← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 163

Sashe 18

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Mahmud shine har can saboda Allah!

"Abbah toh ya zanyi an riga an cire list d'in bansan yanda zanyi ba,nima yamin nisa gaskiya,
amma dai zan gwada sa'a ta nagani ko za'a dawo dani kusa"

"gaskiya kam ka gwada amma ai yobe yayi nisa sosai."

Mahmud bai k'ara magana ba illah tsayawa da yayi yana kallon Abban nasa da mamaki,ganin dayayi kokad'an bai kawo batun y'ar uwarsa dake zaune acan d'inba ko kuma irin yayi farin ciki da hakan yaru ba kamar yadda ya saba.

Aganin Mahmud ai murna ya kamata Abban nasa yayi dayaji batun zuwansa yoben bawai yayi againsing ba,amma ga mamakinsa sai yaga ko ya nuna alamun irin da wani nashi ma acan d'in baiyi ba balle ace zai k'arfafa tafiyar kodan dalilin Anty khadijan.

Lokuta da dama yana mamakin irin
girman laifin da Anty khadija tayiwa Abban nasa da har yasa yake kaucewa duk wani al'amari dazai shafeta.

Gagara hak'uri yayi har baisan lokacin da ya bud'i baki ya tambayi Abban nasa ba.

"Abbah meyasa kamanta da Anty khadija ne?

Yah yusuf najin abinda Mahmud d'in yafad'i sai ya d'ago fuskarsa da sauri ya tsurawa fuskar Mahmud d'in ido kamar wanda akace zai ga wani abu akan fuskar Mahmud d'in idanuwansa har tara ruwa suka yi.

Gani hakan yasa Mahmud lumshe idanunsa tare da d'auke fuskarsa daga saitin daddyn yamaida shi inda yaji takun tafiyah anan ya k'arasa bud'e idanun nasa ya sauk'e su akan K'afar Anty dake tahowa da takunta na k'asaita.

"Ha- ah
"yah na ganku jigum-jigum haka?
"Meke faruwa ne?

Tana maganar ne tare da hanzarto wa izuwa garesu.

Abban ma sai da yaji muryarta kafin ya d'auke idanunsa daga kan Mahmud d'in ya maida shi kanta.

'Zuwa tayi ta zauna a gaf d'in dake tsakaninsu,sannan ta maimaita tambayar tata.

Mahmud bai kalli inda take ba ya bata amsa da fad'in Anty service d'ina Yobe state yafito"

Hannunsa yana yawo akan fuskarsa yayi maganar.

Karkuso kuga yanda Anty ta firgita daga jin an ambaci yobe har taso k'ara saka Mahmud cikin tunani amma sai ya waske.

"Haba no wonder naganku jigum-jigum ai dole"

"Su rasa inda zasu kaika sai wancan garin?

Dukkansu kallonta sukeyi yanzu kam,kowa da abinda ke ransa.

Abbah so yake yayi maganar 'yar uwarsa Khadija amma azahiri yakasa furtawa,aransa kuwa harhad'a maganar yakeyi tsaf
"Yauwa Alhamdulillah fad'uwa tazo dai-dai da zama tunda Khadija nacan ma na tabbata baka da matsala da komai"

Maganar dake ran Abbah kenan amma afili ya gagara furtawa,nawi yakejin harshensa yakeyi akullum indai akan Khadija ne.

Mahmud kuwa mamaki yakeyi aransa shima naganin ko Anty ma bata kawo batun sauk'in da hakan keda shiba ganin Anty Khadija nacan ko kuma irin yaga ta nuna farin cikinta akan faruwar hakan.

Alwashi yaci aransa nasa cewa sai ya tambayi Anty yaji ko me Anty Khadija ta musu suka tsaneta haka,kowa baya son abu agidan indai al'amarin yashafeta ne.

Ahakanma gara Anty dan ita idan ya tambayeta abu tana d'an bashi amsa koda kuwa da fad'a-fad'a ne sa6anin Abbansa da ko magana baya masa indai ya had'a da batun Khadija ne toh sai dai kallo da idanu
babu magana ko kad'an.

Abbansa bai ta6a bashi amsar tambayoyin dayake masa ba akan Anty khadija ko da kuwa sau d'aya.

