← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 163

Sashe 150

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gefe da gefe suka kama Teemah a hankali har suka fice waje wurin mota inda suna shiga driver yaja suka fice daga gidan.

Yayin da Fateemah ke jin ranta kamar zai bar jikinta dan azaba, ha'ki'ka haihuwa ko ka'dan ko yake bashi da sau'ki, babu kuwa wanda zai gane hakan har sai abin ya same shi.

Tun da suka je asbiti ake abu 'daya tun 'karfe uku na'kuda yasa ta a gaba da azaba sai ya tashi sai kuma ya kwanta har tazo tayi bacci ma kusan na mintina arba'in sannan ta farka da wani matsanancin ciwon, gaba 'daya Teemah ta fice a hayyacin ta ta gama saduda da rayuwar ta ya 'kare dan bata ta6a zaton akwai irin wannan ciwon a duniya ba, duk jarabar ta da son yara sai da taji bata 'kaunar haihuwa muddin ranta, fa'di take yi kawai " ku cire min wannan cikin wallahi banaso, ku raba ni dashi dan Allah mutuwa zanyi......waiyo kuyafe min dan Allah.....Yayah na waiyo zan mutu..."
Tun tana kukan da hawaye har tazo hawayen ya daina fita mata ta koma salati, duk wanda yazo mata yi take yi ko da bata kai 'karshe ba sai ta kamo wani, abin dariya abin kuma tausayi.

Hannah kam kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita haka takeji, a ranta take tunanin ashe haka haihuwa take sosai ta tsorata da haihuwa ita kam, lalle uwate abin girmamawa ne dole kabisu, tausayin Teemah gaba 'daya ya cika mata 'kirjin ta har ji take da zata iya data rage mata ciwon.

Ummah bata sanar da kowa halin da ake ciki ba hatta Abbas kansa, cuz gaba 'daya hankalin ta na kan Teemah ne yanzun ganin yanda take shan wahala gaba 'daya ta karya mata zuciya ganin na'kudan yayi tsayi.

Dai-dai an fara 'kiran sallahn shiga masallacin Asubah abu yataso mata gadan-gadan, bayan ta take jin tamkar zai 6alle biyu, Allah kuwa cikin ikon sa mintina biyu basu cika ba sai ga kukan jariri domin da kukan sa ya taho kamar an doke shi.

Yana fita daga jikin ta kuwa Teemah ta fara sau'ke ajiyan zuciya a hankali take furta "Alhamdulillah" har bacci ya 'dauke ta.

Sai hamdala kawai su Ummah keyi yayin da Hannah ke farin ciki da guntun hawayen ta a idanu.

Abbas na alwala yaji tsinkewar zuciya da bai san dalili ba, dan haka sai ya ringa maimaita _innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ har ya kammala alwalar tasa har kuwa ya idar da sallar bai ji zuciyar sa tayi dai-dai ba, kuma ya rasa dalilin da ya kawo hakan, Qur'ani ya 'dauka kawai ya yi ta karantawa har gari yayi haske.

Baby lafiyar sa 'kalau, Teemah ce dai ta 'dan samu matsala sai da aka mata aiki amma ba sosai ba 'dan ka'danne daga nan aka yi discharging nasu.

Ummah bata 'kira shi ba sai 'karfe 8:00am bayan har sun koma gida ta gama gyaran mai jego da baby inda aka shirya shi cikin kayan sa sky blue sun fito ras abinsu sannan Ummah ta 'kirashi da duk wa'dan da suka dace ta sanar mawa.

Abbas ne 'karshe da Ummah ta 'kira, shi kam godiya kawai ya ringa sake wa mahalicci yana tasbihi musamman dayaji cewa lafiyar su 'kalau ita da babyn har ma sun koma gida ai farin cikin sa da'duwa yayi akan nada.

B'angaren Teemah kuwa zama tayi gefen yaron ta tana kallon shi tana sau'ke murmushi, wai yau gata ga babyn ta wanda ita ta haifa da kanta, baiwar Allah kenan yawa ne da ita yakan kuma baka ta inda baka zato ko kuma akasin haka, sosai ta ringa gode Allah a zuciyar ta, bazata iya misalta yanayin farin cikin data ke ciki ba a wannan lokacin.

Babyn ta tsurawa idanu tana so ta gano kamar sa amma takasa, sam bazata iya iya ce ga kamar yaron ba ayanzu domin kuwa ita bagane kamar jinjiri takeyi ba, shiyasa dole ta ha'kura ta barshi, yatsun 'kafar shi ka'dai ta iya gane kamar su irin ta Abbas ne sak sai dai hasken sa da kamar kam takasa ganewa.

Baby baccin sa yake yi cikin kwamciyar hankali, tunda akayi masa wanka yake bacci, itan ma garin kallon shi har bacci ya 'dauke ta a gaban sa, ba ita ta tashi ba sai da azahar.

Hannah ce ke gaya mata wai ai Yayah ya yi ta 'kira abata wayar tana bacci kuma Ummah ta hana a tashe ta.

Shiru kawai tayi dan wani azaban zafi da take ji tun daga 'kasan ta har zuwa cinyoyin ta.

Da 'kyar ta daure ta tashi ta zauna tana cije baki, koda zata tashi tsaye kuwa zafin datajin har sai daya sata sau'kar da hawaye.

Matar da ta gani zaune a gefe ne tana bawa jinjirin zam-zam tace da ita " yi a hankali Fateemah, sai kin daure kinji"

Wa Hannah matar ta mi'ka yaron sannan da kanta ta tashi taje ta ha'da mata ruwa mai 'dumi a bathtub tace idan ta shiga zauna aciki.

