yi yayi kamar bai san ma da ita awurin ba,koda ta mik'e d'in kuwa k'in d'aga kai yayi ya kalleta, amma tak'asan ido babu abinda ya wuce wa ganinsa,ta k'asan idanu yake ta kallon duk abinda takeyi harta gama ta tashi d'in.

Tashin bata wani dad'e ba shima yaji ya k'oshi hakan yasa ya wa su mummy sai da safe ya wuce abinsa.

Ita kuwa Teemah ruwa ma sai data bi kitchen ta d'auka sannan tawuce d'akin ta da shi,tana shiga kuwa ta danna key tana Hamdala,murna fal cikinta dan tana ganin ai ta tsira.

Ruwan tasha ta ajiye ragowan agefen gadonta,sannan ta d'an rage kayan jikinta,school bag d'inta ta d'auko ta dawo ta hau tsakiyar gadon ta barbaza takardu wai nan karatun Test takeyi,batajima ba ta fara hamma,minute-minute kuwa hamman ke zuwa,tsaki tafar jerawa itama aduk sanda tayi hamman,haushin wannan cin abincin datayi yau sosai d'in nan takeji,
"ai duk wannan mutumin nan ne yasani"
tayi maganar azuciyar ta tare da biyoshi da wata doguwar tsuka.

Takai 1hr tana karatun sannan ta tattare shirgin takardun akan gadon,daga nan tayi addu'a adaddafe ta kwanta.

Washegari tana tashi kuwa sai da tayi sallah kafin taje ta yi wanka,zaman shafa mai tayi bayan ta fito daga bayin,sai da ta gama goge jikinta tukunna ta kai hannu ta d'auko man nata datake shafawa kullum.

"Awsh namanta ashe ban fad'a wa mummy ba"
tafad'i tare da dafe goshi.

Da kyar tasamu tashafa man kasancewar babu ya k'are acikin robar,shiri tayi cikin uniform d'inta,tafito ta nufi d'akin daddynta,dayake daman idan daddy yana gari shi take fara zuwa gaisarwa kafin mummy,gani tayi baya nan,hakan yasa ta fito ta nufi d'akin mummy.

Daddy kuwa tafiyace tasame shi ta gaggawa,tafiyar bazata dan jiya kusan 10:15pm aka k'ira shi,Allah ma yasa yana da passport d'insa ,so tun adaren ya k'ira yayi booking flight,6:30am yabar gidan,kasancewar 10:00am zasu tashi.

Gaishe da mummyn tayi sannan ta tambayeta "ina daddyn ta yake?

"Yayi tafiya ne"
Mummyn tabata amsa.

Sai cewa tayi "aida ya fad'a min ma da da tare zamu"

Kallonta mummyn tayi da mamaki sannan tace
"Toki bishi mana,ai baki makara ba"

Dariyah tayi kad'an
"Allah kuwa mummy da binsa zanyi da nasan zaiyi tafiyah,in bahaka inaji ina gani zaman gidannan sai ya gagare ni saboda wannan........,.......sai kuma ta kasa k'arasawa.

Mummyn ce takar6e zancen da fad'in " ahh toh in juninki rashin kunya ne da tsokana aikuwa ba ruwana ni,dan ni nawa ido"

"Mummy hakama zakice"?

"Toh me zance Teemah?
"Bake rashin ji kika ce shine halinki ba?

Fushi tayi data gama jin abinda mummyn ta ce.

Tea kawai tasha shima sama-sama daga nan ta tashi tsaye.

"Mekenan" mummyn ta tambayeta tana kallonta.

"Ni na k'oshi mummy"

D'auke ido mummyn tayi daga kallonta kafin tace
"Ke kika sani ai",kije jakata bak'an nan ki d'auki Kud'i aciki"

fara tafiya Teemah tayi zuwa d'akin mummyn sai tajiyo muryar mummyn na sake fad'in

"Kuma yanda kika saba tafiyah dashi zaki d'auka, bance ad'auki harda na shan kayan zak'i ba,sai wata yayi ki takura min da fitina"

Karaf akunnen Abbas da shima ya zo dan ya gaida mummyn.

Kuma atake ya fahimci me mummyn take nufi,mamaki yafara yi ashe yarinyar nan har haka ta girma amma shine bata da wayo har yanzu?

Da wannan tunanin ya k'arasa inda mummyn take,tana ganinsa kuwa ta sake fuskarta dan mummy ba dai son jama'ah ba,sam bata da wannan al'adar ta k'in dangin mijinta.

gaida ta yayi shima,sannan yad'an zauna kamar mai jiran wani abu, nan kuwa zaman jiran fitowar Teemah yakeyi agurin.

Koda mummy ta masa maganar break fast d'inma cemata yayi a'a bayanzu ba sai zuwa anjima zai ci.
Chapter 9 · 0% Book details