← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 163

Sashe 122

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fita yayi ya bar su inda Anty nurse 'din tace mata ta gyara da kyau ta dubata, hawaye tafara yi ka'dan-ka'dan tare da fa'din " _Anty dan Allah kar kimin allura in kika yimin mutuwa zanyi, Yayah ma mugunta yamin 'dazu........._ "

" _Shiii...! yi shiru bazan miki allura ba karki damu kinji_ "

Kai ta 'daga mata sannan ta bata chance ta duba ta.

Bama wani ciwo taji ba kawai dai 'kan'kanta da rashin 'karfi da jikintan ke dashi ne ha'di da rashin sabo yasa take jin bada'di, ga kuma shigan 'karfin da akayi mata shiyasa take jin zafi sosai.
Da farko nurse 'din tayi tunanin ko ciwo sosai Teemahn taji amma sai kuma taga abin da sau'ki musamman dayake ta yi anfani da ruwan zafi so ba wata matsala sosai.

Data ga haka sai tace da Teemahn " _Dama shi mijin kine_ ?
Da
" _Ummm_ "
Teemah ta bata amsa tana mai jin kunyar ta ga jikinta.

Nurse na cire hanglove 'din hannun take fadin shine kike cewa yayi miki mugunta ko? Waye ya gaya miki ana fa'din haka?ko bakya son shine akayi muku auren ?

Teemah kam shiru tayi tana tunanin me zata ce da Anty nurse 'din, ita kuwa nurse tana har ha'da magunguna taci gaba da fa'din " _kar kinayin taurin kai in bahaka ba kullum ciwo zaki rin'ka ji kinji_ ?

Kai ta 'daga mata alamar " _toh_ "

" _Yauwa Fateemah, ko kinfi son mijinki yana neman wasu matan awaje_ ?
Yanzun ma da kai ta bata amsa daidai Abbas ya turo 'kofan ya shigo dan hankalin sa yakasa kwanciya.
Dukkan su sai hankalinsu yakoma kansa.

Gefen Teemah yazo ya zauna sai nurse tayi masa bayanin babu ma matsala sosai idan taci gaba da amfani da ruwan 'dumi ma komai zai dai-dai ta.

Sai ta bashi wasu magunguna kala biyu tace ta sha wannan zazza6in nata zai sau'ka kuma zai 'kara taimakawa wajen healing ciwon da wuri.

Godiya Abbas yayi mata inda a take yabawa Teemah maganin ta sha sai suka fita tare da nurse suka bar Teemah ita ka'dai inda ta koma ta sake kwantawa.

Suna fita parlourn nurse tace dashi " _yalla6ai kafa so kayi 6arna gaskiya_ "

Kai Abbas ya sosa yace " _Allah ya takaita ai na kuma gode masa_ "!

Sai tace " _hakane amma dai a kiyaye gaba saboda gudun matsala duk dama farkon shine_ _me wahala amma gaskiya a'dan sarara mata na kwana biyu_ "

" _Bakomai wannan ba matsala bane dr. nagode sosai_ "

Daga nan sukayi sallama ta tafi.

Teemah kam fitsari ne ya matsata ta tashi ta shiga bayi, tana tsugun nawa sai ta mi'ke dan azaba zafi take ji sosai amma sai ta daure ta sake tsugunnawan sama-sama tayi fitsarin idanun ta harna hawaye amma haka ta daure dan bata so Yayah yasan da ciwon balle yayi mata batun allura.

Abbas ma 'dakin nata ya koma sai ya be ganta ba motsin ruwa da yajiyo a bayi ne yasa ya fahimci tana ciki, tsayuwa Abbas yayi yana jiran fitowar ta.

Teemah na share hawaye ta fito, tana ganinsa sai tayi turus ta sunkuyar da kanta ahankali ta isa gefen sa kanta a'kasa.

Hannunta ya kamo yajawo ta zuwa jikinsa yace " _me yasame ki kike kuka, what's wrong kuma ba kince kin warke ba_ "

Kai ta 'daga masa.
Abbas shiru yayi yana kallon ta ya san tana jin zafin kawai de tace ta warke ne dan kar yace allura.