Kafin ta mi'ke sai ga Ummah ma ta shigo, tana ganin ta zaune kuwa sai ta washe baki tare da yi mata sannu, Teemah ta amsa sannan ta tashi a hankali kamar mai koyon tafiya ta wuce bayin.

Da hawaye ta samu da 'kyar da azaba ta iya yin fitsari, da farko ma tsoron shiga ruwan tayi amma sai ta daure musamnan data tuna first night 'din ta irin yadda ruwan zafin ya taimake ta shiyasa yanzun ma ta daure ta shiga.
Sai data yi brush kafin ta fito daga bayin tana 'danjin da'din gabo6in ta ba kamar lokacin data
tashi a baccin ba.

Tana fitowa kuwa aka gabatar mata da abinci, inda ta 'dan tatta6a ka'dan ta bari domin ba da'din bakin ta takeji ba yunwar ma bata ji tun safe da Ummah ta bata wani ha'd'den tea mai kauri tasha har yanzu bata ji yunwa ba, sai 'kirjin ta dake 'dan yi mata zogi saboda cikar da sukayi.

Matar ne tace ko zata bashi yasha da yake tun safe daga zam-zam babu abinda ke cikin sa, take Teemah sai ta jijjiga kai alamar "ah ah" matar ma bata matsa mata ba cuz tayi zaton ko zuwa an jima zata bashi.

Kamar wasa kuwa har yamma Teemah bata bawa baby mama yasha ba wai tana tsoro yana mata zafi.

Ummah bata so ta matsa mata itama dan haka kawai sai ta bar ta, amma abin na damun ta azuci.

Da yamman aka sake yiwa baby wanka yana ta faman kaiwan hannun sa baki yana 'ko'karin tsotsa, tausayin shi sosai yake kama Ummah amma bata san yanda zata yi da Teemah ba sam, ko da aka gama shirya shi sai aka bashi ruwa yasha, yana sha kuwa tale sai ya koma bacci abin sa.

Itama Teemah wankan ta sake yi bisa jagorancin wata dattijuwar mata tayi shirin ta cikin riga da zani na atampa tayi simple 'dauri ba na 'daga hankali ba daya ke ma ba wani da'di sosai take ji ba shiyasa powder kawai ta murza a idanun ta tare da sanya kwalli, sai uban turaruka data ringa fesawa ajikin ta kamar baza su 'kare ba.

Fita sukayi dukkan su suka bar Hannah da Teemah a 'dakin yayin da ta sa Babyn agaba ta zuba uban tagumi, so da tausayin sa na ratsa ta, sai ta kamo hannun sa ta ri'ke cikin nata tare da kwantar da kanta agafen sa tana kallon fuskar sa, ita kanta tausayin sa take ji sosai amma tana tsoron sa mishi maman abakin shi dan yanda take jin yake yi mata zogi, koda za'a wanke ma da yamman nan har kuka tayi saboda zafi da zogi gashi sai 'kara cika yake yi base k'aramin takura ta yake yi ba.

Yayi baccin a'kalla mintina kusan hamsin kafin ya farka, sai kuma ya tashi da kuka, wanda ya rikita Teemah ta rasa ma ko ta yanda zata 'dauke shi dan haka kawai itama sai ta sanya kukan.

Hannah ce dake bayi tayi saurin fitowa ta 'dauke shi ta fara jijjiga shi amma kamar ziga shi take 'kara yi kukan nasa sai 'kara 'karfi yake yi ga dukkan alamu an 'kure ha'kurin sa ne.

Hannah tayi-tayi da ita ta bashi yasha amma ta'ki sai kuka kawai takeyi.

A haka Ummah ta shigo ta same su, sai tace
" wai ya akayi ne? Ya tashi ko?"

Hannah ce dake hautsine ta bata amsa da fa'din
" ehh ya tashi Ummah".

Kar6an sa Ummah tayi itama ta 'dan jijjiga shi da kukan ya 'dan ragu sai ta kifa shi akan 'kafafun ta tace da Teemah
" Yunwa fah yaron nan yake ji kar ashi ga hakkin sa dayawa ki daure ki bashi yasha kinji".

Kai Teemah ta 'daga wa Ummah kamar da gaske.
Ummah sai ta 'dago shi ai kuwa kamar yana jira sai ya saki wani sabon kukan kuma, mi'kawa Teemah shi tayi tace
" yauwa Fateemah maza bashi 'kilan zai yi shiru"
Ummah da kanta ta dai-dai ta mata zaman yaron a cinyar ta sannan ta koma gefe.

Teemah kam a hakan ta rungume shi tana bin bakin sa da kallo yanda yake kukan hawayen ta na cigaba da sau'ka.

Ganin hakan ne yasa Ummah ta fice tunanin ta wai ko kunyar ta ne yasa Teemahn ta'ki bashi a lokacin dan haka sai ta fita ta bar su da Hannah a 'dakin.

Hannah kam gaba 'daya taji zuciyar ta ya karye da kukan yaron ita kanta ji take tamkar ta taya shi kukan amma sai ta daure batayi ba.

Zama tayi agefen Teemah ta ringa bata baki akan ta taimaka ta daure ta bashi kar kukan yayi masa yawa daga zuwan shi duniya ya yi sabo da kuka.

Rashin kautawar ta tagani ga tausayin yaron ta daya cika ta dan haka sai ta daure ta ciro maman a hankali kamar tana tsoron ta6awa dan yanda yake yi mata zafi, wanda hakan shine babban dalilin daya sanya tun 'dazun take tsoron bashi.
Da dabara ta gwada saita masa a baki wanda har ya kama sai kuma tayi saurin cirewa ta maida abinta ta rufe, take wani sabon hawayen ya sau'ko mata sai ta kalli Hannah tace
" Allah Hannah da zafi bazan iya ba"
Chapter 150 · 0% Book details