Washe gari kuwa yaje yasamu Anty da tambayar laifin da Anty Khadijan ta musu da har suka d'auki irin zafi haka da ita!

Masifa Antyn ta fara masa kamar ta ari baki garin masifar ne ta d'an kuskure ta ce masa
"Bana son fitina Mahmud kai komai sai ka bishi da tambaya ne?
Meyasa bazaka bar komai ayanda kaganshi ba?
Ina zaman zamana kar ka kuskura kaja min fitinar dana kwantar da ita da kyar"

"Fitina kuma Anty wace iri?

Ya tambayeta da mamaki kwance akan fuskar sa.

"Irinta uwarka"🙈

Tabashi amsa kai tsaye.

"Ah ah naji ne kince kin kwantar da ita da kyar toh kuma ni bansan fitinar ba Anty laifine dan na tambaya?

"Katashi kaban wuri ni banason hauka"

Ta fad'i da matukar 6acin rai dan zuwa yanzun sosai ranta ya fara 6aci dan ganin Mahmud d'in nason ya k'ureta.

Bud'an baki yayi zai sake magana ta mik'e tsaye kamar andannna mata remote hanyar fita ta nuna masa

"I said get out from this room now"

Da wata uwar tsawa tayi maganar hakan yasa ya mik'e tsaye yana k'ara gyara zaman rigar dake jikinsa har ya fara tafiyah sai kuma ya juyo ya kalleta sannan yace

"Hakan da kuke yi ne yake k'ara samin sha'awar tafiya wancan garin dan na san meke faruwa na tabbata zanji koma menene acan d'in ba kamar yanda kuka barni acikin duhu b.........

Bai k'arasa ba ta kar6e maganar

"Mahmud kar ka ce min da kanka kacika wannan garin dan ka muzanta ni........tak'ara sa maganar tana nuna kanta da yatsanta.

Murmushi yayi sannan ya lumshe mata idanu.
ga dukkan mai wayo yasan hakan dayai alamar tabbatarwa yayi mata.

Haushi sosai taji sai kuwa tace
"Za ko kaci ub........🙈

Juyawa yayi ya fara tafiyah ahankali yana jijjiga kansa
yana fad'in "yau kad'ai Anty kin koyi zagi narasa ma'anar hakan fah"

cewa tayi
"Eh zaka ce haka mana dake ka maidani sa'ar ka,zanga kuwa ubanda zai barka kaje can d'in ai, idiot"

Bai kulata ba yanzun kawai ya
cigaba da tafiyarsa har yabar cikin d'akin,yana k'ara jin mamakin Antyn yanda ta wani d'au zafi akan wannan simple abun.

Ai dole ma naje kodan na
tambayi Anty Khadija abinda ta musu suka tsaneta haka.

Kwanaki na k'ara ja lokacin tafiyar Mahmud na sake k'aratowa,kamar yanda hankalin Anty ke k'ara tashi akan batun tafiyar,ita aganinta tasamu ta d'an sake babu batun dangin miji ya zai je ya jaji 6o mata jaraba tana ji tana tana gani.
_Kuji fah ikon Allah_

Babu irin k'ok'arin da batayi ba akan tafiyar amma abun yaci tura gani take kamar ma himma take k'arawa Mahmud d'in akan tafiyar.

Shikuwa dagangan yake komai akan batun tafiyar duk dama har yau Abbansa baice komai akai ba amma yanda Antyn tayi reacting so yake yaji dalilinta nayin hakan kuma tak'i sanar dashi asalin dalilinta dan haka yake abinsa da gangan dan yata tunzura ta ko zata yi zuciya tafad'a masa dalilin amma shiru.

Sai dai tayi ta hantarar sa kamar wani yaro d'an goye ga wani zafin rai data d'auka ta d'orawa kanta da ya rasa manufarsa kwata-kwata.

Tafiyar saura baifi sati ba ne Daddyn Teemah yazo Lagos anan Abbansa yake fad'a masa cewa ai mahmud d'in zai zo Yoben Bautar k'asa.

Daddy dayaji hakan bak'aramin farin ciki yayi ba musamman kodan matarsa Khadija yasan zatafi kowa farin ciki da wannan batun,amma bai nuna zak'ewarsa ba tunda yaga yanayin Yah yusuf d'in asanda yake maganar shima bawani farin ciki ya nuna da faruwar hakan ba.