A hankali ya sake fa'din
" _Toh meyafaru_ ?
Tace _"ni ka kaini wurin Mummy_ !"

" _Ba yau ba sai kin warke zan kaiki owk!_

Shiru tayi bata masa magana ba sai shine ya sake fa'din
" _Baki gaji da zama da towel 'din bane har yanzu_ ?

" _Yanzun ma kaya zan saka_ " tace da shi a hankali.

Sakin ta yayi taje ta dubo kayan sai kuma ta tsaya ta rungume su a'kirjin ta tana kallon shi.

" _Ya akayi in zo insa miki ne_ ?

Da sauri ta jijjiga kanta
" _ko sai na fita_ ?
Yayi maganar tare da 'dage gira.

" _Umm_ "
tace dashi.
Sai yayi murmushi tare da barin 'dakin yace " _ina jiranki a parlour yanzu kar ki sake kwanciya fah kinji._ "

Kayan tasaka cikin natsuwa sannan ta fita ta same shi akan dinning yana break fast, wurin sa ta isa ta zauna tayi shiru daya nemi taci dai tace ahh sai anjima zata ci,sai daya gama sannan suka koma 'dakin sa dukkan su Teemah bacci take ji dan haka sai da ta kwanta Abbas kuwa system 'dinsa yasa a gaba yana operating zaune kusa da ita seconds-seconds yake juyawa ya ganta.

Ranar haka ya wuni agida babu inda yaje illah masallaci, da azahar Teemah ta tashi ta koma 'dakin ta sallah itama, dayake data yi baccin sai taji jikinta yayi mata wani iri zazza6in babu yanzu amma kuma still bata koma normal gaba 'daya ba, ruwa ta watsa ajikin ta ta reda sake zama cikin ruwan 'dumi dan ta fahimci shine ya 'dan sanyaya mata zafin 'dazu dasafe.

Wata ba'kar doguwar riga ta sanya ajikin ta me adon golden colour stones manya, sai data idar da sallah sannan ta 'dauki veil shima golden ta yane kanta dashi, parlour ta dawo dan yanzun kam ba laifi ta 'dan ji dama-dama, anan Abbas yazo yasame ta ya kuwa ji da'din hakan shima cikin shigar 'kananun kaya yake bai so fitan ba amma daya tuna cewa gobe ne tafiyar su Mummy sai yaga dacewar kaita dan suyi sallama ma kuma ko dan ya faranta mata tunda dakan ta ma ta nemi zuwa 'dazun, shaf ya manta da batun tafiyar sai yanzu daya fita Daddy ya 'kira shi dan ya isar masa da wani sa'ko shiyasa ma ya tuna sai kawai ya ce da ita tatashi ya kaita gurin Mummy.

Yana tafiya zuwa 'dakin sa domin 'dauko key yayi maganar so be kula da yanayin da ta shiga ba abinda ka'dai yasani shine zataji da'din hakan.

Teemah kam farin ciki ne yacika sosai har da tashi da 'karfinta dan murna alokacin ne ta tuna da taji zafi a'kasanta amma ahakan ta daure dan kar yace yafasa.

Abbas sam hankalin sa be je kan yanayin tafiyar ta ba saboda yaga ta warware shiyasa ma be damu ba be sani ba ashe idan an kula sosai za'a ga chanji tattare da ita.

Suna shiga parlourn suka tarar da su Ummah ga6a 'dayan su zaune a cikin parlourn, Teemah taso ta isa da gudu amma sai taji tsoron kar taji zafi sai ta 'karasa a hankali, hakan ma dan tana daure wa ne shiyasa sosai take 'karfin hali wurin ganin ta 6oye ciwon ko dan gudun allura ma.

Tana isa ta fa'da jikin Mummy sai kuma ta saki kuka, wanda ya jawo hankalin dukkan su zuwa gare ta, Abbas kam mamaki ne yacika shi ganin lafiya 'kalau suka taho toh menene kuma na kuka yanzu anan.

Anty murmushi take yi dan tana ganin Teemah ta fahimci yanayin ta data ke ciki, Ummah kuma mamaki ne ya ziyarce ta yayin da tausayin Teemah ya cika zuciyar Mummy nan take.

Abbas zama yayi daga 'dan nesa da su ya zuba mata idanu.

Mummy bata tam
baye ta me yafaru ba illah kawai rungumar ta da ta yi itama tana babbuga bayan ta alamar rarrashi.

Ummah kam Abbas take kallo ganin duk ya zama kamar a birkice da ganin kukan Fateemahn.

Anty ne tace da ita
" _zo nan Fateema wai me ya sameki kike kuka haka nan ko duk missing 'din namu ne_ ?

Taso wa tayi a nutse ta dawo wurin Antyn tana me cigaba da zubda hawaye.

Anty mi'kewa tayi tare da kama hannunta suka shige ciki inda sika bar parlourn batare da ko gaisuwa sunyi da Abbas ba.

Fitan sun ne yabawa Abbas daman gaida su Ummah, gama gaisuwar keda wuya kuwa Mummy ma ta bar 'dakin dan sosai yau 'din taji nauyin sirikin nata ya kamata.

Ummah kuwa ganin anbar su su biyu take sai ta 6ata rai ta kalle shi tace dashi
" _Muhammad wace mugun ta kake yiwa yarinyar nan da har_ _take irin wannan kukan_ ?

Ido Abbas ya 'dan zaro waje yace " _mugunta dai Ummah ni 'din_ ?
_Ai kinsan halin yaron ki ba mugu bane, Allah shagwa6a ce ke kawai damun_ _ta wai dan kanta na ciwo_ "
Ya 'karashe maganar da sosa kansa.

Ummah cewa tayi
" _Ni dai kasan banason zalinci koka'dan ballantana rashin imani da tausayi, komai zakayi ka rin'ka tuna cewa shekarun ku ba 'daya da ita ba da kuma raunin ta na 'ya mace_ "!

" _Toh Ummah insha Allahu zan kiyaye_ "
Yasan halin Ummahn sa adun'kule yanzun tayi masa fa'dan, yasan ba mamaki tagano matsalar su ne shiyasa tafa'di hakan dan ta gama gano abinda yafaru.

Yanzune ma yake jin dama be kawo ta ba yazo abinsa shi ka'dai, bayan yasan su Ummah sun girmi tunanin sa, sai dai kuma a wannan yanayin ba ze iya fita yabar ta ita ka'dai ba hankalinsa ba zai kwanta ba sam, dama beyi niyyan zuwa ko'ina ba sai kuma Daddy ya aike shi.

" _Tasha maganin ciwon kan ne_ ?
Ummah ta tambaye shi.
Da " _ehh Ummah tasha magani tun 'dazu ma_ " yabata amsar tambayar tata.
" _Allah ya sauwa'ka toh"_
Toh Ummahn ta sake fa'di atakaice.

Anty kam suna shiga ciki ta zaunar da Teemah a bakin gado tare da tsare ta da tambayar me yafaru.

Da in-inah Teemah tafara magana cewa " _Ya....yah ne...!_

Da sauri Anty ta tare ta da fa'din " _dukan ki yayi_ ?

Sai ta jijjiga kanta alamar " _ah ah_ "

Anty kuwa bata sake tambayar ta sai tace
" _Toh shikenan kiyi shiru ki daina kuka, jikinki na ciwo sosai ne?_
Cikin shagwa6a Teemah ta bata amsa da fa'din
" _K'afata na min ciwo idan...zauna da tafiya... ma_ "
" _Toh yi ha'kuri a hankali zai daina kinji, ina kinyi amfani da ruwan zafi_ ?

Kai Teemah ta 'daga mata.

Anty ma sai ta jinjina kai kawai batare da furta wata kalma ba.
Chapter 122 · 0% Book details