Sai dai duk da haka sai da yatambayi meyasa kuma sai yanzu Mahmud d'in zaiyi service?...... me yasa baiyi karatun da wuri ba?.........

Amsa Abbah ya bashi atakaice.

Haka suka rabu da Yah Yusuf d'in Daddy nacewa Allah ya kawo shi lafiya ina nan ina jiran isowarsa.

Shima dagangan ya daina sako zancen Khadija a tsakaninsu dan ganin kamar yah yusuf d'in baiso.

Dan idan ya matsa masa da tambayar ya sanar dashi laifinta kodan ta nemi yafiyarsa ma sai yaga yatsaya jim kamar an dasa shi wani lokaci har k'walla yake sharewa amma still bazai bada amsa ba.

Ana washe gari Mahmud zai tafi ma Antyn kamar ba d'anta ne zaiyi tafiya ba,ita adole fushi takeyi dashi har wani lokaci ji yake kamar yafasa tafiyan amma inah sai yaga bazai iya ba yazama dole ne ma yaje shi d'in.

Zuwa yayi ya zauna akusa da ita sai tayi kamar bata ganshi ba taci gaba da kallon television d'in data keyi.

Shima sai ya maida kallonsa zuwa inda take kallan sannan ya fara magana

"Yanzu Anty fisabilillahi kin kyauta min?
ace zanyi tafiya amma ko kulani ma sai ki dai nayi bayan kinsan dole ina buk'atar sa hannunki ashirin da zanyi?
Ni ne fah Anty ki ganni dakyau fah idan na tafi ba dawuri fa zan dawo ba"

Amsa shi tayi da

"Sai mai toh Mahmud,idan katafi dan Allah karka dawo Har abada kaga ko zan damu"

Ido ya zaro waje tare da fad'in "har abada dai Anty"

"Uhm,ka gwada mana kagani"
ta bashi amsa.

"Niii d'in "ya kara tambayarta

Harara tabisa dashi kawai

"Toh aini Anty bazan iyaba,ina zan iya rayuwa babu ke akusa dani!"

"okay sai yanzu kasan amfani na kenan,daka maida ni tamkar abokiyar wasan kan kamanta ko?

"Bahaka bane fah Allah,haba Anty kefah uwace ,kar kifiya son kanki dayawa mana,ki tuna abaya dalilin bin umarninki nayi shekaru ina zaman banza agida batare da na k'ara sa makaranta ta ba,alokacin fah dakin bari nayi na tabbata da yanzu na wuce wannan level d'in da jimawa,amma haka na biyeki daga k'arshe kuma bagashi ba ahakan dole nayi batare da burin naki yacika ba.
Toh wannan d'in ma haka kike so na kuma yineh?
Bayan inada right d'in yin hakan Anty?

"bama wannan ba
Nidai dan Allah ki daina fushin nan kisamin albarka awannan tafiyar tawa."

Kinji".

Haka yayi ta lalla6a ta harta sauk'o daga fushin amma dai har yanzu ranta bai d'auki tafiyar ba.

Haka dai ta hak'ura tanaji tana gani washe gari ya kama hanya yayi tafiyarsa dolenta tayi masa fatan Alkhairi badon taso ba sai dan son da take masa a matsayinsa na d'anta k'wallin k'wal a duk fad'in duniya.

Juyi mahmud yayi zuwa d'ayan gefen sannan yace wannan tambayar ta dawo kanki mummy dole in tambayeki dan so nakeyi in sami amsa ta kafin nabar garin nan.

*Serlmern ku ce* 😍
[10/2, 5:55 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DA* *BAZAR MU MUKE* *TUN'KAHO* 😍

In dedication 2 my sisters👇🏼
*Ummie*
*Maijee*
*Zuwairah*
*Ameerah*
and my lil baby sis
*Miemie.* Allah ya barmin ku....(Ameen)

Masoya nagode da addu'o'inku I'm safely arrived,nima ina muku fatan alkhairi gaba d'ayanku,duk wacce tamin addu'a Allah ubangiji ya saka mata da mafificin alkhairi,Allah ya kar6i ibadunmu.👏🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Chapter 18 · 0% Book details